Showing 111001 words to 114000 words out of 298130 words

Chapter 38 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

Angel laifina ne da ban zauna a dakin taron ba, da duk hakan bai faru ba....."

Baisan meke damunta ba da yai silar shigarta wannan Mawuyacin halin, baisan Ya akai aka kulle ta a restroom ba.

Yana acikin wannan Yanayin big guy ya shigo da saurin shi, Yana ganin taj rungume da unaisah Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya.

Daga bakin kofar ya tsaya don baisan me zai taras ba.

Cikin sanyin murya yace"idonta biyu"?
Muryar taj kasa kasa Yace"bansani ba, kamar ta sumane anan, amma daga gani taci bakar wahala"
Big guy yace"mun gano wacece Ta kulle ta a restroom din, Kuma in sha Allah zamu bincikota sai ta dandani kudarta wallahi" Yana fuci Ya faWa

Babu alamun taj Ya fahimci me yake cewa hankaklinsa na akan Angel dinsa yace da shi"please Ka koma wajen yan uwanta kada su ji mu shiru, yanzu zan fito da ita" amsa mashi yayi da okey, a hanzarce Ya fice.

Har ya yun?ura zai mike Yaji alamun lemar wani abu a hannun shi, da sauri Ya dago da tafin hannunsa Yana kallon jinin daya ta6o, sai lokacin Ya fara jin karninsa a hancinsa, Idanunsa azazzare yake kallon jinin Hankalin shi yayi mugun tashi, zuciyarshi ta dinga harbawa da karfi da karfi tamkar zata fasa kirjinshi,duk a zaton shi wani mugun abun akayi mata, zuciya da sake sake sai ta dinga ayyana mashi kodai raping dinta wani yayi ko kuma Wuka aka caka mata.

Zuciyarshi na tashi, Yai hanzarin Sanya hannu Ya dage rigar jikinta, santala santalan cinyoyinta tsakankaninsu duk jinin ne daya gangaro mata.

Sai da ya bincika ta sosai, wata irin nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, ganin ba abunda Yake zargi bane, A hanzarce ya fara wanke mata inda jinin Ya 6ata, kafin Ya lullu6a mata mayafinta ya daure mata qugunta da shi, asaman kafadarsa ya rungumo unaisah, yayin da Wayan hannunsa ke a ruke da rigarta, tuni tajima da farkawa tun lokacin daya fara wanke mata jinin da ruwa sai dai bata iya komai, Jikinta ya sake ga wata irin kasala data mamayeta.

Fitowa yayi da ita sabe a kafadarsa, tunkafin Ya karasa inda su Batool suke, da gudun gaske suka nufoshi, lokaci daya su ka ja burki idanunsa azazzare da tashin hankali suke kallon Taj

Muryoyin su na kerma suke tambayar shi meya faru da unaisah? Bata da lafiya ne? Ko bacci take Yi ne"?

Kokarin danne damuwarsa yayi kafin yace masu"Babu abunda ya sameta, lafiyarta kalou, Ku zo mu tafi gida"
Da sauri Ya wuce gaba suka bi bayan shi, masu aikin dake zarya suna kwashe kayan da akayi amfani da su na hall din sai satar kallon taj suke Yi ganin shi dauke da yarinya kamar ba rai.

Fitowa yayi daga Hall din su Batool suna abiye da shi, Jami'an dake tsaron dakin taron suna ganin shi suka fara tambayarshi meye faru da ita?
Baibi takansu Ba, Ya nufi mota, da sauri jami'insu Ya bude mashi Ya shiga back seat tare da Unaisah, suma su batool suka shiga cikin sauran motocin da aka kawo su, kusan atare su ka bar garden din, da matsakaicin gudu suka nufi hanyar komawa gida
Mutsu mutsun bude idanunta ta somayi wadanda suka kada jawur da su, da kyar ta dan ware su kadan ta kalli fuskar taj dake a rungume da ita, hannayensa duka biyu akan bayanta kamar wani yace zai ?wace mashi ita.

