Showing 30001 words to 33000 words out of 298130 words

Chapter 11 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

na raba ka da yaron saboda lalurar dake atare da shi, bana so wani abu ya cutar min dakai...." gyaWa kai yai"bakomai baba nagode" cikin sanyin murya ya faWi hakan.

Murmushi sheikh imam ya saki yana fadin"aminina yakamata kaga yaron nan da Hateem ya ?wallafa rai akai, dama sauran yaran, zaku sha mamakin kamanninshi da Hateem, daku kanku" ya faWa yana nuna su Deen, ba yabo ba fallasa suka dube shi batare da sun ce ?ala ba.
Baba obie ya Wan yi jim na wani lokaci kafin yace"aminina, acigaba da bashi kulawa ta musamman, Idan yaji sau?i Allah ya raba shi da abun dake damun shi, in sha Allah zamu je mu duba shi, zamu taya shi da addu'a, Allah ya yaye mashi abunda ke damun shi"

Sheikh imam ya amsa mashi da ameen aranshi yayi mamaki yadda suka nuna basu bu?atar ganin yaran duk da ya fahimci kamar suna gudun haWuwa da danish ne saboda lalurar shi.

Duba agogo sharafuddeen yayi"dare yana ?ara yi, Ina so zan wuce"

Baba obie ya dube shi"zaka iya tafiya tun da inada madadinka," ya faWa yana nuna chief Owais da cup din hannun shi
Murmushi sharafudeen yasaki tare da kallon Owais a fakai ce ya kashe mashi ido Waya, murmushin gefen fuska chief ya saki ganin abunda daddynsa yayi masa, ba tun yau ba ya saba yi mashi hakan sometimes tamkar aboki yake Waukar shi.

Gyaran murya Senate lateef yai hankalinsu ya dawo kanshi, fuskarshi babu walwala ya furta.

"Hateem, kada ka manta, akwai taron da zamuyi a National Assembly, domin gabatar da jawabi da kuma ganawa da kakakin majalissar wakilai"

"Ina sane da wannan" atakaice Hateem ya furta hakan.

Sharafuddeen yace"bayan haka zamu ziyarci national Mosque, da kuma National Christian Centre, akwai kuma ganawa ta musamman da zaka yi da sarakunan gargajiya daga sassan kasar mu, after that zaka halarci State Dinner (Liyafar cin abincin dare) tare Ni A Villa"

Sheikah Imam yace"babu hutu kenan Hateem zai fara yawo, ko da yake haka ya dace tun da ba kowani lokaci ake samun damar zuwa ?asar ba, ?wara ka za gaya gari nima dai hadani za'a je villa wurin liyafar ko ba agayyace ni ba sai na je don nasan za'aci kaji" da zolaya sheikh imam ya fada yana murmushi

maganar shi ta ba su nishaWi, gaba Wayansu suka sanya dariya.

Sharafudeen yace"aikune kan gaba baba, kai zaka buWe mana taro da addu'a" sheikh imam yace masha Allah nagode da karramawarnan"
Baba obie yace"Idan da hali ma, yakamata ku le?a masarautar yarbawa ku gaishe da dangin mariganya ?udirat, da kuma masarautar kano suma yakamata aje masu da Hateem, sannan zaka ziyarci National museum dake a lagos, da kuma Yankari Game reserve.... "Tunkan baba obie ya ?are maganar, Hateem ya furta"baba duk ni zan halarci waWannan wuraren daka lissafa? Bani da isasshen lokaci, On saturday next week zan koma canada, ina bu?atar hutu" fuskarshi a yamutse yayi maganar.

Senate yace"dole ne kaje ko kana so ko baka so, mu zamu jagorance ka, Tun da ka shigo ?asar tamu, dole ka zaga dangi, ka kuma ziyarci wuraren buWe ido,"

gyaWa kanshi yai har cikin ranshi baison yawace yawacen nan badan komai ba sai don saboda Danish baisan yayi nisa da estate din, duk da an yanke alakarshi da yaron zaifi mashi kwanciyar hankali idan har yana akusa da inda yake rayuwa.

"On friday zamu shirya maka family dinner, na bankwana" acewar Deen.

Muryarshi asanyaye ya furta "Allah yakaimu lafiya" suka amsa mashi da ameen.


