Showing 147001 words to 150000 words out of 298130 words

Chapter 50 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

Alhaji ubaid

"Wallahi idan kika sa kafa kika bar gidan nan batare da yawuna ba, to ki sani abakin auran ki"!! hankulansu Dr shureim atashe suke kallon shi har suna hada baki wurin furta daddy meyasa?

Dariyar takaici layla tasaki tana tafa hannu tace"sai me donka sake ni? Ni dama ay najima da gajiya dakai tun lokacin da na gane kai bakomai bane face rakumi da akala, Ina amfanin zama da namiji solo6iyo irin ka"?

Rai a6ace ta faWa tana kallon cikin idon shi, Kalamanta sun ?ona masa rai, da?yar Ya iya hadiye yawu mai Waci ba tare da ya iya furta komai ba.

Dauke idonta tayi daga kanshi ta kalli Alhaji musa, dake atsaye ya harWe hannuwansa kan kirjinsa fuskarsa babu fara'a

Harara ta watsa mashi kafin tace

"Hankalinka Ya kwanta Ka shiga tsakanina da mijina, In sha Allah zaka ga sakayyar hakan" wani kallon ?asan ido Ya watsa mata mai wuyar fassaruwa.

"Shureim Benazir, kada ku bi ta idan har na isa daku, Kubarta ta tafi ita kadai tun da bata jin maganata" acewar Alhaji ubaid.

Murmushin takaici layla tasaki, ba tare da ta ?ara furta kalma ba ta juya a fusace tabar falon

"Ka bar su su tafi" Alhaji musa ne ya fada agadarance.

Da sauri benazir taja trolley dinta tabi mommynta, shima shureim yabi bayanta

A bakin motar shureim ta tsaya zuciyarta a kuntace, batai tsammanin zasu biyo bayanta ba

Dr shureim na ?arasowa Ya buWe mata back seat din motar ta shiga ciki, sannan ya sanya masu trolley din kayan su a boot, daga bisani itama benazir ta shiga ciki.

Bayan ya shiga ya zauna a driver's seat, yai ma motar key, zuciyarsa cike fal da damuwar abunda Ya faru, yaji takaicin yadda Alhaji musa ya nuna halin ko'in kula akan tafiyar mamin su, abun da Yafi bata masa rai furucin mahaifinsu yansu shikenan yana ji yana gani auran iyayensu zai rabu"?

"Shureim! Ya akai naga ka dakata da yin driving din"? Cikin rauni na murya yace"mommy Kiyi hakuri mu koma, idan kika tafi ya kike so muyi da rayuwarmu? Ke kanki bazaki so abun da zai tarwatsa farin cikin mu ba...."

Shiru tayi tana nazarin maganarshi, ga dukkan alamu jikinta yayi sanyi lakwas

"Mommy, kina atare damu Ya muka ?are inaga idan baki nan? Duk wani mai nufin mu da sharri zaiji dadin cutar da rayuwarmu, bayan haka mommy tsawon shekara nawa kuna atare da daddy, auren soyayya kukayi kun tara zuri"a da dadi da ba da daWi kunyi hakuri kun jure zama da juna sai akan wannan dalilin zaki kashe auranki? Mu kanmu bazamu ji dadi ba dan Allah ki tausaya mana mommy ku dubi girman Allah ki fasa tafiyar nan ko dan saboda mu"

benazir ce tayi maganar tana duban fuskar mami kamar zata sanya mata kuka.

Zancen zuci ta soma yi

_wannan hanyar dana Waukarwa kaina ba me 6ullewa ba ce, ?wara in tsaya in ?watar mana ?ancin mu, dole Inyi faWa ko da kuwa zan rasa raina ne saina shiga tsakanin mu da shi_

Ba zato ba tsammani suka ga ta buWe motar, wani irin farin ciki ne Ya lullu6e su, da sauri benazir ta fito shima shureim Ya fito suka dauko trolley dinsu dake a boot suka bi bayanta.

Kamar yadda suka bar su hajiya sarah tsaye a falon haka suka taras da su, sunyi mamakin dawowar Hajiya layla, ko kallo ba su isheta ba, Kai tsaye ta wuce room dinta

Da gudu zeenatu ta nufi benazir suka rungume juna suna dariyar farin ciki,

Fuskar hajiya sarah dauke da murmushi ta dubi dr shureim"ta fasa tafiyar ne"?

