Showing 234001 words to 237000 words out of 298130 words

Chapter 79 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

hankali sheikh Imam Ya fito daga dakin, farar jallabiya ce a jikinsa, ya Waure kanshi da rawani, hannun Waya ru?e da cazbaha.

cikin girmamawa suka fara yi mashi sannun da fitowa da fara'a ya amsa masu
tambayoyi suka fara jere mashi kamar yan jarida
"Malam ya ake ciki? Ya jikin marwan? Ta samu lafiya? Dagaske aljanune suka shafe ta? Sheikh zamu iya shiga ciki mu duba ta?

?aya bayan Waya sheikh Imam Yake kallonsu, Ya rasa wa zai fara amsa ma tambayar shi sun ?i bari Yayi magana, ya fahimci sun matsu da su san awani hali take ciki.

har ya buWe baki zai yi magana Saiga baba obie tare da pravin sun nufo wurinsu.

Mi?a mashi hannu baba Obie yayi suka yi musabaha"sannu da kokari sheikh, Ya mai jikin? An dace kuwa"? Fuskarshi da fara'a yace"mu shiga daga ciki ku gani da idonku.." da sauri suka nufi dakin su hajjaty suna abiye da bayansu, agaban katifar marwa suka tsaya cirko cirko, tana a kudundune cikin bargo jikinta sai makekketa yakeyi, tuni pravin Ya haWe fuska tamkar bai ta6a dariya ba, ga wani gumi mai Wumi daya wanke goshin shi, Hanky ya zaro ya fara goge zufar.

An rasa wa zai fara cire bargon murmushi sheikh imam yayi don ya fahimci tsoro suke ji, da zolaya yace ma baba obie"baba kai yakamata ka fara cire bargon mu gani" waro ido baba obie yayi haWi da girgiza kai yace"ya zakai min haka? dan Allah kadaina wannan maganar, kai dai daka fara aikin kai yakamata ka karasa ladarka.."

yar dariya Sheikh Imam yayi tare dakai hannu ya ru?o bargon ya fara jan shi ahankali, pravin kamar ya daura hannu akai ya fasa ihu haka yakeji duk ya rasa sukuninshi kamar wani munafiki sai cizon yatsa yakeyi..
Su hajjaty sun baza na mazurai suna jiran ganin marwa, gabansu sai faduwa yakeyi .

Lokaci da sheikh Imam ya ?arasa cire bargon, gaba Waya suka zabura suna kallonta idanunsu azazzare cike da mamakin ganin bakinta Ya buWe sunyi matukar razana da lamarin, ta ko'ina zufa ce ke tsastsafowa ajikinta kamar wadda aka tsamo daga cikin tafki, kafafunta sun mi?e daga lauyewayar da sukayi, amma yatsun hannayenta basu dawo daidai ba har yanzu da kuturtar sai dai yatsun sun Wan saki ba kamar farko da suka matse ba har suna fidda ruwa mai yau?i yanzu babu ruwan.

Kusan Atare su hajjaty suka ambaci sunanta da karfi Marwa.

buWe baki tayi zatayi magana sai dai ta kasa sautin muryar baya fita dakyau gura gura take magana kamar wadda harshenta ya ?one kwata kwata ba'a iya gane me take cewa, har sun fara murna taji sauki ashe da sauranta, pravin har zai fita daga dakin jin takasa magana yasa shi dawowa ya tsaya yana kallon marwa afakaice yake sakin murmushin mugunta.


Jikin su hajjaty yayi sanyi lakwas, har sun fara sharar kwalla
Baba obie yace"Ikon Allah! sheikh dagaske dai jinnune suka shafe ta? Ya fada cike da son jin karin bayani, a tsanake sheikh imam ya ce
"Eh, bakaken aljanune a jikin ta, sune suka haddasa mata ciwon..." waro idanu waje su hajjaty sukayi wani irin tsorone Ya kamasu murya na rawa abla tace"dama Aljanu suna iya canza ma mutun halittar shi" jinjina mata kai sheikh imam yayi"fiye da haka ma zasu iyayi.." kallon kallo suka jefawa junansu.

AruWe baba obie ya furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un!