Idanunta na faman lumshewa dakyar dakyar take kallon fuskarshi ba tare da sanin shi ba, acikin zuciyarta ta dinga ambaton sunan shi daddyna daddyna dama kaine kake boye min fuskarka..." siraran hawayene suka wanke fuskarta, ganin yana kokarin juyowa yasa tai saurin lumshe idanunta, saukar hannun shi taji asaman kanta, A hankali Yake dan shafa mata shi, wata irin ni'ima taji ta saukar mata, jikin ta yayi sanyi ba kamar dazu da zazzabi Ya lullu6eta ba, bakomai take tunawa ba face lokacin da ya jefata cikin ruwa...

Taj sam baisan cewa babu face mask a fuskarshi ba, gashi har unaisah taga fuskarshi, don ma babu kwarin jiki ai da ta tuhumesa nakin bayyanar mata da kanshi da baiyi ba, dama tuntuni ranta yana bata cewar daddynta ne duk da bata ta6a ganinsa ba, amma kulawar dayake bata fiye da ta sauran yan uwanta da yadda yake janta a jikin shi da kuma muryarshi su suka kara sanya ta hasashen ko shine.

Alhamdulillah Taro Ya tashi Lafiya, tuni Kowa ya koma masaukinsa bayan da suka hallara a gidan prime minister inda suka karasa shagalin nasu acan, a 6angaren chief owais tun bayan da suka shiga Part din Nazli, ba tare da sanin shi ba, ta kashe mashi wayar shi don kada a kira shi, bayan haka ta hada baki da daya daga cikin hadiman gidan ta sanya mashi maganin bacci a coffee, duk don kada ya tafi yabarta, Sai wuraren karfe sha daya na dare tukunna chief Ya farka, a lokacin nazli har tafara bacci, bai bi ta kanta ba, da sauri ya fito daga part din ta ya sauko down, Kafin Ya kunna wayar shi, Layin prime minister Ya fara dannama kira don Yaji idan Yasa an mayar da danish gidansa.

Bayan yai picking Hateem Ya fada masa suna atare da shi a bedroom dinsa, bai tsaya bata lokaci ba Ya nufi part din prime minister, dakyar ya raba shi da danish, kamar karsu rabu, na rana daya kawai sun shaku da juna har kyautar zobe ya ba shi mai tsadar gaske saboda ya dinga tunawa dashi, kuma yayi mashi alkawarin kullum xai dinga kiransa suna gaisawa, bayan chief Ya tafi da shi har kwalla saida Ya zubda daboda kewar rabuwa da danish.......

Asubar Fari, Motoci suka dinga tururuwa wurin fita daga Estate din,da wata irin jiniya mai kuwar gaske tamkar zasu tashi sama, kaitsaye suka nufi shantalelen titin da zai sada su da Airport, gaba daya family din obinna ne dashi kanshi obinnan suka yi masu prime minister rakiya, Kamar karsu rabu da juna, musamman mahaifinsa da yan uwansa, duk irin juriyarsu saida suka share kwallar rabuwa da shi, Hajiya saratu tasha kuka kamar karamar Yarinya, shi kanshi hateem din saida Ya zubda kwallar rabuwa da yan uwanshi, Ji yake kamar idan ya tafi ba lallai Ya kara dawowa ba, hakika kowa yayi jimamin tafiyar prime minister da Iyalansa, ko bayan da suka baro Airport din suna akan hanyar komawa estate nasu lokacin da suka jiyo karar jirgin su

Haka suka dinga leken jirgin ta windows din motocinsu, har Sai da ya bace ma ganinsu tukunna suka hakura kowa Ya sanyawa zuciyarsa salama, kusan duk aranar Su his excellency deeen suka bar abuja, harta su Justice kowa Ya koma inda Yake da zama wasu Nan cikin Nigeria wasu kasar suka bari, Zaki ne kadai bai tafi ba, yanzu estate din Ya rairaye ma zauna cikinsa ne kadai suka rage.



*Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'
'?*



*Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida ta wannan layin 08169856268*_ *~
'=؋?????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
BOSSLADIESWRITERS=؋?
'~*_



3,F 'DB/=؋?=?%?=؞?


~Takun ?arshe=?%?~



Dedicated to Aunty Kubra=؋?=؞?



B5) -( 1HE'F3J) :J1 9'/J) (JF 'D3,F'! E9 *7H1'* E9B/)=؋?=ؘ?=??


