Showing 102001 words to 105000 words out of 298130 words

Chapter 35 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

wani irin tsantsar mamaki da Al'ajabi suke kallon fuskar Danish da ta prime minister, Musamman jami'an Canada sun yi matu?ar girgiza da ganin shi, sun ruWe sai faman Kallo ?urulla suke bin su da shi.

Wata dan?areriyar mota Suka nufa, irin motar da a mafarki kaWai talaka ya ke iya ganin ta, da sauri Wani gabjejen Soja Ya buWe masu murfinta, Cikin motar yadda kasan bedroom tsabar haWuwarta ga wani sanyin A.c dake sanyaya zukata, a tare suka shiga ciki ba tare da sun raba hannun su daga cikin na juna ba, Gimbiya mujeedat da Yazrin motar dake a jere da tasu suka shiga, zuciyoyinsu cike fall da al'ajabin Danish....

Kusan a tare motocin suka soma tafiya A hankali, Yayin da sojoji ke take masu baya, da kafafuwansu suke tafiya ta gefe da gefen motocin nasu.

Lumshe idanu gimbiya mujeedat tayi yayin da brain din ta ke tariyo mata fuskar Danish, bata san ya akai ta tsinci kanta da jin tsantsar kaunarsa ba, farat Waya taji ta kamu da son shi ya kwanta mata aranta, batasan ma ya zata mistalta yadda take ji azuciyar ta ba.

Ita kanta Yazrin zuciyarta ta tsunduma a kogon kaunar matashin da bata san wanene shi ba, jin shi take tamkar Wan uwanta na jini......

"Mommy, fatana Allah yasa ba mafarki na ke yi ba" can cikin kunnanta ta tsinkayi maganar Yazrin da tayi magana cikin harshen larabci.

Numfasawa ta Wanyi muryarta da wani irin sanyi ta soma magana da yaren su na larabci

"ban ga laifin mijina ba, yanzu nake danasanin maganar dana gaya mashi Wazu da mu ka shiga restroom, ban ta6a tsammanin zanga yaron haka ba, ay dole ma ya nemi zaucewa, Ni ko a tarihi ban ta6a jin labarin kamanceceniya irin wannan ba"

"Abun da yafi Waure mun kai shi ne, ba mu haWa alakar komai da shi ba, bamu ta6a ganin ba, ba mu ta6a jin labarin shi ba, sai yau da Allah Ya haWa mu.....

Fuskokin kowan nan su da tsantsar al'ajab

Slowly motor su ta ratsa katafaren entry way na shiga gidan hateem dake a tsare da security, basu nufi ko'ina ba sai cikin ?awataccen Lambun gidan.

Bayan sunyi parking, da sassarfa sojojin dake safa da marwa su ka ?araso tare da buWe ma su marfin motor.

A hankali Prime minister Ya dira kafarsa Ya fito tare da ru?o hannun Danish, Lokacin daya fito daga motar kusan suman tsaye jami'an dake tsaron gidan su ka yi, sai faman yin dogon wuya suke yi suna le?en fuskar danish, Sun saki bakunansu kamar lehen sakarai, ?asa ?asa da murya sautin raWar da sukewa junansu ta soma baiyana

"Abun mamaki bai ?arewa"!

"Kodai idanuwana ne suke nuna min badai dai ba?

"Dama prime minister Yana da Wa Namiji ne?

"To ko dai 6acewa yayi ne sai daga baya aka gano shi? In ba haka ba ni dai a iya sanina ya'yan sa biyu mata....."

Murmushin gefen fuska prime minister ya Wan saki jin tseguminsu, aranshi yana mai jin wani irin annushuwa.

sai bayan da suka soma tafiya tukunna motarsu gimbiya mujeedat ta ?araso, sam bai son sun biyo su ba, saboda ya makance idanunsa danish kadai su ke iya gane masa, Fitowa su ka yi a tare suka bi bayan Su prime minister, wanda Ya mi?i hanyar shiga wurin sha?atawarsa da ke a cikin garden.

Yayin da suke tafiya wata irin ni'imtacciyar iska ce ke ratsa fatar su hakan bakaramin ?aimi ya ?arawa yanayin ba, danish Ya nutsu Yana bin furannin dake a garden din da kallo, dama can shi ma'abocin son furannine da alama dai Garden din ya burge shi...

