Showing 126001 words to 129000 words out of 298130 words

Chapter 43 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

da zagayo da hannayenta kan waist dinsa, tuni yafara jin shi awani yanayi.

Sumbatar wuyansa tayi kafin ta dago da bakinta saitin kunnanshi cikin muryar raWa mai hade da kwarkwasa tace"fadamin me ka ke so nayi maka wanda zai faranta ranka"

"Nagaza yarda da abinda kike fada min, anya kuwa kece? Ko dai aljanune suka shige ki? Nifa ina kokwanto bana so saina shagala ki canza min ainihin kala dinki"

dariya tayi cike da nishadi tace"ka daina kokwanto akaina, ni ce dai hajiya saratun daka sani, matarka uwar ya'yanka"

Murmushi pravin yai cike da jin shaukinta

"Ka yi breakfast ko insa a kawo mana mu yi a daki nima banci komai ba"

"In ban da abunki ay kinsan bana iya cin abinci idan ba atare dake ba, don ma ke dince wani lokaci baki jira na"

"I'm sorry Yanzu bari na kira akawo mana a daki, me kake son ci"?

Yana faman washe baki yace "Duk abin da zaki ci, zabinki ay shine nawa"

Shu'umin murmushin gefen fuska hajiya saratu tasaki tare dakai hannu ta dauki waya ta kira layin kitchen ta isar da sakon akawo masu abinci, bayan abla ta kawo masu atare suka zauna suna ci, kamar sabbin ma'aurata abaki ta fara bashi har sai da suka cinye kafin ta soma jan hankalin shi.

Gaba Waya nema take ta zautar dashi da salonta, kasa jurewa yayi da sauri ya ?ara tighting nata a jikinsa.

_________________________________d'
'?


Bayan shigar chief bedroom dinsa a zafafe Ya faWa Bathroom dinsa don ya watsa ruwa ko ya samu zuciyarsa ta lafa daga radadin da ta ke yi masa.

ganin ya shiga toilet yasa big guy sauke ajiyar zuciya, yayi tunanin zaiyi yadda ya saba ne idan ransa ya 6aci da wuya in bai yi ma kan shi illa ba, wani lokacin mirror yake kaima naushi ya tarwatsa shi har sai hannun shi ya faffashe saboda tsabar zuciyar dake gare shi.

Kafin fitowarshi da sauri big guy ya fita na tsawon mintuna ya dawo hannun shi ru?e da wooden tray mai dauke da breakfast din chief.

Yayi mamakin ganin shi kwance kan gado, jikin shi sanye da bathrobe ya Waura hannunsa Waya kan lallausar sumar kanshi, ya lumshe wadannan kyawawan idanuwan nashi, bakomai yake tunawa ba acikin zuciyarsa face tarihin rayuwar prisoners, labarin yai matu?ar ta6a zuciyar shi.

"Allah Ya huci zuciyarka Yalla6ai, ga breakfast dinka, nasan kana jin yunwa" cikin girmamawa yayi maganar

Tamkar bazai tanka mashi ba, sai da ya dauki lokaci kafin Ya furta"ka koma da abincin bana jin zan iya ci"

Cikin sanyin murya big guy yace"ka yi hakuri Sir, kasan ni mai biyayya ne agare ka, bana yi maka jayayya amma yau bazan iya bin umarnin ka ba, saboda na damu dakai, abun da ke damunka nima shike damuna..." ya fada yana cigaba da kallonsa.

"Sir, ?in cin abinci bashi bane mafita, kana bu?atar kwanciyar hankali da nutsuwa, wanda hakan bazai samu ba sai ka jajirce wurin ganin ka kauda damuwarka, sannan yanzu ne ya kamata mu dage damtse mu yi aiki tu?uru don ganin mun gano su wanene azzaluman mutanan da suke aikata 6arna a kasarmu"

DaWaWan kalamai Big guy ya cigaba da zayyano masa yana kara karfafa masa gwiwa da kwantar masa da hankali, A hankali Ya fara jin saukin radadin da zuciyarsa ke yi mashi.

