Showing 69001 words to 72000 words out of 298130 words

Chapter 24 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

tayi gefenta, tare da kai hannu taja lallausan duvet dinta ta lullu6e fuskanta, ganin hakan yasa Yazrin fitowa daga bayan labulen cikin sanWa ta nufi gadon, tare da hayewa ta janyo wayar Nazli cike da fargaba cikin sa'a ta Wauko ta batare da security din wayar ya shiga ba, hakan ba karamin dadi yayi mata ba.

Whatsapp dinta taso ta shiga sai dai kash password Ya hanata, tunani ta soma yi me Nazli ta rubuta a matsayin password dinta?

Gudun kada ta tayi mistake ta samu matsal
Zurfi tunani ta shiga, can zuciyarta ta raya mata cewar ta jaraba rubuta date of birth din Aki Owais saboda ta ta6a ganin ta rubuta shi a diary din ta amatsayin rana mafi mahimmanci agare ta.

Wani irin tsalle ta daka ganin Ya buWe, da sauri ta shiga nutsuwarta tana le?en Nazli, wadda tuni bacci yayi awon gaba da ita
Yazrin tayi mamakin ganin tsawon lokacin da suka dauka ba suyi magana wa junansu ba, Ranta ya sosu bata ji daWi ba, ji take kamar ta dauki pillow ta bubbuga mata akanta tsabar haushin da taji.
"?ar bakin ciki, In sha Allah baki da miji a duniyar nan daya wuce big bro, bazan zauna na zuba maki ido kina cutar kanki ba, Akhi Owais shi ya dace ya mallake ki, nayi maki sha'awar auran shi saboda samun miji nagari irin shi ba abu ne mai sau?i ba, Ina son kiyi rayuwar farin ciki yar uwata, dole na shirya tsakaninku.... " acikin zuciyarta ta furta maganar tare da cigaba da danna wayar, daga wayarta ta tura video din data dauka, kaitsaye ta yi mashi sending, shaf shaf ta rubuta mashi text message da harshen turanci kamar haka

_Nayi kewarka bugun zuciyata, ina mai baka ha?urin nuna halin ko'in kula da nayi, ba'asan raina ba, nayi danasanin hakan don ba ?aramin cutuwa nake yi ba na rashin jin Wumin jikinka a kusa dani, ka duba whatsapp in ka, na tura maka video dina don ya Webe maka kewar rashi na, nasan zaka ji dadin kallon shi_

fuskar yazrin dauke da murmushin mugunta ta tura mashi message din, bayan ta gama ta ajiye mata wayarta, ta nufi kofar fita daga dakin tana faman sakin dariya, ta riga da tasan me zai biyo baya muddin Nazli taga aika aikan da tayi mata ba ?aramin husuma zata tada ba, zata ce ta zubda mata aji awurin chief owais.

*A GIDAN UNCLE ?AN IYA*

Kusan Atare Su ka yi Parking din motocin su, Mahboob ne Ya fara fitowa daga front seat hannun shi Waya ru?e da key din Motarshi, fuskarshi dauke da murmushi yake kallon Motar zahra.

"Sannu da dawowa Hajiya Zahra Surukar Kaka Obinna" Ya faWa tare da buWe Back Seat din Motar Shi Ya du?ar da kai Yana le?an Baby Junaid dake zaune Hannayenshi rungume da Food basket dinshi, Ga school bag din shi a gefe, Sai faman Waure fuska Yake, Da alama rigimar tashi ce ta motsa.

"Ranka Shi daWe, Mun ?araso gidan, zaka iya takawa da kafarka ne mu shiga ciki ko kuwa ni kake so In goyaka"? Da zolaya mahboob yayi maganar yana dariya.
Yamutsa mashi fuska baby junaid yayi "ni ka goyani" Ya fada A kule.

Juya mashi baya Mahboob Yayi Ya Wan zu?unna Baby Junaid Ya Haye bayan nashi, Bayan Ya mi?e Ya Wauko mashi Backpack dinsa tare da kwandonsa

