Showing 141001 words to 144000 words out of 298130 words

Chapter 48 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

"Zamu Iya tafiya" wani irin farin Cikine Ya lullu6e Salsabeel.

A ruWe ya furta"Danish tayaya akai ka gano ?ofar nan? Ban ta6a sanin akwai ta ba, kuma bana tsammanin????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ko ita tsohuwa tamira tasan da zaman ta" ya faWa cike da son jin ?arin bayani.

Yana faman huci yace"Kada ka manta, ka riga ni tsintar kanka acikin kurkukun ?addara ni kuma nafi ka sanin komai na cikin sa, duk wata ?ofar sirri dake a kurkukun nan nasan da zamanta, tabbas tsohuwa bata san da wannan kofar ba, tsohuwar hanyace da aka jima da toshe ta, ni da kaina na sake ha?a ta da sihiri na, Idan muka bi ta cikin ta, zata 6ular da mu cikin wani kogon dutse dake wajen kurkukun nan, dalilin dayasa na za6i ku raba hanya da su Unaisah saboda nasan zasu iya farmakar mu idan har suka gano abunda ke wakana, inaso na raba masu hankali ne watakil in mukayi hakan wasu su rayu daga cikin mu"

Bazai iya jure kallon Danish ba, Yaron Ya burge shi, Ya yi mashi abunda bazai ta6a mantawa ba, ya taimake sa a lokacin da rayuwarsa take akan ga6ar salwanta, da sauri ya janyo shi ya rungume shi yana kuka, kafin ya raba jikin su cikin sanyin murya yace

"Amma danish su Angel fa? Yakamata ka koma wurinsu suna bu?atar ka, bana so wani abu ya same su"

Girgiza kai Danish yayi "kada ka damu, babu abunda zai cutar da su, saboda na rigada na Waure hanyar da suka bi da sihiri babu wani mahalukin da ya isa ya iya tsaga kofar ya shiga balle har ya cutar da su, kafin nazo nan sai da na kiyasta awannin da za su yi kafin su ?arasa kofar da zata 6ular da su waje ni kuma zan riga su komawa bayan na taimake ku"

Murmushin farin ciki salsabeel ya saki,
Basu tsaya bata lokaci ba suka yi kokarin taimaka ma su Hibba don su mi?ar da su tsaye, saidai mutun biyu daga ciki kafafunsu sun kasa Waukar su sakamakon abunda tsohuwa Zafreen ta yi ma su, bayin Allah sai ihun azaba suke saki, da sauri Danish Ya sungumi deeja ya goyata a bayan shi, ya sanya mayafin daya Wauko a ?asa ya Waureta tamau, kafin ya Wauki Rubina ya Waurata a kafaWar shi dama su biyune basu iya tafiya.

shi kuma Salsabeel ya yi amfani da bargon tsohuwa tamira ya nannaWe gawarta aciki ya Waurata a kafadarsa.

A haka suka bi hanyar mai duhun gaske ga zafi tamkar ana rura garwashin wuta, sunci ba?ar wahala su sarah kamar numfashinsu zai Wauke. Cikin awanni takwas da su Angel sukayi suna rarrafawa akan hanyar su duk wannan abun Ya faru, baifi awa biyar ba su salsabeel sukayi nasarar fita daga cikin gidan kurkukun ?addara hakan na nufin sun riga su Angel ku6uta saboda tasu hanyar batai nisan wadda su Angel suka bi ba.

Bayan su Salsabeel sun 6ula cikin kogon dutsen, Danish Ya sauke deeja da Rubina daya Wauko, shima Salsabeel ya sauke gawar tsohuwa tamira, su hibba duk suka zube agajiye har lokacin bakunansu basu gushe da ambaton sunayen ?an uwansu.

Kallon juna sukayi kowan nan su na haki, da sauri salsabeel ya ru?o hannun Danish, cikin sanyin murya yace "Danish, bazan ta6a mantawa da halaccin da ka yi min ba, kayi min abunda har abada bazan ta6a mantawa dakai ba, kaine silar ku6uta na daga Gidan kurkukun kaddara kuma kaine silar cikar burina na ganin na cika al?awarin mahaifiyata dana Waukar mata akan in rufe gawarta kada in bari ta wula?an ta, Danish ko a mafarki ban ta6a tunanin akwai ranar da zan bar gidan kurkukun kaddara ba, nasha jaraba guduwa nida mahaifiyata amma mun kasa saboda karfin sihirin mu bai kai ba, sai gashi a sanadiyar ka nayi nasarar fita...." tuni hawaye sun wanke fuskarshi.