"Sir, har yanzu kana akan bakanka na bazaka ci abincin ba"? Ya faWa yana duban cute face din Ogan nasa

Slowly ya Wan motsa tausasan pink lips dinsa in a low voice ya furta"zan kokarta" gyaWa kai yai
"Zan tafi yalla6ai, Ka huta lafiya" ya fada tare da sara mashi kafin Ya juya har ya kusa ficewa daga dakin muryar chief ta ratsa kunnansa"nagoda da kulawarka agare ni"
Murmushi big guy yai"kada ka damu yalla6ai"
Har zai fuce ya kuma dakatar da shi"please ka duba dakin Yaron nan, kaga Awani hali Yake a ciki, Idan ya farka a tabbatar Yayi breakfast dinsa, idan ya gama ka tambaye shi me yake bukata in ya fada maka ay gaggawar yi mashi, zuwa anjima sheikh Imam zai zo duba shi"

"Okey, Sir"

Ya fada tare da bude door room din Ya fito waje, dakatawa yayi da tafiya yana tunanin tawace hanya zai faranta ran chief? Don ya fahimci har yanzu akwai sauran damuwa aranshi, tunawa da Unaisah yasa shi saurin zaro wayarsa ya danna ma boss kira, tana fara ringing yai picking Call din
Da zolaya yace"masu ?a, halan Har yanzu kana nan ma?ale da ita"

Sautin muryar boss da alamun dariya yace"To Wan sa ido, ka fara tsokanar taka ko"?

Dariya Big guy yayi" inatayaka murna abokina"

"Nagode sosai mutumina, Ina chief ne ina fata yana lafiya"

"Ba lafiya, Har yanzu akwai damuwa aranshi, Kuma kasan halinshi mutunne mai zuciya, yanzu haka ina a kofar dakinsa, na kai masa abinci yace min bazai iya ci ba"

Muryar bos da jimami yace"amma banji dadi ba, pls ka yi kokarin kwantar masa da hankali kafin inzo"

da sauri big guy yace"anya zan iya? Ko dai zaka turo unaisah ko da godiyane tayi mashi, watakil hakan Ya kwantar masa da hankalinsa"

"Nima nayi tunanin hakan, yanzu zan turo ta in sha Allah" murmushi big guy yai kafin yai mashi sallama a hanzarce Ya nufi bedroom diny Danish.


*d'GARKUWA=ت?*


A kishingiWe Yake kan gadon shi, Ya hakimce kamar wani basarake, wasu hadaddun sleeping dress ne a jikin sa launin red colour sunyi bala'en yi mashi kyau, hannunsa Waya rungume da pillow, lallausar sumar kanshi ta lullu6e gefen fuskarshi, yayin da kyawawan fararen idanunsa ke akan hadadden ceilling din dakin, tun da Ya farka daga bacci bai ta6uka komai ba, gaba Waya ya shagala da tunanin Hateem, wani irin kewarsa yake ji, mutumin ya kwanta masa aransa saboda yadda ya tarairayesa ya bashi kulawa kamar wani nashi, bai ta6a tsammanin zaiji tsantsar kaunarsa ba, sai gashi zuciyarsa takasa samun sukuni saboda tunaninsa, da zarar ya lumshe idanunsa fuskar Hateem yake gani dauke da murmushi......"

Yana son ya sake sanya shi a idanunsa, kwata kwata bai fahimci cewa prime minister kasar ya bari ba.

Har Yanzu kamshin turaren daddy hateem bai bar jikin shi ba, saboda rungumarsa da yadinga yi jiya kamar zai maida shi jikin shi, fragrance din Yana da karfi sosai shiyasa ya kama jikin sa.