An extraordinary romantic love story between prisoners with complex twists d'=؋?=ؘ?



Daga al?alamin Boss Bature=؋?
'





__________________________
'?




A hankali ta buWe idanunta wadanda suka kumbura suntum da su sakamakon kukan da tasha jiya, ?urawa ceilling din dakin idanu tayi na Wan wani lokaci zuciyarta cike fal da tunanin meya faru da ita a jiya? tamkar tayi loosing memory Winta, da sauri ta sanya hannu ta shafa kayan jikinta, lokaci Waya ta yunkura ta mi?e zaune tana faman sauke ajiyar zuciya, ko'ina na bedroom dinsu ta soma bi da kallo kafin ta sauke idanunta akan batool da ke kwance gefenta tana bacci, tayi mamakin ganin kayan bacci a jikinta, ?ar gown ce da bata wuce gwiwarta ba, launin purple colour, ta rude sai faman shasshafa jikinta take yi burin ta ta tunano ya akai aka canza mata kayan jikinta! kamar ma hada wanka akayi mata, hannu tasa ta Wan bugi kanta a kokarinta nata farkar da kwakwalwarta ko taci gaba da yin aiki yadda ya dace.

BuWe ?ofar Wakinsu akayi da sauri taja bargo ta lullu6e kanta, tunkafin ma taga wanene.

Atare suka shigo dakin, boss tare da Ummi da ke abiye da shi cikin shiga ta kimono robe, ta yafa gyale a kafadarta, hannun kowannan su ru?e da Wan ?aramin tray na kayan abincin.

"Barka da safiya daughter" wani irin wurgi tayi da bargon gefe Waya ya faWa kan Batool, ta Wago tana faman zare mashi idanunta.

Sunyi mamakin ganin yadda ta zabura, ummi tace"ko dai har yanzu jikin ne"? Ko kallo unaisah batai mata ba idanunta na akan taj, wanda ke sanye da facemask, A hankali take tariyo abun da ya faru jiya, lokaci daya ta rushe masu da matsanancin kuka wanda yayi silar farkawar batool.

Hankalinsu atashe su ka soma ambaton sunanta, tare da tambayarta meke damunta! Ko ciwonta ya motsa.

Sauko tayi daga kan gadon ta watsa da gudu ta shige toilet taja kofa ta rufe tana cigaba da yin kukan
Kallon juna ummi da taj sukayi a lokaci Waya, fuskokin su dauke da matsanancin damuwa, atare suka daura trays din hannun su kan table suka nufi bakin kofar toilet
Batool dake zaune kan gadon sai faman mutsustsuke idanu takeyi tana ambaton sunan unaisah...

Magiya suka dinga yi mata akan ta buWe ?ofar

"Dan Allah unaisah Ki fada mana meke damunki? Ko cikin ki ke maki ciwo? Idan akwai inda ke maki radadi ki fadamin Yanzun nan zanje na karbo maki magani, wallahi mun damu dake jiya ko runtsawa bamuyi ba, har sai da muka ga kinyi bacci" cikin sigar lallashi ummi takeyi mata magana.

"My daughter ki yi shiru ki saurare ni, nasan meke damunki, ni nasan dama dole kiji haushi, inaso ki kwantar da hankalin ki, saboda mun riga da mun gano wacece tayi maki aika aikarnan kuma in sha Allah zamu hukuntata, idan ma kinaso zamu kawo maki ita, ki rama abunda tayi maki"

Maimakon unaisah ta sassauta kukanta, jin lallashinta da suke yi mata sai ma takara sautin kukan nata tamkar zata fasa kunnuwansu, da gudun gaske sajeed Ya fado dakin Yana haki daga shi sai gajeran wando bai jima da shigowa ba naufal Ya shigo shima yana tambayar meye faru da angel dinsu?
Shigowa suka dinga yi, daga me hamma sai mai mi?a daga gani basu jima da farkawa daga bacci ba, dama da tunaninta suka kwanta bacci jiya shiyasa suka farka da ita aransu, atare Jemimah da Azeeza suka shigo kowannan su kayan bacci ne a jikin shi, ba su jima da shigowa ba, Parveen ta shigo hannun ta ru?e da brush, sumar kan nan a haukace gyaran gashin da akayi masu duk ya tarwatse kowa fa hankalinsa Ya tashi matu?a, Jemimah sai kuka takeyi masu hada tsallanta tana fadin dama tasani mutanan nan sai da suka cutar mata da Angel dinta, wallahi bazata ?yale su ba dole ta rama mata...

