Showing 231001 words to 234000 words out of 298130 words

Chapter 78 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

hankali.

Baccin ne Ya rinjayeta, jikinta ya saki a sukwane ta kwantar da kanta saman pillow, ta lumshe idanunta har lokacin bata daina yin sambatu tana ambaton sunan Angel.

A hankali unaisah take binta da kallo zuciyarta na harbawa da karfi da karfi gani take kamar in ta tafi ba zasu ?ara haduwa ba, lokaci Waya taji tsantsar tausayin matar ya kamata, tayi fatan ace zata cigaba da kula da ita sai dai tasan daddynta bazai barta ba, after that yan uwanta suna bukatarta ita kanta bazataso tayi nesa da su ba, ruwan hawayen da suka taru acikin idanunta ne suka fara yar tseral kan kuncin ta.

"Azeezaty! Ke nake jira muje ko"? Dr jazz ne yayi maganar yana daga tsaye bakin kofar Wakin, mi?ewa tayi daga kan kujerar, kamar wadda aka zarewa laka, ta sunkuyar dakanta saitin fuskar Benazir ta manna mata sumbata har sau biyu kafin ta juya taje ta Wauko backpack dinta, ta kalli hajiya layla mi?a mata hannu tayi alamar tazo, da sauri unaisah ta ?arasa gareta, hajiya layla ta rungumota a kirjinta.

"Toh Azeezaty, mungode Allah yasaka maki da alkhairi, Allah ya baki ilimi mai amfani duniya da lahira, Allah ya baki miji nagari, zamuyi kewar rashinki, Wan zaman da mukayi dake mun saba dake, benazir zatayi kukan rashin ki, Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwarki, Allah yasakama iyayenki da alkhairi..." amsa wa tadinga yi da ameen kamar kar su rabu da juna.

"Ki gaida min da mutanan gidan, in sha Allah zamu zo wata rana har gidan naku"

Murmushi Unaisah tayi"Allah ya kawo ku lafiya, Allah ya ?ara ma mamana lafiya, nima daddyna yace zai kawo ni gidan ku" murmushi hajiya layla tayi taji dadin maganar, sallama sukayi da juna, A hankali take tafiya tana waiwayon Benazir dake kwance tana ta sharar baccin ta....
Dr jazz harya fara gajiya da jiranta, sai faman duba wrist watch dinsa yake yi baya son chief ya karaso don yasan bai son jira.

Har fa ta kusa fitowa daga dakin sai kuma ta juya da sauri ta koma gaban gadon Benazir ta manna mata peck a goshin ta.

Ganin abun nata bame karewa bane yasa dr jazz shigowa dakin Ya tasa keyarta gaba suka fito, baiwar Allah tana tafiya tana waiwayon dakin hajiya layla tana tsaye bakin kofar room din, hawaye sun cika idanunta har saida suka bace ma ganin ta kafin ta juya ta koma ciki zuciyarta cike fal da kewar Azeezaty.

A dai dai lokacin da suka fito, hamshakiyar motar chief ta kunno kai ta entrance gate din asibitin yar uban su launin ash colour har sal?i take da daukar ido, yanayin yadda motar take tafiya slowly yayi matu?ar jan hankalin visitors dake zarya a arean wurin, suka bi da ido har saida ta tsaya a parking sace.

"Muje, Ina tunanin shi ne ya karaso" jaz ya fada tare da jan hannunta, tunkafin su ?arasa take ta kallon hamshakiyar motar, tayi mata kyau, lokacin dayazo kawota ba irin wannan suka hau ba.

Bayan sun ?arasa gaban motar, ta ciki aka buWe mata cardoor din wani daddaWan fragrance ne Ya daki hancinta, mai haWe da sanyi A.c.

"Ki shiga ciki" jazz ya faWa tare da nuna mata hanya, sunkuyar dakai tayi tare da shiga ta zauna, wurga ido tayi akan shi har saida taji gabanta ya fadi saboda wani kyau da taga yayi mata, ya kare gefen fuskarshi da phone dinsa, da alama waya yakeyi, fuskarsa tana asanye da mask.