"Danish, Koda ace ban rayu ba, ni ka gama min komai wallahi, koba komai na sha?i iskar duniya bayan tsawon lokaci da na kasance a kulle" ya faWa yana duban cikin idanunsa "ni dai burina ka yi rayuwar farin ciki tare da yan uwanka, ubangiji Allah Ya kare min ku ya tsareku a duk inda zaku kasance, bani da tabbacin zamu sake haduwa wata?il ma ba lallai mu rayu ba....." bai ?arasa maganarba ya fashe da kuka mai cin rai, da sauri Danish ya janyoshi suka rungume juna sosai suka kankame jikinsu.

Bubbuga bayanshi Salsabeel yai da hannunshi "Wan uwana, ka kula min da kanka, wallahi ina mutuwar sonka tun farkon ranar da aka kawo ka gidan kurkukun ?addara a cikin tsumman ka, naso ka Danish, zan tafi da kewarka, Allah ya rayamin kai Danish, Ina fata wata rana kaima ka zama cikakken musulmi, ka yi rayuwa kamar kowa kayi Aure ka hayayyafa....."

Lumshe idanu Danish yayi cikin sanyin murya yace"ina sonka Wan uwana, nima zanyi kewarka, ka kula min da kanka, ina fata mu sake haWuwa" Yana faWa Ya raba Jikin shi daga na Salsabeel, A hankali ya soma tafiya yana ja da baya yana duban Salsabeel da ?an uwan shi waWanda kwata kwata basa a hayyacin su, wasu irin zafafen hawaye ne suka cika idanuwan Danish bai daina kallon su ba har saida yayi nisa kafin Ya 6ace ma ganin su.


Bai dira a ko'ina ba sai a bakin kogon bishiyar da su Angel zasu 6ula, adai dai lokacin su kuma har sun ?araso bakin kogon bishiyar suna ta faman ambaton sunan shi.

Bayan tafiyar Danish A cikin Dajin salsabeel Ya samu wuri a gefen wata bishiya ya binne gawar tsohuwa tamira, ya zu?unna gaban ?abarinta yai mata addu'o'i yasha kuka kamar ba gobe, har shaida sai da yayi ma kabarin nata saboda yana da burin wata rana ya kawo masa ziyara tare da ?an uwansa prisoners don su yi mata addu'a.

(Masu karatu kunji yadda akai salsabeel da su Deeja suka ku6uta daga Gidan kurkukun ?addara, nasan wasu zasu ce tayaya har suka dau lokacin nan batare da an ritsa da su ba? To idan ba zaku manta ba, shuwagabannin kurkukun ?addara basa a ciki, bayan haka an samu tawayar tsaro, sannan babu wanda yasan meke faruwa a sashen su Angel saboda an rikita lissafin Allon tsafin su, su kan su waWannan giants din da suka shigo sashen har suka ga salsabeel, bawai sun san me suke shiryawa bane, sun zo ne domin tafiya da su Deeja zuwa wani sashe na daban da suke tarasu don su basu ruwan sihiri wanda zai dawo masu da jinin al'adar su saboda su samu damar gudanar da black night Win da za'ayi a ?arshen watan, amma saboda 6arnar da Danish yayi masu yasa duk wani shirinsu ya wargaje, ha?i?a sunji zafin tafiyar garkuwa da kuma yaran daya tseratar daga tarkon su, wannan ne yasa lokacin da suka yi taron zaman tattaunawa Waya daga cikin Elders Yace