"Eh mommy," ya bata amsa, Har cikin ranta taji dadin dawowarsu.

Mutumin kuwa murmushin gefen fuska Ya Wan saki, yayi tunanin security officers din gidanne suka hanata tafiya baisan cewa itace tai ra'ayin kanta ba, fucewa yai daga falon cikin takun isa.

Alhaji ubaid dake kallonsu ajiyar zuciya ya sauke.

"Daddy, dan Allah kuyi hakuri da abunda Ya faru atsakaninka da mommy, ku yi kokari ku sasanta junanku"

Jinjina kanshi yai fuskarshi dauke da murmushi yace"kada ka damu shureim, ni dama ban dauka da zafi ba, itace ke da matsalar, in sha Allah zanje na lallashe ta" ya fada tare dakai hannu yadan bubbuga kafadarsa kafin Ya juya ya nufi dakin layla don su sasanta junan su.

Koda ya shiga Wakin, ya taras da ita zaune agefen gado, kamar mai jin shakkarta Ya raba ya zauna yana duban ta

kafin yai magana tai saurin katse shi da cewa"basai ka bani hakuri ba, ni yakamata na nemi yafiyarka, ka yi ha?uri idan na 6ata maka rai, in sha Allah bazan ?ara ba, zan bi umarninka in zauna har zuwa lokacin da ka so mubar gidan" da wani irin mamaki yake duban fuskarta, kamar amafarki yake jin kalamanta, Wai yau layla ce da kanta take bashi hakuri har take fadin zata bi umarnin shi?


"Allah yasa ba mafarki nakeyi ba" murmushi tayi tare da dubanshi tace"ba mafarki bane mijina, dagaske ne, abun nayi ban kyauta ba, su shureim sun yi min nasiha nima naga rashin kyautuwar hakan shiyasa na dawo.

Ruko hannayenta yai acikin nashi hawaye tuni sun cika idanunsa

Cikin sanyin murya yace"layla bazan iya misalta dadin da naji ba, kin faranta raina ayau, duk da nasan nine mai laifi amma kiyi hakuri ki yafe min, sannan inaso ki sanyani a addu'arki, Ni kaina bansan meyasa bana iya bijirema umarninsa ba, bana son bacin ran musa, saboda ya kyautatamin arayuwa shine silar duk wata nasara da na samu..." bai kare maganar ba tai saurin rufe bakinsa da tafin hannunta, saboda ta tsani taji Yana yabon musa, saboda ita tasan ba hakanan Ya kyale shi ba shiyasa baya iya ganin laifinsa, amma taci alwashin zata gano ainihin wanene Alhaji musa da duk wani abu dayake takama da shi.

Abun da bai ta6a tsammani ba, Yaji layla ta kwanto da kanshi saman kafadarta, bawan Allah sai Ya kara lafe mata kamar wani karamin yaro.

"Kada ka damu, ni bakai min laifin komai ba, In sha Allah zantayaka da addu'a kamar yadda ka bukata, kaima kuma inaso ka dage dayiwa kanka addu'a" amsa mata yai da toh, cigaba da kwantar masa da hankali tayi, har saida ta cika shi da farin ciki ta dinga zolayarsa tana tuna masa farkon haduwarsu kafin su yi aure.


"Yanzu tun da komai Ya daidaita mu koma dining mu ?arasa yin breakfast din" cikin kulawa mom sarah tayi maganar tana dubansu.

"Aunty ki tayani murna" acewer benazir

"Fada min meya faru"?

"Aneelerh ta kirani awaya har mun yi magana da ita"

Murmushi hajiya sarah tasaki"masha Allah, ina tayaki murna my daughter, wlh naji dadi yanzu yaushe zaki je can gidan na su"?

Kallon dr shureim tayi wanda gaba daya hankalinsa na akan zeenatu dake a gefensa sai dadi take ji sun fasa tafiya.

"Yaya shureim yaushe zamuje? Ni ko yanzu ma kace a shirye nake Allah" ta fada a kagare.

"Gobe in sha Allah zan kai ki" da sauri zeenatu tace"yaya shureim nima zan bi ku, dan Allah ku tafi dani" ta faWa a shagwa6e tana kallon shi.

"Kada ki damu ?afa ta kafarki, duk in da zani je a tare zamu tafi" cikin muryar raWa yayi mata maganar, dariya murna tasaki.

