Showing 207001 words to 210000 words out of 298130 words

Chapter 70 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

Ki kai kukan ki wurin Allah, Nima zan tayaki da addu'a in sha Allah.." lumshe idanunta tayi har yanzu bata daina jin kukan ba...


"Daddy, Inaso nayi nesa da gidan nan, na wani lokaci..." tun da yaji wannan maganar Ya fahimci akwai wanda Ya 6ata mata rai, a sannu zai gano koma wanene.

dagowa tayi a hankali suka kalli juna, idanunta sun ?an?ance sun kaWa jawur saboda kukan da ta sha..
"Daddy, Ka kaini part dinka, in zauna gurin Aunty danejo, ko kuma ka kaini wurin aunty Aneelerh dan Allah" marairaice mashi fuska tayi kamar zata fashe da kuka, kallonta kawai yakeyi gwanin bantausayi, arayuwarshi yatsani duk wani abu da zai ta6a lafiyar yarsa, bai son damuwarta.

"Daddy kayi shiru bakace komai ba"?
Numfasawa yayi kafin Ya furta"magana nakeso nayi dake, shiyasa na shigo gidan nan, sai kuma na taras da abunda Ya 6ata min raina..."
"Ka yi hakuri daddy, na daina kukan ay, ba zan kara sanya damuwa araina ba..." ta faWa tare da ?a?aro murmushi akan fuskarta.

Kwantar da ita ya kuma yi ajikin shi don ta samu relief din abunda ke damun ta..
Calmly ya fara zayyana mata maganar da suka tattauna da su chief
"Ita mara lafiyan yar uwarsa ce, kuma kawar auntynki Aneelerh, tana a kwance gadon asibiti kwata kwata bata acikin hayyacinta tun lokacin data rasa yarta da mijin ta, likita yace idan har ba asamo yarinyar da zata iya acting kamar yartaba, to zata rasa ranta ne..." Wagowa Unaisah tayi a hankali ta kalle shi da alama taji tausayin matar.

"Muna so kije a matsayinta Unaisah, nasan zaki Iya!"

"Daddy na amince muje asibitin, dama najima ina neman hanyar da zan kyautatama chief, na ji dadi data kasance yar uwar shi, Allah yasa in zama silar samun warakarta .." murmushi taj yayi

"Ameen, amma akwai abunda nakeso in ja maki kunne akai! Idan har muka kaiki asibitin kada ki kuskura ki faWa ma wani ina raye! Ko ki bayyana wacece ke! Saboda har yanzu rayuwarmu tana acikin hatsari akwai masu bibiyarmu unaisah! WaWanda suka kashe uzair zasu iya kashe ni idan sukaji ina raye!" cikin matsananciyar damuwa yayi mata maganar donta dauki abun serious...girgiza kai tayi"daddy bazan bari kowa ya sani ba, saboda bana so na rasa ka"
"Koda wani ya nuna ya sanki ki ce bake bace, kinji"? ?aga mashi kai tayi...
"Ko kinsan mutun kika ganshi kada ki tanka mashi ko ki nuna kin sanshi, tun da haryanzu bamu san wanene ya sadaukar dake ba!"

Gefen fuskarta yashafa da hannun shi, ki fara shiri zuwa anjima da daddare zamu tafi" ta amsa mashi da toh, jan ta da fira ya farayi duk don ya faranta mata rai ko ta manta damuwar da take a ciki.......

______________________________
'?

wuraren ?arfe biyar, A jere motocin su Alhaji musa suka kunno kai cikin asibitin, A parking space suka dakata, da sauri body guard din dake driving din sa ya fito ya bude mashi mota, gently ya fito, ya Wauki wankan shadda mai Waukar ido, fuskarsa na sanye da mask, Iya idanunsa ne kadai zaka Iya gani, fitowa Alhaji ubaid Yayi daga motar, a tare suka nufi ciki, wani irin farin jini ne da shi duk inda ya gifta satar kallon shi ake, daga nurses har drs din kai harma da visitors.

Duk da ya 6oye fuskarsa hakan bai hana wasu gane shi ba, cikin girmamawa likitoci ke gaishe da shi wasu kamar zasu durkusa ?asa, cikin isa Yake Waga masu hannu batare daya furta magana ba....