_ Wannan ne Karo na farko da muka yi babban kuskure arayuwar mu, wanda idan bamu mi?e tsaye mun nema ma kanmu mafita ba, to tabbas za ayi nasara akan mu, Ko a tarihi ba a ta6a samun prisoners Win da suka tsira daga kurkukun ?addara ba, su ne na farko kuma sune na ?arshe, da farko sunyi nasarar ?etare kurkuku da taimakon Garkuwarmu, Na biyu sun ku6uta daga dajin evil forest da taimakon shi, Babu wani mahalu?in da ya isa ya iya ?etare kurkuku da dajin evil forest salin alin ba tare da ya Rasa ranshi ba, amma saboda suna atare da garkuwar prison mun rasa cin galaba akansu saboda mu kanmu bamu isa mu Iya ja da shi ba, babu wata muguwar halittar data Isa ta tunkaresu muddin Yana atare da su, rashin baccin da baiyi ba shine Yaja har muka gaza tunkarar su, lokacin da baccin Ya Wauke shi munyi nasarar yi mashi abunda zai dawo gare mu sai dai wani abun al ajabi ya ku6uta daga hannunmu Ya koma ma gangar jikin shi_

Kamar yadda suka ce tun tarihin kafuwar kurkukun ?addara ba'a ta6a samun prisoners da suka tsira ba sai akan su, kuma ba kowa bace sila face ?addarar kurkuku, da ace unaisah ba ta kasance a gidan kurkukun ba, wallahi Danish bazai ta6a yun?urin taimaka ma wani don ya gudu daga cikin sa ba shiyasa bai ta6a taimakon su Deeja ba bayan yana da hanyar da zai iya fitar da su.

Salsabeel Ya ci ba?ar wahala wurin Wawainiya da su Hibba, babu wanda bai ji jiki ba a cikin su, saboda yankin da su ka faWo a dajin babu ko kayan marmari da mutun zai sha, yasha jaraba yin amfani da sihirinsa don ya sawwa?a masu wahalar amma abun ya faska, Saida ta kai ga ciyawa su ke ci ko su ci ganye don suyi maganin yunwar cikinsu, ga Deeja ba hankali tun da tafarfaWo sambatu takeyi shi kuma Mubeen wasu irin marurai ne masu masifar zafi suka mamaye fatar jikin shi, kullum sai yayi hauka kamar zai rasa ransa saboda raWadin azaba, ga uwar rana dake ?walo masu ta ko'ina ba sauki, ga damuwar rashin yan uwansu sunyi kuka tamkar zasu kashe kawunansu, ba?in cikin da suka ?unsa baya misaltuwa, hakika salsabeel yayi namijin kokari wurin ganin Ya basu kulawa duk da wani lokacin abun nema yake yafi ?arfinsa, gaba Waya sun jigata sun sha wahala, babban tashin hankalinsu miyagun halittun daji dake kawo masu farmaki, kusan kullum ne sai Salsabeel Ya zubda jinin shi wurin faWa da su.

Satin su Waya acikin dajin suna shan ba?ar azabar rayuwa, acikin rana ta takwas suna cikin tafiya agalabaice sunata yi ma Salsabeel kukan yunwa suke ji ma?oshinsu zafi yake yi masu ruwa zasu sha bawan Allah Ya rasa ya zaiyi da su, da gudu Ya nufi Cikin dajin yana neman inda zai samo musu ruwa tun yana tafiya da kuzarinsa har ?afafuwan sa suka fara sagewa sai da yagama shan wahala bai samu ruwan ba yana kan hanyar komawa wurinsu kwatsam ya faWa wani yanki na dajin ba zato ba tsammani ya hango gungun Sojojin ?asar Ghana da suke yin atisayen horaswa a dajin, da gudu ya tunkare su kamar mahaukaci haka suka ganshi Ya faWo masu, har sun saita shi da bindigu ya zube kan gwiwowinshi ya fara rokon su akan su taimaka mashi da ruwan sha, gaba Waya sojojin suka kewaye shi hannunsu ru?e da bindigu saboda basu yarda da shi ba, sunyi tunanin wani mugunne shiyasa basu bashi taimakon daya bu?ataba, tsawa suka fara daka mashi suna tambayar shi wanene shi? Meyake yi a cikin dajin, sam ya kasa ba su amsa, kwatsam ana haka sai ga su mubeen sun watso da gudu iya ?arfinsu suna neman shi wata dabbar daji ce ta biyo su aguje, a gaggauce sojojin suka harbeta da bindiga tun kafin su ?araso nan take suka tarwatsa kan dabbar ta faWi ?asa tana birgima, ai koda sojojin suka ga prisoners sanye da jajayen kaya masu numbers a jikinsu sai suka fara zargin salsabeel ne Yayi garkuwa da su tun da shi ne babba acikin su kuma jikin shi akwai zanan tattoo, wanda alama ce ta tambarin wata ?ungiya, ba su tsaya bata lokaci ba suka Waure Salsabeel da igiya tamau, su Mubeen sunata kuka suna rokonsu su ?yale masu Wan uwansu amman ko ta kansu sojojin ba su bi ba, gaba Waya suka sanya su a bayan motarsu ta sojoji, ba su nufi ko'ina da su ba sai cikin ?asar Ghana.

