Showing 189001 words to 192000 words out of 298130 words

Chapter 64 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

kansa ta saita mashi a kunnansa.

"Wow!...." wani Irin kyau yayi mata har bata san sa'adda ta manna masa kiss a cheeks din sa ba, mutumin fa gaba Waya ya fara zaucewa wani irin yanayi yake jin kanshi
Cire mashi headset din tayi, ta aje kan mattress din ta janyo eye glss box din tana danna akwatin nan take ya bude jerin hadaddun glass ne na maza ta dauko wani mai walwali launin blue sky ta zura mashi a idanun shi
Tabarakallahu ahsanul khaliqin shine abun da ta furta
Da tafukan hannyenta biyu ta tallabo fuskarsa ta zuba mashi ido tana kallon
Kamar yadda shima yake kallonta ta cikin glass din numfashin su har yana kokarin hadewa dana juna
"Sai naga ka ?ara min kyau my man, bari na canza maka wani" da sauri ta cire na fuskarsa ta dauko wani glass din black colour ta sanya mashi
"Wow kana kashe ni da kyanka...' ta fada tare da cire mashi glass din ta maida shi cikin Wan akwatin
Ta janyo watchbox ta buWe shi jerin tsadaddun agogunane ?an ubansu

ta dauko Waya ta kamo hannun shi ta soma kiciniyar sanya mashi a wrist dinshi
"Ka wani kura min ido kana kallona kamar yau ka fara gani na" tayi maganar da zolaya...
Lumshe idonshi yayi ba tare daya furta mata komai ba....
"Wohoho Ina gwanin wani ga nawa..My man wlh kai na musamman ne, komai naka na kece raini ne...Kalli hannunka irin na ?an gayu wadanda sukaji hutu..." sai faman santin hannunsa take agogon tayi bala'en yi mashi kyau .....
Sam ta manta da abun da ya faru jiya atsakaninsu ta za?e sai zuba take yi masa kamar aku
"Kin fara period neS'Kamar daga sama Taji Ya furta wani bugu zuciyarta tayi mata, a ruWe ta dago tana kallon shi ido cikin ido suke kallon junaW'S'



*Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'
'?*


*Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*"____________________Boss Bature
'?







Sam ta manta da abun da ya faru jiya atsakanin su ta za?e sai zuba take yi masa kamar aku

"Kin fara period neS'Kamar daga sama Taji Ya furta, wani bugu zuciyarta tayi mata, a ruWe ta dago tana kallon shi ido cikin ido suke kallon juna.
har na tsawon mintuna ba tare da sun kyafta ba, gabanta ya soma faWuwa, gaba Waya ta rasa sukuninta, la66anta sai kerma suke.


Sexy voice dinsa ce ta sake ratsa kunnanta"tambayarki nakeyi, ko ba ki ji me nace ba"? Yawu ta haWiya kutt kafin tayi ?arfin halin furta"meyasa ka tambayeni"?

Lumshe idanunshi yayi kafin ya ware su akan fuskarta"naga canji a tare da ke....." Wan zaro ido tayi da tsantsar mamaki take kallon sa, girgiza mashi kai tay ba tare da ta iya furta wani abu ba

"Tell me the truth, have you started menstruating? I want to know. It's something I've been waiting for a long time." rass Taji gabanta Ya ?ara faWuwa muryarta na rawa ta furta"ni.. Ni ban..ma san kan me kake magana ba..." cikin dabara ta tafara zame jikin ta daga kan gadon, kwatsam Taji Ya dam?i hannunta, Idanu zare ta kalle sa.

"Ki bani amsar tambayar da nayi maki" wani irin ?warjini yayi mata kamar ba man dinta ba, kamar mai jin tsoronsa ta furta"na fara, tun ranar da mukaje dinner din prime minister, amma ya Wauke, a washe garin ranar.. " da?yar ta ?ara maganar, ganin wani kayataccen murmushi gefen fuska daya bayyana akan kyakkyawar fuskarshi, hatta dimple dinsa sai da ya lotsa...

"Amma tayaya akai kasan alamomin mace idan tafara period? Sannan meyasa naji kace abu ne da ka daWe kana jira"! AruWe ta jefa masa tambayar saboda abun ya Waure mata kai.

Matsawa yayi kusa da ita da sauri ta zame hannunta daga ru?on da yayi mata, taja da baya kamar taga wani mugun abu.