Kalaman hateem ne suka fara dawo mashi

_zan tafi da kewarka, dan Allah kada ka manta dani, inaso ka Wauke ni tamkar mahaifinka, aduk lokacin da wani abu ke damunka ka sanar da chief zai fada min, zamu dinga yin waya akai akai, daga yanzu inaso ka dinga kirana da sunan daddynka_

A hankali ya dago da yatsan hannunsa yana kallon zoben da ya sanya mashi ayatsa mai kyan gaske, wannan ne karo na farko daya fara sanya zobe,
Daura yatsan yai kan kananun la66ansa Ya sumbace shi a hankali yanayin fuskarshi kamar zaiyi murmushi.

Knocking din kofar dakin da akaine Ya sa shi daura idonsa kan kofar, bakomai Ya fado masa arani ba face Angel dinsa, yasan ita kaWaice zata Iya zuwa duba shi awanan lokacin, Idan ba ita ba sai kuma yan uwansa, saukowa yai daga kan gadon bayan ya jefar da pillow hannunsa, da sauri Ya nufi kofar don Ya tarbe ta, saboda yayi kewarta jiya, idanunsa sunyi maraicin ganin ta,, shi kanshi baiyi tsammanin zai Iya mintuna batare da ita a gafen sa ba, sai gashi jiya daddy hateem Ya sace zuciyarsa.

Ko da ?ofar ta bude yai arba da big guy tuni yanayin fuskarshi Ya canza, shi da ya taso da zumudinsa don Ya nuna ma Angel dinsa kyautar zoben da mutumin nan ya bashi, sannan Ya bata labarin abunda Ya faru atsakanin su ashe ba ita bace.

"Barka da safiya danish" big guy ya fada da fara'a akan fuskarsa, ko kallo danish bai mashi ba, Hankalin shi na akan bayan shi, burin shi Yaga Angel don har yanzu bai fidda rai da ganin ta ba

Da mamaki big guy ya waiga baya don yaga me yake kallo sai dai baiga komai ba.

"Ina fata ka tashi lafiya" ya fada aranshi yana mai mamakin Girman Jikin Yaron ga tsawo tubarkalla uwa uba ga kyau kamar shi ya zana kan shi.

"Magana na ke yi maka ka yi shiru ba ka ce komai ba, ko har yanzu ba ka jin daWin jikin naka ne"?

cikin sanyin murya ya furta"My Angel? Tana Ina"?

Dafa kafadarsa big guy yai"kwantar da hankalinka tana nan cikin koshin lafiya, nasan zata zo dubaka..." kafin Ya kare maganar danish Yace"Ina son ganinta, " ya fada yana kokarin bi ta gefen shi Ya wuce, A hanzarce big guy yai saurin Shan gabanshi, gudun Kada Ya ruguza masa plan dinsa na zuwan angel part din chief.

Wani kallo da danish Ya watsa mashi sai da yaWan ji fargabansa, Karfin Hali Yai wurin furta"Ka yi hakuri bawai ina son dakatar dakai bane, daga gani yanzu ka farka daga bacci ko wanka ba ka yi ba, a haka zakaje wurinta? Itama bazata ji dadin ganin ba, kaje kayi wanka, kafin ka fito zan sa unaisah ta kawo maka breakfast dinka har daki"

cikin sigar lallashi yakeyi mashi magana, badan Ya yarda da kalaman sa ba, ya amince mashi, juyawa yayi tamkar wanda ya rasa kuzarinsa, harta bugun zuciyarshi ya canza ji yake kamar wani abu na faruwa ko yana shirin faruwa
Bayan ya shiga toilet Ya maida kofa ya rufa, ajiyar zuciya big guy ya sauke aranshi ya ayyana wai Allah daga ganin yaron nan zaiyi kafiya, dole saina mike tsaye idan ba haka ba zai iya zame min matsala.

Ya fada tare da juyawa ya fuce daga dakin, Ya nufi sashen kitchen din su don Ya hada masa breakfast dinsa.

*d'UNAISAH ANGEL=؋?*

Bata jima da fitowa daga bathroom ba, sai rawar kai takeyi saboda daddynta Ya fada mata zancen zuwa dakin chief don tayi mashi godiya bisa ga irin kyautatawar da yayi mashi, ruwan ido Ya hana ta canki kayan da za ta sanya, tayi tsaye gaban faskeken closet dinsu, sai faman bin jerin kayan take yi da kallo, fuskarta dauke da murmushi tarasa gane meyasa take jin wani irin nishadi da annushuwa kamar wadda akaiwa albishir da gidan Aljanna.


