Showing 66001 words to 69000 words out of 298130 words

Chapter 23 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

riga da nage baku kaunata, Shiyasa baku damu dani ba" ta faWa haWi da marairaice masu fuska,
"Wallahi aunty Ummi Muna ?aunarki, kuma mun damu dake" Hannah ce tayi maganar
"Ni dai Inasonki aunty Ummi, kiyi hakuri idan mun 6ata maki rai," murmushi ummi tasakar ma Azeeza da tayi maganar.
Ru?o hannunta Jemimah Tayi"Aunty ummi nima ina sonki"
"Naji na Yarda kuna sona, Yanzu mu shiga ciki," ta fada tare da Jan hannun Batool suka nufi ciki tare da su Hannah
Tunkafin Su ?araso, Boss man Yake Kallon Ummi, sam ya manta da ita.

"Barka da hutawa Yalla6ai, Fatan ka wuni Lafiya, Ya iyali"
A hankali Ya furta"Lafiyalou Ummi, Ina fata kema haka"? ?aga mashi gira tai alamar eh, ta faWa tare da samun wuri saman Sofa ta zauna, suma sauran duk suka zauna.

hankalin Sajeed na akan screen din wayar Unaisah, Haris da javed suna zaune gefe da gefen shi tare da naufal sai kallon Game din da Yake bugawa suke yi, baijima da sauke shi akan wayar ba.

Gyaran Murya Ummi tayi masu atare suka dago suna kallon ta.
"Sannunku, ba hello ba Hi kun samu Waya kunata danna waya baku ita ne"
"Ta Unaisah ce," Acewar Sajeed
Da mamaki Ummi tace"Unaisah ke da waya iphone15pro? Amma ban ta6a ganinta ba"
"Dr Laurace ta bata Kyautarta, Waya daga cikin Likitocin da suka yi jinyarsu a america"
Boss man ne Ya bata amsa, Jinjina kai tayi.
"Ina ita Unaisah dinne"? Tayi tambayar tana kallon su
Boss Yace"Bansan meya tsayar da ita ba, tunWazu da muka shigo tare da big guy Ya tafi da ita zai nuna mata kitchen din gidan nan ban ?ara ganin ta ba, ba mamaki ta tsaya taya masu aiki girkin dinner"

"Dan Allah ka nuna min kitchen din, Inaso In kar6o ma aunty Ummi abinci, Yunwa take ji" acewar Batool.
Murmushi boss man Yayi yana dubanta yace"kin damun da auntyn nan naki da alama, kada ki damu, bari na kira big guy awaya, idan suna a kitchen din zansa akawo mata abincin.... " kafin Ya ?are maganar, Parveen tayi saurin cewa"Dan Allah Nima zanci" dariya sukayi gaba dayansu.
Ummi tace"foodie, Baki Gajiya da cin abinci, shiyasa kika fi sauran ?an uwanki jiki"
Kwa6e fuska tai"ay bani kadai bace me cin abincin ba, Ki kalli kumatun jamimah sunyi manya manya da su" maganarta ta basu dariya.
Harara jemimah ta watsa mata"ay dai ban kaiki Cin abinci dayawa ba, Ni madara da bonbita nake sha, Sai dafaffan kwai da Fika fikin Kaza," boss dake kallonsu murmushine dauke akan fuskarshi, Firarsu ba karamin nishadi take sanya shi ba
Wayarshi Ya zaro daga aljihu Ya danna ma Big guy kira, Bugu uku Yayi Picking

Mi?ewa yai da sauri Ya nufi cikin falon nesa da su ya tsaya saboda hayaniyarsu.

"Malam Ina ka shiga ne? Ka tafin mun da rabin raina"

On the other hand sautin dariyar Big guy ta karaWe Kunnuwansa,

"Nifa Yanzu Haka Ina daki kwance saman gadona"

"Bana son Iya shege, To ita ina kabarta?

"Ka riga da kasan Halin Jarin naka, yarinyarce da kiriniya, Tunfa dazu dana nuna mata kitchen din nace mata ta dawo cikin yan uwanta, bayan na fada mata hakan na wuce room dina, yanzu haka bata wuce kitchen din, Cikin kattai" ya karasa maganar Yana dariya.