Benazar tace"kwantar da hankalinki rabin raina, gobe atare zamu je"
"Nagode auntyna"

"Ki daina murna, kin manta da daddyn ki halan, ba lallai ya amince ki fita ba" tur6une fuska tai.

"Mommy pls ki ro?an mun shi yabar ni inje" ta fada tana bubbuga kafafuwanta

"Zanyi mashi magana zuwa anjima nasan zai bari mu tafi da ita" acewar dr shureim
Hajiya sarah na murmushi tace"kunfi kusa ay, nasan kana masa magana zai amince, tun da yana ji dakai na gaban goshinsa" dariya sukai gaba dayan su.

______________________Twinsc'


A kwance yake kan katafaren gadonsu idanunsa na fuskantar ceilling, yanayin fuskarsa sam babu walwala ya haWe rai kamar wanda aka aiko ma sakon mutuwarsa, bakomai ne yake damunsa ba face haWin da mommynsa tayi masa, ya riga da ya san halinta ba lallai ta canza ra'ayin ta ba, shi fa arayuwarshi sam baida ra'ayin yin auren wuri, yafi sha'awar yai sharholiyarsa son ransa, a yadda ya tsara ma kansa sai yakai 45 years zaiyi aure, bugu da ?ari baya jin zai iya auran yarinyar saboda ba'ajinsa ba ce, jiya kafin ya kwanta bacci sai da yayi bincike akanta ta hanyar amfani da wayarsa har ya gano wanene mahaifinta wato karen ?an siyasa, aransa ya ayyana tayaya shi da ya fito daga babban gida shahararren family da duniya tasan da zamansa, zai auri wannan yarinyar, Bayan haka mommyn sa minister ce daddynsa Ceo ne na babban companynsu Obi Tech, tayaya zai auri interior designer? Companyn ma da take aiki ba nata ba....

Abu Waya daya hana shi sukuni, kyawun fuskarta da surar jikin ta, daren jiya dakyar ya runtsa, ba halin Ya rufe idanunsa sai ya tuna lokacin da ta fashe mashi kuka la66anta na kerma, kissing Winta da yayi har cikin zuciyarsa yaji wani irin shau?i da bai ta6a jin sa a wajen wata mace ba, kawai yayi ?arfin halin tofar da yawu ne don Ya muzanta ta.

Motsin buWe toilet ne Ya katse masa zancen zucin nasa, A hankali yakai idanunsa ga duban mai fitowa

Zaid ne ya fito waist dinsa daure da towel, suna haWa ido da juna Ya sakar masa murmushi

"Bro me kake tunani ne? kamar wani abu na damunka? Banza yayi dashi bai tanka mashi ba

"FaWamin meya faru jiya bayan mommy ta kira ka awaya"

Yamutsa fuska yayi, tamkar baisan maganar ya furta"zaka iya tuna yarinyar nan da mommy ta kawo wurin mu"?

Shiru zaid yayi yana kokarin tuna ta can yai murmushi tare da cewa"kana nufin Zahra"? Ta6e baki zayn yai kafin yace"oho na manta sunanta"

"Itace zahra, yarinyar ta kwanta min araina saboda ina son mace mai kamun kai daga gani iyayen ta sun bata tarbiya" ya faWa tare da samun wuri gefen gadon su Ya zauna yana kallon zayn

"Mommy ce ta haWa ni da ita...." bai 6oye masa komai daga abun da ya faru tsakaninsa da zahra.

Har Ya ?are maganarsa zaid bai ankara ba saboda zuciyarsa da ta karaya, har ga Allah bai ji dadin hukuncin da mommynsu ta yanke ba na hada zayn da zahra, saboda yasan halin Wan uwan nasa bai jin magana fiye da shi, yarinya mai kamin kai an haWa ta da Wan iska, ina ma ace shi mommynsu ta hada da zahra da ba abun da zai hana ya gyara rayuwarsa saboda samun mace ta gari wadda zuciyarsa ke muradin mallaka...

"Zaid? Naji kayi shiru bakace komai ba? Nasan kana tayani jimami ne"

Jinjina kai zaid yai kafin yace"zayn banji dadin abun da kayi mata ba, saboda ba laifinta bane, mommy ce ta hada ta dakai, ni nasan ba itace ta shirya faruwar hakan ba..." ya fada cikin sanyin murya yana kallon zayn dake faman ya mutsa masa fuska

"Me zai hana ka jaraba amincewa da bu?atar mommy, ni nayi imanin ba zaka ta6a danasanin auran zahra ba, watakil ta zama silar shiriyarka...." kafin ya ?are maganar zayn ya wurga masa harara tare da katse sa da cewa"kana son ta ne?