A ?alla ta shafe mintuna kafin ta fito sanye cikin wasu riga da wando launin pearl pink masu kyan gaske, tsayawa zayyana kyawunta acikin kayan 6ata baki ne, abun sai wanda ya gani.

Takalma ta Wauko masu tsini launin kayan, ta zura su a kafarta, bayan ta dauko mayafi ta tsaya gaban mirror ta ta soma laga shi akanta.

Ita kanta data kalli madubi sai da ta firgita da ganin wani sihirtaccen kyau daya bayyana akan fuskarta, murmushi tadan saki har dimples dinta suka lotsa.

"Daughter I'm waiting For You, Kin bar daddy awaje Yana ta jiranki"

Muryar taj tajiyo daga waje yana magana, da sauri ta nufi kofar ta fito, waro idanu waje taj yai arude Ya furta"Tabarakallahu ahsanun khalikin! My Angel? Kinga kuwa kyan da kikayi kamar hurul aini" sunnar da kanta kasa tay, fuskarta sauke da murmushi
Ruko hannunta yai a cikin nashi suka nufi dakin chief.
Abakin kofar dakin suka dakata suna kallon juna
Lokaci daya suka sakar ma juna murmushi
RaWa yai mata a kunnanta"ba'ay mashi rashin jin magana ba kamar daddy bane da aka raina" dariya tayi jin abun da yace.

Sakin hannunta yai"ki kula min da kanki," amsa mashi tayi da toh, kamar karsu rabu yana tafiya yana waiwayonta itama sai kallon shi take yi
?aga murya tayi tare da cewa"daddy kada ka tafi ka jirani in fito"

"Ba nesa zanyi ba, Zanje gidane bazan jima ba zan dawo" ta6e mashi baki tayi kamar zatayi kuka, hakan ba karamin nishadi ya sanya shi ba.

Zuciyarta Cike fal da fargaban haWuwa dashi tay knocking kofar, Almost 3 times ba'a bude ba, harta fara tunanin ko dai bacci yakeyi ne ko baya a dakin har zata juya kofar ta soma zugewa a hankali ta buWe, kamshin turarensa ne Ya fara dakar mata hanci har saida ta dan lumashe idanunta.

Kasa shiga tay saboda zullumin hada ido da shi, da kuma jin nauyn magana da shi.

Sai da ta shafe kusan mintuna biyar, tana sa?e sa?e a zuciyarta ba tare da ta motsa ba, kafin ta gama yanke shawara da zuciyarta kwatsam kofar ta soma kokarin rufe kanta, da sauri ta ratsa ta tsakankanin door din da karfi ta faWa dakin kamar wadda aka jeho, ?iris Ya rage ?ofar ta datse da jikinta, wannan gangancin nata ba karamin mamaki ya bashi ba, sai faman nishi take yi hadi da sauke ajiyar zuciya, sai da tagama yan kame kamen ta, kafin a hankali kamar maijin tsoronsa ta soma bin dakin da kallon, Lokacin da ta daura idanunta akan shi har saida gabanta Ya fadi ganin surar jikin shi, Har yanzu bai motsa daga kan gadon shi ba, kamar yadda Big guy ya barshi haka ta taras da shi sanye da rigar wanka, ya daura Apple laptop dinsa kan waist insa, Yayin da kanshi ke akan pillow ya dan lumshe idanunsa, tuni kamshin turarenta yakai mashi karo

Yawu ta haWiya, a tunaninta baya ganin ta cikin sanda ta matsa daga gaban gadon tana faman zare gray eye dinta ta furta"ina kwana, ka tashi lafiya" magana takeyi hankalinta na akan kwantaccen sajen fuskarshi.