Hateem sai satar kallon shi ya ke yi kamar zai lashe shi, shi kuwa wanda akeyiwa kallon bai ma son anayi ba.

Su Gimbiya Mujeedat da Yazrin suna a biye da su ba tare da sanin su ba.

Sauke idanunsa yayi akan Peacocks da ke yawo a garden din sun bubbuWe Tail feathers dinsa gwanin ban sha'awa, ba karamin burge shi su ka yi ba..

Wani ?awataccen wuri suka nufa, inda akayi shimfiWa ta alfarma irin ta sarakuna, a kewaye yake da furanni launuka daban daban, Ga wata lumbutsetsiyar Round mattress mai tudu lallausar gaske, an kewaye ta da matassan kai masu laushi.

"Bismillah mu zauna" muryar Hateem ce ta dawo dashi daga kallon gardeen din da yake yi, A hankali suka zauna saman shimWidar.

Daga inda suke a zaune suna fuskantar swimming pool tamfatsetse, launin ruwan da ke a cikinsa blue sky ne pure, ga wasu fararen agwagi saman ruwan suna ta shawagin su.

A ?alla sun dauki tsawon mintuna babu alamun danish zai mayar da hankalinsa akan prime minister, ya nutsu sai kallon agwagin ya ke yi.

Yayin da shi Hateem din gaba Waya ya tattara nutsuwarsa da hankalinsa akan danish, wani irin kallon kurulla yake jifar shi da shi mai dauke da zallar kaunarsa, Jin shirun yayi yawa yasa shi yin gyaran murya, hakan Yaja hankalin Danish zuwa gare shi, slowly ya juyo tare da Waura fararen idanunsa akan fuskar minister, a karo na farko kenan daya fara kallon shi, nan fa suka fara jifawa juna kallon kallon, ko ?yafta ido ba sa yi, sai da suka kusa shafe mintuna batare da sun kau da ido ga juna ba, su gimbya mujeedat dake a tsaye can gefen wata bishiya mai yalwar rassa da ganyayyaki sun kura ido suna kallon su, Ita da yazrin dake a gefen ta.

Wani irin ?warjini Danish yayi mashi, da sauri ya katse kallon da suke jefawa juna ta hanyar yi mashi magana

"Sorry ban gabatar maka da kaina ba, Ni sunana Prime minister Hateem Obinna, kai fa"? Ya faWa yana duban shi har lokacin danish bai daina jefa mashi kallon ba, babu alamun zai tanka mashi kamar akwai wani abu daya ja hankalin da yasa shi kallon nasa.

"Ka yi shiru baka ce komai ba," kamar kurma haka danish yayi mashi.

Dafe kai Hateem yayi muryarshi da kasala ya furta"please ka yi min magana, ba ka son yadda na ?agu da son ganin ka samu lafiya ba, na damu da kai kamar yunwar ciki na, dan Allah ka saki jiki dani, kada ka azabtar dani da kaunar ka...." fuskar shi a yamutse yake yi mashi magana.

"Ina fata babu inda ke yi maka ciwo yanzu"? Ya jefa mashi tambayar, lumshe mashi idanu danish yayi alamar eh.

"Ya Ilahi, ba zaka yi min magana ba, sai dai ka yi min nuni da ido, ni bana so ka daure ka yi min magana, Inason jin muryarka ko hankalina ya kwanta, namanta ban faWa maka ba, gobe da asuba zan bar ?asar ba lallai mu sake haWuwa ba, shiyasa nakeso ka bani haWin kai mu more lokacin nan da muka samu...." cikin sanyin murya ya ?are maganar.

Har lokacin kallonsa danish ya ke yi, abun ya Waure mashi kai, Ya rasa gane ma'anar kallon nan.

"Ko dai kana mamakin kamannina dakai ne"? shiru yayi mashi.

"Wayyo Allah na, to ko dai baka jin harshen hausa ne inyi maka da turanci ko larabci ko french wanne yare kafi ji a cikin wadannan"? A ?agare da son jin amsar shi ya faWa yana kallon la66ansa burin shi ya motsa su don yayi magana.