Hadadden yard din dake ajikin shi Senator cotton material ne light sky blue, rigar short sleeve ce ta bayyana strong arms dinsa, na karfafan maza masu ji da kan su, lallausar sumar kanshi ta sha gyara, ya sabunta military hair cut din sa

Sunnar da kanta ?asa tayi ganin yana ?o?arin juyawa, janye wayar yai daga kunnanshi, Ya Wago suka haWa ido da jazz sai faman sakar sakar mashi murmushi yakeyi
"babban yaya, sannu da zuwa barka da safiya"
Calmy ya furta"lafiyalou jazz, ina fata kaima haka"
"Alhamdulillah"
"Ya mai jikin?
"Taji sau?i sosai"
"Naji dadin jin hakan, zamuyi magana anjima" amsa mashi yayi da toh, har time din bai kalli Unaisah ba, kamar baisan da zaman ta ba sai bayan da jazz ya rufe murfin motar, ta kamo belt zata daura taji ya ruko yana kokarin sanya mata ita wani irin shock taji, muryarta na Wan rawa ta furta"ina kwana"
"Ina lafiya" atakaice Ya amsa mata, agogon hannun shi tabi da kallo kirar rolex daytona tayi bala'en yi mashi kyau....bayan ya kammala sanya mata ya gyara zaman shi,
A hankali ya dago ido ya kalli senior Agent din dake zaune a driver seat"zamu iya tafiya" cikin girmamawa ya amsa mashi okey Sir,
Key yayi ma motar tare da yin reverse ya karya kwana motar ta fuce daga asibitin.

Ajiyar zuciya ta Wan sauke idanun ta akan window glass din motar, asibitin take kallo cike da jin kewar Benazir matar ta kwanta mata aranta, amma idan ta tuna yar uwar chief ce sai taji hankalinta ya kwanta, ta wani bangaren ta kosa su koma gida ko dan taga yan uwanta almost one week tayi kewarsu"

Fragrance din turaren chief Ya hana ta sukuni, ta wutsiyar ido take satar kallon shi, dogon hancin nan nashi ba karamin tafiya yake da ita ba. Hankalin shi na akan phone dinsa da yake scrolling
Tayi tsammanin gida zasu wuce kaitsaye amma sai taga kamar sun canza hanya, ba wadda suka biyo ba aranar da zai kawo ta, aranta ta ayyana watakil wata hanyar ce da bata sani ba.
Tana tsaka da yin zancen zucinta, suka karaso wani katafaren Obie mall luxury plaza

Tayi mamakin haduwar wurin tunani ta farayi ko me zasuyi a mall din? Ta dai zubama sarautar Allah ido.

bayan shigar su ciki agent din yai parking a katafaren parking space na mall din.

Shiru tayi zuru tana jiran jin me zaice, sai da ya shafe 5 mins kafin taji ya furta"Let's go inside." fitowa sukayi atare, da sauri senior agent din ya fito ya take masu baya, Hankalin Ta ba karamin tashi yayi ba ganin wayayyun ?an mata da samari yan gayu suna zarya a wurin duk sai taji ta raina kanta, wata irin kunyace ta kamata, takasa motsawa daga inda take ganin idon mutane ya dawo kansu, duk da facemask din dake akan fuskar chief hakan bai hana mutane kallon shi ba musamman yan matan dake gifta wa wasu kamar zasuyi tuntu6e tsabar yadda suke kallon shi, ga shi ba halin tunkarar shi saboda senior agent din dake atare da su, wani basamuden mutun ne ?ar?arfa babu annuri kan fuskarshi, ga bindigu dake soke a qugun shi.

Ganin bata da alamun motsawa ne yasa shi ruko hannunta a cikin nashi, rass taji gabanta Ya faWi duk sai ta kama yan kame kame tana faman noke kai, duk da yadda taso ta daure kada tai kauyacin saida ta kasa a hankali take satar kallon mall din yayin da suka nufi main entrance, Security guard din dake tsaron wurin sun gane chief, sai miko gaisuwa sukeyi cikin girmamawa kamar zasu durkusa kasa, tun da taga haka sai ta fara jin kanta wata hajiya gata ga chief, murmushin gefen fuska ta dan saki tana wani tafiya taku dai daya tana hura hanci.