Daure fuska boss yayi tamkar Yana agabanshi,
"Zamu hadu dakai ne, Allah idan wani abu Yasamu Yarinyar nan jikinka ne zai gaya maka dan rainin wayau" ya fada tare da yin rejecting kiran,
Cikin takun sauri Ya nufi hanyar zuwa kitchen din, ba laifi akwai tazara tsakanin kitchen din da main falo,

Lokacin da Ya Isa katafaren kitchen din gidan tamkar a restaurant tsabar haWuwarshi, kai kace ba wurin Girka abinci bane saboda girman shi da ?awatuwarshi, An zuba kayan aiki masu tsada da inganci, gaba Waya masu girka abincin Gidan Jami'an Isod ne cikin chef'uniform, matasan samari masu jini a jika, daga ganin Yadda suke aiki zaka shaida kwarewarsu a 6angaren catering, ko mace bazata nuna masu Iya sarrafa abinci ba, A ?alla sunkai su Bakwai, Babu wanda Ya lura da shigowar Taj acikinsu, Gaba Waya Hankalinsu na akan Unaisah, dake agaban kitchen island tana Yanka masu kayan Lambu, abun da ya Waure ma taj kai, ganin Yadda sukayi mata rumfa kamar zasu haWiyeta tsabar yadda suke binta da mayataccen Kallo, Ta saki baki sai Labari take basu su kuwa sun Kasa kunne suna sauraron daddaWar muryarta, Tunda suka kafe ta da idanunsu ko kyaftawa basa yi kamar zasu haWiyeta.

Gyaran Muryar da Taj yayi masu ne Yaja Hankulansu ga dubanshi, kamar sunga wani mugun abu, A gaggauce su kayi saurin barin Inda Take, kusan atare suka buga ?afa HaWi da sara mashi.
Kallon Harara Ya watsa masu, Cikin harshen turanci Ya furta"wannan wani irin gangancine zaku bar Yarinya tana amfani da wu?a? Kun wani tsareta da idanunku kamar zaku lashe ta" Sunnar dakai su kayi Suna faman sosa keya suka hada baki wurin furta"sorry Sir, ba laifin mu bane, Itace ta bu?aci damu koya mata girki, munyi kokarin Hanata amma saita sanya mana rigima"
Wurga eye balls dinsa Yayi akan Unaisah dake Kallon shi, Har ta ajiye wu?ar hannunta, nufo shi tayi fuskarta da murmushin Ya?e tace"ay ni nace su bani In tayasu aiki, Kuma dama Na iya ba yar koya bace" ta fada tana ru?e qugunta da hannu.
Wani kallo Ya jefa mata me kama da harara, bakomai Yake tunawa ba face lokacin da tana yar ?aramarta, ranar daya tafi aiki yabarta a gida tana jin yunwa taje ta kunna cooker gass da sunan zata yi girki, wuta ta kama a gidan, wai yau itace take mashi kurin ta Iya girki ba yar koyo bace? Girgiza kai Yayi haWi da yin murmushi tacikin face mask dinshi
"Daughter, ?an uwanki sunata nemanki, Yakamata Kizo Mu koma falo" ma?e mashi kafaWa tayi"ay bamu gama girkin ba"
"Bana son gaddama, zo ki wuce mu tafi"
Marairaice mashi fuska tai"dan Allah kabarni wallahi inason In Iya girki kala kala,"
"Kada Ki damu, zansa a koya maki amma ba yanzu ba, dokar Aikin mu ce mace bata shiga hurumin mu, baki ga maza bane a kitchen din"? Cikin lallashi yayi mata maganar Yana nuna mata chefs din dake tsaitsaye cirko cirko suna kallon su
"Yalla6ai, da dai anbarta ta koya tun da ta nuna tana so, kuma ni aganina maca ce ita, wata rana zataso tayi ma mijinta.... "Tunkafin chef din daya dauko Maganar Ya karasa boss Yayi mashi wani kallo mai nuni da kashedi, Hakan yasa shi yin saurin Katse maganar,
Janyo hannun Unaisah Yayi dakarfi Ya fito da ita daga kitchen din, Chefs din basu ji dadin zuwan Shi ba, Ya raba su da Yarinyar data We6e masu kewa yau, zuwanta Ya faranta masu rai, sunji dadin surutun da tadinga yi masu, komai nata burgesu Yake yi.

