Showing 123001 words to 126000 words out of 298130 words

Chapter 42 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

tasaki tana kallon shi, da sauri itama tayi sujjadar kamar yadda yayi, tsawon mintuna kafin suka dago da kansu fuskar kowan nan su dauke da annurin farin ciki
"Daddy fada min me ka ce acikin sujjadarka"
Numfasawa yai kafin yace"nayima Allah godiyane da ya bayyanar min da ke da ranki da lafiyarki"

"Nima haka" murmushi suka kuma saki gaba dayansu,

"Daddy Inaso na tambayeka, tayaya akai ku ka hadu da su salsabeel? Ko ya fada maku yadda akai suma suka ku6uta daga kurkukun ?addara"?
Shiru ya Wanyi kafin yace"ki bari idan yazo sai ki ji daga bakin shi, yanzu nafiso ki kara samun kwanciyar hankali" amsa mashi tayi da toh

"ki tashi mu shiga toilet ki wanke fuskarki kizo mu ci abinci"

Ya fada tare da ruko hannunta suka shiga toilet, bayan sun wanke fuskokin su suka fito atare
A gefen gado suka zauna Ya bude masu abincin tray din da suka ajiye kan table
Cikin kulawa yake bata abinci abaki tana ci, tsabar dadi kamar ta zuba ruwa a kasa tasha, wai yau gata ga daddynta

"Daddy, Ina aunty Aneelerh da babynta"?
Murmushi Yasaki kafin Yace"suna nan cikin koshin lafiya, kwanakin baya nabibiyi layin wayarta amma ba'a Waga ba sai wata rana dana ci sa'a aka daga wayar kinsan wanene ya daga" girgiza mashi kai tay alamar a'a yana murmushi yace"?aninki baby junaid," waro idanu waje tayi da tsantsar farin ciki tace"daddy sunan shi junaid" daga mata kai yai alamar eh

"baki ga yaron ba kyakkyawa dashi, ga wayau sai ma in yana surutu.." cike da zumudi tace"daddy inason ganin shi tare da aunty aneelerh, dan Allah ka kaini wurin su nayi missing dinta"

"Zan kaiki in sha Allah, amma ba yanzu ba, ki Wan ?ara hakuri" tur6une mashi fuska tayi, bakinta cunkushe da abincin daya tura mata, yar dariya yai tunawa da kuruciyarta.

"Banji kin tambayeni danejo ba"!
Sakin fuskarta tay, "tana araina daddy, bazan ta6a mantawa da halaccinta agareni ba, ni dai ba abun da zance sai dai inyiwa Allah godiya saboda Ya hadani da mutanan kirki masu sona tsakani da Allah' ta fada fukarta da Wan murmushi,

"Yaushe zaka kaini Wurinta in ganta"?

"Ko zuwa anjima idan kika kara jin sauki sai muje ko"? Daga mashi kai tay alamar eh.

Shiru suka dan yi kafin ta kuma cewa"daddy mommy adama fa? da uncle abdallah!! Suna nan suma"?
Daga mata kai yai alamar eh,
"Alhamdulillah Ya Allah" ta furta da matsanancin farin ciki, ashe da rabon in sake ganin yan uwana.

"Ina granny Wina da sauran mutanan buzaye"

Jiki asanyaye ya ajiye cokalin dake a hannun shi, nan take ta fahimci babu lafiya, muryarta adan rude tace"daddy menene"?

Cikin sanyin murya yace"unaisah sun riga mu gidan gaskiya, mahaifina da mahaifiyata, da kuma kakata kusan duk a lokaci Waya suka rasa rayukansu nima sai daga baya naji labari..."

Cikin sanyin murya tace"ubangiji Allah Yajikansu ya gafarta masu, Allah ya jaddada rahama agare su..." amsa mata yayi da ameen
Shiru suka danyi na wani lokaci batare da ya cigaba da bata abincin ba
So take ta tambaye shi dangane da mahaifiyarta sai dai takasa saboda zuciyarta taki bata hadin kai, Har yanzu bata daina jin Wacin radadin abun da tayi mata ba, ta tsani mahaifiyarta fiye da komai na duniyar nan, tana son ta haWu da ita ba don komai ba sai don taji dalilin dayasa ta yi watsi da ita, idan ba ta son ta meyasa ta haife taS'


*HAJJATY =؋?*

A zaune take gaban dressing mirror, fuskarta dauke da murmushi bakomai take tunawa ba face fuskar Naufal, ta kasa mantawa da shi, Yaron ya kwanta mata aranta, daren jiya data kwanta bacci har mafarkinsa tayi,
da alama bata jima da fitowa daga wanka ba, duba da towel din dake daure a chest dinta
Tun dazu takasa tabuka komai gaba daya ta shagala da tunanin naufal, ta ?osa pravin ya shigo donta nuna mashi hoton naufal tasan zaiyi mamakin ganin me kama da ita.