Sun dauki tsawon lokaci suna tattaunawa a tsakaninsu har wuraren ?arfe sha Waya Na dare, Kafin daga bisani sheikh Imam ya rufe masu taron da addu'a, daga nan su ka yi wa junansu sallama, Har bakin entry Hall, Baba obie yayi masu rakiya, Hateem Ya shiga mota tare da sharafuddeen, Sheikh Imam tare da Boss man suka shiga mota Waya, suma sauran kowa Ya nufi Gidan shi dake a estate din, banda chief Owais, baba obie Ya ru?e shi, yace shi zai taya shi kwana yau tunda shi yakawo abunda ya tsoratar da shi babu musu owais ya amince mashi domin shima yayi kewar kakan nashi.

Tun acikin mota, Sharafuddeen yake tausar Hateem akan yayi ha?uri dangane da hukuncin da baba Obie ya yanke mashi na raba shi da yaron, sannan ya kwantar da hankalin shi, ya yi mashi al?awarin ko bayan baya ?asar zasu kula da rayuwar yaron, ba zasu ta6a bari ya wula?anta ba, kalamanshi sun tausasa zuciyar Hateem, shi abinda yafi damunshi raba shi da akayi da yaron, yanzu shikenan bazai sake zuwa inda yake ba, har ya koma canada , abun ya ta6a zuciyarshi baiso haka ba, har cikin gidanshi sharafuddeen ya shiga, suka gaisa da gimbiya mujeedat, ita kadaice bata runtsa ba saboda rashin dawowar mijinta, Su Yazrin tuni sun nutsa a baccin su, bayan sharafuddeen yayi masu sallama ya fito daga gidan security detail dinshi suka buWe mashi mota ya shiga, batare da 6ata lokaci ba, suka nufi Aso Villa domin komawa ga muhallinsa.

Bayan barin su gidan da kusan mintuna talatin, Hajjaty ta lalla6a taje ta Wauko wayarta data ajiye ?asan table, jiki na rawa ta nufi dakin don ta kaima pravin, tana shiga ta taras da shi yanata faman yin zarya adaki kamar mai fama da Wan kanoma da basir, duk ya ?agara da son jin abunda suke tattaunawa, jin sallamarta yasa shi yin saurin tambayarta ina wayar, da sauri ta mi?a mashi, yasa hannu ya kar6a tare da kunna recording din, ya soma sauraron tattaunarsu, hajjaty dake kallon shi, ganin yadda yake tsuma zufa ta wanke fuskarshi yasa tace mashi lafiya, rai a6ace ya jefar da wayar saman gado yana fadin wannan wace irin masiface? Wato dole dai sai yaran nan sun zauna a estate din nan, wallahi bazai yiwu ba, duk yadda zanyi saina yi silar barin su, nasan owais ne ya tunzura obie har ya amince da zaman su, saboda ya makance akan ?aunar shi, Idan sunsan wata basu san wata ba....." yana huci yai maganar, hajjaty dake kallon shi, tsantsar mamaki ne akan fuskanta, harta fara kokwanton anya pravin baida wata manufa akan yaran? Meyasa ya tada hankalin shi akansu? Tayi zurfi a tunaninta taji ya buWe kofar Wakin Ya fuce waje, Jiki asanyaye ta nufi gefen gadonta ta zauna tare da kwantar da kanta, tayi tsammanin zai dawo dakin amma sai taji shiru, ranta ne ya bata cewar ko ya tafi dakin hajiya saratu ne hakan yasa ta ja bargo ta lullu6e jikinta....



*d'EX-PRISONERSd'*



Bayan Sun kammala Cin dinner dinsu, sam sun kasa runtsawa saboda tunanin Wan uwan su Danish, Wazu da marece sun je duba shi, Yanzu ma kuma Bayan sun sanya kayan bacci a jikin su sun yi shirin kwanciya, Wakin shi suka nufa, gaba Wayan su ne a kawaye da gadon shi, sun yi tsaitsaye cirko cirko suna kallon shi.

Unaisah da Batool sun sanya kayan bacci kala Waya Riga da wando launin black gray, rigar tana da hula duk sun lullu6e kawunansu da ita, Jemimah da Azeeza ma kalar nasu sleep dress din iri Waya ne Yar gown ce dai dai gwiwa ta tsaya masu launin pink colour, sun daure kawunansu da head scarf, Praveen da Hanna launin nasu farare ne riga da wando masu zanen flowers ajikinsu.