Adai dai Lokacin Zahra Ta fito daga motarta, tayi shiga cikin Lafaya, Hannunta Waya ru?e da ?ar purse dinta
Fuskarta da fara'a take duban Baby Junaid Da Mahboob
"yau wata rana mun dawo gida atare, baby junaid dina zo nan" ta faWa tare da mi?a mashi hannu, babu musu Ya soma kiciniyar saukowa daga saman bayan mahboob, daukarshi tayi Mahboob yace"Wato ni kake gudu? Zamu hadune Wan rainin wayau, tun da naje dauko shi Daga school Yake ta jin haushina saboda naje amakare shi kaWai Ya rage ba'aje daukarsa ba, baisan nima bada son raina ba, Motarce ta samu matasala sai da nakaita gyara tukunna naje daukoshi da ita"
Dariya zahra tayi"Gaskiya baka kyauta ba, taya zaka bar mana Baby Shi kadai Ga yunwa, meyasa baka kirani awaya naje daukosa ba"

"Banyi dabarar yin Hakan ba, Yanzu dai tun da mun dawo gida, gashi nan ki kaima jatumarsa, nagaji da kallon kumburarran fuskarshi"

"Mahboob baka da mutunci, zamu rama ne" ta faWa tana dariya, baby junaid kuwa Ya Waure fuska, Kumatunshi sunyi jawur da su, da alama kuka Yake so yayi.

Atare suka nufi cikin gidan, tana agaba mahboob Yana abayanta
Bayan shigarsu Falo, Suka taras da mami da Ummi zaune suna kallo a plasma tv din falo, Cikin girmamawa suka gaishe da su.

"Sannun ku da dawowa, Ya gajiyar aiki"? Cikin Kulawa mami tayi maganar, atare suka hada baki wurin cewa"yawwa mami"
Ummi dake kallon Baby junaid tace"to fa, Me akayi masa ne naga yana Waure fuska"
Mahboob Na dariya Yace"wallahi Ummi Rigimarshi ce ta motsa, Kinsan Halin shi.

Zahra tace"bawani nan, shine Ya?i zuwa Waukarshi da wuri, Yabar shi a school yana ta jira"

"Gaskiya mahboob Baka kyauta mana ba, saboda Allah, Haka akeyi? Sai kabar mana Yaro ga Yunwa" Ummi ce ta faWa tana satar kallon baby junaid duk don ta nuna mashi taji Haushi.

"Ay mashi uziri mana, hakanan dai Mahboob bazai?i zuwa Waukar baby junaid ba sai dai idan wani uzirinne Ya ru?e shi" mami na fadan hakan Mahboob Yace"ay har bayani nayi ma zahran, motana ne Ya samu matsala sai da nakaita gyara, in sha Allah Hakan ma bazata ?ara faruwa ba zan dinga zuwa ina dauko shi akan lokaci"
Ummi tace"haka Yakamata"
"Zonan babyn mommynsa" acewar Ummi ta fada tana mi?a mashi hannu, ma?e mata kafaWa yayi alamar bazaije ba, Saima Ya ?ara ?an?ame Zahra, mami na dariya tace"In banda abunki sai kace bakisan halinsa ba idan Yana fushi Yafi bu?atar jin Wumin mommynsa,"
"Ina auntyn tawa take"?
"Tana a kitchen"
Maimaita kalmar kitchen Zahra tayi, aranta ta furta me kuma Aunty Aneelerh take yi a kicin"? Batayi ?asa a gwiwa ba, Ta nufi kitchen din Mahboob Har Ya zauna kan sofa, sai kuma Ya mi?e Yabi bayan zahra.
Tunkafin su ?arasa kitchen din suka hango Aneelerh ta haWa uban gumi a kitchen tana girki, Ita kadai.
Sam bata Ji alamar shigowarsu ba, ta zage damtse sai motsa miya take Yi
"Aunty Aneelerh"? atare suka haWa baki wurin kiran sunanta, da sauri Ta rufe soup pot din, Ta juyo tana fuskantarsu, kafin ta Waura idanunta akan Baby Junaid,
Murmushi ta sakar masu "Sannunku da dawowa,"
"Yawww, Auntyna, Yau ke kike Aiki akitchen Ina Ana"? Zahra ce ta jefa mata tambayar, Mahboob Yace"Allah yasa dai lafiya"
Girgiza kai tayi cikin sanyin murya ta soma magana"ba lafiya...." gaba Waya ta labarta masu abunda Ya faru zuwansu dakin Ana tare da su mami, Hankalinsu Ba ?aramin tashi yayi ba, Musamman Mahboob.