Wayar ta dake ajiye kan mirror din ta dauka ta budo hoton shi tana kallo har zooming din fuskarsa take yi
Jin motsin shigowar mutun yasa tayi saurin juyawa don ganin wanene
Pravin ne ya shigo sanye da farar jallabiya, fuskarshi babu annuri ko miskala zarratin kamar wanda aka fada ma sakon mutuwarsa
Sam bata lura da yanayin shi ba, cike da zumudi ta mike ta nufe shi tana fadin"honey, ina ka shiga tun jiya bansaka a idanuna ba"? Fadawa tayi kan kirkinsa tai huggin nasa kafin ta Wago da fara'arta tace"ka yi shiru baka ce min komai ba"? Wani kallo ya soma jefa mata mai kama da harara, da alama ta manta abunda tayi mashi jiya shiyasa ta za?e tana shige mashi
Ganin baida alamun yi mata maganane yasa tace"fadamin baby, ko dai hajiya saratu ce ta 6ata maka rai"? Banza yai da ita baice uffan ba..
Murmushi tadan saki"nasan itace ta bata maka rai, bari na nuna maka w?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 ani abu nasan zakayi farin ciki idan ka ganshi" ta fada da sauri ta nufi mirror
Goya hannayensa yai akan kirjinsa yana jiran karasowarta.

"Baby, duba ka gani, jiya a wurin taro bayan tafiyarka naga wannan yaron mai kama da Wan mu Naufal kyakkyawan gaske" cikin annushuwa ta mika mashi wayar don ya kar6a ya gani, rai amatu?ar 6ace yakai ma wayar bahagon naushi tayi sama ta ?undumo kan tiles ta bada wani sauti mai karfi.

idanunta azazzare ta dago tana kallon shi, Huci yake yi tamkar mayunwacin zaki Ya furta"kin manta abunda ki kai min jiya"? Dafe kai tayi da hannu daya idanunta tuni sun cuko tab da kwalla, ranta abace tace"pravin! Meyasa zaka jefar min da wayata? Laifin me nayi maka? Saboda kawai naki bin umarninka? Wai meke damunka ne pravin? Agaban mutane fa ka ruko hannuna kaja ni zaka fitar dani daga hall tayaya bazan ki binka ba? Ko so kake afara zargin mu ?

Kafin ta ?are maganar Ya daka mata tsawar data firgitar da ita, nuna ta yai da yatsan hannun shi"yi min shiru! Bana son jin komai daga gare ki, ashe harni ban isa in baki umarni ki bi ba! Hankalin ki ya kwanta Kin kunyata ni a idon jama'a..." hawayene suka soma sintiri akan fuskarta, muryarta na rawa tace"pravin ka fahimce ni mana, kasan bazan ta6a kin bin umarnin ka ba, hakanan batare da kwakkwarar hujja ba! Ni nayi hakanne saboda bana so wani ya tuhume mu..." yatsansa ya daura kan la66anta, shiru tayi tana kallon shi
Can kuma ta fashe da kuka tasa hannu ta ture yatsan nasa tana fadin"baka kyauta min ba, Tun jiya nake zumudin in nuna maka hoton sajeed Yaron dake kama da danmu amma shine ka fasa min waya..."?
Ta6e la66ansa yai kafin ya furta"ki yi hakuri rainane ya 6aci, " ya fada tare da zukunnawa ya dauki wayar yana fadin"zan siya maki wata"

"bana so, ni dai ka gyaramin tawa, saboda bana son na rasa hoton sajeed"
Harara ya watsa mata tareda cewa"meye alakarki da shi ne? Kawai daga ganin yaro yana kama dake? Mutun nawa kika sani suna da masu kama dasu a duniya? Kamar kanki farau"
"Ni wannan bai dameni ba, Ina son shi saboda inajin shi kamar Wana dana rasa"
Rai a6ace ta fada kafin ta juya ta koma kan gado ta zauna, tana cigaba da matsar kwalla
Murmushin gefen fuska pravin yasaki Yana dubanta,
Komawa gefenta yai ya zauna bayan ya ajiye wayar ya ruko hannunta acikin nashi
"Look, bana so ki sanya damuwa aranki, idan har rashin naufal ne ke damunki, nayi maki alkawarin nan bada jimawa ba zaki haifi wani babyn, sai ki sanya mashi sunan naufal din"
Wani kallo ta jefa mashi batare da tace mashi ?ala ba, lallashinta Yacigaba dayi duk don ya samu yashawo kanta.