Hala zalika Mazan ma kowan nan su yana sanye da kayan baccin sa.

Tun suna daga tsaye har dai suka kaiga samun wuri gefe da gefen gadonshi suka zazzauna, banda Gabriel dake atsaye ya goya Azeeza a bayan shi saboda makantar daren ta, duk da lalurar ta fara sauki yanzu, tana gani ba laifi saboda hasken dake gauraye da gidan tamkar da rana, yana ?ara ?arfafa mata ganinta sai dai babu clear amma takan iya shaida fuskokin su, shiyasa bata damuwa yanzu bama kowa yasan tana da lalurar ba sai ?an uwanta.....

Fuskokinsu babu walwala, yayin da suke kallon shi, musamman Haris hawaye tuni sun ji?e fuskarshi.

"Allah ya baka lafiya Wan uwana rabin raina, Danish na tausaya maka, Ina jin raWaWin da ka ke ji acikin zuciyarka, In sha Allah ?arshen wahalarka ne Yazo"

murya arauna ce Haris Ya furta maganar, idanunsa akan fuskar Danish dake akwance tsakiyar gadon kamar matacce.

"Danish, ban sani ba ko kana ji na, dan Allah ka kwantar da hankalinka, kada ka ta6a sanya damuwa akan abunda ke faruwa dakai, ko jiya da muka guje ka don ba mu san kai bane, amma Yanzu mun riga da mun sani, kuma in sha Allah, a kowani hali na rayuwa duk runtsi duk wuya muna a tare dakai, har ?arshen rayuwar mu" Batool na ?arasa faWar maganar ta fashe da kuka tamkar ranta zai fita, da sauri ta kifa kanta saman mattress din daga gefen hannun shi, ta Waura nata hannun akan nashi.

"Batool ki daina yin kuka, zaki ?ara karya mashi zuciyarshi, saboda Ina ji araina yana sauraron mu ba bacci yake yi ba" cikin kwantar da murya Unaisah ta furta maganar, idanuwanta akan Batool cikin shesshekar kuka tace"ya wahala sosai, ko motsi bai iyayi, mu kallon shi kawai mu ke yi, shi ka Wai yasan raWaWin da yake ji acikin zuciyar shi, sai yaushe ne zaiji dadin rayuwarshi"? Cikin jin ?unar rai ta furta maganar tare da dago da kanta idanuwanta sun kaWa jawur..

Fashewa da kuka Azeeza da jemimah su ka yi, sautin su ya karaWe Wakin, Naufal Yace"Dallah meye haka? Kuka shi zai mana maganin damuwar Wan uwan mu ne? Ku bar mu muji da abunda ke damunmu mana" zuciyarshi a jagule yayi maganar,

Muryar Jemimah da shesshe?ar kuka tace"Ni wallahi tausayinshi nake ji, bawan Allah, lokacin da muna a daji bamu lafiya shi ya rin?a Wawainiya damu har muka ji sau?i....." kafin ta ?are maganar, parveen cikin raunin murya ta katse ta da cewa"Idan muna jin yunwa shi yake sama mana abinci, sannan Ya hana idonshi bacci duk don saboda mu, amma meyasa mu muka kasa taimaka mashi awannan halin"? Muryarta na rawa ta jefa masu tambayar.

"Saboda bamu da yadda zamuyi Parveeen, addu'a ce kadai zamu Iya taimaka mashi da ita," acewar Javed shima fuskarshi ayamutse take.

"Ba iya addu'a ba javed, Idan muka tona asirin miyagun mutanan can da suka ?as?antar da rayuwarmu, Ina da tabbacin zamu Yi nasarar kawo ?arshen matsalar Danish damu kan mu, don kuwa nasan har Yanzu suna nan suna bibiyar rayuwarmu bazasu ta6a ?yalemu ba kodan saboda kada mu tona masu asiri dole subi diddiginmu" sajeed ne Yai maganar..

Unaisah ta natsu tana kallonsu, ba tare data tsoma baki ba, saboda ita a halin yanzu ta fahimci wani abu, tun da har jami'an isod suka gano salsabeel to kuwa tana da tabbacin sun san komai game da rayuwarsu!! Kallonsu kawai su ke yi.

