Showing 273001 words to 276000 words out of 298130 words

Chapter 92 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

ya wuce A kira shi da so hada shaukin junansu da suke ji, yar wakar da ta kunna masu kadai ta jefa su awani hali dama da biyu ta kunna ta


Kasa jurewa yayi da wata irin kasala Ya mi?e zai bar dining din gudun kada yayi wani abu ba dai dai ba da zaisa su sake samun sabani da ita, da sauri ummi ta dakatar da wakar ta dube shi.

"Danish Ina zakaje? Naga ko abincin baka fara ci ba" tamkar baisan furta magana yace"bana jin yunwa" marairaice mashi fuska su Haris sukayi"pls danish, kada ka tafi ka zauna ka ci abinci" girgiza kai yai, Shi kadai yasan me yake ji ajikin shi, In har ya cigaba da zama Yana kallon Unaisah komai zai iya faruwa a yanzu haka jikin shi sharkaf Yake Ga gumi da ya wanke shi duk da sanyin a.c din dake a dining room din, su basu lura ba amma ita Ummi tasan me yake ji a wayance tace"ko dai kana da uziri ne"? ya Waga mata kai alamar eh.


Shu'umun murmushi Tasaki Okay, Muna jiranka idan ka gama uzirin naka, ka dawo kaci abincin" bai kula ta ba Ya fuce daga dinning din ba don ya gaji da zaman shi ba, sai don bayason yaja ma kan shi bala'e.


Fitarshi keda wuya Unaisah ta buWe idanunta da suka kaWa jawur da su, ga wani zafi da temperature din jikinta ya dauka kamar mai fama da zazzabi.

ta rasa gane meke mata dadi, fitar Danish daga Wakin yasa taji batasan cin komai, mineral water kadai ta sha ta mi?e jikinta na tsuma ta nufi hanyar fita daga dakin muryar aunty Ummi ta katse ta"Wai lafiya? Shi ya fita baici komai ba, kema kin mi?e zaki fita? Meke damunku ne"? Ta tambaya kamar batasan meke wakana ba.

Yamutsa fuska Unaisah tay tare da kallon Ummi datay maganar
"Wayata zan dauko adaki, yanzu zan dawo" ta fadi hakanne don kada su zargi wani abu.

kumshe dariya ummi ta yi abakinta, tana lura da yadda jikinta ke tsuma.

"Okay, muna jiranki" fucewa tayi daga dining din tana tafiya da nawa kamar wadda kwai ya fashe mawa, tana shiga dakin su ta faWa toilet taja ?ofa ta datse, zama tay akan toilet seat tayi shiru tana tariyo abunda ya faru a dining room.

Ta rasa gane dalilin dayasa take tsintar kanta awani yanayi duk idan tagan shi ko taji muryarshi! Batasan menene ba, ta kasa ganewa.

bata gama zancen zucin ba, zatayi tsarkin fitsarin da tayi taga wannan farin ruwan mai yau?i wani irin kyankyami da kyamane suka kamata, da sauri tayi tsarkin ta fito ta tsaya abakin kofar toilet tana faman sauke ajiyar zuciya, bayanin aunty Umminsu ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ta fara tariyowa a lokacin da take faWa mata dalilin dake kawo shi, abun da ya daure mata kai kallon juna kawai sukayi ba wani abu ba amma sai gashi ta gan shi, dole ta nemi ?arin bayani agurin Aunty ummin su.

ga yunwa tana ji sai dai bata jin zata iya komawa dining room din, faWawa tayi kan bedmattress ta janyo pillow ta rungume shi a kirjinta, wani sanyine ke ratsa zuciyarta, ga wani dadi da take ji a jikin ta.

ta shafe tsawon mintuna shabiyar a kwance ba tare data motsa ba.


"Sister, Aunty Ummi tace kizo wai" muryar hawwa ce ta katse mata zancen zucin ta, ba tare da ta bude idanunta ba tace"okay, gani nan zuwa" bayan fitar hawwa daga dakin ta sauko daga kan gadon ta, ta gyara mayafinta, tana ?okarin fitowa daga dakin kamar daga sama taji Sallamar Salsabeel da sauri ta juya ta dubi kofar falon, a tsaye yake ya Wauki wankan shadda kamar ba shi ba, hannun shi ru?e da trolley, kwata kwata bai lura da ita ba.


