Showing 9001 words to 12000 words out of 298130 words

Chapter 4 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

kawo maku abincin" amsa masu sukayi da toh, Jiki asanyaye suka zauna duk basu ji dadin abunda khadeeja ta aikata ma sojojin ba
"Dan Allah kuyi hakuri Idan mun 6ata maku rai" sarah ce tayi masu maganar
Murmushin ya?e suka sakar mata"kada ku damu, ai munyi maganinta yanzu" juyawa sukayi atare suka nufi kitchen, abun da suka daura kan gass harya fara ?onewa shaf shaf suka ?arasa Yin girkin.

Khadeeja dake adaki, Sai kuka takeyi tana bubbuga ?ofa da hannunta kamar zata 6alleta, sumar kanta duk ta rufe fuskarta
Gajiya tafara Yi da buga ?ofar, Ta Juya zata je ta kwanta karaf idanuwanta suka sauka akan Wayar dr jazz da suka bari kasa, Ga kayanshi daya bari riga da wandon shadda, jiki na 6ari taje ta dauki wayar, duk da bata Iya amfani da ita ba sai da tayi ?o?arin kunnata, saboda ta haddace Yadda jazz yake latsawa agabanta, Cikin sa'a ta kunna wayar haskenta Ya kawo,
Gefen gado ta zauna tana yin shesshe?ar kuka
Ta soma kacaccala mashi wayar, kasancewar babu password a wayar Yasa ta samu damar dannata son ranta, batare da saninta ba ta shigar mashi contact dinsa adai dai kan sunan My Mom ta latsa Kira, Ringin wayar ta fara Yi, Khadeeja ta natsu tana jiran jin wazai Yi magana kamar yadda taga Ana yin amfani da ita ayi communicating

Kiran wayane Ya shigo layin Mom turai, a lokacin tana acikin bedroom dinta ita da sir mubarak akwance saman gado, ita kadai ce idonta biyu, shi Sir mubarak Ramuwar baccin dabaiyi ba jiya yake Yi.
Jin wayarta na ruri ne Yasa ta sauko daga kan gado, taje gaban mirror ta duba sunan mai kiranta
Mamakin ?arara akan fuskarta ganin sunan My Own Son Ya bayyana akan screen din wayarta
Murmushi tadan saki tana fadin"Allah Sarki My son, Ciwo Ya hana kazo inda nike shiyasa ka kirani awaya, bari Naji me Yake bu?ata" ta faWa tare da Waga wayar ta kara a kunnanta, hada ?o?arin yin sallama.

Shesshe?ar kukan Khadeeja ne Ya fara cika kunnanta, Zaro ido waje turai tayi muryarta da alamun ruWani ta furta"Wacece ke kuka"?

*Daga Al?alamin Boss Bature>???*


*Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida*

_~*
'=؋?BOSS LADIES WRITERS
'=؋?
'*~_



_=?%?=ث?THE PRISONERS=?%?=ث?_


~TAKUN ?ARSHE~


Daga Al?alamin Boss Bature


Dedicated To Aunty Kubra=؋?




_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and crueltyd'._



_______________________
'?


Shesshe?ar kukan Khadeeja ne Ya fara cika kunnanta, Zaro ido waje turai tayi muryarta da alamun ruWani ta furta"Wacece ke kuka"?

"Khadeeja ce, Ina Jazz Wina Yake" kafin Turai ta bata amsa kiran Ya katse, abun ya Waure mata kai, Ya akai wayar Jazz taje hannun mace? Maimaita sunan khadeeja tayi aranta kafin da sauri ta fito daga dakin ta nufi bedroom dinsa.

A lokacin suna daga zaune gefen gadon shi, Shi da Ibad dake bashi abinci abaki, hannun ibad ru?e da plate with spoon, har yayi wanka ya sanya jallabiya a jikin shi.

Shigowa mom Turai tayi dakin gaba daya suka dago suna kallonta.

Ajiyar zuciya ta sauke fuskarta da fara'a ta ce"My son, how's your body? I hope you're getting better now."