Bayan isar su, A headquarter suka ru?e salsabeel wurinsu, su kuma su Hibba Asibiti suka mi?a su ganin muggan raunin dake a jikin su, babu irin bugun da sojojin nan basuyi ma Salsabeel ba don ya faWa masu me yakai shi daji tare da ?ananun yara amma ya?i faWa masu, sai ce masu yai bazai iya tuna komai daya faruwa da shi ba, ya faWi hakanne saboda bai yarda da sojojin ba yasan ma koya faWa masu gaskiya ba lallai su yarda ba, A ?alla ya shafe kwana uku a hannun sojojin kafin ya faWa masu cewa su ?an nigeria ne, iya abunda zai iya tunawa kenan a rayuwarsa, ba su sake shi ba har sai da su rubina dake a Asibiti suka samu lafiya sunata tambayar ina Wan uwansu Salsabeel tukunna sojojin suka gane cewa ba mugu ba ne, ba su tsaya 6ata lokaci ba don sun fahimci al'amarin su babba ne ba kamar rahoton da Asibiti suka bayar, hakan yasa suka tuntu6i hukumar sojin Nigeria don su sanar da su dangane da yaran inyaso sai su mi?a case Win wurin su.

Lokacin da sa?on Ya riski su Sir Mubarak, bayan ya duba duka bayanan yaran, nan take ya yanke shawarar kiran chief owais don ya sanar da shi zancen case Win saboda yafi dace wa da hukumar Isod, su yakamata case din yaran ya kasance a hannun su saboda abune da ya shafi 6angaren bincike.

Chief Owais yayi farin ciki lokacin da Sir Mubarak ya sanar da shi, dama a lokacin sunata faman bincike kan yadda zasu gano Unaisah, daga shi har taj sunyi tsammanin cikin yaran zasu ga Angel, sai dai ko da sukaje Ghana suka dubasu babu ita aciki, aranar da sukaje basu kwana ba, sai da suka haWa yaran gaba Waya tare da Salsabeel suka tafi da su a privet jet din chief suka shigo Nigeria....

Bayan komai Ya lafa, Sun sama masu gidan da zasu zauna, basu fara bincikar su ba don sun lura da ba'a hayyacinsu suke ba, sai dai suna lura da duk wani motsin yaran sunyi matu?ar yin al'ajabi da irin rayuwarsu, ba su san komai ba, kamar ranar aka haifo su duniya, daga sunci abinci sai bacci, ba zancen yin sallah, ranar da boss ya kunna masu kallo a tv sunga tashin hankali, kuka suka dinga yi ganin ba?on abu da ba su ta6a gani ba, a ?arshe deeja ce tayi silar mutuwar tv Win.

Chief ne ya Waukar ma su Jazz a matsayin likitan da zai dinga duba lafiyar su, kafin ya bashi aikin sai da ya gargaWe shi akan kada ya kuskura ya sanarma kowa ko da kuwa mommynsa ce, shiyasa dr jazz ya?i sanar ma kowa nashi wanda silar hakan yaja har sir mubarak ya fara zargin shi akan wayar da yake yawan kama shi yanayi ta maganar gidan kaji, matsalar da aka samu shi Sir Mubarak baisan da zancen Aikin da Jazz ya ke yi ma chief owais ba, sannan baisan a gidan da chief owais ya killa ce su ba, amma Yana bibiyar case din yaran don jin wani hali ake ciki game da binciken su.