"Yaya salsabeel," muryar ta ce ta fargar da shi, murmushi yayi tare da nufarta yana jan trolley Win.


"Unaisah ykk"


da fara'a tace"lafiyalou, ya salsabeel kwana biyu baka leko mu ba, munyi fushi"

ta fada tana haWe fuska yar dariya yayi"i'm really sorry, wlh kuna araina, yanzu hakama da kika ganni saboda ku nazo"


Mi?a mashi hannu tayi"kawo na ru?e maka trolly din" mi?a mata yai tasa hannu ta ru?e handle din"Menene aciki? Ko kayanka ne"? Girgiza kai yai" mu karasa ciki, zan nuna maki abunda ke a cikin shi" amsa mashi tayi da toh suka nufi cikin falon akan sofa Ya zauna, Ta aje trolley din agaban shi Yace mata ta kira sauran yan uwanta ya faWa yana hangen su a dining room suna cin abinci sam basu lura da shi ba, da sauri ta juya ta nufi dining room din ta shiga ta kira su, tun da suka ji ta ambaci ya salsabeel ya zo kowa ya ajiye spoon din hannun shi, Cike da zumudin son ganin shi suka fito daga dakin su dukan su hada Ummi.

Kafin su karaso ya mike fuskanshi dauke da fara'a ya gaishe da ummi ta amsa mashi da fara'arta, kallon su Haris yayi daya bayan Waya aranshi yana tariyo lokacin da suke a prison, rayuwa ta canza sun wadatu da kwanciyar hankali


Hannu ya mi?a ma mazan sukayi musaba, Ya dubi Yan matan dake ta faman hade rai
Dariya yayi"fushi kuke dani"? Khadeeja tace"eh mana, tun yaushe rabon da kazo gurin mu, ka manta damu.."
Mubeen Yace"kullum sai munsa ran zuwanka amma saika ki zuwa"
gaba daya suka rufe shi da korafe korafen su dakyar Ya samu ya shawo kan su, har suka hakura da fushin da sukeyi da shi bayan sun gama gaisawa da junansu yace su zauna zasuyi magana mai muhimman ci.

Bayan Kowan nan su Ya samu guri Ya zauna kan Sofas suka nutsu suna jiran jin me zaice masu.

"Ya salsabeel, Wannan akwatin fa? Ko tsaraba ne ka kawo mana" parveen ce tay maganar tare da nuna akwatin da hannu

"Eh tsaraba ce amma bata abun ci ba, Kayan sawa ne" kallon juna su kayi da mamaki akan fuskokin su.

"Ina Danish"? Ya tambaya yana kallon su

"Yana a daki" suka haWa baki gurin bashi amsa"

Yace"okay, wani ya kira min shi" Haris ne Ya mike da sauri Ya je kiran shi.

falon yayi tsit baka jin hayaniyar komai, duk sun ?agara da son ganin menene acikin trolly din me kuma ya Salsabeel zai fada masu mai mahimman ci'?

Jim kaWan saiga Haris Ya dawo tare da Danish, Har ya canza kayan jikin shi yanzu silk pyjama ne a jikin shi na bacci.

Tun shigowarsu Falon, Unaisah take satar kallon shi, bayan sun rungume juna da salsabeel a amutunce suka gaisa da junan su kafin daga bisani kowan nan su Ya zauna suka nutsu suna kallon salsabeel

"Mu farayiwa Annabi salati" suka amsa mashi da toh, bayan sun gama yayi shiru yana binsu da kallo Waya bayan Waya kamar mai nazarin wani abu, Azeeza da Jemimah sai faman kumshe dariya su ke yi kamar wasu zautattu.


?aya bayan Waya ya fara kiran sunayen su, duk wanda ya kira sunan shi sai ya amsa mashi da Na'am, ummi dai tayi shiru tana jiran jin me zaice ma su

Numfasawa yayi kafin ya fara magana cikin nutsuwa

"Gobe Idan Allah Ya kaimu da rai da lafiya, za'a tafi daku Isod headquarter...."

