Showing 258001 words to 261000 words out of 298130 words

Chapter 87 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

Hankalinsu Ya kwanta sosai, Yanzu basu da sauran damuwa, har yanzu junaid bai farka daga bacci ba, maganganun da sukayi baisa ya farka ba, wani irin bacci yake yi mai nauyin gaske.

_________________________________
'?

*UNAISAH ANGEL=ؓ?*

Tana a zaune tsakiyar Bedmattress dinsu, kayan baccin jiya ne a jikinta riga da wando da alama ko wanka batayi ba, gaba daya hankalinta na akan notebooks din da ta jera kan katifar, ta sanya farin glass a idanunta kamar wata malaman makaranta, ta ru?e red pen a hannunta, ta nutsu tana dudduba notebooks din data kar6a a hannun su Parveen, Assignment Win da ta basu jiya shine yau take dubawa, ta rasa gane me suka rubuta, duk jagwalgwalo ne, wani rubutun kamar na ?an china wani shigen na thailand, tun da tafara checking note books din fuskarta Wauke da murmushi wani lokacin saita kwashe da dariya hada kifawa kan katifa ba karamin nishadi suka sanyata ba, ta fahimci kwata kwata basu gane abunda take koya masu, kwakwalwarsu bata daukar karatu, bayin Allah sai taji ta karajin tausayinsu da kaunar su.


Motsin buWe toilet door ne Yasa ta Wago dakai ta dubi kofar, Batool ce ta fito daga ciki, ta sanya bathrobe kafafuwanta sanye da slippers, ta nannaWe sumar kanta da farin towel, dakatawa tayi da yin tafiya ganin irin kallon da Unaisah ke yi mata duk saita sha jinin jikinta, da sauri ta bi kanta da kallo don ta ga ko tayi wani abu badai dabai ba, ganin lafiyalou babu wani aibu yasa tace"Sister, meyasa kike kallona? Akwai wani abu ne"? Murmushi ta Wanyi tare da girgiza mata kai"bakomai wlh, You look so gorgeous, like a pearl" kayataccen murmushi Batool ta saki har dimples dinta suka lotsa, taji dadin yabon da unaisah tayi mata.


"tun dazu nake jira ki fito nima in shiga inyi wankan," ta faWa tare da saukowa daga kan gadon ta fara tattara notebooks din ta Waurasu kan bedside drawer.

"ki zauna ki jira ni, idan na fito zan za6a mana kayan da zamu sanya, har make up zamuyi" dadine ya lullubeta"amma pls kada ki daWe"
"Toh" da sauri ta nufi mirror chair ta zauna tana jiran fitowar ta.


Tsawon mintuna kafin ta fito daga toilet din, tayi Waurin gaba da towel fari, ta naWe sumar kanta da towel kamar yadda Batool tayi...tsayawa tayi tana kallon batool ganin ta daura kanta gaban mirror idanunta arufe alamar bacci takeyi da alama taji dadin wankan da tayi shiyasa ta 6uge da bacci


Karasawa tayi gaban mirror din ta Wauko hairdryer ta jona ta a socket, takai hannu ta tum6uke towel din da batool ta Waure kai da shi, ta saita hairdryer din akanta iska ta fara busowa buuuuu a firgice Batool ta farka tana kokarin buge dryer din hannunta.


Dariya Unaisah tayi"Sorry na katse maki baccin ki, inaso na gyara maki gashin ne naga kin wanke shi, ajiyar zuciya ta sauke tare da jingina bayanta jikin kujerar ta dafe saitin zuciyarta da hannu"kin bani tsoro sister, wallahi nayi azan wani mugun abunne"

Still fuskar Unaisah da murmushi ta cigaba da cakuWa sumar kanta tana busar mata da ita


"Duk in na tuna farkon haduwar mu a prison, sai inji na kara kaunarki a zuciyata, saboda kin so ni a lokacin da kowa ke guduna, bakisan wacece ni ba, amma ki ka kirani da sunan sister dinki, duk da irin ?yarar da nake maki hakan baisa kin juya min baya ba, har saida kika dasa min kaunarki a cikin zuciyata"