"Bansan Ya zanyi ba, Ta?i faWa mana abun da ke damunta, Ni tsorona kada wani abu Ya faru da ita" fuskarta da tsantsar damuwa ta furta maganar
"Nima hankalin bai kwanta da ita ba, dafarko nayi tsammanin Damuwar halin da ?an uwanta suke aciki ne ke damunta, ashe ba haka bane, daga gareta ne" Acewar Mahboob.
Kafin Zahra ta furta magana baby Junaid Ya fashe da kuka, Dama ranshi a6ace Yake, da sauri Aneelerh Ta mi?a hannu ta kar6e shi cikin sigar lallashi take jijjiga shi tana fadin"Am sorry My baby boy, kayi hakuri nasan nice na 6ata maka rai,' muryarshi da shesshe?ar kuka Yace"wayyo Allah mommy, Kuna ta surutu Kin ?i kulani, baki missing Wina ba" dariya zahra da mahboob su ka yi, hakan Ba ?aramin 6ata mashi rai yai ba, Hada Jifar Su da harara

Shafa sumar kanshi tayi"Na kar6i laifina, ay min afwa... " zumbura mata baki yayi,
Zahra tace"aunty Aneelerh, Ki tafi dashi Waki Ni zan ?arasa girkin, Inyaso da anjima Sai mu ?arasa tattaunawa"

"Keda kika dawo daga aiki a gajiye kuma kike neman in bar maki girki, a'a gaskiya Ki bari na ?arasa ai ba ni kadai nake yi ba, Tare da Ummi muke Yi, bata jima da komawa falo ba.. "
Kafin Ta ?are maganar???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?, Mahboob Yace"tun da tace zatayi kibar mata kawai, Nima saina tayata, baby junaid yana bu?atar kulawarki, Kije Ki lallashe shi"
Murmushi tasaki Tana kallonsu, Har cikin ranta take jin tsantsar kaunar Yan uwanta, HaWin kansu Na burgeta, fatanta Allah Ya dawwamar da farin ciki arayuwarsu, Hakika suna kyautata mata.
"Nagode, zahra, Mahboob, Allah Ya barmu mun ku,"
Amsa mata su ka yi da ameen
"Zan shiga ciki, pls zahra Ki dafa mashi indomie" amsa mata tayi da toh, Bayan fitar Aneeleeh daga kitchen din, Mahboob Ya ajiye food basket din Junaid, Yabi bayan aneelerh hannun shi ruke da backpack din Baby junaid,
Bayan Ya ajiye mashi adaki, Ya fito Ya nufi nashi room din, shaf shaf Yayi wanka Ya sanya gajeran wando da ?ar singlet, Kafin Ya nufi kitchen don Ya taya zahra girki kamar wani mace, atare suka cigaba da kula da girkin, suna tattauna fira dangane da matsalar Ana.
"Amma kai a tunaninka meke damunta"?
"Sister Ni kaina nakasa gane wani tunani zanyi dangane da matsalar Ana, sai dai kawai mubita da addu'a, Allah ya yaye mata abunda ke damunta,'
"Ni aganina, Mu kar6i Contact din ?an uwanta , mu tuntu6esu may be sunsan meke damunta, tunda sunfi kusa da ita"
"Nima nayi tunanin hakan, Yanzu dai mu jira, zuwa lokacin da su Abie zasu dawo gidan, nasan zasu Kirata su tambayeta,"
"Hmm kana ganin zata Iya faWa masu gaskiya? Bayan Aunty Aneeleeh tace tare da su mamie suka je dakin nata amma ta?i fada masu, ai ni aganina idanma akwai wanda Ya dace ta fadamawa baiwuci su mami dinba"

Jinjina kai Mahboob Yayi"kin fadi gaskiya,"
"Ni abunma Ya fara bani tsoro, da naji aunty aneeleeh tace Ana ta dinga kwala masu ihu tana fadin su fita subar mata dakinta, Anya mahboob bata da matsalar kwalwa?
Mahboob Yace"Bana tunanin hakan, wata'kil Aljanune suka shige ta, mu cigaba da tayata addu'a Allah Ya kawo mata saukin abunda ke damunta"

"In sha Allah zamuyi mata"
Daga haka basu ?ara magana ba, sun maida hankali akan Girkin da suke Yi.

Fitowa Aneelerh tayi daga Bathroom, Bayanta goye da baby junaid, tayi mashi wanka, sai faman hade mata fuska Yake Yi, Riga da wando ta Dauko ta zura mashi ajikinshi, ta feshe shi da turare, zama tayi gefen gadonta,ta Waura shi saman laps dinta, hannunta Waya dafe ta shi,tarasa meke yi mata daWi, Ita dai Hankalinta bai kwanta da halin da Ana take aciki ba, Ji take aranta kamar wani abunne Zai faru, zuciyarta batayi mata daWi, sam ta manta da baby junaid Tayi zurfi a tunaninta, Har Ya fara lumshe ido zaiyi bacci, Muryar Zahra ta fargar da su,
hannunta biyu ru?e da plate din indomie, Sai tiriri Take Yi, daga saman indomie din ta shimfiWa mashi Soyayyan kwai, Mahboob Yana abiye da bayanta, Hannun shi ru?e da mugs biyu na kakkauran Tea.