Kafin su karasa ga medical room din, suka hango dr shureim tare da Aneelerh da zahra atsaye suna tattaunawa....

"Shureim"! Alhaji ubaid ne Ya kira sunan shi, kusan atare zahra da Aneelerh suka dago tare da kallon su...Rass Aneeleeh taji gabanta ya faWi ba ita ba hatta zahra saida taji wannan yanayin datayi tozali da Alhaji musa, Yayi matukar jan hankulansu...

?ura mashi ido Anila tayi, a lokacin dr shureim Ya karasa wurin su, kamar taso ta gane wanene, sai ta ga kamar uncle din benazir, bazata ta6a mantawa da Wan tahalikin nan ba, saboda kyautatawar da yayi masu tun da kuruciyarsu, kafin daga baya lokacin daya taka matsayi mai girma gaba Waya suka daina jin duriyarshi.

"Aunty Aneelerh wanene wannan"?
"Kamar uncle din benazir, banga fuskar dakyau ba amma inaji araina shi ne. ." bata ?are maganar ba, su Alhaji ubaid suka karaso wurinsu, atare suka haWa baki wurin gaishe da su
Alhaji ubaid ne kadai Ya amsa masu, da fara'a Yace"Aneelerh sannunku da kokari, Ya mai jikin"? Ita yake yi ma magana amma hankalin ta na akan Alhaji musa ya wani kau da ido kamar bai gan su ba.

"Alhamdulillah daddy, Jikin nata da sauki ba kamar jiya ba"

"Aneelerh ga Uncle musa ku gaisa ko baki gane shi ba..." dr shureim ne ya faWa
Murmushin yake ta saki"ina wuni..." ?asa ?asa da murya ya furta"lafiya..." zahra na gaishe shi ko kallo bata ishe shi ba, Ya wuce Ya nufi dakin Alhaji ubaid yabi bayan shi.

jinjina kai zahra tayi aranta ta ayyana wannan wani irin mutunne? daga gani Yana da girman kai da izza.

"Shureim ko dai Ya manta dani ne? Naga kamar bai gane ni ba, duk sai naji ba dadi..."
Shiru shureim yayi har cikin ranshi baiji dadin halin ko'in kulan da alhaji musa Ya nuna ma Aneelerh ba bayan ya santa farin sani...

Murmushi ya Wanyi kafin Yace"bana tunanin ya ganeki"

Ajiyar zuciya taWan sauke kafin suka cigaba da magana game da yarinyar da suke jiran zuwanta anjima...

Lokacin da su Alhaji musa suka shiga dakin, Hajiya layla tana azaune kan prayer mat, hannunta ru?e da cazbaha, kamshin turaren Alhaji musa ne Ya fara dakar hancinta kafin sallamarsu ta ja hankalin ta ga duban su, kamar taga wani mugun abu haka ta zabura ta mike tana kallon shi cike da mamakin ganin shi, saboda bata tsammanci zaizo ba tun da bai damu da benazir ba....

Tunda ya shigo idonshi na akan Benazir wadda ke kwance ta lumshe idanunta sai sambatu takeyi ?asa ?asa, kai tsaye ya nufi gaban gadon Ya zauna kan chair din dake fuskantarta
"Sannu daughter, Ya jikin naki"? Ya faWa tare dakai hannu Ya shafa goshin ta, a firgice ta bude ido tana kallon shi, la66anta na kerma ta furta"Uncle! Daddy! ina babyna? Ina Angel dina, dan Allah ku nemo min taj ya kawo min babyna"

Lumshe ido Alhaji musa yai kafin a hankali Ya furta"calm down your mind, zansa a nemo maki ita, but ki fara kwantar da hankalin ki"

rurruke hannunshi tayi acikin nata"dan Allah ku kawo min ?ata da mijina, uncle ku taimaka min kada na mutu ban gansu ba...."

tun shigowar shi bai dago Ya kalli hajiya layla ba, kamar babu ita adakin, wato yafi karfin yayi mata magana.