Bayan wasu yan kwanaki, Su chief suka tuntu6i Salsabeel suka tsare shi da tambayoyi dangane da rayuwarsu, bai 6oye masu komai ba gaba Waya ya sanar da su, wa'iyazubillah kusan zaucewa sukayi saboda tsananin tashin da hankulansu suka yi, ba su ta6a jin labarin daya gigita su ba irin wanda Salsabeel ya ba su, abu kamar ashirin wasan kwaikwayo amman wai a zahiri yake faruwa zuciyoyin su sun karaya ainun.

to a cikin labarinsa ne suka ji ya ambaci sunan Angel, sunyi matu?ar girgiza da jin cewa tana a cikin su, kuma sun raba hanya da su, hankalin su ba ?aramin tashi yayi ba, musamman taj kamar zai zauce jin cewa Angel dinsa tana a cikin su, ba dan zuciyar imani ba da tuni ya haWiyi zuciya ya mutu, ganin yadda yake kuka kamar ?aramin yaro yasa Salsabeel tambayar shi meya faru, Chief ne ya bashi amsa da cewa yarsa ce Angel Win da ya ke magana akai, wani irin farin cikine ya lullu6e Salsabeel ganin Mahaifin unaisah, jiki na rawa ya ru?o hannun shi tamau ya fara jinjina mashi yana faWin ya gode ma Allah saboda yarinyarsa tana da kaifin basira Allah yayi mata baiwar da zaiyi wuya asamu mai irin ta, bayan haka yace da shi ya kwantar da hankalin shi, in sha Allah babu abun da zai faru da su saboda suna atare da garkuwa yayi imanin in har ba lokacin mutuwarsu ne yayi ba to kuwa zasu ku6uta batare da sun cutu ba, abun da ya dace shine su tayasu da addu'a kuma a bibiyi dajin evil forest inda rabon agansu toh, shi kanshi Salsabeel Win yayi mamakin daWewarsu a dajin, amma da yayi zurfin tunani sai ya tuna cewa Danish baisan inda zai kai su Unaisah ba, shi iya rayuwarshi daga gidan kurkukun ?addara sai cikin dajin evil forest, bai ma ta6a sanin akwai wasu mutane dake rayuwa a wajen dajin ba, kuma hada ?arin ba su da taswirar dajin da komai zaifi zuwa masu da sau?i, saboda dajin evil forest kurman dajine yana da wuyar sha'ani.

Jami'an isod sun yi matu?ar ?o?ari wurin ganin sun gano su a dajin, kusan kullum ne sai jiragensu sun kewaye shi suna shawagi Allah ne dai bai nufa za su haWu da su ba.

Babban abun da yaja ma su Angel daWewa a dajin, Lokacin da Danish ya ke yin amfani da sihirinsa wurin jigilar Waukarsu idan dare yayi lokacin sun yi bacci yana yin tafiya mai nisa da su duk don su nisanta da gidan kurkukun ?addara silar hakan yaja har suka 6ace hanya suka bar yankin da ya kamata su faWa, sukai can wani yankin daban.

_Alhamdulillah, Kunji yadda akai Su salsabeel suka ku6uta daga gidan kurkukun ?addara, da kuma yadda akai suka haWu da Chief Owais, kuma cikin ikon Allah daga baya sai gashi suma su unaisah an ceto rayuwarsu, a ranar da sojin america suka tuntu6i chief da case din samun yara yan Nigeria a daji, wani irin farin cikine ya lullu6e su, anci sa'a a lokacin yaje babban burnin america kuma sai ga labarin tsintar su unaisah, tunkafin suga su wanene ransu ya basu cewar sauran yaran ne kuma zaiyi wuya in babu ita acikin su, cikin ikon Allah sai ga hotunansu sun gani wayyo Allah tsabar murna lokacin da chief ya turama taj hotunansu da yake shi yana a Nigeria, ko runtsawa baiyi ba adaren ranar da suka shaida baiyanarta_

_A tsanake salsabeel ya ?arasa ba su labarin yana duban fuskokin su_



*Mu haWu Jibi Idan Allah yakaimu da rai da lafiya, don jin yadda zata kaya*


Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'
'?*


*Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login