"Kamar yadda na faWa maki, naga sauyi atare dake..." abun da ya sanyata aruWani yanayi da tagani atattare da shi, ga wani annurin farin ciki daya wanke fuskarsa.

"My man, Ya kamata na tafi tun da na kawo maka abincin, su aunty ummi suna jirana" adabarbarce tayi maganar jiki na 6ari ta sauko daga kan gadon da?yar ta saci kallon shi suka haWa ido"pls kada ka zauna da yunwa, idan ka kammala cin abincin ka yi wanka, ka sanya sutura a jikin ka, sannan pls ka daina kaWaita kanka aWaki ka dinga fitowa wurin su Haris...." tana magana tana ja da baya, tana kaiwa bakin kofar da sauri ta buWe ta fuce daga gudu.

Sai da ta 6ace ma ganin sa, kafin ya kau da idonsa daga kallon ta, kasa cin abincin yayi saboda bashi Yake bu?ata ba, akwai wani abu da zuciyarsa take muradi, sai dai yasan ba abune mai sau?i Ya same shi ba, wata irin kasala ce ta baibaiyeshi cikin sanyin jiki ya kwantar da bayansa kan mattress din, haWi da lumshe idanunsa.

Nannauyar Ajiyar zuciya Unaisah ta sauke bayan ta sauka downstairs, Hannun ta Waya dafe da saifin zuciyarta, bakomai take tunawa ba face kalamansa da suka tsaya mata arai, yayi matu?ar bata mamaki bata ta6a tsammanin Danish Yana da wayau har haka ba, ko tayaya akai yasan alamomin mace idan ta balaga"!? Ta jefa wa kanta tambayar da bata da amsarta..wucewa dinning tayi zuciyarta cike fal da tunanin sa...


_____________________________
'?


Da marece Hajiya saratu tana a gym room na gidan, cikin shiga ta activewear black colour riga da short dai dai gwiwarta, A hankali take running kan threadmill, ta haWa uban gumi kan fuskarta da jikin ta.

Maganganun da suka tattauna da su zahra ne suka fara dawo mata akanta, Abun Ya tsaya mata aranta, tun bayan tafiyarsu take ta tufka da warwara, tana matu?ar son taimaka masu, but how? Tasan owais mai biyayyane agare ta, komai takeso zaiyi mata, sai dai bata jin girman kanta zai bari ta nemi alfarma agurinsa Kuma bata jin zata iya taka kafarta zuwa gidansa.

"Me ya kamata nayi"? Ta jefa ma kanta tambayar, Farat Waya ta tuna da hajiya laurat! Ita kadai ce zata Iya bata shawarar daya dace.

Fitowa tayi daga gym room din ta nufi part din su.

Tana shiga daki, ta nufi toilet ta shiga, within 15 mins, ta fito sanye da bathrobe, ta zauna kan mirror chair, phone dinta ta dauka ta danna ma hajiya laura kira

Sai da kiran ya kusa katsewa kafin hajiya laura tay picking

"Matar yaya barka da marece?ya kike"? Ta faWa da murmushi akan fuskarta
On the other hand Hajiya laurat tace"Amarya kuma uwargida a wurin praving, lafiya lou, fatan kema haka..."

jinjina kai ta Wanyi kamar tana agabanta

"naji kinyi shiru? FaWamin meke damun ki? Don tunda naga kiranki a irin wannan lokacin raina Ya bani wani abu na damunki"

"Shawara nakeso Ki bani...." ta faWa kamar bata son furta maganar, A hankali ta zayyana mata komai dangane da zuwansu zahra...

"Bansan Ya zanyi ba! Nayi masu alkawarin zuwa gobe zasu ji kirana, nasan sun kwallafa rai, ni kuma Allah bana son in nemi alfarma awurinsa, nasan owais yana da biyayya zaiyi min abun da nakeso amma ina jin nauyin zubda ma kaina mutunci..."