Ita ko tayi tsaye tana kallon ikon Allah, sam batayi farin cikin zuwan shi ba, gani take kamar ba alkhairi ne Ya kawo shi ba...

Gyaran murya Alhaji ubaid yayi mata

"Layla ya jikin nata"?

"Da sauki, mun samu taci abinci har wanka na taimaka mata tayi"

"Ya ake ciki game da yarinyar da Aneelerh zata kawo"?

"Sai zuwa dare zata zo asibitin"

"Allah Ya kawota lafiya, amma iyayenta ba su nemi komai ba"?

"Sai dai sunzo zamuji"

ajiyar zuciya yadan sauke

"Ba kiga musa ba ne? Naga baku gaisa ba" ya fada tare da nuna shi da hannu...
Harara ta watsa mashi kafin tace"ay shi yakamata ya fara yi min magana bani ba, sai kace dai Nina tursasa mashi yazo asibitin"?

gaba daya maganganun da suke tattaunawa akan kunnansa ko ajikinsa.

Sun Wan jima kafin ya mi?e Alhaji ubaid Yabi bayansa suka fito daga dakin
Sai da suka fara zuwa office din likitan dake kula da ita don jin karin bayani dangane da lafiyarta, kafin suka fuce daga asibitin.

_________________________________
'?

Wunin ranar Danish bai le?o ko kofar dakin sa ba, babu wanda Yasan halin da yake a ciki, kamar yadda ita ma ta killace kanta adaki, wuni tayi kudundune cikin bargo lokacin sallah kaWai ke tada ta, tuni zazza6i ya lullu6eta jikin ta har kerma yakeyi kamar zatai hauka saboda azabar raWaWin da zuciyarta keyi mata, tayi kukan har ta gaji ta gode ma Allah, danish ya dasa mata tsanar shi a zuciyarta, ko sunan shi bata son ambato, hauka tadinga tana bubbuga mattress da hannayenta kamar yar dambe duk ta hargitse dakin a karshe ta fashe da kuka tana fadin"ka karya min zuciya my man, na tsane ka! Bana son ka! Bana son ganin ka! Ban ta6a tsammanin zaka iya cutar da rayuwata ba! Meyasa kayi min haka? ..." tajima tana haukanta ita kadai kamar zata zauce.

Wuraren ?arfe takwas na dare, taj ya kirata awaya yace ta shirya ta same su a parking spot, jiki na rawa na shiga toilet, dama a kagare take data bar gidan kodan ta nisanta da shi, watakil ta samu relief din radadin da heart dinta keyi mata.

Bayan ta fito shaf shaf ta shirya cikin abaya, ta dauko kaya kala uku ta cusa a backpack dinta, ta goya jakar abayanta, ta zura takalmanta kafin ta dauki wayarta, babu wanda Yasan da zancen tafiyarta, harta fuce daga gidan.....

Cikin sauri take tafiya kamar zatayi tuntu6e, a parking space ta hango daddynta tsaye, ya sanya face mask a fuskarshi
Kallo Waya yayi mata ya fahimci har yanzu akwai sauran damuwa atattare da ita
Baisan ya zaiyi da ita ba, taki fada masa damuwarta, buWe mata murfin motar yayi, wani sanyayyan kamshin turarene Ya daki hancinta, nan take ta gane kamshin wanene da sauri ta dago ta kalli daddyn nata
Murmushi ya sakar mata kafin yace"ki shiga mana"
"Wanene a ciki"? Ta jafe mashi tambayar
"Chief ne, tare da shi zamu tafi" jim ta Wanyi kafin ta kutsa kai ciki, har saida gabanta ya dan fadi lokacin da ta sauke idonta a kanshi, yana daga zaune ya Wauki wankan shadda blue sky tayi bala'en yi mashi kyau, laptop dinsa ce akan laps dinsa, ya dan lumshe idanunshi....
Bata san ya akai ta tsinci kanta da jin wani irin sanyi acikin zuciyarta.