?iri ?iri danish yana neman ya zautar da prime minister, zuciyarshi a jagule yace"nayi maka uziri tun da ba ka jima da farkawa ba, may be har yanzu baka gama dawowa normal ba, a hakan ma na samu kwanciyar hankali, ganin ka da nakeyi ba karamin faranta raina yayi ba" ya fada yana Wan murmushi sama sama.

"Nasan kana jin yunwa bari nayi magana akawo mana abinci" wayarsa ya zaro daga aljihunsa har time din yana lura da kallon da danish ke jefa mashi har ya fara jin shakkar ko dai ifritan dake jikinsa ne suka motsa, dauriya ce kawai irin ta Hateem

"Namanta ban tambayeka ba, wani kalar abinci kake son ci"? Shiru yai masa, hakan yasa shi yamutsa fuska "Okey,Tun da baka iya yi min magana kar6i waya ka rubuta min ta text message sai in karanta" ya faWa tare da mi?e ma danish wayar, baiyi tsammanin zai kar6a ba, sai gani yayi yasa hannu ya kar6a, Ya soma daddanata, Wani irin dadine ya lullu6e hateem, abun mamaki ya dauki lokaci yana yi mashi dogon typing har mamaki ya kama Hateem sai da ya mula yasha iska tukunna Ya mi?a ma Hateem wayar, Cike da zumuWi ya kar6a don ganin me ya rubuta mashi
Har saida gabanshi ya Wan faWi ganin jagwalgwalon da danish ya rubuta mashi, irin wanda yara sukeyi idan suka dam?i waya.

da sauri ya dago suka haWa ido da juna, baisan sa'adda dariya ta kubce mashi ba, ya dinga 6a66aka dariya har fararen hakoransa suka bayyana masu kyan gaske.

Shi duk a tunaninshi dagangan Danish ya rubuta masa jagwalgwalo awaya, alhalin shi baisan amfanin wayar ba, Shi bai ma ta6a ganin waya ba sai da suka shigo duniyar mutane, sannan bata ta6a zuwa hannunsa ba, yadai san ana daddanata da yatsun hannu shiyasa ya kar6a ya yi mashi abun da zai iya.

"Please meke damunka ne"? Bayan Ya tsagaita da yin dariyar ne yayi mashi maganar, shiru yayi bai tanka mashi ba.

Yanke shawarar kiran Chief Owais yayi saboda ya tambaye shi dangane da Danish don kada a samu matsala tun da shi baisan ya rayuwarshi take ba, yana son yaji ko kurma ne.

Bugu uku Chief yayi picking call din

"Uncle yanzu nake shirin kiranka, Don inji ko lafiya"?

"Owais baisan ya zanyi da shi ba, dama ka fada min yana da wuyar sha'ani, wallahi tun Wazu ya?i yi min magana sai dai kallona da yake ta yi, na rasa gane kanshi, har waya na bashi don ya rubuta min abunda yake son ci amma a karshe sai ma ya rubuta min jagwalgwalo, Ko dai kurma ne"?

muryarshi tamkar zai fashe da kuka yayi maganar.

Da buWar bakin chief sai cewa yayi"ina fata akwai sojoji a kewaye da ku"? ya fadi hakanne gudun kada lalurar Danish ta motsa musamman yanzu da yaji halin da suke a ciki.

"Babu, Mu kaWaine"!

"Uncle ka sanya sojoji su yi maku ?awanya saboda yaron ba shi Waya bane, bana so asamu matsala"

"In sha Allah ba za'a samu matsala ba, kafin mu zauna nayi mana addu'a, kuma nayi imanin babu abun da zai cutar da ni ko shi bi'iznillahi" da kwarin gwiwa prime minister yayi maganar

Yana iya jiyo sautin ajiyar zuciyar owais.

"Uncle, ba kurma ba ne, abun da nake so da kai, ka Wauka tamkar Jiriri ne sabon haihuwa, saboda bai son komai ba, wayar da ka bashi baisan amfanin ta ba, please ka bashi kulawa yadda ya dace sannan ka ?ara ha?uri da shi, A hankali zai fara sakewa" amsa mashi yai toh, kafin yai katse kiran.