Senior agent din ne ya ruke mata shopping cart, ganin taki daukar komai sai kalle kalle takeyi ne yasa agent din yi mata gyaran murya ta kalle shi"ki dauki abunda kikeso, sannan ki daukarwa yan uwanki"

waro ido ta danyi tare da juya kai ta kalli chief, yana tsaye gefenta ya goya hannayen shi kan kirjin shi in a low voice ya furta"Do what he said" amsa mashi tayi da toh, nan fa tafara ruwan ido ta rasa me zata dauka ba sabon ba, ga mutane suna ta yin shopping dinsu hankali kwance ita ko kamar an daure mata hannayenta,

Sun lura da yanayin ta ganin zata 6ata masu lokacine yasa chief kallan agent din ya bashi umarnin duk abunda yaga idanunta sun kalla ya daukar mata shi ko da mara amfani ne, ya amsa mashi da okey sir.

juyawa chief yayi a hanzarce ya koma mota ya zauna saboda baison kallon da mutane sukeyi mashi.

Bayan fitar chief, Unaisah ta mi?i hanya, agent Win yana abiye da ita jira yake yaga me idonta zai kalla, ita kuma taki yarda ta kalli komai tunda taji umarnin da chief ya bada, tafi son tayi ta kallon yan mata da samarin dake shopping a wurin.

Adaidai wurin Confectionery, ta tsaya tana kallon chocolates din dake a jere ga cookies kala kala, da sauri agent din ya fara jidar mata su iri iri yana turawa a cart din duk abunda ta kalla saiya dauke shi, har saida ta kau da ido tukunna ya dakata. Tafiya ta cigaba dayi ta nufi gurin data ga an rubuta Female Fashion Floor, kayayyakine kala kala na mata da zarar ta kalli abu, cikin sauri agent din yake daukar mata shi koda kuwa mara amfanine kai har bras da pads saida ya kwasar mata saboda umarnin boss dinsa yake ki.

Gabanta har faduwa yakeyi ganin cart din ya fara cika, ita fargabanta ba tasan kudin kayanba kada su yi almubazzaranci.

Hakan baisa ta juya ba sai ta nufi Boys' Corner kayan mazane tundaga kan suturu masu kyau da tsada har izuwa takalma, shades, caps, watches komai fa babu ce kadai ke babu, da sauri agent Win yafara jidar kayan da yaga idanunta suna kallo, saida yaga ta kau da ido kafin ya dakata, cart din har ya cika yayi sauro, hakan yasa agent din yayi magana da wani sales assistant dake akusa da su yace mashi ya dauko masu wani cart din da sauri yaje ya dauko ya ruke mashi suka cigaba da take mata baya, aikin yi fa ya samu, ita fa hankalinta ma baya akan kayan, kawai gurin ne ya burge ta shiyasa ta?i tafiya, idonta take ba abinci, a wani Tech zone ta tsaya tana kallon kayan dake gurin da sauri ta juya duk suna abiye da ita kamar wata sarauniya, mutane sai kallon ta sukeyi suna mamakin kayan da ake kwasar mata, ko yar wacece?