"Meya kawo maganar so? Kawai daga na baka shawara amatsayinka na dan uwana" guntun tsoki zayn yaja"bani bu?atar shawarar ka, nayi zaton zaka tayani jimamin abun takaicin daya same ni ashe ba haka bane dakai da mommy kanku Waya..." ya fada yana cije la66ansa"har abada bazan ta6a sonta ba, zan amince da ita ne saboda mommy, sannan zan aureta badan ina sonta ba sai don in mayar da ita abun biyan bu?ata na amma babu maganar mutunci atsakaninmu muddin ta aure ni taga ma jin dadin zaman duniyar nan" muryarsa a kausashe ya furta maganar

Runtse ido zaid yai har cikin ranshi baiji dadin kalaman zayn ba, baisan ya zaiyi ya shawo kan mommynsu akan ta janye maganar haWa shi da zahra saboda zayn ba mutumin kirki bane, muddin ya auri zahra bakin cikinsa zaiyi silar mutuwarta, dole ya nema mata mafita tunkafin afkuwar lamarin, Indai daddyn su baisan da maganar ba zaiyi kokarin tunzurasa akan kada ya amince da maganar mommynsa....Saukowa zayn yai daga kan gado daga shi sai yar singlet da short Ya nufi toilet Yana huci Ya shige ciki, zaid dake zaune gaba daya kamar an zare lakarsa shi dai ya damu da zahra baya son mommynsu tayi silar jefa ta cikin wani hali

wayar dake a kan side drawer din su, Yakai hannu ya dauka Ya danna wa landline din kitchen tana fara ringing maid ta Wauka, ya bada umarnin akawo masu breakfast dinsu, Kafin Yai cutting kiran ya ajiye wayar kan drawer

Badajimawa ba, Abla ta shigo dakin da tray mai dauke da kayan abinci, ta ajiye masu kan drawer bayan ta gaishe da zaid ta juya ta fuce..

________________________Dattijon Arzi?i>?
?

A zaune yake kan lallausar darduma, hannunsa ru?e da cazbaha, a hankali Yake motsa la66ansa, kusan rabi da kwata na hankalinsa na akan chief owais dake kwance saman dardumar ya Waura head Winsa akan laps din baba obie, kyawawan idanunsa suna a lumshe tamkar na mai jin bacci, su duka biyun daga ka kalle su zaka shaida tsantsar nishadin da suke aciki, musamman baba obie, ransa fari fat tunda owais ya kawo mashi ziraya yau kusan wuni yayi awurinsa duk inda zasuje atare suke tafiya, ba su jima da dawo daga masallaci ba suka shigo garden don su sha iska, sai faman satar kallonsa yakeyi kamar ya haWiyesa haka yake ji tsabar kaunarsa da ya ke ji.

"Grandpa, wannan kallon na menene"? Idanunsa a lumshe Ya jefa mashi tambayar.

Fuskar baba obie da fara'a Yace"Kallon so da kauna ne rabin raina, wallahi yau ka faranta min rai, gaba daya ka debe min kewar hateem dake damuna...." A hankali chief Ya Wan bude idanunsa Ya saci kallon fuskar baba obie karaf suka hada ido cikin na juna
"Baba...." Ya fada ba tare da ya ?arasa maganar ba
"Na'am sanyin idaniyata, Naji ka kira sunana kuma ka yi shiru" gyara kwanciyarsa yayi batare daya bashi amsar tambayar sa ba.

"Duk cikin jikokina babu wanda Ya more ni kamar ka, kaga cinyar nan tawa tun kana ?arami kake tumurmusarta, gashi har yanzu baka daina taushe min ita ba' murmushin gefen fuska Chief yai masa har chin dimple dinsa Ya dan lotsa.

"Meya fi raina"? Ya fada Yana kallon fuskarsa.

"Ni fa idan ina atare dakai, sai naii kamar an mallaka min komai na duniyar nan, ni dai Allah Ya jarabce ni da sonka kakana ina fata Allah ya dawwamar da farin ciki atsakanin mu zan cigaba da tayamu addu'a Allah Ya Ya ?ara mana tsawaicin kwana ko dan na cika maka burinka akaina......."

tun da yafara magana baba obie ke kallon shi da wani irin matsanancin farin ciki akan fuskarsa, dakatawa yayi da jan cazbahar Ya Waura tafin hannunsa kan sumar Owais a tsanake Ya soma shafata kamar yana yi masa susa.