Danish nata kallon sa bayan ya gama, har zai kira don a kawo masu abinci, ya jiyo motsin tafiyar mutane da sauri yakai idanunshi kansu, Hadimai ne su biyu sanye da uniform na ma'aikatan gidan, kowaccensu hannayenta na a ru?e da faffaWan faranti, daga saman su anjera kayan abinci nau'i daban daban, wannan ba aikin kowa bane face Gimbiya mujeedat, itace tayi tunanin zasu bu?aci abinci shiyasa tayi saurin kiran landline na gidan ta isar da sakon a kawo masu abinci.

Ya Wanyi mamakin ganin su da abinci, bayan bashi ya bada umarnin su kawo ma su ba, kwata kwata baisan da zaman gimbiya mujeedat da yazrin ba, har yanzu bai gan su ba, saboda bai son sun biyo su ba.

Cikin girmamawa hadiman suka russina har suna hada baki wurin furta"sannu da hutawa yalla6ai" suna magana suna satar kallon danish kamar kwayan idanunsu zasu faWo ?asa.

"Wanene ya bada iznin a kawo mana abinci"?

Da sauri sukace"umarni ne daga wurin gimbiya mujeedat"! nuna masu tsakiyar shimfiWar yayi, anan suka ajiye masu kayan abincin kafin suka juya zasu bar garden din suna tafiya suna waiwayon Danish har da tuntu6en su tsabar gulma da kitsibibi.

ta riga tasan halin hateem bai cika yarda ba, hakan yasa ta tura mashi tezt message.

_I ordered them to bring you food because I was worried about you, tun da muka shiga dinner hall baka ci komai ba_

Murmushine dauke akan fuskarshi bayan ya gama karanta sakon nata, yai mata reply da cewa"Nagode Gimbiyata"

Tuni ?amshin soye soyen da aka kawo masu ya buWe hancinansu, shi kanshi danish din yunwa yake ji, tamkar baici abinci ba.

Farantin farko yana dauke da ban?ararrun kaji anyi masu jar suya sai mai?o sukeyi, ga tsiren nama daban kuma, yaji kayan lambu dana kamshi, ga wasu luxury warmers daga gani abinci ne a cikin su, Wayan tray din Glasses ne da ke dauke da exotic sodas Fresh coconut water, premiun juices and coconut milk, sun haWo masu da silverware and tissue box duk wani abu dai da zasu bu?ata......

'Bismilla me zamu fara ci ko in za6a mana"? Cikin kulawa yayi maganar yana duban danish dake ta faman haWiyar yawu.

Bai jira amsar shi ba, Ya zuba masu sakwara with egusi soup, taji uban naman ganda manyan yanka ta dahu tu6us.

Ya lura bai da alamar ci, Hakan yasashi yanke shawarar bashi abaki,.

Wanke hannunsa yayi a bowl kafin ya zura shi a plate din ya debo sakwarar da miya yakai mashi saitin bakin shi, bai yi tsammanin zai ci ba, ganin ya damtse bakinsa can kuma ya Wan buWe kananun la66ansa a hankali hateem ya sanya mashi abaki, yadda yake tauna tamkar baisan ci nan da nan ya haWiye, cigaba da bashi yayi abaki yana ci, kamar wani karamin yaro, shi kuwa hateem dadi yake ji yana bashi abinci yana ci, Ba zato ba tsammani yaga danish ya sanya hannun shi ya Webo sakwarar ya mi?a mashi don yaci shi ma, yaga tun dazu yake ta bashi shi baici ba...

Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar Hateem, bakomai ne ya faWo masa a ransa ba, face maganar Owais da yace yaci gaba da bashi kulawa a hankai zai saba da shi, tabbas kuwa hakane.

BuWe baki yayi danish ya sanya mashi ya soma ci, yayin da suke kallon juna, tuni yaji hawaye sun cika idanunshi sai dai bai bari sun zubar masa ba, da sauri yayi kokarin danne su...

Cigaba da bama juna abinci su kayi, su gimbiya mujeedat dake kallon su ita da yazrin, murmushi ne Wauke akan fuskokinsu, tsabar Jin dadin yanayi yasa suka samu wuri saman wasu kujerun shan iska suka zauna...

Bayan sun gama da plate din sakwarar, Tsiran naman suka fara ci, Idan ya bashi shima sai ya bashi abaki, suna ci suna kallon juna.