Sautin dariyar Hajiya laurat ne Ya cika kunnanta, nan take ta haWe rai"bana son iya shege, Oh dariya ma na baki? tun da bazaki bani shawara ba, zan kashe kiran"

Da sauri Hajiya laura tace"Am sorry hajiya, kin bani mamaki ne! Kamar kina jin shakkar tunkararsa, Ki aje wani jin kai gefe Waya, Yaron nan Wan yayanki ne, kuma Wanki, kina da iko da shi, ba alfarma zaki nema a gurin sa ba! abun da yakamata shine Ki bashi Umarni, kiransa zakiyi awaya kice mashi yazo inda kike Ya same ki, Idan Yazo ki zauna ki faWa masa komai sannan kice mashi gobe zasu zo ganin yarinyar, baki bukatar wani abu da zai sa girmanki ya zube a idon su...."

tiryan tiryan hajiya laura ta tsara mata komai, tunkafin ta karasa maganar, Hajiya saratu ta fara sakin murmushin gefen fuska, saboda shawarar tayi mata 100% shiyasa take ji da hajiya laurat, matar karshe ce wurin Iya bada shawara..

"I can't thank You enough, Hajiya ta, nagode da shawararki, shiyasa yayana Yake ji dake saboda kin Iya tsara kalami ga iya bada shawara...." sautin dariyar Hajiya laurat ne Ya karade kunnanta
Bayan ta tsagaita da yin dariyar tace"nima naji dadi da kika dauki shawarata, Yanzu faWa min Ya ake ciki game da hajjaty? Har yanzu baki gano komai ba"?
Ta6e baki hajiya saratu tayi"Hmm Matar wayon tsiya gareta kamar dila, yarinyar dana sanya tana yi mata le?en asiri, har yanzu bata gano komai ba, amma tace min tabbas akwai wani abu da take kullawa adakinta, saboda bata son kowa Ya shiga...."

Hajiya laurat tace"munafuka, ay daga ganin ta zatai wayau, kuma wallahi ba wayanta bane akwai wanda ke Waurata akan hanya,..."!
"Kamar ya bangane me kike nufi ba.."?
"Ina nufin ba ita kadai take shirya plan ba, akwai wani dake taimaka mata..." da tsantsar mamaki hajiya saratu take sauraronta, tabbas Ta yarda da kalaman hajiya laurat saboda matar tana da kaifin basira...
Sun jima suna tattaunawa akan hajjaty kafin daga bisani su ka yi sallama.

______________________________
'?


Kusan atare motocin su suka kunno kai cikin estate din,

Bayan sunyi parking, Pravin Ya fito cikin shiga, ta suit, Ya jingina bayan shi jikin motar, Idanunsa akan motarsu twins dinsa, fitowa sukayi kowannansu Ya dauki wankan suit, sun kwaso gajiyar aiki sai faman lumshe idanu sukeyi
Tunkarar shi sukayi da sauri shima Ya nufe su, gaba Waya ya hadesu Ya rungumesu, tare da daura hannayensa abayansu.

"Yau mun dawo gida atare, ya gajiyar aiki" dagowa sukayi atare suka dube shi
"Daddy Ba dadi, wallahi, na gaji, ni fa kasan bana son wahala.." zayn ne yayi maganar,
Zaid Yace"Alhamdulillah daddy, kaima ya gajiyar naka aikin"?
Murmushi yayi kafin yace"ay ni bana aiki, ina da masu yi min komai, illa Iyaka in karshen wata yayi in kwashi Albashina...." kallon juna sukayi da mamaki akan fuskokin su,
Ko ajikinsa Yaci gaba da fadin"tuntuni naso In wayar maku da kai amma kuka ?i yarda, Kunfi so ku yi ta wahala akan albashin da bai taka kara ya karya ba, har atm dina na baku don kuyi irin rayuwar da kukeso amma kuka ki kar6a saboda baku yarda dani ba ko.."
Shiru sukayi suna kallonshi, kafin Zayn yai kafin halin cewa"daddy ta yaya zamu kar6i kudinka? Bayan ba halal dinka bane!! Baka aiki kuma kana kwasar albashi, hakan na nufin haramun kake ci, daddy kaji tsoron Allah, ka riga da kasan hukuncin wanda Ya gina kansa haram..." bai ?are maganar ba, Pravin yayi saurin dakatar da shi ta hanyar Waga mashi hannu, da kakkausar murya ya furta"Enough! Don't you dare repeat what you just said to me!! Gidan ubanwa nake cin haram? duk wani kuWi da nake da su, Hakkina ne ina da goyan bayan waWanda suka Waura ni akan mu?amin da nake da shi. ..." Yana faWin hakan rai a6ace Ya nufi cikin gidan, da sauri zaid yabi bayanshi tare da shan gaban shi.