Murmushi Batool tayi"nima har yau idan na tuna farkon haduwarmu sai inji na kara kaunarki, abun da ya daure min kai a lokacin ya kuma bani mamaki, irin masifar son da nake yi maki, wallahi ko yan uwana da muka taso atare da su tun kafin mu mallaki hankalin mu ban yi masu irin son da nake maki ba, Allah ya jarabce ni da kaunarki a zuciyata..." ta fada tare da runtse idanunta.
Unaisah dake kallonta ta cikin mirror, tuni taji kwalla ta cika idanunta wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta..
Shiru sukayi na wani lokaci kafin batool ta ce"sister akwai wani abu dake damuna"!
"Menene"? ta tambaya tana kallon fuskarta
Cikin sanyin murya ta furta"Danish, wallahi na damu da shi, bansan meyasa ya canza mana ba, ba kamar lokacin da muna a prison ba, gaba Waya, baya son kowa yaje kusa dashi, ko magana nayi mashi dakyar yake amsa mini, har tambayar shi nayi meke damun shi yace min bakomai..." yanayin yadda tayi maganar tamkar zata fashe da kuka..
"Hatta su Haris sun fahimci baya son suna zuwa dakin shi, shiyasa suka janye jikin su, ni so nake naji idan wani abu muka yi mashi sai mu bashi hakuri ya yafe mana" shiru unaisah tayi batare data iya furta komai ba, Dama tasan dole su damu da halin ko in kulan da yake nuna masu, batasan meyasa yake takura rayuwarshi ba, kwata kwata baya son kowa ya ra6e shi in ba ita ba, yanzu da suka samu sa6ani atsakanin su abun Ya ?ara ta6ar6arewa, har cikin ranta bata jin dadin hakan

Kokarin kwantar mata da hankali tayi"pls kada hakan Ya dameki, sai kace bakisan halin shi ba tun a prison, dama can shi ba mai san shiga mutane bane, kinfi kowa sanin halin danish, baya son hayaniya, shi indai zai samu gado ya kwanta yayi bacci toh bashi da wata damuwa, ki daina tunanin ko kunyi masa laifi ne, wlh babu abunda kukayi masa abun a jininsa yake, kuma bawai ya daina damuwa daku bane, kuna aran shi" ajiyar zuciya Batool ta sauke, kalaman unaisah sun kwantar mata da hankalin ta.


Bayan ta gama gyara ma Batool gashin, ta zauna itama ta gyara mata nata daga bisani Unaisah tayi masu make up, powder suka shafa da lip gloss mai kyalli launin pink.

Bayan sun gama suka koma gaban closet Win su, inners suka fara sanyawa, Unaisah ta Wauko mata sabuwar bra ta mi?a mata don ta sanya ta kar6a tafara kiciniyar sakata kamar zatai dambe saboda bata saba ba, batasan ya zata sakata ba, dariya unaisah tayi"bari na taimaka maki" ta faWa tare da ru?o hannun bra Win ta sa?ala mata shi, ajiyar zuciya ta sauke da sauri ta koma gaban mirror tana kallon kirjinta, Yau ne karo na farko data fara sanya bra, tayi mata cuf cuf yadda kasan wadanda suka Wauko bras din sun san size din ta.

Unaisah dake kallonta ji tayi dama ita, yamutsa fuska tayi"idan kin kammala kallon madubin ga kayan da zaki saka nan na zabo maki" ta faWa tare da daura mata su kan gado.

Batare da bata lokaci ba, kowan nan su ya sanya kayan shi, tsayawa sukayi agaban mirror suna kallon tsantsar kyan sukayi
gaba Wayansu Long sleeved gown ce a jikinsu launin Ice blue sai kyalli take da Waukar ido, ga wata hadaddiyar Silver necklace da suka saka a wuyan su, yayin da wrists din hannunsu ke asanye da Beaded Bracelets, sun saki curly hair dinsu ya lullu6e gadon bayan su, yadda kasan wadanda zasu halacci gasar miss word su kansu sun jinjina ma haWuwarsu, sun tasa madubi gaba sai jujjuya jikinsu sukeyi.

Saida suka gama kallace kansu kafin unaisah ta dauko masu fragrance set suka fara barin ruwan turare ajikinsu saida kamshin ya gauraye dakin su tukunna su ka dakata da shafa shi.

