Showing 6001 words to 9000 words out of 298130 words

Chapter 3 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

kallon mai shigowa, Chief Owais ne Yake nufo su cikin shiga ta tsadaddun suit launin ash colour, wani irin sanyayyan ?amshin turarene ke fita daga jikinsa, tunkafin Ya ?arasa garesu idanuwanshi suka sauka akan hannayen prime minister dake a ru?e dana Garkuwa, walking gently ya nufi bakin gadon ya Wan dakata da yin tafiya, mi?ewa Boss yayi tare da sarah mashi.

"Uncle am ready, yakamata mu tafi suna jiran mu, tun Wazu suke kira awaya" tamkar baisan furta maganar yayi ta.

Shiru babu alamun prime minister zai amsa mashi.

Boss man ne yace"Sir, wani abu ne ya faru wanda ya Waure mana kai, yanzun nan kafin ka shigo Danish Ya dam?i hannun prime minister Ya ru?e shi sosai, ina da tabbacin shine dalilin dayasa ya shiga yanayin nan"

?age girarsa yai alamar yaWanyi mamaki kafin ya furta"Okey, kayi mashi magana ta yadda zai ji ka"

Boss ya amsa da toh, sannan ya je daga gefen prime minister yadan russina tare da cewa"Yalla6ai, Chief Ya shigo Yana son yin magana dakai"
Tamakar bazai Wago ba, A ?alla sai da ya ?ara mintuna biyar cuf tukunna A hankali Ya dago da fararen idanuwanshi waWanda suka kaWa jawur da su tamkar mai fama da ciwon ido.

Zagayowa chief yayi ta 6angaren da prime minister yake a zaune Ya tsaya yana duban fuskarshi.

'Uncle are you okey," ya tambayane ganin yadda idanuwanshi suka yi ja.

Can ?asan ma?oshi sound din muryarshi ke fita"Owais, kaga yadda ya ru?e min hannuna? meaning, he feels what I feel about him."

"Uncle, don't let that bother you, zamu dawo ne anjima sai ka ?ara duba shi.

Jinjina mashi kai yai ba tare daya furta komai ba, shi kanshi chief yana mai al'ajabin ?aunar da Uncle Hateem ya ke ma Danish.


Ganin ya?i sakin hannun Danish, yasa shi sake furta"uncle, we ave to go" Magana chief yakeyi mashi amma gaba Waya hankalinshi na akan danish, ganin babu alamun zai motsa yasa chief, ru?o hannunshi cikin kulawa yai mashi alamar ya tashi su tafi, yun?ura prime minister yayi da niyar ya mi?e daga saman gadon sai dai wani iko na Allah Danish Ya?i bari ya raba hannun shi da nashi.

Muryar mai girma Hateem na rawa ya furta"My son, Yaron nan Ya?i sakin hannuna, baison in tafi nabar shi"

"Uncle, kada hakan ya dame ka" chief ya faWa, tare dakai hannu ya dam?i hanun danish da?yar ya 6an6areshi daga ru?on da yayi ma hannun hateem, shatun akaifun danish har saman fatar hannun prime minister, wurin yayi ja.
Hakan ya sosa ran Chief Owais, baiji daWin yakushin da Danish yayi mashi ba, shi kuwa Hateem ko kaWan baiji zafi ba, baima lura da yakushin ba.

Chief da boss ne suka kwantar da Danish, tare da lullu6a mashi bargo har saman ?irjinshi, kafin suka bar Wakin, bawan Allah prime minister yana tafiya yana waiwayon Wakin, gani yake kamar idan ya tafi bazai ?ara ganin shi ba.

__________________________
'?

BARI MU ?AN KOMA BAYA MUJI MEKE FARUWA A 6ANGAREN SU ARMY BOY DA TIGER.

Bayan Gari Ya waye suna akwance Saman Sofa, sun saki baki da hanci suna sharar bacci, ba zato ba tsammani Muryar Khadeeja ta farkar da su, Daga can saman bene ta kware murya da ?arfi tana fadin"Wayyo Allah, Mayu sun kwanar mana agidanmu, wai ku ba zaku tafi gidan ubanku ba" A firgice Suka farka suna faman mutsustsuke idanuwansu, kafin suka kalle ta, a lokacin harta nufi bene tana saukowa down, Sumar kanta a hargitse babu kayan mutunci a jikinta Rigar baccin jiyace bata cire ta ba, dai dai gwiwarta rigar ta tsaya mata, hannunta Waya ru?e da qugunta, ta dambara janbaki saman la66anta har kan kumatunta, ga wani man baki data shafa sai ?yalli yake yi.