Har zata gifta gaban wani education hub ta dakata tana kallon writting material din dake a gurin, bakomai ta tunaba face yan uwanta bata da burin dayawuce su iya karatu da rubutu, yanzu ne taga abu mai amfani da zata iya nuna tana so..harta buWe baki zatayi magana idonta ya sauka akan agent din da assistant din sun dage sai kwasar mata kayan sukeyi, tun daga kan notebooks, Dictionary, pens, pensil, markers, drawing book, duk wani abu da idonta ya kalla saida suka Waukar mata shi, gaba daya sun kashe mata baki, kamar sakarya haka ta saki baki tana kallonsu, ganin abun nasu bame karewa bane yasa tayi saurin furta"dan Allah ku dakata Ya isa haka! wadannan kayan sunyi mana yawa.."
Agent din yace"banga alamun sun isa ba, Ni umarnin chief nake bi, in kina so mu dakata to ki kau da idonki daga kan kayan da sauri ta juya baya ta fara kokarin neman checkout counter dakyar ta gano gurin ta tsaya tana faman sauke ajiyar zuciya kamar wadda tasha gudu, har cashier din sai da ta dan bashi mamaki, ganin yadda ta fado gaban counter din, bayan ya auna kayan da suka siya total 800k har saida taji yan hanjin cikinta sun kaWa murya na rawa ta kalli agent din"dan Allah ku rage kayan su koma na dubu goma" maganarta taso ta basu dariya agent din yace"da alama bakisan wanene chief ba, idan duka kayan mall din kikeso zaisa a mallaka maki su, babu abunda zai ragu na daga tarin dukiyar da yake da shi.." jinjina kai cashier din yayi" amma dai yalla6ai, ita din bakuwa ce a family din su? Daga mashi gira agent din yai, murmushi cashier din yayi a lokacin har an kammala sanya masu kayan a cikin shopping bags har kusan huWu,
Agent din ya zaro master card din da chief ya bashi ya mi?a ma cashier din don ya ciri kudin, ?in kar6a yayi fuskar shi dauke da murmushi ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?yace

"Grandpa dinsa Ya hana a kar6i kudinsa, ku tafi kawai" girgiza kai agent din yayi"ka kar6a ka ciri kudin, chief baya son siyan kaya batare da an kar6i kudinsa ba, gani yake kamar sadaka aka bashi" dariya sukayi cashier din yace"nasan halin shi ay, har yau bai canza ba kenan, kudin ay duk nasu ne ko an kar6a hannunsu yake komawa, pls ka bashi hakuri ni bazan iya cirar kudinsa ba, zaija min ne..." duk yadda agent din yaso ya kar6i card din yakiya dole suka hakura yace ma unaisah su tafi, ita dai hankalinta yaki kwanciya, ta ruWe da alamarin, taya zasu sayi uban kayan nan kuma aki kar6ar kudinsu? Abunda bata sani ba, mall din mallakin famiy dinsu ne, juyawa tayi da sauri ta nufi hanyar fita agent din yabi bayanta, ma'aikatan mall din suka bi bayansu da shopping bags din..

Bayan sun sanya masu kayan a boot din motar, agent ya bude mata car door din ta shiga ta zauna tare da kallon chief ya nutsu yana daddana wayar hannunsa, shigowa ciki agent din yai ya zauna a driver's seat ta mirror ya kalli chief.

"Sir, we've completed the purchase, and the goods are in the boot."

Fuskarshi babu annuri Ya furta"Why didn't I receive a debit alert?

"Sir, grandpa Winka Ya hana su kar6i kudinka, ba yadda banyi da cashier din ba amma ya?i kar6a yace baya son yaja ma kan shi" ta6e baki chief yayi kafin a hankalli ya dan juya suka hada ido da unaisah dake ta kallon shi, da sauri ta sunnar da kanta ?asa cikin sanyin murya tace"mungode Allah yasaka da alkhai..." bata kare maganarba ya toshe mata bakin ta da yatsan hannun shi..idanunsu acikin na juna ko kyaftawa basayi wani irin kallo suke jefawa junansu hatta agent din dake driving dinsu sai satar kallon su yakeyi ta cikin mirror fuskar shi dauke da murmushi yajima baiga macen data dace da chief irin yarinyar nan ba, sun burge shi.


da sauri ta sauke idonta kasa ta kama yin yan kame kame kamar zata nutse kanta cikin cinyoyinta, zame yatsansa yai daga kan la66anta, laushinsu ba karamin fusgarshi sukayi ba, muryar shi tamkar tame jin bacci ya furta"kada ki ?ara yi min godiya bana so" daga mashi kai tay"bazan ?ara ba"


*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE=?%?
'?*


*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*ASSALAMU ALAIKUM
Mata masu abun duniya=?%?=?%?=?%?
*Zuzeam empire* takawo muku babbar gara basa
Duka akan 5500 ki daure ki mallaki naki kar dama ta wuceki Garabasa gara basa =????=????=????=??<؁?=؃? ?