Sai da ta zauna gefen shi kafin ta samu kwarin gwiwar yi mashi sallama tare da gaishe da shi...
Calmly ya amsa mata...
Nutsuwa tayi idon akan glass din motar da bai karasa rufewa ba, tana iya hangen filin gidan....
"Zamu Iya tafiya" chief ne Ya faWa, security din dake zaune a driver seat Ya tada motar, A hankali Ya fara driving dinsu, motarsu big guy tana abiye da bayansu su biyu aciki tare da daddynta, sai motar jami'ansu dake abiye da su....

Lokacin da motocin suka haura kan titi, ajiyar zuciya ta sauke tare da kwantar da kanta, ta lumshe idanunta, bakomai take tariyowa ba face abunda Ya faru tsakanin ta da danish, tayi fatan ace mafarkine ba gaske ba..........bata san sa'adda hawaye suka gangaro takan kuncin ta ba, kwata kwata ta manta da chief acikin motar,

Ranta ne ya bata ana kallonta, a hankali ta buWe idanunta waWanda suka kaWa jawur, karaf idanunsu suka shiga cikin na juna.....
Daga ita har shi sun kasa sarrafa kansu, wani irin kallo suke bin juna da shi mai wuyar fassaruwa
?amshin turarenshi ba karamin kashe mata jiki yayi ba..."

Tsananin tausayinta ne Ya kama shi, har yau yana mai mamakin kananun shekarunta da kuma irin wahalhalun rayuwar da ta fuskanta, shi tunda yataso rayuwarsa baisan menene wahala ko rashi ba.

"I don't want to see your tears..."

*
'DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE
'?*

*Mu haWu Jibi, Idan Allah yakaimu da rai da lafiya, Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu duniya
*Zuzeam empire* takawo muku babbar gara basa
Duka akan 5500 ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa =????=????=????=??<؁?=؃? ?

Wa.me/+2348144015291 For more information say hi =?K? Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam empire tashirya tsaff dominku=؃?=؃?=؃? muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu

*DAHUWAR KAZA*

Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato *Ni ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya*
Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt *Akwai kyauta <؁? mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya*

*INA MASU JEGO DA AMARE*
Karku bari wannan dama ta wuceku
*08144015291*
Zuzeam empire

ASSALAMU ALAIKUM Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 08144015291. 1000 kacal =?L?
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd

Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar g1da set
Mai jego set

Dadai sauransu


___________________________________
'?



EPISODE


*OIH*

Kwance take tana sharar bacci cikin kwanciyar hankali, cikin bacci ta yi kwakkwaran juyi zata gyara kwanciyarta kwatsam tayi arba da fuskar mutun wani irin firgita tayi a haukace ta zabura zata mike da sauri Benazir ta cafko hannun ta ta ru?e shi gam, suka ?urawa juna ido batare da ?yaftawa ba, Hankalin Unaisah ba ?aramin tashi yayi ba, ta rasa gane meyasa cikin ?an kwanakin nan matarke tsareta da ido kamar zata lashe ta, aranta ta ayyana kodai ta6in hankalin nata ne Ya motsa? Kada fa ta hau ta da bugu tun ba hankaline da ita ba..tuni tasha jinin jikin ta, tana faman haWiyar yawu kutt murya na rawa ta furta"am..um.. mamana! Tun yaushe kika farka"? Dakyar ta kare maganar ganin yadda Benazir tayi mata rumfa kamar zata danne ta, babu alamun zata tanka mata tayi shiru tanata kallon ta...babban tashin hankalin unaisah hajiya layla bacci takeyi balle ta kawo mata Wauki, tuni ido ya raina fata.
"Dan Allah na ro?e ki, ki daina kallona haka, babaynki ce fa, ki na bani tsoro. .." sai da tay wannan maganar, Benazir ta saki murmushin gefen fuska har dimple
dinta ya lotsa...
"Babyna ne"? La66an unaisah na kerma tace"ni ce, dan Allah kada kiyi min komai..." ?ar dariya benazir tayi, wani irin nishadi take ji..
Shafa sumar kanta tayi har wani kyafkyafta idanu take Yi kamar wata mara gaskiya
Unexpected ta ji ta manna mata sumbata kan kuncinta, kafin tayi wani yunkuri ta kara mata wani kan la66anta, runtse idanu tayi kamar zata fasa ihu ta furta"na shiga uku, tawa ta same ni"! dariya benazir tayi kafin ta janye jikinta daga na unaisah ta koma kan gadonta ta kwanta idanunta na fuskantar ceilling..." wasu zafafan hawayene suka wanke fuskarta da sauri ta cusa kanta jikin pillow,
Satar kallon ta unaisah tayi, ta rasa gane meke damun matar, ta fara tsorata da lamarinta, kwanakin nan ta canza mata, ba kamar farkon da tafara jinyarta ba, ko meyasaS'