Kallon juna su ka yi fuskarsu babu walwala, Army boy yace"Allah ya wadaran naka Ya lalace wannan masifaffiyar yarinyar Allah Yayi mana maganinta, saboda jaraba baccin ma bazata bari mu ?arasa shi cikin dadin rai ba, Ni dai harga Allah an takura min, yakamata sir ya bamu iznin komawa gida"

Takaici Ya hana Tiger cewa komai, Jira yake kawai Ta ?araso Yaji me zatace masu
Da gudu ?an uwanta suka fito daga Wakunansu, suka biyo bayanta,

A tsakankanin sofas din khadeeja ta dakata da yin tafiyar tana jifarsu da matsiyacin Kallo Tace"mayu masu cinye ma mutane abincinsu, Yanzu sai ku girka mana abunda zamu ci" zaro ido su ka yi suna kallonta.

Mamaki take basu, A iya sanin su dayawa mata suna jin shakkar sojoji amma ita wannan mai kunnan zoman babu alamun tsoronsu a fuskarta.

Tsawa Army boy Ya daka mata"ke karki kuskura ki ?ara kiran mu da sunan mayu idan ba haka ba zan harbe ki da bindiga" maimakon taji tsoron maganarshi saita galla mashi harara tana fadin"Ai wallahi sai kun girka mana abun da zamu ci, tunda kuka cinye mana sauran abincinmu na jiya"

Dafa kafadarta hawwa tayi"dan Allah ki ?yalesu, Ki zo mu koma Waki, ki yi wanka ki canza kayan jikinki," murguWa mata baki tayi"ni babu inda zanje, wallahi sai sun girka mana abincin da zamu ci, saboda Yunwa nake ji"

Girgiza kai sojojin sukayi suna kallonta kafin suka kalli sauran ?an uwan nata,
"Jiya bamu samu damar Yin magana daku ba, muna fata kun tashi lafiya"
Atare suka hada baki wurin amsa masu da lafiyalou"
Tiger Yace"Ku fada mana sunayenku muna son ji"

Namijin cikinsu ne Ya fara Yin magana.

"ni sunana MUBEEN" Jinjina kai tiger yayi"Ke fa" Ya nuna Macan dake a gefenshi, Fara ce sol tana da kumatu da ?ar kiba
"RUBINA"
"Suna mai daWi, Kefa mai idanuwan ?an chaina, ya fada da zolaya yana nuna ta gefen rubina
"YASMIN SUNANA"
"Good Girl, and You " Da ido Ya nuna ?an matan dake ruke da hannun junansu Waya Doguwa Waya madaidaiciya
"Ni sunana Hibba ita kuma Sarah"
"Masha Allah, Naji dadin haduwa daku, Allah yayi ma rayuwarku albarka" amsa mashi sukayi da ameen
Khadeeja masifaffiya tace"?warama da baku tambaye ni sunana ba, don ba fada maku zanyi ba" murmushi suka saki ba tare da sunce mata ?ala ba.

Bubbuga ?afafuwanta tayi"ni dai yunwa nake ji, ku tashi ku shiga kitchen ku girka mana abinci"
Army yace"bamu Iya girki ba, Ko kin ganmu da zannuwane Waure a ?ugunmu?
Harara ta watsa mashi
Tiger yace"Yar uwa khadeeja, baku da maiyi baku girkine a gidan"?
Hawwa ce ta bashi amsa da cewa"yayanmu salsabeel shine yake girka mana abinci"

Zaro ido Tiger yayi"kina nufin wannan ?aton mutumin"?

?aga mashi kai tayi alamar eh
Sarah tace"ba koda yaushe yake girka mana abinci ba, yaya omar yana kawo mana daga gidan su," sun gane wa take nufi, wato Big guy shi ne suke kira da Asalin sunan shi Umar.

Kallon agogo Army boy yai a lokacin ?arfe goma sha biyu na safe.

"Da alama sun manta yau basu kawo maku abincin da wuri ba, Ya za'ai kenan"?