Wa.me/+2348144015291 For more information say hi =?K? Ina uwar gida da Amaren bayan sallah zuzeam empire tashirya tsaff dominku=؃?=؃?=؃? muna gyaran ciki muna saida kayan gyaran jiki dilka sabulu dadai sauransu

*DAHUWAR KAZA*

Kin taba cin *DAHUWAR KAZA 5in1* wato *Ni ima, Matsi, Chikowa, MAllaka, da Karin soyayya*
Duk me buqata TAYIMUN magana ta Pvt *Akwai kyauta <؁? mai tsoka ga mutun 5 da suka fara siya*

*INA MASU JEGO DA AMARE*
Karku bari wannan dama ta wuceku
*08144015291*
Zuzeam empire

ASSALAMU ALAIKUM Mata ga wani sirri mai abun mamaki amma mata aji tsoron Allah kada ayi amfani da wannan dama kijuya mai gidanki yanda bai kamata ba amfaninshi shine a tafin kafar ki kawai zaki shafa lokacin kwanciya zakiga daukar hankali wurin mai gida amman don Allah karki juyashi yanda bai kamataba amana ce na baki 08144015291. 1000 kacal =?L?
Munada kaya kala kala wanda bazasu faduba kedai kidau number kimin magana ngd

Infection set
Sabon budurci set
Niima set
Basir set
Matsi mallaka
Amarya set
Uwar g1da set
Mai jego set

Dadai sauransu




*Daga al?alamin Boss Bature=?%?
'?*



"Good" ya furta tare da gyara zaman shi, babu wanda ya ?ara furta kalma a cikin su, shiru motar baka jin sautin komai sai sanyin A c dake ratsa fatar su, aranta Allah Allah take su karasa gida don ta nuna ma yan uwanta tsarabar da tayi masu tasan zasu ji dadi.

_________________________
'?

Gaba Waya ?an aikin gidan suna atsaitsaye gaban door room din marwa, fuskokinsu babu walwala idanunsu sun kumbura saboda rashin isasshen bacci da basu samu ba adaren jiya, sai zullumi da fargaban abunda zai biyo baya sukeyi tun wuraren karfe shida sheikh imam ya karaso gidan, tunkafin karasowarshi bayan kammala sallar asubahi baba obie ya tura su hajjaty tare da security suka dauko marwa daga asibiti yanzu haka tana acikin dakinta tare da sheikh imam malik sautin ru?iyar da yakeyi mata ya cika kunnuwansu bayin Allah sunyi zuru zuru, hankalinsu atashe tun safe ake abu Waya har yanzu ba wani labari mai dadi, a kalla sun shefe awanni abakin kofar dakin suna jiran sheikh imam malik.

"Idan har ya tabbata aljanune suka Waura mata ciwon, ni dai inaga zan tattara kayana in koma kauyenmu da zamane, zaifi min kwanciyar hankali don bana jin zan iya cigaba da zama agidan nan...." cikin rawar murya safa tayi maganar.

Abla tace"ni kaina na tsorata wallahi, jiya a zaune na kwana saboda fargaba da zullumin abunda ya faru da marwa, wlh ta bani tausayi baiwar Allah rana daya mutun ya tashi ba baki ga kuturta!"

Sofia tace"nifa saboda tsoro jiya bayan mun dawo gida, dana shiga daki karatun kur'ani na kunna awayata sai da asuba na kashe"

kowa yana tofa albarkacin bakinshi banda hajjaty dake tsaye ta goya hannayenta kan kirjinta, ita dai hankalinta bai kwanta da ciwon marwa ba!

Jin motsin buWe kofane yasa sukayi shiru suna jiran tsammani, A


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login