In a cool voice yace"Mom da sauki, ina samun kulawa a wurin ?an uwana, yaya Zaki ma bai jima da fita ba"

Murmushi tasaki tana kallon Ibad tace"our last born, Sannu da ?o?ari, kana Ji da Wan uwan nan naka"

Ta6e baki yayi kafin yace"to ya zanyi mommy, daddy ya 6allo mana aikin Jinya, Yana can kwance Kinyi mashi wanka Yana bacci, Ya ya Zaki kuma ya gudu ya barni da aikin bashi abinci abaki"

Tuntsirewa tayi da dariya, shima jazz Win dariyar yake Yi, shi kuwa ko ajikin shi bilhakki dagaske Yake Yin maganarshi.

Tsagaiwata tayi da yin dariyar tace"Ibad na fahimci maganata ta tsaya maka aranka, Nifa ba daddynku nayi ma wanka ba, Taimaka mashi nayi ya rage kayan jikin shi, idan ba haka ba ni taya zan Iya yi ma shi wanka ?ato dashi, Kallarni ka gani ?ar ?arama dani" hura mata hanci yayi batare da yace komai ba

"Jazz where's your phone"? Ta faWa tana kallon shi.

He was silent for a while, Yana ?o?arin tuna inda Yabarta.

"Mom, kamar nabarta a gidan Yaran da nake Kula da lafiyarsu"

Mi?a mashi wayar tayi"Duba ka gani, wata yarinya ta kira da layinka, tana kuka, wai jazz dinta take nema"

Da mamaki akan fuskarshi Ya kar6i wayar, Yana duban Kiran da akayi da layinshi, tunkafin Ya danna kiran ranshi ya bashi cewar Khadeeja ce.

Da sauri Ya kira layin, ringing uku ta Wauko tana fadin"Ni ku ?yale ni tun da ba zaku bani muyi magana da Ya jazz ba, kun wani isheni da kira,"

Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarsa, jin muryar deejan sa, mom turai da Ibad sun tsareshi da ido suna kallon fuskarshi.

"Khadeeja ni ne fa" a kwance take kan gado Jin muryarshi Yasa Ta yi zumbur ta mi?e zaune tana fadin"Ya Jazz dama baka mutu ba"? da wani irin farin ciki ta furta maganar.

Murmushi ya saki tamkar yana a gabanta yace'ban mutu ba My deeja, lafiyata qalou, Yanzu haka ina agida, wannan layin da kika kira, Na mom Wina ne"

Shagwa6a ta sanya mashi" I hate U ya jazz, Shine ka manta dani, duk nabi na tashi hankalina akanka ashema kana gida"

"No, it's not like that, Khadeeja. I miss you. I've been thinking about you tun time din dana dawo hayyaci na"

Kallon juna mom Turai da Ibad su ka yi alokaci Waya, kafin suka maida dubansu gare shi.

"FaWamin Kin yi breakast da safe kuma kin sha maganinki"?

"Ni ban sha uban komai ba, babu wanda ya bani, waWancan ?attan da aka bar mana agida jiya suka cinye mana abincin mu, yau kuma na sanya su dole su girka mana, aiko suka shiga kitchen suna yi, basu sani ba na Wauki bindigarsu nadinga tsoratar dasu hawwa......." hankalinta kwance take kora mashi jawabi, a firgice ya Wago da ido yana kallon Mommyn su, ga dukkan alamu suna jin maganar da deeja take Yi mashi,"

Muryarshi a ruWe ya furta"Dagaske kike ko wasa"?

Dariya tasaki kafin tace"Wallahi dagaske nake maka, don ma sun min wayau sun kulleni a Waki, ai da tuni na kakkashe su"

Zaro Ido Ibad Yayi, Mom Turai tayi dariya, gani su ke yi kamar zolaya ne abun da yarinyar take faWa ma jazz, shi kuwa yasan zata aika, Fiye da haka ma shiyasa ya Wauki maganar ta serious.

"Khadeeja, Ina fata baki raunata kowa acikinsu ba"

"Wlh ban kashe kowa ba, ai na faWa maka sun ?wace bindigar"

Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke
"Dan Allah My baby girl kada ki ?ara yun?uri Waukar bindiga kinji ko?

"Toh,"

"Yawwa ai nasan kina jin magana ta, idan har kina so na zo gidan karki ?ara rashin ji," muryarta a ladab ce tace"In sha Allah" kamar wata mai hankali

"Good Girl, Kafin nazo kiyi wanka, Kici abinci ki ?oshi," tace "Toh"

"Namanta ban tambaye ki ba, Where did you find my phone?"