Zu?unnawa sheikh imam yayi daga gaban katifar marwa idanun shi akan fuskarta Ya soma magana"kada ki sanya damuwa aranki, Allah yana atare dakai, duk wani abu da kika ga ya faru dake mukaddarine daga Allah, bana so ki kuntata kanki, ko ki ?yamaci kanki, balle kiyi tunanin illata kanki saboda wannan lalurar data same ki, kiyi kokarin cinye jarabawarki kada ki gaza, Aljanun da suka haddasa maki ciwon nan suma bayin Allah ne, babu abunda ya fi karfin mahaliccin mu...." tun da ya fara magana idanun marwa suka cicciko tab da kwalla ita kadai tasan me take kitsawa aranta.

"nayi al?awarin zan taimaka maki amma fa dole sai kema kin taimaki kanki, kiyi kokarin bin abun da Allah da Manzonsa sukace ayi domin samun kariya daga sharrin su, da zuciya Waya in sha Allah zaki ji sau?i, jikinki zai dawo kamar yadda kike ada" jinjina mashi kai tayi alamar ta gamsu da maganar shi.

"Ma.. malam muma ataimaka mana dan Allah, ka faWa mana hanyoyin da zamu kare kan mu daga sharrin su"

cikin shesshekar kuka abla tayi maganar.

murmushi sheikh imam yayi tare da kallonsu Waya bayan daya sai yaji sun bashi tausayi ganin yadda jikinsu ke ta kerma kamar mazari

"Ku samu wuri ku zauna zanyi maku bayani" da sauri suka kewaye sheikh imam suka zauna kan ?asa suna jiran jin me zaice.

Mi?ewa yayi da sauri ya Wauko kujerar mirror Ya ajiye agaban baba obie don ya zauna.

"Nagode sheikh" ya fada tare da zama kan kujeran.

Tun shugowar pravin dakin sheikh imam bai Waga ido Ya kalle shi ba, sarai ya san da zaman shi, dama tunfil azal basa jituwa tsakanin su ko gaisuwa bata ta6a haWasu ba,

Shiru yayi kamar akwai abunda Ya hana shi fara magana, wayar pravin ce ta fara ringing daga cikin aljihunsa da sauri ya fuce daga dakin don ya amsa kira.

Fitar shi keda wuya sheikh Imam Ya fara magana yana duban marwa cikin tattausa harshe yace mata"kiji tsoron Allah! Rass gabanta Ya fadi, su hajjaty suka kalle shi da alamun rudani akan fuskokin su.


"Idan akwai wani abu da kike aikatawa badai dai ba to ki daina! Sau dayawa mu muke ja ma kanmu shiga cikin masifa, Allah ya gatanta mu ya bamu hanyoyi da dama da zamu iya ba kanmu kariya amma muna wasa damar mu...." ga dukkan alamu Sheikh imam Ya canza maganar daya dauko da farko hannunka mai sanda yayi mata kuma ta fahimce shi hakan yasa ta du?ar da kanta ?asa hawaye suna cigaba da wanke fuskarta.

"Kina yin azkar? Girgiza mashi kai tayi alamar a'a

"Baki iya ba ne"? ?aga mashi kai tay alamar eh.

"Ya salam! Wannan wani irin ganganci ne? Da ranki da lafiyarki? Wallahi da ace kina kokarin kiyayewa babu wani mahalukin daya isa ya cutar dake in ba Allah ne ya kaddara za'ayi galaba a kanki ba, azkar garkuwa ne agare mu, ita kuma addu'a da kike gani takobin mumuni ce kuma ita addu'a tana iya canza kaddarar mutun, daga mummuna zuwa mai kyau.

Nasiha ya fara yi mata jikinta yayi sanyi lakwas, su abla tuni ido ya raina fata don su kansu bakowane keyi ba har kwara hajjaty itada ta musulta daga baya tana kokarin yi akai akai

"Gaba Waya inaso ku bani aron hankulanku, ku saurari abunda zan fada maku..." amsa mashi sukayi da toh,

