Showing 27001 words to 30000 words out of 298130 words

Chapter 10 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

family din nan"

Girgiza kai hajjaty tayi"a'a pravin, bana tunanin hakan, Ina kyautata mashi zato, saboda shi aminin obinna ne, kuma yajima yanayi ma family din nan hidima, gaskiya Imam malik bazai iya yarda ahaWa baki da shi don cutar da familyn obinna ba"

Ta6e baki pravin yai kafin yace"hmm bakisan halin malaman nan ba, yawancin su fuska biyune dasu, A fili musa a zuci fir'auna, duk wanda fa kika ga ya ra6i familyn obinna ba alkhairi bane ya kawo shi"

"Kana nufin hada mu kenan?" Hajjaty ta jefa mashi tambayar
da buWar bakinsa sai cewa yai"ai mu mun riga da mun zama jini Waya da su, ina magana ne akan ire irensu Imam malik masu zuwa kar6ar zakka"

Shiru hajjaty tayi tana nazarin maganar shi, kafin tace"yanzu shi yaron yana agidan owais, tare da sauran yaran daka fada min"?

"?warai kuwa, Ya kawo mugun abu ya ajiye agidansa, babu fa wanda yasan yazo ?asar nan, shigowar sirri yayi, kedai kawai Allah ya shiga tsakanin mugu dana gari amma fa akwai matsala idan har basuyi gaggawar Waukar mataki ba......" ya faWa yana mai nuna damuwarshi.

Ru?o hannayenta yai acikin nashi"My wife, Ki bani haWin kai don ganin mun taimaki ahlin nan kodan saboda halaccin da su ka yi mana, Inaso muyi masu gwanintar da zasu yi alfahari da mu wata rana" wasa wasa pravin yadinga tunzurata har yasamu nasarar shawo kanta.

Cikin sanyin murya tace"In sha Allah, zan baka haWin kai mijina, zamu haWa hannu don ganin mun ya?i duk wani mugu dake da mummunar manufa akan zuri'ar baba Obie" da ?warin gwiwa ta furta maganar, babu wasa a kalamanta.

Wani irin daWine Ya ziyarci zuciyar pravin yayin da yake kallonta.

"Zan tayasu da addu'a, ubangiji Allah Ya kare su daga sharrin ma?iya da mahassada, Ya Allah duk wani mai mugun nufi akan zuri'ar baba Obie, Ya Allah Ka toni asirinsa, ka hana shi zama Lafiya, Bayin Allahn nan ni ban ta6a ganin mutane masu kyakkyawar zuciya irinsu ba, amma ahaka wasu bakin ciki su ke yi da ci gabansu......" har cikin zuciyarta take furta maganar, don ita harga Allah tana ?aunar familyn baba Obie, tana matu?ar sonsu bata son duk wani abu da zai cutar dasu koda kuwa Hajiya saratu ce.

"Yanzu abunda za'ae, kiyi sauri Ki yi sallar, Idan Kika Kammala ki Wauki wayarki ki tafi second falo, ina da tabbacin acan zasu zauna suyi tattaunawar, ki riga su zuwa ki sa?a wayar inda ba zasu gani ba, bayan kin danna recording, Inyaso daga baya idan suka tafi saiki koma falon ki Waukota ki kawo min, yaya sharafuddeen ma Yazo gidan, naji jiniyar shigowar motocinsu, Har le?awa nayi ta window naganshi"

Amsa mashi tayi da toh, ta nufi closet din kayanta ta dauko Hijab ta tura a jikinta, saida ta kabbara sallah tukunna Pravin ya shiga toilet domin yin alwala, a Wakin yai sallar magrib da isha'i kafin Ya gama sallar, tuni hajjaty ta fuce daga Wakin, zama yayi kan darduma yana ta yin sa?e sa?e acikin zuciyarshi,

Kamar yadda ya tsara mata haka ta aiwatar, tun kafin su shiga falon hajjaty ta riga su zuwa ta kunna recording da dabara ta shiga falon kamar tana gyara shi, a hankali ta ajiye wayar a karkashin sofa table, kafin ta fito daga falon ta nufi kitchen domin shirya masu abun da zasu sha.