Ranta Ya 6aci, Ganin yadda ya janyota daga kitchen din, da sauri ta fusge hannunta tana fadin"Ni ka ?yale ni, in tafi da kaina" Ta faWa tana daure mashi fuska, Sam Yakasa ce mata komai sai dai kallonta da yake yi.

"Bansan meyasa ka takura rayuwata ba, girki fa kawai na ro?a kabarni In tayasu amma ka hanani, dan Allah menene ala?ata dakai ne? Na lura so kake kana Yin iko dani, Idan don saboda taimakon da kukayi mana ne ay dan Allah ku ka yi ko"? A fadace ta faWa tana zare mashi gray eyes dinta tamkar zata rufe shi da bugu,
Har saida Yaji gabanshi YaWan fadi, sau?inta ma yasan halinta,
"Meyasa ni kadai kake ma haka?
"Saboda ke jini na ce" a zuciyarshi Ya furta maganar
"Kiyi ha?uri Idan na 6ata maki rai, bana son 6acin ranki, ?an uwanki ne suke ta nemanki, bayan haka kamar yarda na fada maki dokar aikin mu ce mace bata shiga hurumin mu, waWannan chefs din da kike gani dukansu a lokacin baya ba mutanan kirki bane, Dayawansu ?an shaye shaye ne da masu bin matan banza, wasun su mugayen ?an ta'adda ne wadanda suka gagari Iyayensu da hukuma, Ire iren su chief Yake kamowa Ya koya masu hankali, Idan suka shiryu sai ya maida su Jami'an Isod..."

Waro ido waje tayi jin Ya ambaci mugayen ?an ta'adda.

"Ba Zanso abun da zai cutar min dake ba, Ha??ina ne kula da rayuwarki Unaisah dan Allah kada ki hanani Yin aikin lada... " in cool voice ya faWa...

Wani irin kallo yaga tana bin shi da shi, kamar akwai wani abu da take son ganowa
Muryarta na rawa ta furta"dan Allah ka cire min face mask din fuskarka inason ganinka"
Girgiza mata kai yayi"zaki ganni amma ba yanzu ba, amma meyasa kike son ganin fuskata"?
"Saboda muryarka, tayi min kama da ta daddyna wallah sai nake ji kamar daddyna ne kai, duk da nasan ma ba shi bane, ina ji araina baya araye ma" idanunta har sun ciko da kwalla.
"Kina ji aranki ni daddyn ki ne" Waga mashi kai tayi alamar eh"
"Ki ?addara aranki cewa Ni ne" ya faWa tare da ru?o arm dinta, Ya janyota jikin shi, haWi da kwantar mata da kanta saman kirjinsa, wani irin sanyine taji ya ratsa zuciyarta, lumshe idanunsa yai a hankali ya sanya hannu tare da zame face mask dinsa, Sumbatar head dinta yai, kafin da sauri ya maida mask din fuskarsa.
Tsawon mintuna biyar cuf suna manne da juna, sai daga bisani ya raba ta da jikin shi, baiwar Allah jikinta yayi sanyi tamkar an watsa mata ruwan sanyi,
Shafa gefen fuskarta yayi da tafin hannunsa"Ina sonki my daughter" murmushi tayi mashi"Nima ina sonka daddy na"


*Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'
'?*

*(KaWan daga cikin na sati mai zuwa idan Allah yakaimu da rai da lafiya, unaisah zatayi waya da Benazir=?
? Garkuwa zaiyi tashin bazata, kada ku bari abaku labarin walimar hateem=??>?#? Ni kaina zumuWin ta nake yi=?%?=?%?=?%?)*

*Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*_ *~
'=؋?BOSSLADIESWRITERS=؋?
'~*_



3,F 'DB/1=؋?
'=?%?


~Takun ?arshe=?%?~



B5) -( 1HE'F3J) :J1 9'/J) (JF 'D3,F'! E9 *7H1'* E9B/)=؋?=ؘ?=??


An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists d'=؋?=ؘ?



Daga al?alamin Boss Bature=؋?
'



__________________________
'?






Har Ya ru?o hannunta za su shiga ciki sai kuma Ya dakata yana faWin "Au namanta, Auntyn ku ummi tana bu?atar abinci ban sani ba, ko akwai abunda chefs suka gama girkawa yanzu"? ya tambaya yana duban ta.