Kallon juna su ka yi arude suka maimaita sunan Headquarter, Sajeed Yace"me za mu yi acan Win"? Da alama sun ruWe, murmushi Salsabeel yayi kafin yace"zaku gana da manyan jami'an Isod" Hankali tashe Unaisah tace"mu Win"? Jinjina mata kai yayi"kwarai kuwa, Lokaci yayi da zasu gana da ku, don suji daga bakin ku, Suna bukatar bayani game da rayuwarku a gidan kurkukun ?addara, zasuyi maku tambayoyi da suka shafi rayuwar da kukai agidan kurkukun ?addara da kuma shi kanshi gidan kurkukun"

Ya fada yana duban fuskokin su sunyi shiru suna sauraronshi kowa da abunda ya?e sakawa aranshi.


"Nazo ne don in ?arfafa maku gwiwa, nasan akwai masu jin tsoro har yanzu acikin ku, to inaso ku aje tsoron nan gefe Waya da duk wani shakku da zakuji, yanzu lokaci ne da zaku bada gudummuwa ku taimaka masu gurin kawo karshen kurkukun kaddara, bayanan da zaku basu da su zasuyi amfani wurin yin binciken waWanda suka azabtar da rayuwar ku, kada ku 6oye masu komai, duk mun ?an?antar abu da kuka sani ku faWa masu zai iya zama mai amfani agare su"


tun da salsabeel ya fara magana Danish Ya rufe idanunshi gam kamar baya atare da su, sarai salsabeel Ya lura da yanayin shi.


"Ku faWa masu irin kuncin rayuwar da kukayi, Ku faWamasu azabtarwar da sukayi maku da kuma wulakanta rayuwarku da su ka yi, ku kaWai kuka san meya faru arayuwarku, tunkafin ku mallaki hankalinku kuke a kulle ba shige ba fuce, idan har kuka 6oye wani abu baku fada ma su ba, kanku zaku cuta, kwara ku tona masu asiri don uban su kowa yasan me suke aikatawa" ya faWa tare da bugun sofa din da yake zaune akai da hannun shi.

"ku daina ganin ayanzu kun tsira kun samu rayuwar ?anci wallahi har yanzu rayuwar ku tana acikin haWari saboda ba zasu ?yale ku ba, suna nan suna bibiyar rayuwarku don su salwantar daku saboda kune prisoners na farko da suka fara karya dokar kurkukun kaddara, tayaya ku ke tunanin zasu ?yale ku? Ay ko dan kada ku tona masu asiri dole su nemi hanyar da zasu shafe babin ku"


Maganar salsabeel ta Waga hankulansu, Tuni ido ya raina fata, wasu daga cikinsu har sun fara sharar kwalla,

ya faWa masu hakanne don Ya tsoratar da su ya kuma tunzura su don su fusata su samu kwarin giwar tona masu asiri idan jami'an sirrin suka tambaye su.

"Ko ba don saboda ku ba, Ku tuna ?an uwanku da kuka bari agidan kurkukun ?addara! WaWanda basu ji ba basu gani ba kamar ku dai, suna can ana azabtar da rayuwarsu, Sun maida su kamar dabbobi sai azabtar da su sukeyi, meye ribarku idan ku kun samu jin dadin rayuwa su kuma suna awahala? Baku da burin ku dauki fansar abunda akayi maku? Sannan ku cecei rayuwar yan uwanku? Za ku ja baki ne kuyi shiru acigaba da salwantar da rayuwar kananun yara da basu ji ba basu gani ba"? Ranshi a6ace yayi maganar yana kallon su, Jiki asanyaye sajeed Ya sauko daga kan sofa, Ya dawo ?asa ya zauna hannayen shi biyu tallabe da kan shi, Idanunshi sun ciko tab da kwalla.

Shesshekar kukan su ne Ya cika falon, kalaman salsabeel sun fama raunin dake acikin zuciyar su..."

Salsabeel bai dakata ba saida ya tabbatar sun fusata sun harzuka kafin ya tsagaita da yin maganar Yana jiran jin me zasu ce.

Cikin shesshekar kuka sajeed yace"wallahi ko ba ka fada mana ba, ba zamu raga masu ba, ni ashirya nake da duk wata tambaya da za'ayi min, nayi alkawarin zan fadi iya abunda nasani saboda nima twin sister dina tana can, bana so su kashe min yar uwata duk da bani da tabbacin tana araye kota mutu...." kuka ne Yaci karfinshi, Ya kifa kanshi saman sofa.