Shiru yayi jim kafin ya fara magana"abunda ya kamata ku sani shine, Zikirin safe da yamma yana da matu?ar mahimmanci sosai, wanda inda Musulmi yasan mahimmancin sa da kuma kariya da yake bashi da bai barshi ba koda na kwana Waya ne, don haka ina ?ara jan hankulan ku da Ku yawaita Lazimtar Zikirin safe dana yamma.." atare suka hada baki wurin furta in sha Allah malam zamu kiyaye
Shiekh imam ya Waura da cewa"abu na gaba Yin alwala, mutum ya kasance yana yawaita zama cikin tsar?i domin hakan na bada kariya, bayan haka akwai Qiyamul laili, da kuma Neman tsari yayin shiga bayan gida (toilet) idan zaku yi bacci ku yi alwala, sannan ku karanta ayatul kursiyu bayan ita sai falaki da nasi suna da Muhimmanci sosai..." jinjina kai kowan nan su yayi sheikh imam ya numfasa yana dubansu kafin ya dasa da cewa

"Sannan FaWin La ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu, lahul mulku wa lahul hamdu wahuwa Ala kulli shai in kadir sau Wari safe da yamma
FaWin Bismillahillazi la ya durru Ma asmihi shai un fil ardi wala fissama wahuwa ssami ul alim sau uku safe da yamma, FaWin  A uzi bikalimatillahit-tammat min sharri ma khalaka sau uku safe da yamma"

baba obie ya nutsu yana sauraron sheikh imam har cikin ranshi yaji dadin yadda ya zaunar da yan aikin gidan yana koyar dasu yadda zasu kare kansu hakan ba karamin faranta ranshi ranshi yayi ba, shi kanshi ya karu da sheikh imam.

"Malam, wallahi ni yawan mantuwa gare ni, kona yi kokarin yi sai wani abun yaja hankalina..." Sofia ce tay maganar, shiekh imam Yace"akwai islamic apps na waya, da zaki iya sauke wa.." da sauri hajjaty tace"ina da shi zan tura mata nima dashi nake amfani, shi yake tunasar dani lokacin yin ibadata da kuma lokacin yin azkhar" murmushi sheikh imam yayi idon shi akanta yace"kinyi masu wayau, zaman tare baice haka ba, meyasa tuntuni baki sanar da su ba"?

Sunnar da kanta ?asa tayi
Calmy ta furta"ay ni bansan ba su amfani da shi ba"

GyaWa kai yai"haka ya dace, In ka san abu na karuwa ne, to ka yi kokarin sanar da wasu suma su amfana, na tabbata da ace shirin labarina ne aka saki jiki na rawa zaki fada masu koba haka ba"? Gaba daya suka sanya dariya.

Murmushi baba obie yayi, shima sheikh imam din murmushine akan fuskarshi.

Baiwar Allah marwa duk da halin da take aciki saida tayi murmushi fuskarta sharkaf da hawaye...

Nasiha ya cigaba dayi masu akan su daina shagala duk runtsi duk wuya kada su yi sakaci da ibadarsu da kuma neman tsari daga gurin Allah, cike da gamsuwa suke sauraran shi daga bisani yace Idan har ku ka kiyaye zikirorin dana faWa maku, sannan ku ka kuma ?aurace wa saSon Allah toh ha?i?a Allah zai kare ku daga kowani irin sharri, kuma zaku yi rayuwa cikin kwanciyar hankali domin da Ambaton Allah ne da yimasa biyayya ake samun natsuwa. Allah yasa mudace" atare suka amsa mashi da ameen haWi dayi mashi godiya
Baba obie yace"sheikh muna godiya sosai, jazakallahu khairan..." da fara'a ya amsa mashi da ameen...
Kafin ya kalli Su abla"ina bukatar mutun Waya da zai dinga kula da marwa"

shiru su ka yi kowa tsoron kusantarta ya ke yi, yanzu ma da suke adakin don sunga sheikah imam ne ga baba obie shiyasa suka saki jiki.

"Kada ku bani kunya mana! Kun riga da kunsan lalurar nan ba ita ta daura ma kanta ba! idan har kuka ce zaku juya mata baya ko ku ?yamace ta zaku sa ta tsani kanta ne harta aikata ma kanta abunda bama fata, ayanzu bata da wasu yan uwa na kusa da ya wuce ku, ku take gani amatsayin yan uwanta wadanda zasu share mata hawaye...."

cikin sanyin murya hajjaty tace"wallahi bani ?yamar marwa, kawai abune da bamu saba gani ba, muna jin tsoro amma in sha Allah zamuyi kokarin bata kulawa, ni nayi alkawarin zan dinga zuwa dubata...."