"AWaki kabarta saman kayanka, nan na Wauke ta"

"Okey, pls Ki ajiye min inta, kada kice zaki yi wasa da ita"

"Toh, Idan kazo gida zaka gyara min gashin kaina kuma kayi min kalar kitson kalaban nan da ka ta6a yin min"

Da sauri ya Wago suka hada ido da mom Turai.

Fuskarta Wauke da murmushi tace"Eyyeh, Lallai ashe Jazz har kitso ka Iya yi ma mace, gama wayar ka bani labari"

da zolaya ibad yace "mommy kin huta, da zuwa saloon, daga yanzu Jazz zai dinga yi maki gyaran gashi" mi?a mashi hannu tayi suka tafa kamar wasu abokai.

Du?ar da kai Jazz yai"Khadeeja sai anjima, please take care of your self for me"
"You too," sallama su ka yi da ita.

Kunya duk ta kama shi, sai faman sunnar dakai ?asa Yake Yi.

"Jazz kai muke sauraro ni da mommy" ibad ne yai maganar.

Fuskarshi a yamutse ya furta "Khadeeja ce yarinyar da daddy ya baku labarin ta, She's mentally ill. There's no love between us. ina kula da ita ne saboda rashin lafiyarta"

mom turai da raha tace "Don't lie to me. I'm your mom and I understand you. Yarinyar nan dai sonta kake Yi" shiru yayi bai ce komai ba, don yasan da wuya ta fahince shi, zolayar shi suka dinga yi tun yana Waure fuska har yakai ga sakin dariya.

______________________
'?


A hankali Motar su Ta shigo gidan, bayan jami'in yayi parking, Salsabeel Ya fito daga ciki Yayi mashi sallama kafin ya nufi ?ofar shiga falo.


Yana shiga falon ya hango su Hawwa zazzaune kan carpet, An jera masu kayan abinci saman Tray, komai da Khadeeja ta ba sojojin Umarnin su girka masu saida suka girka shi, tun daga kan Chicken pepper soup, fried fish, Chips, wainar kwai, Doya da kwai.

Gyaran murya yayi masu tare da buWe baki Yayi sallama, A hanzarce suka Wago suna kallonshi, aiko da sauri suka mi?e da sauri hada gudu suka nufeshi, Waya bayan Waya yake rungumarsu a jikinshi.

"Ya salsabeel Ina kaje tun jiya baka dawo ba, Ka tafi kabar mu da kewarka"
Fuskarshi Wauke da murmushi yace"Eyyah am sorry, nima nayi kewarku, ay min afwa wani uziri ne Ya ru?e ni, amma tunda na dawo yanzu komai ya wuce"
Yayi maganar idanuwanshi akan fuskokinsu
"Ina Khadeeja"?
Nan fa suka haWa baki suna bashi Labarin Ta'asar da Khadeeja tayi ma sojojin da aka bar masu.

Hankalin shi ya Wan tashi sai dai baiyi mamakin abun da Khadeeja ta aikata masu ba, ya riga daya san halin kayanshi.

Jin motsin tafiyar mutane yasa shi saurin kai idonshi inda suke.

Fitowarsu kenan daga kitchen, wanke wanke Suka tsaya yi a kitchen din sun gyara komai da suka 6ata, har sun maida suturarsu.

Wani Wan iskan kallo suka watsa ma Salsabeel, Hakan Ya tabbatar mashi da ransu Ya 6aci sun harzu?a.

Tamkar mai jin shakkarsu ya furta"Am...dan Allah Kuyi ha?uri, Yanzu na shigo gidan su Hawwa suke bani labarin abun da khadeeja ta aikata maku, banji dadi ba, Yalla6ai ne bai bani damar dawowa da wuri ba, da duk hakan bata faru ba....."

Fuskokin su babu annuri ko miskala zarratin
Tiger yace"malam bamu bu?atar Jin komai daga bakin ka, tun da ka dawo gidan falillahil hamdu, Ka ci gaba da kula da ?a'?anka, Mu kaga tafiyar mu sannan duk abun da ka gani badai dai ba kada ka tuhumi kowa, Khadeeja ce sila" Rai a6ace Ya ?are maganar, Ya nufi Dining table Ya du?a ya dauko masu bindigoginsu.

Army boy yace"Zan baka shawara, Yarinyar nan ku gaggauta kai ta Gidan Mahaukata, can ne Yafi dacewa da ita, Idan ba haka ba wata rana zaku kuka da kanku, don wannan tafi bomb bala'e"

Army na kammala yin maganar suka nufi ?ofar fita daga falon, da sauri salsabeel Yabi bayansu yana basu ha?uri.