"Akwai naga sun kammala Rice and chicken stew tare da coleslaw hada zobo ma ... " kafin ta ?arasa lissafa mashi yace"Okey, Ki jira ni, bari na shiga ciki in kar6o mata" amsa mashi tayi da toh.

Bayan shigarsa kitchen din ta soma tunanin ko awani hali Garkuwarsu ya ke a ciki? ta yi matu?ar damuwa da shi, ganin shi da take yi a mawuyacin hali ba karamin karya mata zuciya ya ke yi ba, rabon da ta sanyashi a idanunta tun da asuba da su ka shiga yi mashi addu'a, da tunanin shi ta wuni ta bari sai da anjima ta shiga duba shi.

"My babe, I'm back" Muryar Boss man ce ta fargar da ita, da sauri takai dubanta gare shi, Hannayen shi ru?e da handle din wooden tray mai faWi, daga saman shi haWaWdun warmers ne babba da ?arama tare da plates da sauran tarkacen kayan abinci"

Mi?a mata yayi kar6i nan, ta sanya hannu ta kar6a cikin kitchen din Ya koma jim kaWan Ya dawo hannayen shi ru?e da wani madaidaicin faranti mai Wauke da mixed drinks masu sanyi.

Ganin tana kallon shi yasa shi kashe mata ido Waya, murmushi tasakar mashi, a tare suka jera zuwa cikin falon.

Jikin Batool Har Kerma Yake Yi wurin mikewa da wani irin sauri ta nufi Unaisah zata rungumeta, ganin Tray a hannunta yasa ta dakata tana faman Waure mata fuska tace"Ina kika shiga inata nemanki"

"Ina a kitchen fa, Girki Na tsaya taya masu aiki" ta faWa tare da wucewa ta sauke tray din hannunta saman Carpet, Parveen tun da tayi tozali da Abinci takasa samun sukuni, Tafi kowa zalama.

A Plate Batool ta zuba ma Ummi abincin ta hada mata da pineapple juice ta mi?a mata, fuskarta da fara'a ta kar6a tana fadin nagode My babe," a tsanake ta soma Ci.

?aya bayan Waya unaisah ta soma kasa masu abincin tana mi?a masu a plate, bayan ta gama da su itama ta zuba nata tare da Boss man a plate Waya, suka zauna suna ci gwanin ban sha'awa, falon Yayi tsit baka jin sautin komai saina taunar abincin da suke ci...

"Ummi Ina son Yin magana dake bayan sallar magrib" Boss ne yayi mata maganar, amsa mashi tayi da toh.

"Amma wannan Win abincin daren mu ne"? Acewar Parveen, Harararta Naufal Yayi.

"Kusan ?arfe shida na marece, A haka Har kike tambaya, toh abincin dare ne, mu da cin wani abincin sai gobe da safe in Allah yakaimu" javed ne Ya bata amsa Yayin da yake kur6ar lemu me sanyi.

"Ba'a magana idan Ana cin abinci," Boss ne ya faWa yana duban su.

"Dariya fa da murmushi suma ba'ayi"?

Jemimah ce ta jefa mashi tambayar yayin da take cunkusa abinci abaki tana tauna.

Dariya suka sanya gaba Wayansu cikin raha.

"sajeed Ina wayata"

Dafe kai Yai da hannu Waya"Am sorry sister, Na cinye maki chargy, bansan ko kina da charger ba"

"Akwai charger bani wayar" da sauri ta mi?e taje gaban sofa din da yake a zaune, Wayar Ya zaro daga trouser pocket nasa ya mi?a mata ita.

Tasa hannu ta kar6a, kafin ta nufi bedroom dinsu, shigarta keda wuya wayar hannunta ta soma ringing, tana kokarin Waga Wayar ta kashe kanta kamar tayi hauka saboda ta gane number da suka kirane ita da sajeed.'
Cikin takun sauri ta nufi backpack din su, ta buWe ta dauko cazar wayar ta jona a socket, akan idonta wayar tayi haske alamar ya Wauka, lumshe idanunta tayi tare da jingina bayanta jikin gadon, zuciyarta a cike fal da tunanin shi.