"Kalamanka sun sanyaya min zuciyata, Owais kai na dabbanne, wallahi yadda nake jinka bana jin ko iyayanka, kai tamkar bugun zuciyana ne, wallahi bansan Yadda zan misalta maka kaunarka da nake yi ba....." kafin Ya ?are maganar, ruwan hawayen da suka taru cikin idanunsa suka gangaro kan fuskar chief, lokacin da yaji saukar su a ruWe Ya zabura ya mike daga kwancen da Yake, Idanunsa akan fuskar baba obie
da alamun ruWani Ya furta"baba meyasa ka zubar da hawayen ka? shiru yayi batare daya iya furta masa wani abu

"Fadamin mana, ko dai maganar da muke yi ce ko kuma akwai wani abu dake damunka"? Girgiza kai yai"a'a owais kada ka damu babu abun da ke damuna, kawai bana son duk wani abu da zai shiga tsakanina dakai, Ina jin fargaban duk wani abu da zaisa ka juya min baya, ni dai bana son 6acin ranka......' ru?o hannayen baba obie yai acikin nasa yatsun hannunsa har kerma sukeyi"baba bazaka iya boye min komai ba, idan har kana da damuwa kallo Waya nake yi maka na fahimta, Ina ji araina da akwai wani abu dake damunka dan Allah ka fadamin habibi na, nayi alkawarin zanyi iyakar bakin kokarina wurin kawar maka da damuwarka...." da ?warin gwiwa ya furta maganar Yana kallon idanun baba obie da suka kada jawur gray eyes dinsa sunyi ja tsufansa duk Ya ?ara fitowa.

Wani murmushi yayi mai ta6a zuciya kafin yace"Idan na faWa maka abun da ke damuna zaka 6oye min sirri na ba zaka fada ma kowa ba sannan zaka rufa min asiri" jinjina kai owais yai da alamun rudani akan fuskarsa
kamar baison furta maganar Yace"najima inason sanar dakai, sai dai inajin fargaban yadda zaka dauki abun aranka, ka yi min alkawarin ba zaka fusata ba" ya fada la66ansa na kerma, ba karamin rikita tunanin chief owais Yayi ba, gwiwarsa harta sage In a low voice Ya furta"ni mai rufa maka asiri ne babana, bazan bari kowa Ya sani ba, tona maka asiri tamkar tonawa kaina asirine da zuri'armu" jinjina kai baba obie yai sai da yafara kallon garden Din Ya tabbatar babu mai kallon su kafin Ya matsa gab da chief owais Yayi masa raWa a kunnansa.

Lokaci Waya chief ya Wan janye kunnansa da tsantsar mamaki Yake kallon baba obie wanda tuni yasha jinin jikinsa, ba zato ba tsammani a lokaci Waya suka tuntsire da dariya kamar wasu zautattu, Yaushe rabon da inga chief yayi dariya irin wannan ni kaina namanta, komai nasa mai jan hankali ne.

dariyar tayi matu?ar tafiya da imanina, saboda gaba Waya ta bayyana zunzurutun kyan fuskarsa, dimpla dinsa duk sun lotsa, fararen hakoransa kamar auduga tsabar hasken su, sun Wau lokaci suna ti?ar dariya kafin daga bisani chief ya kifa kansa bisa kafadar baba obie, hankalinsa ba karamin kwanciya yayi ba, da farkon yai tsammanin wani mugun abunne zai faWa masa ashe ba haka bane
Muryarsa tamkar tame jin bacci Ya furta"Grandpa are you kidding me"?

Baba obie na murmushi yace"Wasa nake maka owais, Ni ina ni inayin aure, tsofe tsofe dani, ga tarin ya'ya da jikoki"

"Wannan ba hujja bace, Indai Kana son Yin auren ka fadamin, in sha Allah I will try to find a righteous life partner for you."

Da zolaya baba obie yai masa dundu akan bayansa tare da cewa"Owais wlh wasa nake maka, kawai don inga reaction dinka ne, kuma nagani tunda gayanan na sanya ka yin dariyar da ka dade baka yi taba"


Sauke ajiyar zuciya chief yai kafin ya sake furta"please ko da nan gaba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login