Ajiyar zuciya ta sauke, kafin ta sauko daga kan gadon, ta lalla6a cikin sanWa take tafiya, backpack dinta ta buWe ta curo wayarta ta nufi toilet ta shige ciki,

Text message ta tura ma daddynta

"Daddy, barka da dare, daddy ni dai nagaji da zaman asibiti, gida nakeso in dawo" tana tura mashi text din jim kaWan saiga kiran shi, tayi mamaki saboda batasa rai zai bata amsa ba kusan karfe shabiyu na dare, tayi zaton yayi bacci.

Picking call din tayi tare da kara wayar a kunne"My daughter! Me kike yi har yanzu baki kwanta bacci ba? Wani abu ya faru ne"?

Cikin muryar raWa ta furta"ba abun da ya faru, kawai bana jin dadin yawan kallona da matar takeyi, duk in na farka tsakar dare saina ganta akaina ta tsare ni da idanunta"

Sautin dariyar shi ce ta ratsa kunnanta aiko ta haWe fuska kamar tana agabanshi tace

"Daddy dariya kake yi min?

"Sorry daughter, maganarki ce ta bani dariya, but ki ?ara hakuri Anila ta fada min next tomorror za'a sallame ta"

Shagwa6e fuska tayi, ko tsoro bata ji ita kadai a toilet


"daddy ina yan uwana? Yau banji muryoyin su ba"

"Suna nan cikin koshin lafiya, basu da wata damuwa"

Shiru sukayi na wani lokaci, zuciyar ta sai azalzalarta takeyi akan ta tambaye shi ina Danish amma ina takasa furtawa...

Kamar taj ya karanci abunda ke zuciyarta sai taji yace"Daughter, labari me dadi, dan uwanki Danish ya fara koyon rubutu da karatu a wurin chief, abun saiya baki mamaki yana da kaifin basira, kamar ke lokacin da kina ?arama, kwakwalwarsa tana ja, abun burgewa sun shaku sosai da chief in kika gansu kamar ?an uwan juna, tare sukeyin komai......." batasan ya akai ta tsinci kanta da sakin murmushin gefen fuska ba, har cikin ranta taji dadin jin labarin nan da daddynta ya bata..

"Daddy, na taya shi murna, kuma naji dadi wlh, Allah ne kadai zai iya biyan chief, yayi mana hallacci arayuwar mu, ina jin dadin kyautatawarshi agare mu, Allah yasaka mashi da mafificin Alkhairinsa....." addu'o'i ta cigaba da yi mashi daddynta yana amsa mata da ameen

Kafin daga bisani yace"daughter, ki koma bacci, bana so ki makara sallar asuba, kiyi addu'a kafin ki kwanta sannan ki kula min da kanki"

"Toh daddy, kaima ka kwanta kayi bacci, ka kula min da kanka" bayan sunyi sallama da juna, kasa motsawa tayi daga cikin toilet din, wani irin yanayi take jin kanta mara misaltuwa, tanaji aranta kamar tayi missing din wani abu da zuciyarta take muradin son gani, ta wani bangaren taji dadin labarin cigaban da danish ya samu s???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?osai har wani dan murmushi ta saki

Lumshe idanu tayi tare da jingina bayanta jikin wall na tsawon mintuna kafin ta juya ta buWe kofar, cikin sanda take tafiya tana satar kallon gadon benazir, ta lullu6e jikinta da bargo da alama ta koma bacci, hakan ba karamin dadi yayi ma unaisah ba..
Kan gado ta haye ta kwanta tare da jan duvet tayi covering jikin ta


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login