"Dan Allah Ku tsaya, bai kamata muyi irin wannan rabuwar ba, nasan ban kyauta maku ba, amma dan Allah kuyi hakuri kada ku ru?e mu aranku"

Ta6e baki su ka yi, Tiger yace"hmmm bakasan masifar da yarinyar can taso taja mana ba, shiyasa har kake da ?warin gwiwar Yi mana magana, Badan Allah Ya kawo mana mafita ba, da yau mu dukan mu zamu ba?unci lahira"

Jiki asanyaye Salsabeel Yace"ina ?ara baku hakuri, Allah Ya huci zuciyarku"

"Dama ahuce take, bamu hanya mu wuce" matsa masu hanya yayi, duk bai ji Wadin abun da ya faru da su ba. har suka fuce bai daina bin bayansu da kallo ba.

Sai da yajiyo tashin motarsu, tukunna ya sauke ajiyar zuciya, Ya juya ya kalle su Hawwa.

"Awani Waki suka Kulle ta"? Sarah ce Ta nuna mashi kofar dakin, Azafafe Ya nufi upstairs, Yana isa bakin ?ofar Ya sanya hannu ya murWa key din.

Tsabar 6acin rai ko sallama baiyi ba ya faWa Wakin, a gaban mirror ya taras da ita zaune, ta sanya undy ta jashi har saman kirjinta, ga dukkan alamu wanka tayi shine ta zauna tana gyara jikinta kamar wata mai hankali.

Gyaran murya yayi mata, zumbur ta mi?e tana faman ?yaf?yafta idanuwanta, hannayenta biyu ta Waura asaman kanta kafin tace "sun faWa maka abunda na aikata"?

Takaici ne Ya ishe shi wato har tasan ta aikata badai badai ba.

"Meyasa"! AWan tsawace Ya jefa mata tambayar, Ta6e mashi baki tafara yi alamar zata fashe mashi da kuka da sauri Ya zare mata ido haWi da cewa"Yi min shiru! kar in kuskura Inji kukan ki," da buWar bakinta sai cewa tayi"ai dama ba ka so na, Kafi son su hawwa, shiyasa kake min fada" sassauta fushin fuskarshi yayi tunawa da karancin hankalinta

"Am sorry, raina ne Ya 6aci, bawai bana sonki ba, pls ki daina rashin ji dan Allah"

Washe mashi baki tayi "Nadaina, bari na Wauko maka wayar Ya jazz, na kira shi har mun gaisa ashe bai mutu ba Yana nan da ranshi" ta faWa tana dariya ta juya ta nufi gado ta dauko wayar taje ta mi?a mashi Yasa hannu Ya kar6a.

da mamaki yace "Taya akai ki ka yi waya dashi"? Watsa hannu tayi"nima bansani ba, na daddana saina kira,"
Call log Ya shiga, numbar farko data bayyana ta Mom turai, Ya danna ma Kira, Bayan ta Waga wayar cikin girmamawa salsabeel Ya gaishe da ita, daga bisani Ya tambayeta Ya jikin jazz, tace mashi da sauki, bata tambayi wanene shi ba sai ta ba Jazz wayar suka cigaba da yin magana,

Hankalin shi ya kwanta Jin muryarshi raWau tamkar bai ta6a yin ciwo ba, sun jima suna yin wayar har jazz ya tuna mashi da maganin khadeeja kafin suka yi sallama Ya adana mashi wayar a hannun shi
Tattara Yaran yayi a falo, hada shi suka zauna suna kwasar girkin da Su Tiger suka Yi masu, dama da yunwar shi Ya dawo, aikuwa dai sunyi kullu wash rabu hani'an, su mama Tiger An Iya girki, sai santi su ke yi, musamman khadeeja, bakinta dama dama da mai?o.


*

Baiwar Allah, Ta hana zuciyarta sukuni, tun lokacin da tayi masu Benazir la6e a toilet, kunnuwanta suka jiyo mata maganganun da suka tsaya mata aranta, ha?i?a tayi danasanin sauraransu, don tun safe take faman jinyar zuciyarta, kiri kiri taki cin breakfast dinta, har lunch bata ci ba, yini tayi a cikin bedroom dinta da raWaWin abun azuciyarta, Tani tayi ?o?arin shawo kanta donta faWa mata meke damunta ta?i ta sanar da ita, ba irin lallashin da ba ta yi mata ba amma ta?i sakin jikinta.