Gaba Wayan su sunyi curko curko abakin kofar toilet din

"Please ku kwantar da hankulan ku, ku bari muyi kokarin shawo kanta sai muji meke damunta" ummi ta fada tana duban su kafin ta mayar da dubanta ga boss man.

"nifa ina tunanin watakil ko tayi zaton kai ne kayi mata wanka a daren jiya shiyasa take kuka"

Dafe kanshi yai da hannu Waya saboda shi ma ya yarda da maganar ummi, cikin muryar lallashi Yace"Unaisah, bani ne nayi maki wanka ba, Aunty umminku ce, bayan na dawo dake jiya na kawo ki gida da taimakonta kika tsarkake jikinki har kikayi wanka.. " kafin Ya kare maganar, cikin muryar kuka tace"ni ba wannan bane damuwana ba, daddy meyasa za ka yi min haka?

Hankali atashe taj ya Wan zaro idanu Ya dubi ummi babu alamun ya fahimci abunda Unaisah take nufi sai ma cewa yayi"kinyi mafarki ne da daddynki"? A tsiwace tace"ba mafarki nayi dashi ba, a zahiri na ganshi jiya, saboda me zaka dinga 6oye min kanka daddy, ko ka daina sona ne" ta faWa tana haki

Dariya ce ta kubcewa ummi ganin yadda taj ya daura hannayensu biyu saman kanshi alamar Ya shiga Uku gaba daya yabi ya ruWe Sai lokacin Ya tuna da abun da Ya faru Jiya, da kanshi Ya cire facemask dinsa Ya jefar da shi saboda baya ahayyacinsa ashe idonta biyu taga fuskarshi

Muryarshi tamkar zai fashe da kuka Yace"am really sorry my Angel, nayi laifi ay min afwa, nasan ban kyauta maki ba, amma dan Allah ki fahimce ni, ki nutsu ki saurari me zan fada maki.." kafin ya kare maganar ta katse shi da cewa"ni bazan saurari komai ba daddy, kawai ka daina sona ne ba ka damu dani ba, kuma ba ka yi kewata ba shiyasa kake 6oye min fuskarka..." ta fada tana jan majina kafin taci gaba da cewa"Daddy, what did I do to deserve this punishment from you? Daddy kasan kuwa irin kalubalan rayuwar dana fuskan ta? Daddy duk halin da na shiga ban ta6a mantawa dakai ba, bana kwana batare da na sanya ka acikin addu'ata ba, kullum zullumina ya rayuwar daddyna ta ?are? Meya faru da shi bayan Ya jefa ni cikin ruwa, Ya rayu ko ya mutu.... "

Ba ta kare maganar ba saboda kukan daya ciyota, ta kuma fashewa da wani kuka tamkar ana zare ranta, abunne Ya tsaya mata aranta ya 6ata mata rai duk irin kewansa da tayi amma shine ya boye mata kansa.

Gaba Waya hankulansu Sajeed Ya koma kan fuskar tajuddeen, kalaman Angel ne suka fahimtar da su wanene shi

Muryar na rawa Azeeza tace"dama kai ne daddyn Angel wanda kullum take bamu labarin shi"?

Da sauri Parveen tace"idan bazan manta ba, duk in muka zauna fira unaisah saita bamu labarinka, itace tafara sanya mana kwaWayin ganin ka, da zumudin son muje gidan su don muyi rayuwar ?an ci, har fada mana takeyi daddyn ta zai kar6emu kamar ya'yansa..... Kasa karasa maganar tayi nan take ta fashe da kuka.

Cikin karyayyar murya Batool tace"ashe kai ne daddyn Angel, Ni burin da nake dashi idan Allah yasa na haWuwa dakai shine inyi maka godiya saboda Angel ta faWa min kaine ka ilmantar da ita, ka tsaya mata tsayin daka har ta samu ilmin addinin da take da shi, uwa uba kaine silar da Angel tazo duniya...." tana magana hawaye na wanke fuskarta.