*=؋?NAZLI=?Q?*

Sautin daddaWan kiWa ne da ke tashi a katafaren gym room (Wakin motsa jiki) da ke a gidan prime minister, an ?awata shi da manyan injinan motsa jiki, a tsaye take saman thread mill tana gudu cikin shiga ta kayan motsa jiki, sport bra tare da short launin black colour, sunyi bala'in yi mata kyau, sun bayyana farar fatarta sol ko kwarzane babu, tamkar bata ta6a yin rarrafe ba arayuwarta saboda hasken fatarta harta gwiwar ?afarta tayi jawur da ita, dirar mace doguwa ga kyan sura, ta Waure lallausar ba?ar sumar kanta sai sal?i take yi da she?i ta sauko har saitin waist din ta, gaba Waya ta tattara nutsuwarta akan abun da take yi, sautin music din ba ?aramin ni'ima yake samar mata ba, kyawawan idanunta na akan tan?ameman madubin dake manne da bango, zufa ce ta soma tsastsafo mata ta ko'ina ta ji?e sharkaf da ita, babu alamun gajiya atattare da ita, daga gani ta ?ware a 6angaren gym.

Bakomai ne acikin zuciyarta ba, face zallar begensa, duk yadda taso ta hana kanta tunawa da shi abun yaci tura, tayi tunanin zata iya sarrafa zuciyarta wurin hana ta tunaninsa sai dai abun yaci tura, a kowani da?i?a son shi ?ara ninkuwa yake yi a zuciyarta, ga dukkan alamu Nazli batasan menene So ba, ko da yake girman kai da izza sun hana ta gane cutarwar da take yima kanta, shiyasa ta kasa mi?a wuya"

Tunanin shi ne ya haifar mata da jin Kasala, ba arzi?i ta dakata da motsa jikin, ta kai hannu ta Wauki short towel fari ?al ta soma tsane jikin ta da shi, bayan ta kammala fitowa tayi daga gym room din ta nufi bedroom dinta, kai tsaye ta shiga bathroom domin yin wanka.

Shigowa Wakin Yazrin tayi cikin shiga ta riga da wando black and white, tayi rolling veil akanta, hannunta ru?e da wayarta.

Ganin babu ita a dakin yasa tayi tsammanin ko ta fita ne har zata juya ta juyo motsin ta a toilet da sauri ta la6e a bayan labule.

Gently ta zuro ?afafunta dake sanye cikin slippers, bathrobe ce a jikinta fara ?yal, hannunta Waya ru?e da towel sai faman tsane sumar kanta take yi.

Yazrin dake a la6e bayan labule, wayarta ta danna ta shiga camera ta Wage labulen a hankali ta soma Waukar Nazli video batare da sanin ta ba.

Dressing mirror ta nufa cikin takun qasaita, wasu tsadaddun mayukan gyaran jiki ne asaman mirror din, bayan ta zauna ta soma bin ko'ina tana shafe shi a tsanake, kafin ta dauko bakhhoor burner ( turaren wuta) ta soma turara jikinta da sumar kanta, komai nata cikin aji take yin shi, Nazli macece mai tsafta ga son gayu, kuma ma'abociya son ?amshi.

Duk wani motsinta, Yazrin na kallonta ta cikin camera, bayan ta gama gyaran jikin nata, closet ta nufa jim kaWan ta fito, har ta canza kayan jikin ta zuwa kimono robe, yazrin da ke ta daukar ta video kayataccen murmushi ne kan face dinta, aranta ta ayyana ukhty Nazli badai iya gayu ba, bata gama zancen zucin nata ba, taga Nazli ta haye saman Royal bed dinta hannun ta ru?e da wayarta, bakomai take kallo ba face hotonsa, har zooming dinshi take yi da zira ziran yatsun hannunta, hoton da take kallo tsohuwar ajiyace a kalla yakai shekara biyar, lokacin yakai masu ziraya a canada, ba tare da sanin shi ba ta dauki hotan, dama duk in yaje basa jituwa da Nazli, har ya bar ?asar basa sakarma juna fuska kai kace makiyane, Yazrin ce kadai suke mutunci da juna, kuma a lokacin suna matu?ar ?aunar junansu, amma izza ta hanasu bama juna kulawa sai dai su yi magana ta text message, tamkar basa a gida Waya.

fita tai daga gallery ta shiga wurin messages dinsu
Har ta rubuta "I miss u.... ' sai kuma ta goge, zuciyarta na raya mata zubda aji ne ta nuna ta damu dashi, shi ne yakamata yafara yi mata magana
Jefar da wayar


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login