Bayan tafiyar hajjaty, da ?an mintuna Gaba Wayan su suka shigo Second Falo din wanda ya kasance na musamman dake A gidan Baba Obie, an wadata shi da Luxury Furniture ba kasafai suke amfani da shi ba, sai Idan za su yi zaman tattaunawa tukunna ake buWe shi, wani irin ni'imtaccen sanyin A.c ne ka ratsa cikinsa, dare ne tamkar da rana saboda wadatattun Chandeliers masu haska ko'ina sako da Lungu, Idan ba agogo Ka kalla ba ko sararin samaniya ba zaka ta6a gane dare ne ba a gidan baba Obie.

Bayan kowan nan su ya samu wuri ya zauna saman sofa, Sheikh Imam ya fara buWe masu taron da addu'a, kafin daga bisani, baba Obie yaba Owais damar yi masu bayani dangane da Yaran da yake ru?o a hannun shi.

A tsanake Ya labarta masu tun daga farkon zancen har zuwa karshe kamar yadda Ya fada masu Wazu.

Mutum Waya ne baisan da zancen ba, Lokacin da abun ya faru baya agidan sai yanzu yake ji daga bakin Owais.

"Owais dama bayan yaran dake acan gidan da Jazz yake Aiki Akwai wasu A gidan ka" Fuskar Sir mubarak da alamun ruWu ya furta maganar.

Jinjina mashi kai Owais Yai alamar Eh, nan take ya yanke shawarar sanar dasu dangane da abun da ya faru tsakanin shi da jazz jin cewa sun san da zancen yaran, bayan ya labarta masu, kowan nan su ya jinjina ma lamarin sai dai har yanzu mutun uku basu Goyi bayan zaman Yaran a estate din ba.

Sheikh Imam ya Waura da cewa"naji daWin taruwar da mu ka yi anan kuma ina fata zamu samu maslaha, da farko dai Yaran ba masu cutarwa bane, ba abun da ku ke tsammani bane, Ni shaida ne akan hakan, Mutane ne su kamar kowa, hatta shi kan shi Yaron da yake rikiWa cikakken mutunne, kamar yadda Owais ya faWa maku Ni da kaina na duba shi, kuma nayi magana da shaiWanun jikin shi, wata?il ko dan baku ta6a ganin mutun ya rikiWa bane akan idon ku, shiyasa abun Ya ruWar daku, Amma Ni nasha gani akan idona mutun ya rikiWa Koya 6ace Idan muka ja mashi ayar Allah....." ya Wan dakata da yin jawabin yana kallon su, Senate Lateef ya haWe fuskarshi babu annuri ko mis?ala zarratin shi fa yana akan bakan shi.

Duk sun natsu suna sauraran sheikh Imam sai da yakai Aya tukunna Senate Ya fara magana rai a 6ace"Ni bazan ta6a goyan bayan tsintattun Yaran su zauna a family din mu !! Bazai yiwu ba wallahi, Saboda Shi jiya mahaifin mu ya kusa zaucewa adaren jiya bai runtsa ba, Da firgici Ya kwana, sannan itama saratu bata runtsa ba a zaune ta kwana saboda gizan da macijin keyi mata, A haka akeson a ?a?aba mana su a family? ya jefa tambayar yana kallo su sheikh imam babu wanda yai yun?urin dakatar da shi "Ai daga ji babu Alkhairi Atattare da su yakamata aduba maganar ya faWa yana mai ?ara jaddada maganar shi.

Gaba Waya idanuwansu akan shi, sai da ya ?are maganar, His excellency abdul Razak Yace"Ni ban hana ataimake su ba, Amma bazai yiwu su zauna mana a estate dinmu ba, tun da yaran basu da asali, me zai hana a Wauke su akaisu Orphanage home dinmu dake anan garin Abuja, In yaso sai mu dinga tallafa masu, amma fa ban da wannan yaron mai fama da aljanu ba zamu lamunta da zaman shi agidan marayu ba, zai iya cutar da mutane, kawai aware shi shi kaWai yayi rayuwarshi har zuwa lokacin da zai samu warakar lalurar shi"

Tun da suka fara magana Shiekh Imam da chief owais suke bin su da kallo, Shi dai Prime minister ya rasa ta cewa ganin yadda suka ha?i?ance akan ?in amincewa da zaman yaron, Mai girman sharafuddeen ma yana sauraransu sai dai hankalin shi yafi karkata akan Wan uwanshi, ya fahimci hankalin shi ba a kwance yake ba dama shi tul fil azal bai cika son rikici ba mutunne ma'aboci son zaman lafiya bayason hayaniya.