"Daddy ka yi hakuri, naga ranka ya 6aci, Dan Allah ka yi hakuri da abun da zayn yace maka! ka yafe masa kada ka ruke sa a zuciyarka..."

Murmushin gefen fuska pravin yayi"kada ka damu my son, komai Ya wuce"
Ajiyar zuciya zaid Ya sauke, Tare da ruko hannun daddyn nasu suka shiga parlour.

Zayn dake kallon su har sai da suka 6ace ma ganin shi, kafin ya jingina bayan shi jikin motarsu, kalaman zahra ya fara tariyowa, a lokacin da ta kira shi Yana a office, ya gama watsewarsa tare da abokiyar aikinsa yana akan network shiyasa Ya zazzaga mata masifa son ranshi aranshi ya ayyana ko sun samu shiga estate din? Ta6e la66ansa Yayi irin bai damu din nan ba, Ya wuce Ya nufi cikin gidan

"CHIEF OWAIS=ت?=؋?*

Yana a cikin Katafaren Office dinsa dake a isod Headquater, office Win Ya haWu, an ?awata shi da high-end supplies komai na cikinsa launin blue sky ne kalar da yafi so, office din Yana da mugun tsaro gaba daya na'urori ne ke sarrafa komai na cikin sa.."

DaddaWan ?amshin turarensa Ya gauraya da ni'imtacciyar iskar dake ratsa sa?o da lungu na office din, a yayin da yake azaune kan wata tamfatsetsiyar Excutive chair ?ar ubansu, Ya Waura kafarsa Waya bisa Waya, daga gaban shi luxury table ne mai Wauke da High-end computer da sauran kayan amfaninsa dake a baje kan table din

A hankali Ya buWe idanunsa dake a lumshe, Ya cigaba da operating computer din gabansa,

Adjusting webcam dinsa yayi, kafin ya danna video call Ya dan dakata Yana jira a amsa mashi.

a hankali fuskar commender ta bayyana ta cikin screen din

Murmushi suka sakar ma junansa, Cikin harshen turan ci suka fara magana
"Commander, good to see you, sir," ya faWa tare da sarah mashi da hannu

"Chief, good to see you too," shima ya sarah mashi.

"What can I do for you?"

Numfasawa chief yai kafin yace"I'm calling to extend an invitation to a high-level meeting in Nigeria, dangane da yaran da kuka dam?a mana case din su" Ya ?are maganar, Cike da sa ran zai amsa mashi

Jinjina kai commender din Yayi na Wan wani lokacin Kafin Ya furta" okey, What's the current situation?...bayani ya fara kora masa dangane da halin da ake ciki na binciken prisoners.

Tun da ya fara commender Yake Wan jinjina kanshi alamar gamsuwa, bayan ya ?are maganar yace"yanzu wani mataki zaku fara Wauka"?

Chief yace"That's what we'll discuss during the meeting"

"Tunani mai kyau, zanyi magana da na sama dani, idan har na samu goyan bayan su, zamu halaccin meeting din, yaushe ne kuma a ina za'ayi"?

"Upper week, in Abuja. I'll send over the details. Thank you, Commander..." Ya fada tare da sara ma shi da hannu.. Shima commender din Ya sara mashi
bayan sunyi sallama Ya kwantar da kansa jikin kujerar

"DDG Is coming" Muryar na'ura ce ta ratsa kunnansa, A hankali Yakai idonsa ga duban Glass door ta office dinsa wadda ke kokarin zuge kanta

Big guy ne Ya shigo sanye Cikin kakinsa, Cikin girmamawa Ya sara mashi.

"Sannu da aiki Yalla6ai, Na ji shiru baka fito ba, ko baka lura da time ba ne"? Kallon agogon hannunsa yayi ?arfe biyar na marece, har time din ta shin sa yayi bai lura ba.

"Have a seat"

Zama big guy yai kan kujerar dake fuskantar chief kamar yadda ya umarce shi
"Munyi waya da commender..." a ?agare big guy yace"ina fata Ya amsa bu?atarmu"!
Calmly ya zayyana masa tattaunawar da su kai, wani irin farin cikine Ya bayyana akan fuskar shi"Allah Yasa mu ji alkhairi" Ya amsa mashi da ameen

Shiru sukayi na wani lokaci kowa da abunda Yake sa?awa aranshi

"Ya kamata ka tashi muje in kaika gida, burina ka huta..." murmushi chief yayi"nagode da kulawarka agare ni, Ina boss ko har ya tashi aiki"?