A yanzu haka tana daga kwance saman prayer mat, ta lullu6e jikin ta da dogon hijabinta launin milk, daga gaban dardumar qur'anic stand ne an bude shi alamar karatu take cikin yi bacci yayi awon gaba da ita.

Damuwar halin da take aciki Ya hana Tani samun sukuni, fargabanta kada ace wani abunne ke shirin faruwa da ita shiyasa ta canza mata.

Shigowa Wakin tayi domin gyara mata bedroom din, karaf idanuwanta suka sauka akan zeenatu dake ?udundune tana bacci.

Cikin takun sauri Tan???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?i ta nufi dardumar, aranta tana fadin'baiwar Allah, daWina da ita duk halin da zata shiga bata mantawa da yin ibadarta"

Zu?unnawa tayi agaban prayer mat din, muryarta ?asa kasa ta ambaci sunanta.

"Zeenatu! Zeenatu! Ki tashi ki koma kan gado ki kwanta, kwanciya kan prayer mat, bai da amfani jibi yadda ki ka ?udundune kanki duk kin takure kanki"

Tani sai zuba takeyi babu alamun zeenatu zata farka,
"Oh Oh ni wannan baccin naki bame ?arewa bane da alama, dan Allah ki tashi" still bata tanka mata ba.

Hannu ta Waura saman jikin zeenatu ta bubbugata, nan ma ta?i farkawa, lokaci Waya Tani ta fara Jin fargaba acikin zuciyarta, hankalinta yayi mugun tashi, a ruWe ta Waga murya tana ?wala mata kira da sauti mai karfi"Zeenatu! Zeenatu! Nashiga uku, Wayyo Allahna, meke faruwa dake ne, Zeenatu dan Allah ki tashi" jikinta na rawa ta soma kiciniyar tu6e mata hijabin data ?udundu ne kanta aciki da?yar ta samu ta yakice hijabin ta nannaWeta gefe daya kan darduma, koda Tani ta Waura idanuwanta akan jikin zeenatu saida gabanta Ya faWi, ganin wata irin zufa dake tsastsafo mata ta ko'ina, Rigar jikinta ta manne ma fatarta, sumar kanta kuwa duk ta yamutse babu gyara, shafa wuyanta Tani tayi nan fa taji yaWauki zafi sosai.


A gigice ta mi?e ta watso da gudu ta nufi babban falon gidan, a lokacin Dr shureim Yana daga zaune kan Sofa, Benazir tana a gefenshi, fuskarta Wauke da murmushi take kallon shureim dake bata labarin ?uruciyarta.

Kamar mahaukaci haka Tani ta nufo su ta zagayo ta gaban Sofas din, kusan atare suka dago suna kallonta da alamun ruWani akan faces dinsu
Dr shureim Yace"Tani! Lafiya? Meke faruwa"?

Sai faman yarfa hannu take yi duk tabi ta ruWe.

"Pls ki buWe baki kiyi mana magana" acewar Benazir, da?yar ta iya tattara natsuwarta wuri guda, da karfin hali ta furta"Zeenatu ba lafiya! Tana acan daki rai hannun Allah, kwata kwata bata motsi..." kafin ta ?are maganar, da gudu Dr shureim da Benazir suka nufi part dinta, tsabar sauri mayafin jallabiyar Benazir har faWuwa yake yi kan kafaWarta da sauri take sanya hannu ta gyarashi, Tani tana abiye da bayansu.

Suna shiga Wakin idanuwansu suka sauka akan zeenatu dake a kwance magashiyan tamkar bata numfashi.

Slowly dr shureim ya zube agabanta kan gwiwowinsa, ya sanya hannayenshi biyu ya tallabo da kanta ya Waura saman laps dinsa, Benazir ta zu?unna gefenshi, fuskokinsu da alamun ruWu suk soma ambaton sunanta"Zeenatu! Zeenatu"!

"Tani, bata da lafiya ne"? Benazir ce ta jefa mata tambayar
Muryar Tani tamkar zata fashe da kuka tace"wallahi ban sani ba nima, yanzu nashigo Wakin na taras da ita a kwance, nayi tsammanin ko bacci ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login