Saboda tsantsagwaran kauna da zarar abincin ya 6ata ma danish gefen bakinsa da sauri yake cirar tissue ya goge masa bakinsa, daga shi har danish din sun jima basu ji abinci mai yawan gaske ba irin nayau, kusan rabi da kwatar abincin saida suka cinye shi, bayan sun gama suka koma suna shan coconut milk da fresh juice.

Sauke farantan hateem yayi can gefe Waya ?asa, kafin ya mayar da hankalinsa akan danish, rungumo shi yayi ajikinshi, hannun shi Waya dafe da bayan shi, Wayan hannun yana ruke da wayar shi, Camera ya shiga don ya yi masu hotuna ko ya samu waWanda zai dinga gani yana Webe kewarsa, da sauri Danish ya runtse idanunsa alamar baya so, kokari yake ya buge wayar gaba Waya hakan ba karamin Waga hankalin hateem yayi ba, cikin sanyin murya ya furta"pls ka bari nayi mana hoto mana, inaso na samu wanda zan dinga kallo bayan na koma ?asa ta," cikin sigar lallashi yake yi mashi magana akan ya buWe idanunsa, dakyar ya samu ya Wan buWe su, maimakon ya kalli camera din sai ya dinga kallon fuskar hateem din, babu yadda baiyi dashi ba akan ya kalli camera amma ya?iya kamar wani karamin yaro, A haka hateem yadinga daukarsu hotuna idanun danish akan fuskarshi, wasu hotunan ya rufe idanunsa, hada video yayi masu mai Wan tsayi, ya kwantar masa da kanshi saman kafadarsa, da wanda ya sumbaci forehead dinsa, kamar wani Wan cikinsa, A kalla ya dauki hotunansu sunkai Talatin, bayan video da yayi masu kusan goma.

Kafin ya gama Wauke Wauken hotunan, kwatsam Yaji danish Ya ?an?ame shi da hannayensa da farko ya Wan ji fargaba amma daga bisani da yaga yana lumshe idanunsa sai yaji hankalin ya kwanta, wani baccine mai daWi yayi awon gaba dashi, kanshi asaman shoulder din hateem, A hankali Ya gyara mashi kwanciyarshi, ya rungumo sa, kamar zai maidashi cikin shi, hannayen danish na abayan hateem ya ?an?amesa kamar wani yace zai ?wace masa shi.

Wani kallon so da kauna hateem yake binsa dashi yayin dayake yin baccin, A hankali ya soma shafa bayan shi da yatsun hannayensa kafin ya zura hannun cikin sumar kansa tamkar yanayi mashi susa, harta numfashin danish sai da ya canza saboda daWin da yaji na abunda Hateem ke yi ma sa.

Bakinsa yakai saitin kunnan danish, cikin muryar raWa yayi mashi magana.

"Do you feel what I feel about you?"

Ya faWi hakan batare daya sanya ran danish zai tanka masa ba, a tunaninsa yayi zurfi a baccin nasa.

Kamar daga saman yajiyo daddaWar muryarsa tamkar ana busa sarewa ta ratsa kunnansa da cewa "Yes, I do. I feel more than you might think"

wayyo Allah dadi prime minister tamkar zai zauce tsabar murna da jin maganar danish, Cigaba da kallon fuskarsa yayi tamkar zai haWiye sa.

"Nakasa yarda cewa kaine kayi min magana da bakin ka, ko dai kunnuwana ne suke jiyo min ba dai dai ba"? da biyu ya fadi hakan saboda yana son ya ?ara jin muryar shi.

"No, ni na maka magana" danish ya bashi amsa idanunsa a rufe, har time din basu raba jikin su daga na juna ba

"Meyasa ka damu dani"? Danish ne ya jefa mashi tambayar
Murmushi hateem yayi kafin ya furta"tun lokacin da nafara Yin tozali dakai, Naji na kamu da matsananciyar kaunarka, duk da bansan wanene kai ba, amma naji ka kwanta min araina, ka sace min zuciyata, babban abinda yafi jan hankalina gare ka shine kama da muke da juna, Ina jinka tamkar ni na haifeka, Allah ne kadai yasan son da nake maka Danish, wallahi bana son rabuwa dakai,


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login