Wani irin tausayin su ne Ya kama Ummi, Tuni taji hawaye sun cika idanunta, lamarin rayuwar yaran tana matu?ar tada mata hankali, har yau tana jin labarin su tamkar a mafarki saboda abun yafi karfin tunaninta.


Fashewa jemimah tayi da kuka tana fadin

"nima wlh saina tona masu asiri, mugaye azzalumai kawai, hadama wannan tsohuwar data kusa kashe mu nida su Azeeza, Inaji ina gani majnoon dina ya mutu, wlh saina daukar mashi fansa, koda zan rasa raina ne..." rai a6ace tay maganar, idanunta sunyi jawur ga ruwan hawaye dake zarya kan kuncin ta,

dafe kai Deeja tayi da hannunta tamkar zata fasa masu ihu, idanunta sun rune zuwa ja, kwata kwata bata son jin maganganun da su ke yi,

mi?ewa tayi da sauri ta fuce daga falon, duk suka bi bayanta da kallo babu wanda yayi yunkurin dakatar da ita.

"Bazan ta6a manta irin azabtarwar da sukayi mana ba, wallahi rantsuwar Wan musulmi ba gudu ba ja da baya sai mun fallasa su kwara duniya tasan me suke aikatawa, ay yaya Salsabeel ba sai ka sha wahalar yi mana bayani ba, dama mu lokaci kawai muke jira in ma takama har prison din aje damu ayi faWan da mu, wallahi zamu bada goyan baya Wari bisa Wari ko da silar hakan zai ja mu rasa ran mu wlh sai inda karfin mu Ya ?are, Kome suke son ji zamu faWa masu...."


tun da Unaisah ta fara zazzaga masifa, suke kallonta jikinta har jijjiga ya ke yi tsabar fusata da 6acin rai, an ta6o inda keyi mata ?ai?ayi.." bata ?are maganar ba, Danish Ya mi?e daga zaunan da yake kan Sofa, gaba Waya suka bi shi da kallo Salsabeel Yace"Danish Ina zakaje ban gama magana ba"? Ko kallo bai ishe shi ba, Ya fuce daga falon, sam unaisah takasa karasa maganar,

Da tsantsar mamaki suka bi bayan shi da kallo har ya 6ace ma ganin su.


Haris Yace"ka gani ko ya salsabeel? Danish Ya canza kamar bashi ba, Yanzu ji muna magana mai mahimmanci Ya tashi Ya tafi kamar abun bai shafe shi ba, haka muke fama da shi baya son shiga cikin mu kuma baya son muje gurin shi..." cikin jin kunar rai Haris yayi maganar yana kallon Salsabeel.
Korafe korafe suka dinga fada mashi akan danish,
Unaisah tace"nasan ma zai yi wuya ya bamu hadin kai, kuma yafi mu sanin komai dangane da gidan kurkukun ?addara"

a marairaice tay maganar,
Shiru salsabeel yayi jim yana Wan jinjina kan shi kafin cikin sanyin murya yace"sai kun yi hakuri da shi, saboda ba yin kan shi bane, sau dayawa wasu abubuwan da za ku ga yanayi wallahi ba shi bane"! A matu?ar ruWe suka kalli Salsabeel, Musamman Unaisah Maganarsa Ta jefata a ruWani, Har dai tagaza jure tace"Ya salsabeel ban fahimci me kake nufi ba! Naji kace wani lokaci ba shi bane"! Kallon ta salsabeel yayi"ina nufin wani abun da ya ke yi bayin kan shi bane, shaidanun dake a jikin shi ne, su ne suke Controlling din shi, zai iya wuni ba acikin hayyacin shi ba, nasan baku taba lura da hakan ba, shiyasa baya son shiga cikin ku, kuma baya son wani yaje gurin shi, idan ba wanda yake son gani ba, amma abun da yakamata ku cigaba da taya shi addu'a, In sha Allah idan mukayi nasarar raba shi da evils din jikin shi, zaku sha mamaki, zai dawo ainihin wanene shi...."


"Yaya salsabeel amma dai bazai manta damu ba ko"? Batool ce tay mashi maganar,

"Taya zai manta daku? Abokan kuruciyar shi, sai dai wasu abubuwan da yake yi zai daina su, zai canza sosai fiye da yadda baku ta6a zata ba.."