"Wallahi ba mu ta6a sanin wanene mahaliccin mu ba, sai a sanadin zuwan Angel GIDAN KURKUKUN ?ADDARA, , In da mu ka yi rayuwar kulle, cikin duhun jahil ci, harta toilet atare muke shiga da ?an uwanmu maza Angel itace ta tsawatar mana ta fada mana cewa babu kyau mu daina haramunne wani yaga tsiraicin wani......" kuka ne ya kubce ma batool, ummi dake sauraransu a matu?ar ruWe take Wan zare idanunta akan fuskokinsu, gaba Waya sun jefa ta a cikin ruWani lamarin yayi mu?ar girgiza ta, tayi matukar razana.

Bata gama shan mamaki ba cikin sanyin murya haris Yace"Allah ne kadai zai iya biyanka daddy, zuwan Angel cikin rayuwarmu tamkar baiyanar haske ne a cikin duhu, wallahi baki bazai iya furta irin wahalar da unaisah tayi akanmu ba, duk da kasancewar ta ?arama a cikin mu amma tana da kaifin basira kuma tana da hankali, Angel ta zama jigo na rayuwarmu, ta share mana hawayenmu a lokacin da muke kukan radadin kuncin rayuwar da muke aciki, Angel uwace agare mu, saboda ta kwatar mana ?ancin mu da aka tauye mana......" zu6ewa haris yayi kan gwiwowinsa hawaye naci gaba da sintiri kan fuskarsa, Gaba Waya sun gama kashe ma tajuddeen jikinsa, yayi sanyi la?was zuciyarsa ta karaya, wasu irin zafafan hawayene masu Wumi suka soma wanko fuskarshi yayin da yake kallonsu Waya bayan daya, yana mai jin tsantsar tausayin su da kaunarsu azuciyarshi, Angel ta gama masa komai a duniyar nan baisan ma ina zai tsoma kanshi ba tsabar yadda Yake jin mahaukacin sonta na kara nunkuwa acikin zuciyarshi, ba zai iya misalta irin alfarin da ya ke da ita, burin kowani ubane ya sami ?a kamar Angel wadda zata kare masa martabarsa da kimarsa a idon duniya, wadda zata daukaka darajarsa ta kuma yi silar shigar shi aljanna, hannu Waya ya daura akanshi Yana cigaba da kallon su jikin shi har kerna kerma ya ke yi.

Duk wannan abun dake faru a kunnan chief owais da Big guy wadanda basu jima da zuwa bakin kofar dakin ba, sunzo zo ne don su duba jikin Unaisah sai kuma suka ji abunda ba suyi tsammani ba wannan dalilin ne yasa suka dakata suna sauraron su

Cikin shesshe?ar kuka Naufal Yace"daddy duk yadda zamuyi maka bayani ba lallai ka fahimce mu, amma wallahi muna kaunarka muna son ka daddyn Angel" wasu hawayen nan suka kuma wanke fuskar taj, idanunshi sunyi jawur da su gaba Waya ya rasa bakin magana sai dai kallonsu da yake tayi gwanin ban tausayi

"Unaisah itace take ?arfafa mana gwiwa, itace komai namu, itace muke gani muji dadi, unaisah ko mun 6ata mata rai bata yin fushi damu ba, sai ma taja mu ajikinta saboda tasan bayin kan mu bane, rayuwa mu ke a cikin duhun jahilci, ....."

gaba Waya suka dubi batool da ta dauko maganar hawaye na sintiri kan kuncinta, dakatawa tayi da yin maganar na Wan wani lokaci kafin taja numfashi taci gaba cewa"Waya daga cikin abun da unaisah tayi wanda har a bada bazai ta6a gogewa acikin zuciyata ba, shine musuluntar da yar uwar mu unaiza da tayi, unaisah bata bari unaizah ta mutu a matsayin arniya ba, sai da ta taimaka mata ta kar6i shahada duk don saboda ta tsira a lahira..." muryarta na rawa tayi maganar, kusan atare suka rushe da kuka tunawa da yar uwarsu unaizah, maganar batool ta fama masu raunin dake acikin zuciyoyin su.

zu6ewa su ka yi gaba dayansu saman gwiwowinsu agaban tajuddeen, suna kuka


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login