Gyaran murya baba Obie Yai masu, hankalinsu ya dawo kanshi.

"Kun gama magana"? his excellency deen yace"Eh baba, mu kawai Yaron ke bamu son zaman shi acikin estate dinmu, su sauran Yaran ni bani da ja akansu, tun da su lafiyarsu ?alau suyi zamansu agidan owais din ko akai su gidan marayun mu...." kafin Deen ya ?are maganarshi, senate lateef yai hanzarin tarar numfashinshi da cewa"bazai yiwu ba, Nifa ban lamunta da su zauna a estate din nan ba, sannan dole ayanke ala?ar su da danginmu, idan taimakon nasu ya zama dole zamu haWa masu kuWin da zasu ishesu suyi rayuwarsu, shi kuma Prime minister Hateem satin da zamu shiga ya hanzarta barin ?asar nan, zaifi mana kwanciyar hankali, tun da na fahimci idanuwanshi sun makance akan yaron da bai hada ala?a da shi ba"

ya faWa fuskarshi aWaure, yayin da yake kallon Prime minister Yaci gaba da cewa"Sarai kaga abunda ya faru adaren jiya, amma ka kau da idonka, damuwarka akan yaron ce ba akan mahaifinmu ba, maimakon tun da asussuba ka kamo hanya kazo gida donka duba shi ka ga ya yakwana jiya sai ba ka yi hakan ba duk kabi ka zauce akan yaron da bakasan asalin shi ba...."

Tsabar yadda senate ke magana har wani gumi yake fitarta, duk da sanyin A.c na falon, Lamarin yayi mugun Waurewa Sheikh Imam kai sai faman jinjina kai yake yi, maganganun senate ba ?aramin fusata Chief owais su ka yi ba, tun da ya du?ar da kanshi ?asa bai Wago da shi ba, ?o?ari yake yi don ya lallashin zuciyarshi idan ba haka ba komai zai Iya faruwa!!.

Senate yaci gaba da cewa"kai kuma Owais," ya faWa yana nuna shi da hannu"ka 6ata min rai! Meyasa ka ke yin komai gamon kan ka? ba tare da ka nemi shawarar mu ba? ko dawowarka Nigeria Yakamata ka sanar damu, amma sai ba ka yi hakan ba kamar kai ke da kan ka, sannan ka kwaso mana wasu tarkace acikin family batare da ka sanar damu ba, me hakan ke nufi? Bamu da amfani ne ko bamu isa dakai ba ne?" a zafafe Senate Lateef yayi maganar yana duban chief owais, wanda yayi shiru yana sauraron shi batare daya yi yun?urin tanka ma shi ba.

"Allah Ya huci zuciyarku, Na fahimci gaba Waya ranku Ya 6aci dangane da abunda ya faru Jiya Ina mai baku hakuri amadadin Owais" mai girma sharafuddeen ne yayi maganar yana mai tausasa harshen shi.

"Bai kamata kan wannan maganar mu Waga hankulanmu ba, Owais dai muke iko dashi, Sannan Kune manyan Family duk abunda kuka zartar dolen mu ne muyi biyayya akai, ko munaso ko bamu so," Jin maganar sharafuddeen yasa senate yafara sassauta fushin fuskarshi, hatta sauran sun Wan samu natsuwa.

"Baba, Hukunci ya rage naka, Kai muke sauraro duk abunda ka zartar dangane da yaran nan wallahi zamuyi maka biyayya" in a calm voice sharafuddeen ya faWa yana duban baba obie.

Gaba Waya hankali ya dawo kan Baba Obinna, dake zaune kan sofa, sandar shi tana a jingine da sofa hand.

sun ?agara da son jin amsarshi, saboda shi kaWaine mai faWa Aji.

"Mubarak!" da sauri sir Mubarak ya Wago ya kalleshi cikin girmamawa ya amsa mashi da na'am baba.