"Tun wuraren huWu ya koma gida, kasan mutun mai Iyali, ba kamar mu da muke tazurai ba..." da zolaya yayi maganar, harara chief Ya dan watsa masa batare daya furta wata kalma ba

Ya mi?e Ya nufi kofar fita, da sauri big guy yabi bayansa a tare suka fito daga office din.

Tsayawa fasalta haduwar isod headquarter bata baki ne, abun sai wanda Ya gani, lifter suka hau ta sauke su down, ta ko'ina ka kalla Jami'an isod ne sanye cikin kakinsu tun daga senior agents dinsu har izuwa jenior agent, duk inda suka bi cikin girmamawa jami'an suke sara masu, Har suka fito daga headquater din, kaitsaye suka nufi katafaren parking space din su, dankara dankaran motocine makil tare da bikes dinsu killace a harabar.

Da sauri wani agent Ya bude masu backseat na motar da zasu shiga, bayan sun shiga kowan nan su Ya zauna, agent din dake jigilar daukar su Ya yi wa motar key cikin ?warewa Ya fara driving dinsu zuwa gida.....

Dai dai lokacin da motar su ta kunno kai cikin gidan, Wayarsa ta fara ringing, lokacin da ya duba sunan mai kiransa yayi mamakin ganin aunt saratu, Cos Ya manta when last Yar tahalikar nan ta kira da sunan tayi magana da shi.

Picking call din yayi tare da kara phone din a kunne, Cikin ladabi Ya yi mata sallah tare da gaishe da ita

Ko sallamar shi bata amsa ba ta furta"Owais, bayan sallar magbrib, Ka same ni a pool yard, Ina son yin magana dakai"! Cike da bada umarni ta furta, bata jira amsar shi ba, Ta katse kiran.

Kurawa screen din wayar ido yayi ba tare da ?yaftawa ba..."

"Yalla6ai, Mun ?araso"! Big guy ne Ya fargar da shi, sam bai lura sun karaso ba, Fitowa yayi da sauri Ya nufi Cikin main falo din gidan

Yana shiga bedroom dinsa, Ya rage kayan jikin shi, Ya shiga toilet domin Yin wanka,

*HAJJATY*

Safa da marwa Take Yi atsakar dakinta, tun safe take sa ran zuwan pravin shuru bai leko ba, Hankalin ta ba karamin tashi yayi ba, gani take kamar wani mugun abunne zai faru da ita, saboda abun da ya faru jiya yayi matu?ar daga mata hankali.

Yanke shawarar fita neman shi tayi, da sauri ta dauko mayafi ta yafa akanta, Tana kokarin fita suka ci karo da juna har saida ta bangaji kirjin shi, da sauri taja da baya tare da dafe gefen kanta da hannu daya

"I'm sorry wifey, Ina zaki je ne"? yayi maganar yayin da yake nufar cikin dakin idanunsa akan fuskarsa

From head to toe Ya kalle ta, farat Waya ya gane akwai wani abu dake damunta, da alama ko wanka batayi ba.

"Baki da lafiya ne" ya yi maganar tare da ru?o hannunta suka zauna gefen gadon ta

"Baki ji ina magana ba? Fashewa tayi da kuka tare da kifa kanta akan kafadarshi

Hankalin shi yayi matu?ar tashi jin kukan hajjaty, yana daga cikin abunda Ya tsana arayuwarshi.....

Cikin shesshekar kuka tace"pravin ina cikin tashin hankali, Saboda akwai mai bibiyar rayuwata, daren jiya bana acikin kwanciyar hankalina, a tsorace na kwana, ko baccin kirki banyi ba, ina ta jira ka dawo shiru baka zo ba..."

Tuni yanayin fuskarshi Ya canza zuwa tsantsar 6acin rai,

"Fada min meya faru dake a daren jiya? Wani ya shigo ne"?....Wagowa tayi da kanta hawaye na sintiri kan kuncinta ta kwashe komai ta sanar da shi...

Tafukan hannayensa ya daura kan fuskarta,A hankali Ya fara share mata hawayen ta

"Ki yi hakuri, in sha Allah koma wanene ke naman ki da sharri kan shi zai koma, Allah Yana atare dake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login