HAJIYA SARATU


_safa da marwa take yi a tsakar dakinta, zuciyarta cike fal da tunanin abunda Pravin yayi mata jiya a dakin taro, tun jiya abun ke ci mata tuwo akwarya, abun sai nanu?arta yakeyi, zuciyarta ta gama hasala, wai har ita pravin zai kunyata gaban yan uwanta da abokananta? A ina ya samu ?warin gwiwar yi mata haka? ru?e qugu tayi da hannu Waya fuskarta babu annuri_


*Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'
'?*



*Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*_*~
'=؋?BOSSLADIESWRITERS=؋?*~_



3,F 'DB/=؋?=?%?=؞?


~Takun ?arshe=?%?~



Dedicated to Aunty Kubra=؋?=؞?



B5) -( 1HE'F3J) :J1 9'/J) (JF 'D3,F'! E9 *7H1'* E9B/)=؋?=ؘ?=??


An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists d'=؋?=ؘ?



Daga al?alamin Boss Bature=؋?
'





__________________________
'?



=ث?HAJIYA SARATU=ث?




_safa da marwa take yi a tsakar dakinta, zuciyarta cike fal da tunanin abun da Pravin yayi mata jiya a dakin taro, tun jiya abun ke ci mata tuwo akwarya, abun sai nanu?arta yakeyi, zuciyarta ta gama hasala, wai har ita pravin zai kunyata gaban yan uwanta da abokananta? A ina ya samu ?warin gwiwar yi mata haka? ru?e qugu tayi da hannu Waya fuskarta babu annuri_

Maganganun da suka Tattauna jiya ita da su Har excellency ta soma tariyo bayan fitowarsu daga hall kafin su nufi gidan prime minister.


"Meyesa pravin zai ja hannunta abainar jama'a? Menene alakarsu? Wai ku ba ku zargin wani abu atsakanin su"? Hajiya laurace ta fada babu wasa akan fuskarta

"Najima ina zargin matar nan, na dai yi shiru ne ban fada maki ba, saboda bana so in shiga tsakanin ki da mijin ki, amma ni kwata kwata hankalina bai kwanta da ita ba, tun daga kan yanayin yadda take daukar wanka zaki fahince akwai wata a kasa ba banza ba, ni ay ban ta6a ganin yar aikin da ta samun ?anci kamar hajjaty ba"! Her excellency muhibbat ce tai maganar,
Hajiya jamila tace"yanzu wani hukunci zaki yi masu"? ta fada tana kallon hajiya saratu.

Da sauri Hajiya madina tace"please, ku daina tunzurata ku bar ta taji da abun da ke damunta, ni banga abun Waga hankali a maganar nan ba!"

Hajiya saratu da ke sauraronsu Waya bayan Waya sai da ta cika ta batse kafin tace

"Wallahi bazan ?yalesu ba! Daga ita har shi sai sun fuskanci 6acin raina, sai tayi danasanin kasantuwarta yar aiki a gidan nan"! Ta fada a tsiwace tana huci

"Ni shawarar da zan baki kawai ki kore ta daga gidan ta koma can kasarsu acigaba da bautar shanu, idan ba haka ba Allah kaWai yasan muna?isar da take shirya maki, ?wara tun wuri ki yi maganinta kafin ta jaza maki matsala" Acewar hajiya Muhibbat

Dafa kafaWarta hajiya laurat tayi"idan da zaki bi shawarata kada ki tanka masu! Nasan yanzu hankulansu atashe yake saboda sun san dole ki tuhume su, abun da yakamata ki yi shine ki manta da zancen hukunta su, ki yi tamkar babu abun da ya faru, za su yi zaton kin kyale su ne, ki bari sai sun shagala tukunna ke kuma ki fara bincike akan su, ta haka ne kadai zakisan meke atsakanin su amma yanzu idan kikace zaki hukuntasu to ba za ki san menene alakarsu ba, kwara ki fara bin diddiginsu har zuwa lokacin da zakiyi nasarar kama su dumu dumu"

Jinjina kai hajiya saratu tay alamar gamsuwa da shawarar Hajiya laurat..