"Wlh munyi kyau, Allah Ya zuba mana ruwan kyau sister" batool ce ta fada tana yarfa hannayen ta,
murmushi unaisah tayi tana kallon kanta ta cikin mirror
"Sai yau na kara ganin kamanninmu Allah, dukanmu tubarkalla dogaye ga dogon hanci, Wan bakin mu heart shaped, gaskiya mungode ma Allah..." proudly ta faWa
"Bari na dauke mu hoto" da sauri ta dauko wayarta dake ajiye kan pillow, ta dawo kusa da batool suka hada kai ta fara daukar su pics har kusan kala ashirin..


"Bari inje in nuna ma aunty ummi wankan dana dauka nasan zata ruWe da kyawuna" da gudu ta fuce daga Wakin hannayenta ruke da bazar rigarta kamar wata amarya, har ta fuce daga dakin unaisah bata daina kallonta ba har saida phone dinta ta fara ringing kafin ta kau da idonta, screen din wayar ta duba ganin sunan My man yasa ta Wan yi murmushin gefen fuska kamar yasan jiran kiran shi takeyi girman kai ne ya hana ta fara neman shi, zama tayi daga gefen gadon ta Waga kiran tare da kara wayar a kunnanta


Tayi shiru bata ce komai ba, tana jiran jin me zaice mata.

"My Angel..." bai ?are maganar ba ta katse shi da cewa"Wazu na tura maka message, nace ka sauko down muyi breakfast why didn't you come?"

Ta faWa tana haWe fuska kamar tana agaban shi.


Softly ya furta"Naga sakon da kika tura min, amma ban fahimci me kika rubuta ba, shiyasa ban zo ba" jikinta ne yayi sanyi lakwas duk sai taji ba dadi

"Meyasa baka kira ka tambayeni me na rubuta maka ba? Shiru yayi bai bai tanka mata ba.

"I have no answer,"? Still baice mata komai ba.

"Okey, kayi breakfast dinka"?

Sai lokaci taji ya Wan sauke ajiyar zuciya"nayi, Haris ne ya kawo min adaki"

Lumshe idanunta tay, wani irin yanayi take jin kanta, Sautin muryarshi ba karamin rikita ta ya ke yi ba, A hankali ta kwantar da bayanta jikin pillow, dadin muryar shi take ji, idan suna yin waya har bata son suyi sallama da juna


______________________________
'?

Lokacin da motar dr shureim Ta biyo kan titin Obie Estate tun kafin su karasa Benazir take bin ganin da kallo yau ne karo na farko da ta fara zuwa, ta ruWu da ganin haWuwar katafaren entrance gate din dake abuWe ga wasu fusatattun sojoji dake tsaron ?ofar cikin taku na majiya karfi suke kai komo abakin gate din sun kasa sun tsare babu mahalukin daya isa ya ?etare kofar batare da an basu izni ba.

Hatta dr shureim bai ta6a zuwa ba, ya dai san estate din amma bai ta6a shiga ciki ba.

rage gudun motar yayi slowly yayi parking dinta gefe guda, don yasan ba lallai su barsu su shiga ciki ba.

."Anila kina ganin zasu barmu mu shiga"? Benazir ce tay mata maganar tare da dubanta

"Eh, amma dole saida iznin wani daga cikin mutanan gidan," ta fada tare da daukar wayarta daga cikin handbag, A hankali ta kwantar da baby junaid kan seat ta dubi dr shureim"bari na kira daddyn azeezaty din" amsa mata yai da toh, ta bude murfin motar ta fito daga waje ta danna ma shi kira, bayan ya Waga ta kara wayar a kunne.

"Taj, munzo yanzu haka muna a bakin entrance gate na estate din"

On the other hand taj yace"tare da wa kike zo"? Lokaci daya taji gabanta Ya fadi, tunawa da gargadin da sukayi mata sam ta manta.

Dakyar tay karfin halin ce mashi"tare da Benazir, sai yayanta dr shureim shine ya kawo mu..." bata kare maganar ba taj ya furta"why Anila? Why? Kin manta kashedin da chief yayi maki? Akan me zaki zo da su gidan nan? Ke kadai fa nace kizo saboda Angel tana son ganin junaid"

Hankalin ta ba karamin tashi yayi ba duk tabi ta rude, ta fahimci ranshi ya 6aci

"Kina atare da su ne"?