Da sauri Mubeen Yace'ai akwai yogurt da madara a frigde, hada bread a store, Idan muna jin yunwa kafin akawo mana abinci su muke Wauka mu ci,"

Ran khadeeja Ya gama 6aci, Bubbuga ?afafuwanta tayi hankalinsu ya dawo kanta, idanuwanta rufe ta soma zazzaga masu masifa tana fadin"ni wlh bazansha yogurt da bready ba, ai kune kuka cinye mana sauran abincinmu a kitchen, wlh idan baku je kun girma min abunda nakeso ba zan kira yaya Omar awaya in fada mashi kun ci mana abincin mu"
AruWe suka hada baki suna fadin"Me yai zafi, Kinji munce bazamu girka maki ba ne?

Nuna masu hanyar kitchen tayi da hannunta"ku tashi ku shiga ku dafa min abinci"

Agajiye suka mi?e tayi gaba suka bi bayanta sune har cikin kitchen.

?an uwan dake a falo, saman sofa suka zauna, su kansu ba zasu Iya da rigimar khadeeja ba, Sara ce ta Wauko masu Robobin madara, Ta mi?a ma kowan nan su, suka zauna suna sha
Daga falo suna jiyo sautin muryar khadeeja dake acikin kitchen.

"wainar kwai zaku soya min" ta fada tare da buWe kofar store ta dauko masu egg container ta kawo masu shi akan Countertop ta daura shi.

Cikin kwantar da murya Tiger yace"khadeeja wannan kwan yayi maki yawa ina laifin a soya maki biyar" harara ta galla mashi"ai bani kadai zanci ba, hada ?an uwana suma suna jin yunwar" roba ta Wauko masu inda zasu kaWa kwan hada abun kaWawar,
Kafin ta nufi freezer tana fadin"hada Chicken pepper soup zaku yi mana, Sannan Ku soya mana kifi mubeen yana son ci" Bin ta da kallo su ka yi baku nan su a buWe kamar sakarkaru haka suka bi ta da kallo.

Kaji ta Wauko Guda Uku Manya manya masu tsokoki ajikinsu ta ajiye masu

Tace"chicken peper soup zakuyi mana, akwai kayan miya da kayan ?amshi duk zan Wauko maku su" hankalinta kwance takeyi masu magana, har wani ?yafkyafta masu idanu takeyi.

Da?yar tiger ya iya bude baki yace"Yar uwa khadeeja, bakomai muka Iya girkawa ba, Kuma wannan abincin yayi yawa, ga kwai ga kuma kaji"?

Zum6ura mashi baki tayi"wanda yasa kuka cinye mana abincin mu na jiya," ta faWa tare da juya masu baya ta nufi cikin store, gabansu har faWuwa yake yi, Jim kaWan ta dawo hannunta ru?e da Manya manyan doyoyi guda uku ta ajiye masu a?asa tana faman yin nishi tace"idan kun gama girka wadannan saiku fere doyar ku soya mana ita da kwai" Baki abuWe suke sauraronta
Komawa cikin store tayi sai gata ta kuma dawowa hannunta Wauke da ?aramar roba, dankalin turawane acikinta
"Chips zaku soya mana da shi" ta ajiye robar, har ta juya zata koma Army boy yayi saurin shan gabanta, Muryarshi a tausashe Yace"khadeeja, Ya isa haka, wai ke meke damunki? Mu fa mazane ba mata ba, bamu Iya girki ba, Bindigogi muka Iya ru?ewa, taya zaki kwaso wannan uban kayan abincin kice mu girka maki"?

Fashe mashi tayi da kuka tana bubbuga ?afa tace"wallahi idan baku girka ba saina fada ma Yaya omar kun cinye mana abinci, Kuma In ?ala maku sharrin kun ta6ani" Waro ido waje su kayi har saida gabansu Ya fadi jin abunda tace, Ita kanta da tayi maganar bada wata manufa ta furta ta ba.

Lallashinta suka soma yi"shikenan, Munji zamu girka maki, Yanzu ki koma falo ki zauna, ashagwa6e tace toh, kuma zan dinga le?owa ina duba ku" amsa mata sukayi da toh
Bayan fitarta daga kitchen din tiger yace"Allahumma ajirni filmusibati wa aklikni khairan min ha, Yarinyar nan ba ?aramar makira bace"
Army boy yace'ai duk laifinka ne, kaine jiya kasa na kwaso masu abincinsu da duk hakan bata faru ba, yanzu gashi ta daura mana wannan uban aikin"

"Idan laifina ne kaima hada laifinka ai, tunda atare muka cinye masu abincinsu"

Ran kowan nan su Ya 6aci, tamakar zasu rufe juna da bugu

"FaWa ku ke yi ko"? Muryar Khadeeja ce ta fargar dasu, arude suka hada baki wurin fadin"A'a aunty, Muna yanke shawarane akan meya kamata mu fara girkawa"

Murmushi ta saki har dimple dinta Ya lotsa, Hannunta Waya ru?e da Robar milk da take sha.