Bayan ta dawo daga duniyar tunanin taja gauran Numfasawa haWi da Wan jinjina kanta, cikin takun sauri ta nufi wayarta dake ajiye kan pillow ta dauka ta kira landline na kitchen.

Tana fara ringing akayi picking, kara wayar tai a kunnanta.

"Inason ganin Marwa, ta same ni adaki bana son bata lokaci"

ta fada tare da katse kiran ta ajiye wayar

Cigaba da zagaye bedroom din tayi, yayin da take dunkule tafin hannunta na dama tana tura shi ana hagu kamar ?ar dambe.

Knocking kofar da akayi mata ne yasa ta dakata.

"Wanene"?

"Aunty ni ce marwa"

"Okey shigo ciki"

Turo kofar tayi, Jikinta sanye da uniform na ma'aikatan gidan ta shigo, cikin girmamawa ta gaishe da hajiya saratu, bata amsa mata ba, sai tay tamkar ba ta ji me tace ba.

Tuni marwa ta sha jinin jikin ta, tsoranta kada ace wani laifin ta aikata da yasa hajiya saratu ta kira ta don tasan halinta masifaffiya ce.

Muryarta na rawa tace"Am.. Aunty gani, naji kina nemana"

Wurga mata harara hajiya saratu tayi da sauri ta dukar da kanta kasa
Tsawon lokaci bata tanka mata ba, gani ta ke kamar zubda ajine ta nemi taimakon yar aiki, sai dai ba yadda zata yi itace kadai hanya mafi sauki agareta.

Zama tayi gefen gadonta, cike da isa ta dubi marwa"ke zonan"! da sauri marwa ta dawo ta zukunna agabanta.

"Wani aiki nakeso kiyi min, bana so kowa ya sani daga ni sai ke! Na yaba da hankalin ki ne shiyasa na za6e ki saboda nasan zaki Iya......" Tun da tafara magana marwa ta soma zare idanunta cike da fargaba.

"Kafin na faWa maki, zan gindaya maki sharadi, Idan har na kuskura naji maganar nan abakin wani, ko kika bani matsala wallahi thumma tallahi na lahira sai yafi ki jin dadi...." Wani irin yawu marwa ta haWiya jiki na bari tace"in sha Allah zan kiyaye."

Ta6e baki tayi kafin ta Waura da cewa" me kika sani dangane da head maid din gidan nan? ya mu'amalarta daku take? Sannan Wacece aminiyarta acikin ku? Shin tana fada maku sirrinta"?

Shiru marwa tayi aranta ta ayyana to fa! Ko me hajjaty ta aikata ma aunty masifatu da take neman karin bayani dangane da ita? Watakil watan cin ubanta ne ya tsaya

A fili kuma tace "Abun da nasani dangane da ita, macace mai saukin kai, tana da mutunci kuma tana kyautata mana, ba ta shiga sabgarmu, sannan bata cika zama yin fira da mu ba, macece mai kamun kai bata da surutu, sannan bata da aminiya acikin mu balle har wani yasan sirrinta, wannan shine Iya abunda sani"

Tur6une fuska hajiya saratu tayi, ita ba haka taso taji daga bakin Marwa ba.

"Okey, ki nutsu ki saurareni," jinjina mata kai tai
"Daga yau inaso ki fara shisshige mata, saboda ina zarginta, inason kisan duk wani sirrinta, ki zama aminiyarta, bayan haka duk wani motsinta ya kasance a tafin hannunki, idan har kikaga wani abu ba dai dai ba, to kiyi hanzarin sanar dani," amsa mata tayi da toh

"Idan har na samu abun da nakeso nayi maki alkawarin zan baki mukamin da take da shi agidan nan, bayan haka zanyi maki kyauta ta musamman, kin dai san wacece ni, basai nayi maki bayani ba"

Wani irin farin cikine Ya lullu6e marwa musamman da taji Hajiya saratu ta ambaci zata bata mukamin hajjaty ga kuma kyautar da zata samu, aranta ta ?udiri aniyar saita yi ma hajjaty kutse koda kuwa bata kama ta da laifin komai ba, ita zata ?ala mata sharrin da za'a sauke ta daga kan mukaminta.