"Sannunku da kokari, nasanya ku aiki ko hutawa ba ku yi ba"

"Pls ki daina fadin hakan, Mu yakamata mu Yi maki sannu, anbarki da girki a kitchen, Su mami suna a falo fira tai dadi" Mahboob Ne yai maganar
Asaman Table zahra ta daura plate din, Mahboob Ma ya sauke nashi mugs din, atare suka fuce daga dakin.

Baby junaid tunda yayi tozali da indomi Ya soma sakin murmushin murna, Har wani lashe le6ensa Yake Yi
"Mommy da zafi, kuma ni Yunwa nake ji Allah" ashagwa6e Yayi maganar
"calm down Your Mind my baby boy, Ni zan baka da hannuna, kasan dai mommy bazata bar baby junaid dinta Yaji zafi ba ko"? ?aga mata kai yai alamar"
"Yawwa my boy" ta faWa tare dakai hannu ta dauki fork, ta soma nannaWo taliyar tana hura mashi da baki idan ta huce saita tura mashi abaki, kusan atare suka cinye indomie din dakwai, Kafin suka sha tea din su.
"Kada kayi bacci, Yanzu za'a fara kiran sallar magrib," Waga mata kai yai alamar toh, Janshi ta soma yi da fira duk dan kada yayi bacci.

Bayan Kammala sallar Magbrib, A lokacin Abie da Uncle Wan Iya sun shigo gidan, babu wanda Ya tuntu6esu da maganar Ana, sun bari ne sai sun huce gajiyar da suka kwaso ,Har saida suka kammala cin abincinsu, Tukunna Ummi ta sanar da su Halin da ake ciki, babu 6ata lokaci, Abie Yasa suka hallara A falon gidan gaba Wayansu, Ana ce kaWai ke babu acikin su.

Aneelerh da zahra da Mahboob suna zazzaune kan Carpet, A lokacin baby junaid Ya jima da yin bacci, Yana can kwance saman gado.
Abie da Uncle Wan Iya suna a zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, Abie Yana sanye da farar jallabiya ya manna farin glass a idanunsa, Yayin da Uncle Wan Iya yake asanye da Riga Yar shara ta farin Yadi, daga ciki ya sanya gajeran wando ba?i.
Su Mamie da Ummi suna zaune saman Sofa mai mazaunin mutun biyu, dukansu Hijabai ne a jikin su. tamkar mutuwa ta gifta babu mai magana acikinsu, Har na tsawon mintuna kafin daga bisani Uncle Wan Iya yayi masu gyaran murya, suka Wago suna duban shi, da hannu Ya nuna Mahboob
"Je ka kira ta" Amsawa mahboob Yayi da toh, ya mi?e ya nufi bedroom din Ana, abakin ?ofar Ya tsaya tare da kai hannu yayi knocking kofar kusan sau uku bata buWe ba, Har ya fara tunanin ko bacci tayi ne sai kuma Yajiyo mutsu mutsunta ta cikin Wakin.
A hankali ta turo ?ofar Wakin, tare da le?o da kanta,
Ko da mahboob yai tozali da fuskarta sai da gabanshi ya faWi ganin yadda ta kumbura suntum, idanuwanta sun kaWa jawur, daga gani kukan take cikin yi
In a calm voice Ya furta"ina fata ban katse maki baccin ki ba"
Muryarta adisashe tace"ban kaiga Yin baccin ba,"
Jinjina kai yayi"Uncle ne yace in kira ki, su na a falo shi da su mamie da abie"
Shiru tayi jimmm kamar bazata motsa ba, har saida ya maimaita mata maganar tukunna tace Toh, ka jirani mu tafi atare"
"Okey"
Maida ?ofa tayi ta rufe ta, badajimawa ba sai gata ta fito sanye da doguwar riga, ta yafa mayafi akanta,
Jin ta ru?o hannun shi acikin nata ne yasa shi saurin kallonta, sam hankalinta ba akwance Yake ba, bai yi yun?urin raba hannun shi daga nata ba, A haka suka nufi falon, sai da suka kusa isa yayi saurin zame hannun shi daga nata, Takun tafiyarsu ne Yaja hankalinsu mami ga dubansu
Cikin girmamawa Ana ta gaishe da su, tare da samun wuri gefen Aneelerh ta zauna tana faman jan numfashi, bayan mahboob Ya zauna.