Shiekh imam yace"Alhamdulillah, naji dadin jin hakan daga gare ki, zuwa anjima in sha Allah zan aiko maki da magunguna na musulunci, sannan kafin in tafi zan kar6i contact dinki saboda in tura maki addu'o'in da zaki dinga tofa mata aruwan wankanta dana shanta,.."

"Toh malam, muna godiya Allah ya saka da alkhairi..."

mi?ewa yayi bayan yayi masu sallama baba obie ya ruko hannun shi suka fita daga dakin....

Kamar jira suke sheikh Ya fita daga dakin da sauri su abla suka gudu zuwa kitchen Ya rage saura Hajjaty adakin.

Bata san sa'adda ta fashe da kuka ba, gashi ba halin Yin magana, da hannu ta dinga bugun katifa tana kuka, da sauri hajjaty ta rukota tana lallashin ta idanunta cike tab da kwallo, wani irin tausayintane Ya kamata.

"Marwa ki daina kuka, In sha Allah zaki ji sauki ki dawo kamar yadda kike ada, nayi alkawarin zan taimaka maki muyi duk abunda sheikh imam yace"

tunda hajjaty ta fara magana marwa tayi shiru tana kallonta wallahi tayi danasani yafi sau a ?irga, kuma tayi mamakin yadda hajjaty ta amince zata kula da ita sa6anin sauran yan uwansu da suka gudu daga dakin.

Bata ta6a tsammanin hajjaty tana da saukin kai, da tausayi ga mutunci irin na yau ba, sai taji ta tsani kanta, hakanan batai mata laifin komai ba mace mai kyakkyawar zuciya amma saboda abun duniya ta amince zata yi mata le?en asiri don abata matsayinta akuma koreta daga gidan wa'iyazubullah, bakomai ta tuna ba face hajiya saratu, ita da tayi silar jefata halin da take aciki, amma kwata kwata bata nuna damuwarta akanta ba, ko kalmar sannu ay ya kamata ta furta mata, ayanzu ta gane wasu mutanan sai kana da amfani agurinsu suke kula ka da zarar sunga bazasu amfana dakai ba sai su watsar dakai, tayi danasani taso ace tana da baki da yau saita fallasa asirin wanda yayi silar jefata halin da take a ciki ko da zata rasa ranta neW'

Amma duk da haka bata makaro ba, ta Wauki alwashin saita tona asirin wanda ya cutar da ita!

"Marwa"! Muryar hajjaty ce ta dawo da ita daga duniyar tunanin data lula
"Kiyi hakuri Kinji yar uwata, bana son ganin hawayenki, nasan kina jin yunwa bari na kawo maki abinci in kika kammala ci sai in taimaka maki kiyi wanka..." kifa kai marwa tayi jikin pillow ta rushe da kuka mai tsuma zuciya, tamkar ranta zai fita, zuciyarta ta karaya, a halin yanzu ba rayuwarta ta ke jima tausayi ba, rayuwar hajjaty itace abun tausayi....dakyar hajjaty ta shawo kanta har ta samu marwa ta daina kuka, da sauri ta mike taje kitchen donta haWo mata abunda zata ci.

___________________________________
'?


*Hajiya Saratu*

A zaune take kan mirror chair jikinta sanye da sleeping gown ta manyan mata, fuskarta sam babu walwala ta zabga tagumi da hannunta Waya bata jima da farkawa daga bacci ba, ko wanka ta gaza shiga tayi, saboda rashin kwanciyar hankali, duk bayan yan mintuna saita duba wrist watch din hannunta, lumshe idanunta tayi yayin da acan ?asan zuciyarta take tariyo maganganun da suka tattauna ita da Hajiya laurat a jiya, bayan ta taso daga office tsoro da fargaba suka hana ta dawo gidan, tace ma driver dinta ya wuce da ita aso villa acan suka haWu da hajiya laura tun daga kan yanayin fuskar Hajiya saratu ta fahimci babu lafiya akwai wani abu da yake damunta, bayan sun zauna a pool yard masu yi masu hidima suka kawo masu coffee da kayan marmari tace mata bismilla su fara sha, girgiza kai tayi alamar bazata sha ba, hajiya laura tace wai meke damunki ne? kiyi magana mana, a shirye nake da in taimaka maki don mu shawo kan matsalar, ajiyar zuciya hajiya saratu ta sauke tana faman yamutsa fuska ta kwashe komai daya faru dangane da ciwon marwa ta sanar da hajiya laura.