"Idan ma faWa ku ke yi ku kuka sani, Nidai ina jiran abinci, kuma wallahi Kafin In shanye madarar nan ku gama min girki na, idan ba haka ba hmmmm kunsan sauran" Ta fada tare da juyawa ta fuce daga kitchen din.

Army ya Waura hannayenshi biyu saman kanshi"mun shiga uku, wannan wata irin bakar rana ce"?

Tiger yace"Ba surutu Ya kamata mu tsaya muna yi ba, Mu fara mata girkin kada ta shanye madarar"

Tu6e rigunansu sukayi, Ya rage saura wandunan kakinsu a jikinsu, sham sun manta da bindigogin su da suka ajiye afalo.

Kamar mata haka suka fara aikace aikace, wanke nama, Fere doya, Gyaran cefane, da yankan kayan lambu suna haWa uban gumi zufa ta ko'ina, da waya sukeyin amfani wurin yin browsing yadda akeyin chicken paper soup da sauran abunda basu Iyaba, duk bayan ?an mintuna sai khadeeja ta le?o kitchen don taga idan suna yin aikin yadda ya kamata, bayin Allah kamar ba sojoji ba, ta takura masu ta addabi rayuwarsu

Yayin da take zaune a falo cikin ?an uwanta, Hawwa tace"khaeeja baki kyauta masu ba, dan Allah Ki yafe masu aikin yayi masu yawa"
Gatsina mata hanci tayi batare da ta tanka mata ba
Sarah taja guntun tsoki tana kallonta tace"kinji haushin rayuwarki, kuma wallahi saina fada ma Yaya Jazz abunda kika yi masu"
Banza tayi dasu tamkar bata ji me suke fadi ba,
Yasmin tace"please ku daina yi mata magana, Itama bayin kanta bane, Lalurace Yaya jazz fa yace mu runka hakuri da yar uwarmu"
Hibba tace"duk da haka halintane, Deeja tafiye rashin jin magana, bata da ha?uri, saina fada ma Yaya salsabeel"
Duk wanda yayi magana saita kalli la66ansa
Robar yogurt din dake a hannunta ta ajiye kan carpet, Ta yun?ura ta mi?e tana yin mi?a, duk suka bita da ido, bindigar da ta gani sakon kujera takai hannu ta dauka ta saita su da ita tana fadin"wallahi dukan ku sai kun mutu, banzaye kawai, Har ni zaku dinga yi ma faWa"

Dariya suka saki gaba Wayan su, saboda basu san meye amfanin bindigar ba.

Hawwa tace"dalla malama Ajiyeta a ?asa, Kada ki lalata masu abunsu"

Harara ta watsa mata tana faman cije la66a tace"ta kanki zan fara hawwa Jiya Hada kulleni adaki don kada In futo waje, yau idan na kashe ki bazaki sake Yi min haka ba
Tana ?are maganar ta daddage ta ru?e bindigar dakyau, Tana ?o?arin harbawa, Mubeen yayi saurin Janyo Hawwa gefe daya, ba zato ba tsammani harsashin bindigar Ya harbi jikin kujarar inda Hawwa take zaune, Wani irin Haya?i ya fita Wurin da bullet din ya shiga nan take ya fashe.(=?3?)

Nan fa ido Ya raina fata, Gaba Wayansu sun rude sun gigice, Amatu?ar firgice suka mimmi?e tsaye suna faman zare idanuwansu
Dariya tasaki tana fadin"kunyi tunanin bansan yadda akeyin amfani da ita ba ko? To ai na ta6a ganin video a wayar Ya omar, wasu suna kakkashe mugaye da ita, Waya bayan Waya kuma zan kashe ku yanzun nan" Ta faWa Tana saita su da ita, fashewa sukayi da kuka suna yi mata magiya, saboda rashin hankali Ta kara sakin wani harsashin kaitsaye ya sauka a tsakankanin ?afafuwan Rubina, Baiwar Allah Kuka hada majina, sau?in ma bai ta6a fatar ta ba.