"Banji kace komai ba"

Murmushin gefen fuska Sir mubarak ya yi kafin yace"Baba, ni bani da matsala wallahi, yaran nan ba akaina zasu zauna ba, owais ne ke kula dasu akan me zan damu? Na yarda da shi kuma nasan bazai ta6a kawo abunda zai cutar da zuri'armu ba, Ni dai inayi mashi fatan Alkhairi duk shawarar da ka yanke zamuyi biyayya"

Chief yaji daWin maganar sir mubarak, dama yasan bazai bashi matsala ba.

"Aminina, naji kayi shiru, inaso naji daga gare ka" baba obie ne ya faWa yana duban Imam malik.

Murmushi ya saki, Yana mai fara'a yace"wannan abu na ku ne na ?an siyasa, Kun san yanda ake jefa ?uri'a waWanda suka fi rinjayi, maganarsu yakamata aWauka, Nidai anawa ganin kenan, Yaro dai bame cutarwa bane, jarabtace ta ubangiji babu wanda yafi ?arfin Allah ya jarabce shi acikin mu, shi kuma owais Jinin ku ne Ku kan ku kun yaba da hankalinsa, ni banga wani abu da zaisa ace za'a yanke ala?arshi da yaran ba yakamata aduba maganar nan" cikin Hikma Imam malik yake yi masu magana, har cikin ranshi baison yaji suna maganar korar yaran daga familyn Obie.

Jinjina kai Baba Obie yayi kafin ya kai dubanshi ga sharafuddeen.

"Meye ra'ayinka dangane da yaran"?

"Baba, Ni bani da matsala, kamar yadda yaya Mubarak Ya faWi, Nima haka, Kafin mu yanke hukunci yakamata mu yi wa kan mu adalci dasu kansu Yaran, Abun da Ya faru da Wan uwansu bayin kanshi bane, Allah ne yake jarabtarsa, gaba Wayanmu musulmai ne kuma munyi imani da ?addara mai kyau ko mara kyau, so yakamata mu kar6i yaran nan hannu biyu mu rungume su, Sannan Yaran nan fa ba muke Waukar Wawainiyarsu ba, ba agidan mu?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? suke zaune ba, Agidan owais suke zaune shi ne ke kula dasu kuma shine ke da alhakin duk wani abu da zai faru, babu yadda za'ai araba owais da yaran nan! Saboda Bincike su ke yi a kansu, Hukumar Sojin america suna da sanya hannu akan case dinsu, bazai yiwu owais ya rabu da su ba...." jin wannan maganar ta sharafudeen yasa senate Waure fuska, gani ya ke yi kamar hada ba?ar magana sharafudeen ya gaya mashi daya faWi cewa agidan owais suke zaune kuma shi ke Waukar Wawainiyar shi, maganar ta sosa ran shi, Deen da abdul razak sun fara aminta da kalaman sharafudeen akan zaman yaran.

Bayan Sharafuddeen Ya kammala maganarshi, Baba Obie Ya ambaci sunan Hateem, A hankali ya Wago da idanunsa waWanda suka kaWa jawur da su, Muryarshi adisashe ya furta"Bani da abin cewa, duk hukuncin da aka yanke baba zanyi biyayya"

Shiru su ka yi na wani lokaci babu wanda ya ?ara furta magana acikinsu falon yayi tsit kamar mutuwa ta gifta.

Shigowa falon hajjaty tayi da sallama a bakinta, hannunta biyu ru?e da faranti daga saman shi Tea pot ce tare da cups, daga bayanta Abla ce tare da Sophia kowan nan su ya ruko tray na kayan abinci, Amsa masu sallamar sukayi cikin girmamawa suka sauke trays din kafin suka gaishe da su sheikh Imam da sauran mutanan falon, da fara'a suka amsa masu, kafin daga bisani suka fuce daga Wakin.

Babu wanda yai yun?urin ta6a kayan abincin, kowa kanshi ya Wauki zafi.

"Aminina, bismillah" Obie ne ya furta hakan harya yun?ura da niyar ya zuba mashi Tea a cup da sauri Imam malik yace"Alhamdulillah, kafin na baro gidan Hateem na cika cikina babu yunwa atare dani,"

Cikin kulawa obie yace"Ban yarda ba, amma tun da kace haka, Bari na zuba maka tea din kasha, nasan zaka ji dadin shi, Hajjaty ce ta haWa shi"

Sheikh Imam na murmushi yace"na fahimci ba ?aramin ji kake da matar nan ba"
Murmushi obie yai batare dayace komai ba.
Owais ne ya mi?e ya nufi tray din ya dauki tea pot ya tsiyaya masu tea a cups din yabi kowan nan su Ya mi?a mashi, ba tare da ya zuba nashi ba ya koma ya zauna.