"Wallahi ina cikin tashin hankali, zama gidan ma ya gagareni, yanzu haka da kika ganni daga office ko gida ban wuce ba nayo nan don in fada maki halin da nake ciki"

Shiru hajiya laura tayi jim da alamun ruWani akan fuskarta tace"ni abunda bangane ba, kina nufin dare Waya ta farka da lalurar"?

Waga mata kai hajiya saratu tayi, al'amarin ya Waure mata kai
"Kuma an kaita asibiti?
"Bani da masaniya, amma bari na kira baba naji halin da ake ciki" tay maganar tare da curo waya ta danna ma baba obie bayan ya Waga, ta tambaye shi awani hali marwa take a ciki, ya sanar da ita abun da likitoci suka ce, tayi mashi sallama ta Wago ta kalli hajiya laura da tayi zugudum tana kallonta, ta sanar da ita abun da baba obie ya faWa mata, ga mamakinta sai taga hajiya laura ta saki murmushin gefen fuska takai hannu ta dauki cup of coffee ta kurba still da murmushi akan fuskarta, hakan ba karamin Waure ma hajiya Saratu kai yayi ba fuskarta a Waure tace"bana son iya shege meye abin murmushi aciki?

Yar dariya laura tayi"kwantar da hankalinki mutuniyata, kinsan wani abu"? Girgiza kai tay alamar a'a

"Wallahi ko nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba yarinyar nan marwa silar ciwonta yana da ala?a da aikin le?en asirin da kika sanya ta!! Hankali atashe Hajiya saratu ta zaro ido tana kallon laura aruWe ta furta"ban..ban gane me kike nufi ba?

"Ke yanzu har sai nayi maki bayani? Yakamata ki gane mana, kiyi amfani da brain dinki, ciwon yarinyar nan aikin asiri ne, wlh ture akayi mata, in ba haka ba taya za'a ce rana Waya mutun ya tashi da cutar kuturta sannan ba baki, ai ke daga ji kinsan Waura mata ciwon akayi, Ni abun da na fahimta watakil hajjaty ta kama marwa tanayi mata le?en asiri, shiyasa ta kulle mata baki don kada ta iya furta magana, bayan haka ta ja mata cutar kuturta don kada ta samu damar da zata yi rubutu da hannayen ta balle harta tona mata asiri...."

Dafe kai hajiya saratu tayi yayin da zuciyarta ke bugawa da karfi da karfi gaba Waya tabi ta ruWe.

Hajiya laura taci gaba da cewa"hmmm wallahi Wan adam ba abun yarda bane! Dama na jima ina zargin hajjaty, indiyawan nan basu tsoro Allah, ko a fina finan su zakiga suna yawan zuwa wurin bokaye don ayi masu asiri, matar nan munafuka ce wlh, tana amfani da rauhanai shiyasa ta mallake mutanan gidanku har ta samu gindin zama take iya shegen data ga dama, yanzu gashi ta kassara rayuwar marwa....."

Runtse idanu Hajiya saratu tayi, hankalinta Ya tashi har wani dishi dishi take gani a idanunta muryarta na rawa ta furta"inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Na shiga uku"!

hajiya laura tace"ay mun sha ja maki kunne akan ki kori hajjaty daga gidan kika ?iya, ay ni banma san ya akai kika yi gangancin da pravin ya Wauko maki bakauya yar kauyan india masu bautar shanu ya ajiye maku agida, to wallahi kwara tun wuni ku dauki mataki akanta in ba haka ba hmmmm nan gaba Allah kadai yasan me zata aiwatar.." maganganun hajiya laurat sun tsaya mata arai sun kuma Waga mata hankali, bata ta6a jin faWuwar gaba da tashin hankali irin na jiya ba, ta jima a vila suna tattaunawa da hajiya laurat har shawarwari ta bata dangane da yadda zata kare kanta daga sharrin hajjaty da kuma hanyar da zata bi don ta gano ainihin wacece ita.

Bayan sunyi sallama da juna, hatta shiga motarta tana zullumi da fargaban hajjaty, ta tsorata da ita ba kadan ba, ko bayan data dawo gida kasa shiga bedroom dinta tayi saboda tsoro, dakin baba obie ta fara shiga ta zauna wurin shi har saida aka fara kiran magrib ya tashi zai tafi masallaci kafin ta dawo dakinta sam ta kasa


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login