Hankalin Unaisah Ya tashi ba kaWan ba, Aranta ta ayyana idan har maganar Salsabeel ta tabbata tabbas akwai damuwa ba kadan ba, sai dai ta hana zuciyarta gasgata maganar shi.


BuWe trolley din gaban shi yayi duk suka kura ido suna jiran ganin me zai fiddo daga aciki.


Ga mamakin su Uniform dinsu ne na gidan kurkukun kaddara, a ninke sun sha guga tare da cotton scarfs dinsu, wanda tsohuwa tamira ta basu kyautar su

daga gefen shi ya Waura su, kafin ya dube su sun saki baki suna kallon kayan bakomai suke tunawa ba face rayuwarsu ta gidan kurkukun ?addara har tsohuwa tamira sai da ta faWo masu aran su, jikinsu yayi sanyi lakwas kamar wadanda aka zarema lakarsu.


"Ga uniform dinku nan, Gobe su zaku sanya, Da wuri za'a tafi da ku in sha Allah"

kaWan daga cikin ne suka amsa mashi da toh.
Wrist watch din hannun shi ya duba karfe 9 na dare.

Kafin ya maida duban shi Ga sajeed daya kifa kan shi saman sofa.

"Pls, yanzu ba lokacin damuwa bane, lokacine na Waukar fansa, yin kuka ko sanya damu arai bazai ta6a zama mafita agareku ba, hakan zai sage maku gwiwa, shiyasa nakeso ku sanya jarumtaka da rashin tsoro a cikin zuciyarku, ku dage da addu'a, Wallahi komai ya kusa zuwa karshe, Idan kun ba su hadin kai, za mu yi nasara bi'iznillahi"

"In sha Allah ya Salsabeel zamuyi abunda kace, mun gode da ?arfafa mana gwiwa da kayi, kuma mun yi maka al?awarin ba zamu ba ka kunya ba," Unaisah ce tay maganar har cikin ranshi yaji dadin jin hakan daga gare ta.

"bayan na tafi, ki ba kowa na shi" ya faWa yana nuna mata uniform Win ta amsa mashi da toh.

ya jima agurin su kafin daga bisani ya yi masu sallama ya ta fi...

Bayan tafiyar shi, ta bubbuWe Uniform Win bata sha wahalar gane na kowa ba, saboda numbers din da ke a jikin su, kwata kwata basu san ganin kayan saboda bakiin tarihin dake atare da su, ba dan sun so ba, kowa ya dauki na shi, itama Unaisan ta Waukar ma su nasu ita da Batool su ke da black uniform..

A daren ranar cike da zullumin tambayoyin da za'ayi masu suka kwana, in ka cire mutun Waya wadda gaba daya tunaninta akan maganar Salsabeel ne, ta tsaya mata aranta, tana matu?ar jin tsoron abunda ya faWa masu dangane da Danish.

Awashe gari, tun da sassafe suka farka daga bacci, batare da 6ata lokaci ba, suka shirya cikin uniform din su sunyi kyau kamar Waliban high school na ?asar korea, yan matan sunyi rolling cotton scarfs dinsu akansu, mazan kuma a wuyansu suka laga shi kamar yadda Mazan pakistan suke rolling scarf a wuyan su, bayan sun yi breakfast su ka hallara a falo suna jiran aba su umarnin su fito, Unaisah sai ?ara tunasar da su takeyi akan in sunje su saki jikin su, kada suji shakkun tona asirin abunda ya faru arayuwar su, da yake suna jin maganarta duk suka amsa mata da toh.

Suna atsaye suka soma jiyo takun takalman mutane, at same time suka dubi in da sautin ke fitowa daga can Upstairs, Chief Owais ne Ya fito daga Bedroom din Danish jikin shi sanye da kakin sa, Danish yana abiye da bayan shi, White shirt ce a jikin shi tare da dark jeans, Kwata kwata fuskarshi babu annuri ko miskala zarratin ya haWe rai, ru?o hannun shi chief ya yi a cikin nashi, a tsanake suke taka stairs cases, gaba daya Su Haris Sun zuba masu ido suna kallon su, da alama sun burgesu kamar wa da ?ani, kullum suna ?ara mamakin kamannin su.

kafin su karasa saukowa down, Sallamar taj da big guy ta karaWe kunnuwan su, atare


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login