"?wara kowa yasan me suke aikatawa, mu faWa masu kawai, su taimaka su rabamu da su, Su ?yale Wan uwanmu yayi rayuwarshi cikin salama" Hanna ce ta faWa tana faman tada jijiyoyin wuyanta.

Calmly Unaisah ta furta"ku daina surutu kuna hana shi natsuwa, yakamata mu je mu kwanta, tun da mun ganshi inyaso gobe da safe sai mu dawo mu ?ara duba shi"

Shiru su ka yi, ba tare da sun motsa ba saboda basu sun yin nesa da shi, da da halima a Wakin shi za su kwana, yayin da su ke cigaba da kallon shi tamkar zasu haWiye shi, tsananin tausayin shi suke ji ga wata irin ?aunarsa da su ke ji.

Parveen da Jamimah sai hamma su ke yi, ita jamimah hada gyangyaWin bacci.

"Please ku tashi mu tafi Wakunan mu" Nawfal ne yai maganar, tare da mi?ewa ya zagaya ta 6angaren da garkuwa yake akwance ya du?ar da kanshi ya manna mashi sumbata akan forahead dinsa, ganin hakan yasa Jemimah yin sauri rarrafawa tsabar iyayi saman chest dinshi ta haye tukunna ta manna mashi sumbata kan cheek dinsa har sau biyu, murmushi kowan nan su yasaki abun ya ?ayatar da su.

?arasa hawayewa gadon Batool tayi har zuwa gefen Garkuwa in a cool voice ta furta"Wan uwana rabin raina, idan kana saurare ni, nayi kewarka sosai, Allah ya baka Lafiya sanyin idaniyata" gefen fuskarshi ta manna ma kiss, kafin ta sauka daga kan gadon, da sauri Haris ya zagaya ta inda su nawfal suke a tsaye daga gaban gadon ya russina tare da ru?o hannun Danish ya buWe tafin hannunsa A hankali ya sumbace shi kafin Ya furta"ko ban faWa maka ba, nasan kasan da irin ?aunar da nake yi maka jinin jikina, Allah ya tashi kafaWunka" bayan Haris Ya saki hannun shi, Javed Ya mi?e ya nufi Side da danish yake, Ya manna mashi kiss a forehead nashi.

"Big bro, our guardian, Allah ya baka lafiya" ya faWa cikin nuna tausayawarshi.

Sajeed dake agoye da Azeeza, Ya matsa kusa da Danish,Ya sauketa daga gefen gadon, da rarrafe ta lalubo Danish ta Waura fingers dinta saman fuskarshi ta shasshafa shi, duk suna ta kallonta.

Haris da zolaya yace"kada ki lashe mana Wan uwa, Kiss Waya zaki manna mashi ya wadatar" kusan sau uku ta sumbace shi, biyu kan cheek dinsa, Waya kan tsinin hancin shi, bayan ta gama nata, Sajeed ya ru?o Hannun shi kamar yadda Haris yayi, a hankali Ya sumbace shi gently ya furta"ka kula mana da kanka our super star, zamu kwana da tunaninka, gobe da sassafe zamu zo duba lafiyarka, garkuwar mu"

Murmushi duk suka saki, wani irin daWi suke ji, mayar da goyan Azeeza Sajeed yayi akan bayan shi.

Hanna ma ta sumbace shi, Ya rage saura Unaisah, dake zaune tayi zugudun kamar mai tunanin wani abu.

"Genie saura ke" acewar jemimah idanuwanta sunyi luhu luhu saboda baccin da take ji.

"Unaisah we are waiting for u, ki yi mashi kiss kamar yadda muka Yi mashi kafin mu tafi" Sajeed ne yai maganar, tamkar bata ji me suke cewa ba, tayi kasa?e tana faman wurwurga eye balls dinta.

Dafa shoulder dinta Batool tayi"Sister, Kin yi shiru, ki motsa mana, Ko kin manta abun da muka ce zamuyi idan mun fita daga Wakin Danish"

Haris Yace"menene za ku yi" da sauri tace"karatu ne zamu yi kafin mu kwanta bacci" Ya furta okey,

Jiki asanyaye Unaisah ta ?arasa haurawa kan gadon, crowling slowly ta nufi Danish, koda ta ?arasa inda yake a kwance, saita sanya hannu ta zame hular kanta, nan take nannaWaWWiyar sumar kanta ta warwaro ta sauko kan kafaWunta, rumfa tayi mashi da gashinta ta yadda ba zasu Iya ganin sumbatar da za ta yi mashi ba.