Maza suna a kitchen suna girki, sun bar psycho afalo tana aiki, duk irin girman sautin harbin bindiga basu ji ba, Mubeen Ne ya watso da gudu Ya shigo kitchen din ya Waga murya Yace"ga khadeeja can ta daukar maku abunku tana harbin mu" gabansu ne yayi wani irin mugun faduwa, aguje suka fito daga kitchen din adai dai lokaci ta saita kan Sarah jikinta sai kerma yakeyi

Tsawa Tiger Ya daka Mata, da sauri Ta juyo da bindigar ta saitasu tana dariya tace"Ajalin ku ne ya fito daku daga kitchen, dama haushinku nake ji, Jiya kunkashe min jazz dina"
Hankalinsu idan yai dubu toh Ya tashi, Khadeeja ta saka su a tsaka Mai wuya, Ga girki sun baro a kitchen Ga wani tashin hankalin dayafi gigitasu
Dole suka zube kan gwiwowinsu muryoyin su na rawa suke yi mata magiya"dan Allah Anty khadeeja ki rufa mana asiri, wlh bamu kashe maki jazz dinki ba, Yana nan da ranshi, yaji sau?i raunin jikinshi ya warke, Ki taimaki rayuwarmu ki ajiye bindigarnan a?asa....." tamkar zasu fashe da kuka haka suka dinga ro?onta, zuciyarta kamar ta kafuran farko babu alamun sassauci tace
"Nafa san me nake Yi, baku isa ku raina min wayau ba, Idan dagaske Ya jazz bai mutu ba toh Yana ina"?
Fuska amarairaice Army boy yace"Yana asibiti, likitoci suna duba lafiyarshi,"
?asa ?asa da murya Tiger yai mashi raWa"kai dole fa mu nemi mafita wallahi, Idan ba haka ba zata Iya kashe mu ko ta kashe ?an uwanta tun da ba hankali gareta ba, ga kuma Abinci mun bari kan gass"

Army boy yace"to ya zamuyi! Ni wallahi komai ya kwance min,"
"Gulmata kukeyi koh"? Ta fada tana jifarsu da harara
Atare suka girgiza mata kai alamar eh, tace"idan ma gulmata kukeyi daga yau Idan na kashe ku bazaku sake yi ba"
"Ku lallashi yar uwarku, zata Iya ja mana bala'e daga mu har ku" Tiger ne yayi maganar Yana kallonsu Hawwa.

Duk wanda yayi yunkurin buWe baki zai bata ha?uri da bindiga take saita shi,
Kwatsam Wayar Tiger Ta soma Yin ringing, adabarbarce ya zura hannu ya zarota daga aljihun wandonshi, duk sun rude, ganin sunan Major ya bayyana ne yasa hankalinsu Ya Wan kwanta,
Picking call din yayi tare da kara wayar akunne
Ko sallamar major bai amsa ba, Ya furta"Jazz Ya Jikin Naka"? On the other hand Muryar Major da alamun mamaki yace"Jazz Kuma? Baka ga sunan wanda Ya kira ka bane"?
Tiger bai kula maganarshi ba yaci gaba da fadin"Kamar ka sani tun safe khadeeja take son Yin magana dakai, Ai saida na fada mata baka mutu ba lafiyarka ?alou amma taki jin maganata"
Tun da ya ambaci sunan Jazz khadeeja ta jefar da bindigar kan carpet, ta nufe shi tana fadin"Bani shi muyi magana" jiki na 6ari Army yayi saurin Mi?ewa ya dam?i ?eyarta yana fadin"bashi bane don ubanki, Har mu zakija ma bala'e, masifaffiya kawai, Kin bi kin ?untata rayuwurmu kin hanamu sakat, wlh baki isa ba, AWaki zan kulle ki," kuka tadinga yi mashi tana zagin shi, Waukarta yayi ya nufi saman bene da ita, Daki ya shigar da ita ya kwantar saman gado, Ya fito da sauri yaja ?ofar Ya datse ta da mukullin daya gani ajikin ?ofar, Ajiyar zuciya ya sauke kafin Ya nufi falon, A lokacin Tiger Ya kammala yin wayar da major, Ya mi?e dasauri Yaje ya dauki bindigar ya hada da Wayar da suka ajiye kan sofa, duka biyun Ya turasu karkashin dining table
Kallon sauran yaran su ka yi"ku koma ku zauna Yanzu zamu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login