Abie dake kallon Ana Ya soma Magana a tsanake

"Inaso ki natsu ki saurare ni," jinjina mashi kai tai alamar toh
"Ki Wauka tamkar mahaifanki ne suke yi maki magana, kada ki ji shakkun faWa mana abun da ke damunki, saboda mu kaWai ne makusantanki a yanzu, Ha??inmu ne mu kula da rayuwarki, Idan wani abu ya same ki ba zamu ji daWi ba" wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta, ha?i?a kalaman abie sun yi tasiri a zuciyarta.
Uncle Wan Iya ya Waura da cewa"banji daWin abun da Ummi ta fada min ba, baki kyauta mana ba, ashe baki Wauke mu yarda muka Wauke ki ba, meyasa zaki zauna abu na damunki ki gaza gaya ma kowa? Meye amfanin 6oye mana eye"? Muryarshi da faWa yake yi mata magana, alamar ranshi ya 6aci.

Sunnar dakai ?asa Ana tayi yayin da idanunta ke akan Yatsun hannayenta
"Meke damun ki ne, inaso ki faWi mini gaskiya"? Ya jefa mata tambayar, Su Aneelerh da su mami sun natsu suna kallon ta.
Numfashi taja tare da sauke shi A hankali ta furta"Idan na 6ata maku rai, dan Allah ku yafe ni, Aunty Aneelerh, mami, ummi, Zahra, Mahboob, abie, uncle, Allah ne kaWai zai Iya biyanku, duk da kasancewata yar aiki agidan nan, Sannan ba musulma ba amma kun daukeni tamkar jinin ku, ko dan saboda nuna damuwar da ku ka yi akaina zan fada maku gaskiyar abun da ke damuna...." ta faWa tana mai ?an?an da kanta, gaba Waya duk sun ?agara da suji meke damunta, musamman Mahboob Ya kasa Wauke idanunsa daga kan fuskarta, wani irin tsantsar sonta da ?aunarta yake ji, ga matsanancin tausayinta dake addabar zuciyarsa.
"Cikin kwanakin nan, Ina yawan yin mugayen mafarkai, waWanda suke neman haukata ni, bansan meyasa hakan yake faruwa dani ba, idanuwana suna gane min abunda yafi ?arfin gani na wanda silar hakan yasa nafara zaucewa, ni gani nake ma kamar mutuwa zanyi..... " muryarta na rawa ta ?are maganar nan take ta fashe da kuka mai sautin gaske, Hankalin su ba ?aramin tashi yayi ba, Jikin kowannansu yayi sanyi
"Kiyi shiru, Kukan Ya isa haka, Ki faWa mana me kike gani a cikin mafarkin naki"! Uncle Wan Iya ne yai maganar
Cikin shesshe?ar kuka tace"wallahi duk yadda zanyi maku bayani ba lallai ku fahimce ni ba, ni kaWai nasan halin da nake aciki, ni kaWai nasan bala'en da nake gani, Ba tun yanzu ba, tun ina ?aramata idan nayi mafarki mummuna yana zama dagaske, hatta rasuwar iyayenmu saida nafara yin mafarkin zasu yi hatsarin mota, sai gashi ya tabbata, uncle Wina ma ni nayi mafarkin mutuwarsa kuma ya tabbata, da wuya inyi mafarki mummuna bai zamto gaske ba, ni damuwata mutanan da nake a tare da su bana son wani abu ya sami wani daga cikin ku...." tashin hankalin da ba'a saka mashi date, A matu?ar ruWe Zahra take kallon Aneeleerh, Ummi ta kalli Mamie, Idanuwansu azare, mahboob kuwa kusan suman zaune yayi.

Shiru tayi Tana faman yin shesshe?ar kuka,
Abie dake kallonta, nazarin maganarta yakeyi, yaso ace musulmace ita, kodan ya bata shawarar ta run?a yawaita yin azhkar, da sauran addu'o'in neman tsari.
Tsawon lokaci falon yayi tsit, babu mai magana acikinsu, sai kallon kallo da suke jefawa junansu.
Muryar Uncle Wan Iya ce ta katse Shirun nasu
"Ki daina sanya damuwa aranki, Mafarki ba gaskiya bane, shaidan ne


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login