Sajeed Ya buga ?afa yace"ba mu yarda ba wlh, You are trying to be smart Unaisah, dole ki janye sumar kanki mu gani da kyau" Ya faWa yana sakin murmushi.

Haris yace"kiyi yadda kowa yayi" Batool da su javed sai murmushi suke saki, shiru tayi bata tanka masu ba.

Babu Mai Iya ganinta acikinsu, Waura tsinin hancinta tayi akan nashi, numfashinsu ya soma kokawa dana juna, hatta bugun zuciyarshi saida ya canza, dogon wuyan shi ta fara manna ma sumbata har zuwa kan chin dinsa ta sumbace shi a hankali kafin slowly ta Wago da kanta, ta sumbaci forehead dinsa, ta dawo kan eye lids dinsa Waya bayan Waya ta sumbace su, tana ?o?arin kai mashi sumbata kan soft lips dinsa ba zato ba tsammani taji an dam?o sumar kanta, da ?arfi ya Wago da ita, A firgice ta juyo don ganin wanene Ya katse ta......

Rass taji gabanta Ya faWi ganin Big Guy, wata irin kunya ce ta rufeta, da sauri ta sanya tafukan hannayenta ta rufe face dinta, su Haris dake atsaitsaye sai ti?ar dariya suke yi, ashe tunda ta dukufa tana sumbatar danish suka jiyo motsin buWe ?ofa, suna kallon shi yai masu alamar suyi shiru da bakinsu, nan fa kowan nan su Yaja baki yai shiru, Lamarin ya Waure mashi kai, don bai fahimci me ta ke yi ma danish din ba, yadai ga tayi mashi rumfa da sumar kanta, Cikin sanWa yaje gaban gadon Ya daddage Ya dam?o gashinta kanta.

"Ki ji tsoron Allah Jari, FaWa min kike Aikata ma bawan Allahn nan" fuskar shi Wauke da murmushi yayi maganar yana bin ta da kallon tuhuma, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"wallahi Ni ba ?ar iska bace, ba abun da kake tunani bane, Ka tambaye su ka ji" ta faWa tare da Wago da kanta a lokacin ya sakar mata gashin kanta, duk tabi ta ruWe, gani ta ke yi kamar kallon ?ar iska yake yi mata, tun akan abun da Ya faru Wazu da suka kama ta a Wakin Danish ta cire mashi ma6allin gaban rigarshi, shiyasa take fargaban kada ace kallon yar iska yake yi mata.

Sunnar da kanta ?asa tayi, fuskarta a tur6une babu annuri, sai faman ?yafkyafta idanunta take Yi

"?an uwan Jari, ku fada min me take aikatawa tunda ita bazata fadamin gaskiya ba" Ya fada Yana nuna su Sajeed Da hannun shi
Har suna hada baki wurin maimaita sunan JARI,
da shagwa6a66iyar Murya Jemimah tace"Unaisa Win mu ce Jari"

Big guy yace"Yeah, Ita nake nufi, ko bakusan cewa ita Win Jari bace"? Da mamaki suka girgiza mashi kai gami da tambayarshi ma'anar jari.

"Shi Jari wani abu ne da idan ka sanya shi zaka samu riba, yar uwarku jari ce gare mu baki Waya, tun da muna ?aruwa da ita, kamar dai yanzu da take koya mana wani ba?on abu...." tunkan ya ?are maganar Unaisah tai saurin furta"wlh bani na faraba ai, Naufal ne Ya fara Yi mashi kiss, kowa yayi nice ma ta ?arshe, Kuma ni bama kiss nake mashi ba, Fala?i da nasi nake karanta mashi..." a shagwa6e ta ?are maganar.

Dariya suka saki gaba Wayansu, bayan sun lafa, Big guy yace Ku tashi muje in rakaku Wakunan ku, Dare Yayi sosai, Yakamata kuna bacci da wuri saboda karatun asubahi da ake koya maku" amsa mashi su ka yi da toh, yakai hannu ya Wauki Jemimah, kafin su bar Wakin saida Kowan nan su yayi mashi addu'a suka tottofe mashi jikinshi, har sun fita Unaisah ta dawo


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login