Shu'umin murmushin gefen fuska tasaki.

"Baki da matsala dani aunty, in sha Allah zaki samu abunda kikeso"

"Zaki iya tafiya" mikewa marwa tayi zuciyarta cike fal da murna, dama ta jima tana jin haushin hajjaty saboda yadda tayi masu zarra agidan, komai itace akan gaba, gata head maid ga farin jini awurin mutanan gida, bayan ba wani aiki takeyi ba acikin gidan sune masu wahalar girka abinci, ita aikin ta tsara abunda za'a girka ne da kuma bada umarnin yadda abu zai kasance.

Dole ta Wana mata tarkon da bazata Iya fidda kanta ba, ko dan ta ?wace mukamin ta, wannan alwashine ta daukarwa kanta!

Ta fada aranta, yayin da take nufar hanyar komawa kitchen

Bayan fitar marwa, hajiya saratu ta sauke ajiyar zuciya, yanzu ne ta samu kwarin gwiwar shiga toilet yin wanka

Lokacin da fito, A zaune ta same shi gefen gadonta, sam bataji alamun shigowarshi ba.

Tun da ya Wago suka hada ido da ita yai saurin sunnar da kanshi kasa, wani irin nauyinta yaji, baisan ta ina zai fara shawo kanta ba, Yasan dole ta tuhume shi akan abun da Ya faru jiya.

Kau da ido tai daga kan shi, Ta juya ta nufi closet, jim kaWan Ta fito har ta sanya riga bubu ta atamfa, gaban mirror ta tsaya tare dakai hannu ta dauki turare ta soma feshe jikin ta da shi, yadda ta share shi kamar batasan da zaman shi a dakin ba.

Shi kuwa gogan Ya kasa dauke idanunsa daga gareta.

Kamshin turarenta ne yakai mashi karo har ya gaza jurewa duk da shakkarta da ya ke ji ?arfin hali yai wurin furta"Har Yanzu fushi kike dani? Banza tayi da shi
Mikewa yai tsaye ya nufeta, daga bayanta ya dan dakata Yana bin ta da kallo.

Kafin cikin sanyin murya yace "Tun jiya nake ta so na baki hakuri, nasan ban kyauta maki ba, ni kaina ba'a hayyacina na aikata hakan ba, bansan meyasa na ruko hannunta ba, wallahi sharrin shaiWanne"

Murmushin gefen fuska tasaki, ba tare da ta bari ya gani ba, dama dagangan ta dauki wankar da zai zautar da shi

"Na cancanci kowani irin hukunci daga gareki, a shirye nake dana kar6e shi, ni dai bana son 6acin ranki"

ya faWa tare da Waura kansa saman kafadarta saboda karfin hali irin nashi
Lumshe idanunsa yai tare da shakar kamshin turarenta.

"Kinyi shiru baki ce min komai ba" sai da ta mula tasha iska tukunna Tace"laifin me kayi min"?

"Kin riga da kin sani"

"In dai dangane da abunda ya faru jiya ne to ka manta kawai, bana son tada maganar, ko alokacin abunda yasa raina ya 6aci saboda ina kishin ka ne banji dadi ba, amma yanzu komai ya wuce"

Tsabar mamakin kalamanta yasa shi saurin Wagowa yana duban fuskarta ta cikin mirror.

"Amma dai wasa kike min ko"? Murmushi ta sakar mashi tare da cewa"na taba maka wasa irin wannan"?
Girgiza kanshi yai"a'a, baki taba min ba, amma dai nayi mamaki, Allah yasa ba mafarki nake ba" juyowa tayi suka fuskanci juna, fuskar ta dauke da ?ayataccen murmushi ta Waura hannayen ta a kan kafadunsa.

Lamarin ya Waure masa kai gaba daya ta canza mashi kamar ba hajiya saratun daya sani ba.

Cikin sanyin murya tace"hubby, kada ka ?ara maimaita kuskuran da kayi, bana so, kasan inada kishi, akan ka zan iya komai daga ciki har da kisa"

Zaro idanunsa yayi"in sha Allah hakan bazata faru ba, zanyi kokarin ganin na kiyaye duk wani abu da zai bata maki rai"

Ba zato ba tsammani yaji tayi huggin Winsa tare


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login