"A'a na fito daga cikin motar ni kadai ce, Zanyi maka bayani, nasan zaka fahimce ni"!

Shiru yayi yana sauraron ta

cikin sanyin murya tace"ka yi hakuri idan na bata maka rai, nasan ban kyauta ba, amma ba yadda zanyi ne, bazan iya jure ganin Benazir cikin mawuyacin hali ba, wlh baka ga yadda ta koma ba, saboda rashin Unaisah bata da kwanciyar hankali, ko abincin kirki bata iya ci duk ta rame, Kai kace min da zarar ta dawo hayyacin ta, in sanar da ita cewa yarta ce, yanzu tasan komai..." bata kare maganar ba, Taj yace"kina nufin kin fada mata har abunda ya faru da mu"? Yamutsa fuska tay tamkar zata saka mashi kuka tace"na faWa mata, amma na gargadeta akan kada ta bari kowa yasan kuna araye, sannan nace mata kada ta bari unaisah ta gane itace mamanta kamar dai yadda kukayi mana bayani haka itama na sanar da ita, kuma tayi min alkawarin ba zata sanar da kowa ba"

"yayanta fa kin fada mashi? Shiru tayi gabanta na faduwa
Har saida ya sake maimaita tambayar da yayi mata kafin tace"A'a bai sani ba, mun dai fada mashi zamu zo gurin Azeezaty ne, kuma kasan dr shureim bai son ka ba, bazai iya gane komai ba, balle shi da bai cika shiga sabgar da bata shi ba wlh baida matsala, mutunne mai kamun kai"

saida takai aya kafin yace"Anila na fahimce ki, amma Bana so Benazir ta yi wani abu da zaisa unaisah ta gane cewa mahaifiyarta ce, pls komai ya tafi yadda muka tsara shi, idan kika bari aka samu matsala ke da chief ne"


"In sha Allah baza asamu matsala ba, zamu kiyaye"

Tana jiyo sautin ajiyar zuciyar shi"okay, zanyi magana da chief, ku ?ara hakuri," amsa mashi tay da toh, bayan sunyi sallama ta buWe murfin backseat ta shiga daga ciki ta zauna tana faman sauke ajiyar zuciya, atare dr shureim da anila suka kalle ta

"Ya ake ciki"?

Murmushi ta danyi tare da kallon benazir tace"yace mu jira, za'a bamu iznin shiga" ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke.

Dr shureim yace"junaid har yanzu bai farka ba, ko dai kin bashi sleeping pill ne" yar dariya tayi"a'a wlh, nima nayi mamakin baccin shi kamar wanda yasha ?waya, may be ko dan jiya bai samu isasshen bacci bane..." ta faWa tare dakai hannu ta shafa gefen fuskarshi.

Benazir tace"Allah nafara gajiya da jira, Allah yasa kada su shanya mu awaje, nifa na?osa naga babyna" cike da zolaya dr shureim yace"bari maman babyn taji kina kiran sunan ?arta da sunan taki, kotu ce zata rabaku" dariya sukayi gaba dayan su.

Kafin wani daga cikinsu Ya ?ara furta kalma, Suka ji anyi knocking window glass din motar

da sauri dr shureum ya sauke glass din

Wani soja ne tsaye fuskar shi a murtuke ba annuri ya furta"Who is Anila?" Yawu ta hadiya muryar ta na dan rawa tace"I am sir"

"Okay, ku shiga daga ciki, an baku izni" kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, dr shureim ya tada motar ya nufi drive way din da zai sada su da cikin estate Win, Anila ce ta dinga nuna mashi hanyar da zai bi har suka karaso gidan chief, basu sha wahala ba, motarsu na karasowa bakin gate din jami'an dake tsaron shi suka basu iznin shiga ciki bisa umarnin mammallakin gidan hakan na nufin an san da zuwan su, tun da motarsu ta shiga benazir ta ke ta jinjina kai wato sunyi mamakin haduwar katafaren villa din, daga gefen wani stunning fountain dr shureim ya tsayar da motar.