"Ba za ka sha ba"? Hateem ne yai mashi maganar, Calmly ya furta"bani bu?ata"
Bayan kowan nan su ya kur6i tea din, baba obie ya soma magana yana duban fuskokin su.

"Na yanke shawara....." bai ?arasa maganar ba, ganin yadda suka Wago suna kallonshi Ya fahimci sun ?agara da son jin mai zai ce ne.

"Dangane da abun da ya faru jiya, na ruWe ne shiyasa harna firgice, amma yau da Owais Wina yayi min bayani na fahimce shi, na yarda yaron mutunne kuma ba mai cutarwa bane, tun time da abun ya faru har ya shigo gida na, ya samu damar da zai iya cutar da mu amma bai yi hakan ba, sannan naga ?ar uwarshi taje gare shi ta lullu6e shi da rigarta tana kuka tana rokon shi akan ya canza halittar shi ya zama mutun, nayi mamaki ?aramar yarinya bata ji tsoron tunkarar shi ba a suffar maciji, sannan baiyi yun?urin sarar ta ba, hakan ya ?ara tabbatar min da cewa mutunne da gaske......" wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar Owais da Hateem da sauran masu goyan bayan zaman su, In ka cire Senate lateef donshi har ga Allah bai yarda da yaran ba.

Numfasawa baba obie yai, kafin yaci gaba da yin maganar sai da ya fara kur6ar tea din hannun shi.

"Na amince su cigaba da zama a estate din mu"! A matu?ar ruWe Senate lateef ke kallonshi da tsantsar mamakin yadda ya amince da zaman tsintattu a zuri'ar su, zuciyar shi ta sosu sai dai bai yi kuskuran katse mashi maganar shi ba, wani irin annurin farin ciki ne ya bayyana akan fuskar Hateem da sauran magoya bayan zaman yaran a estate din.

"Amma abu Waya ne ban yarda da shi ba"!! ya faWa Yana Shafa gemunshi da hannu Waya, yayin da idanuwanshi ke akan fuskar Hateem da chief Owais, kamar yadda yake kallonsu haka suma suke kallon shi.

"Hateem, bana so wani abu Ya ?ara shiga tsakaninka da Yaron, babu kai babu shi, ban amince ka taka inda yake ba Har ka koma Canada," Ras yaji gabanshi yai mugun faWuwa, baisan sa'adda ya sauko daga saman sofa ya dawo kan carpet ya zauna, motsa la66ansa ya soma yi da niyar yin magana da sauri sharafuddeen Yai mashi gyaran murya nan take Ya fahimci me yake nufi, ?o?arin haWiye damuwarshi yayi, In a cool Voice yace"Shikenan baba, Na amince, amma dan Allah Ina neman alfarma awurinka" a marairai ce yayi mashi maganar.

"Ina sauraronka"

"Nayi ma Gimbiya mujeedat al?awarin zan kawo yaron gidana don ta ganshi....." da sauri senate ya katse shi"mugun abun zaka kai gidanka? Inda iyalanka suke? Wannan wani irin gangancine"?

Deen yace"yakamata aduba lamarin nan fa, gaskiya ba zamu lamunta ba hauka kake yi da zaka Wauki mutun mai hatsari ka kai gidanka? What if something happens?" he said in a tense voice.

"In sha Allah Ba abun da zai Faru, Nidai kawai ay min alfarmar dana nema" ranshi a?untatace yayi maganar.

"Hateem Kayi ha?uri, tunda Yaron baida lafiya, ba yadda za'ai ma ya Iya taka ?afarshi balle har Yaje gidanka, sai dai Idan Yaji sauki kafin lokacin da zaka koma canada" Imam Malik ne Yayi maganar yana dubanshi

Jinjina kanshi ya Wanyi, ba tare da ya ce komai ba.

Baba obie dake kallon shi ya fahimci babu nutsuwa atare dashi, cikin kwantar da murya yace"Hateem, kada hakan ya dame ka, kasan ina son farin cikin kowan nan ku, ba zanso abun da zai 6ata maka rai ba, dalilin dayasa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login