Rungume baby junaid anila tayi akan kirjinta, ta buWe murfin motar ta fito, kafin dr shureim da Benazir suka fito daga ciki, A hankali suke karewa tamfatsetsen ginin kallo, ba su ta6a zaton za'a samun daular data kai ta Alhaji musa haduwa a birnin abuja ba, sai gashi yau Allah ya haWasu da gidan director general Of Isod.

Jikin motar suka jingina bayan su, kowa da abun da yake sakawa aran shi, musamman Benazir ta kosa ta ga taj da Angel dinta murmushi kawai take saki ita kadai tasan dadin da take ji

"Bani junaid din in ruke maki shi" mi?a mata shi anila tayi bayan Benazir ta kar6e shi ta rungume a kirjin ta, Jami'an dake kai komo sai kallon su suke yi.

"Ina zamu nufa"? Benazir ta fada tana kallon Anila, tayi shiru saboda batasan ina zasu dosa ba, har ta yanke shawarar kiran Taj, kwatsam Horn din mota Ya karaWe kunnuwan su, kusan atare suka dubi hadaddiyar motar dake tunkaro kirar black Mercedes


Agaban su motar tayi parking, sun ?ura ido suna jiran ganin wanene mamallakin ta.

Ta ciki aka buWe car door din, gently ya fito daga ciki gaba daya suka bi shi da ido, yana sanye da kayan kakinsu na isod ya rufe fuskan shi da mask, zagayawa yai ta other side Win motar ya buWe murfin, slowly chief ya fito daga cikin, hannun shi ru?e da wayar shi, fuskarshi sanye da face mask, gaba daya dr shureim Ya kasa dauke ido daga kallon su, musamman Benazir gabanta har faduwa yakeyi gani take kamar taj ne sai dai takasa gasgata hasashenta saboda face mask din dake akan fuskar shi yasa ta kokwanton anya shi ne? sai kallonshi take yi shi kuwa ya haWe fuska yama ki yarda su haWa ido da juna don kada ta samu sararin da zata gane shi ne, Hankalin Anila ba karamin kwanciya yayi ba, aranta ta ayyana ashe ma suna atare da chief din tasan already ya fada mashi kwa6ar da tayi masu, fatanta Allah yasa kada ya tuhumeta.

Cikin girmamawa Anila ta gashe da su, chief ya amsa mata, dr shureim Ya mika masu hannu sukayi musaba a mutunce suka gaisa da juna.

Anila ta lura da taj, dama tasan za'a rina, ita ta gane shine kuma tasan saboda Benazir ya sanya face mask, sannan yaki tanka masu don kada taji muryar shi.


"Ya jikin naki" muryar chief ce ta katse mata zancen zucin nata, da sauri ta kalle shi har saida taji gabanta ya fadi, kwata kwata bata kalli fuskar shi ba, sai da yayi mata magana, ta so ta ruWe sai taji kamar muryar Zaki.

jin tay shiru bata amsa ba yasa Aneelerh tayi saurin ce mashi"jikinta da sauki, Alhamdulillah" A hankali ya dubi taj sarai ya fahimci dagangan ya?i magana saboda ex-wife dinsa, ita kuma baiwar Allah ta tsareshi da ido saboda ta gane shi ne.."
"Bismilla..." ya fada tare da nuna masu walkway din da zasu bi

Gaba yai tare da taj su Aneelerh suka bi bayansu, baiwar Allah Benazir ta zama kamar mutun mutumi, jikinta duk yai sanyi la?was cikin muryar raWa tace ma anila"taj ne ko"? Jinjina mata kai anila tayi" shine amma kiyi hakuri dan Allah, kada ki sanya damuwa aranki, har yanzu yana akan dokin zuciya ki bashi lokaci nasan zai kula ki." hawaye ne suka cicciko idanunta, ganin shi da tayi ya fama mata ciwon son shi dake a cikin zuciyarta.


Gaba Waya ya canza mata, ba kamar taj din da ta sani bane ada, Ya zama babban mutun dashi, ga kyawun sura da cikar kamala, har wani ?warjini yayi mata, lallai da da yanzu ba Waya ba, cos ba zata taba manta yadda ta azabtar da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login