"Lafiya" taji ya amsa mata da sanyin murya, tayi mamakin jin voice dinsa irin na danish.
Shiru tayi tana faman wurwurga eye balls dinta, bata ta6a jin nauyin wani dan adam ba sai akan shi, kamar ma kunyar shi take ji
Wasa takama yi da yatsun hannunta, batasan cewa yana kallonta ta cikin laptop dinsa ba.

"Idan kingama tsayuwar zaki iya tafiya" sexy voice dinsa ce ta kuma ratsa kunnanta, muryarta da en ena tace"am.. um. wai Dama daddy ne yace inzo in yi maka godiya"

Shiru yayi yana maimaita maganarta a zuciyarsa kafin ya furta"bake ki kayi niyar zuwa ba? Shiya tursasa maki kizo"?

Dafe kai tay da hannu daya alamar ta kwafsa.

"Mantawa nayi, ni nayi niyar zuwa inyi maka godiya".

Ta6e pink lips dinsa yai na Wan wani lokaci kafin yace"ba'ay min godiya, duk wani abu da nayi nayine don Allah, ina fata kin fahimce ni" amsa mashi tayi da toh,
shiru suka kuma yi, Ganin yaki sake tanka matane yasa tai kafin halin cewa"tun da bakason ay maka godiya, to ka fadamin wani abu da zan dinga yi maka tunda kaima ka kyautata mana duk da nasan bazan iya biyan ka ba" ta faWa tana cuke la66anta.

A hankali ya dan ware reddish eyes dinsa, duk wani motsinta akan idonsa sai dai ita batasan Yana kallonta.

"Will you do whatever I tell you?"da kwarin gwiwa ta amsa mashi Eh
"Okey," ya furta tare da sauke Laptop dinsa gefe Waya, a hanzarce ta juya mashi ?eya, Ganin zai mike kuma taga bathrobe ce a jikin shi, murmushin gefen fuska ya dan saki.

Saukowa yai daga kan gadon Ya nufi walk-in closet dinsa, Jim kaWan Ya fito sanye da thobe launin ruwan toka, tamkar a jikinsa aka dinka ta tsabar yadda ta bayyana surarsa.

Kamar yadda yabarta haka ya same ta atsaye ta juya baya.

Zama yai gefen gadon da alama bata san ya dawo ba.

"Zaki Iya zuba min abinci"? Wan zaro idanunta tayi kafin ta amsa mashi da toh, juyawa tayi a hankali ta saci kallonsa Idanunsa na akan wayar hannunsa, taji dadin ganin hankalinsa baya akanta

Cikin takun sanda ta karasa daga gaban table din.

"Me kakeso nafara zuba maka"

"Duk abun da yai maki" farfari tayi da idonta hada Wan gumtse baki alamar mamaki, sam batayi zaton zai kulata har haka ba, kallo Waya da tai masa ta fahimci mutunne mai ji da kansa

Coffee ta mika masa yasa hannu ya kar6a A hankali Yake kurbarsa, Angel sai faman satar kallon la66ansa take Yi, ba karamin rudarta yakeyi ba, ga kamshin turarensa dake ta kai mata hari.

Komai ta zuba masa cinye shi yake yi, mutumin da bai cika cin abinci ba, amma yau har saida yaso ya ?wari cikin sa, ba tare daya ankare ba..

Bayan ta kammala serving nasa tace"ko akwai wani abun da zanyi maka? Ko in gyara maka bedroom din ka"
"Idan kin ji zaki iya" ta6e baki tadanyi kafin tafara tunanin shiga toilet dinsa ta gyara masa shi, watakil kafin ta fito shi kuma Ya fita sai ta gyara dakin

Juyawa tayi da sauri ta nufi toilet din, sai lokacin Ya dago Yana bin bayanta da kallo har sai da ta 6ace ma ganinsa tukunna ya kau da idonsa.


*>?
?ZAHRA>?
?*


A ?udundune take kan darduma ta lullu6e jikinta da hijabi, tun bayan sallar asubahi bata farka daga bacci ba.

Shigowa Dakin Aneelerh tayi, hannunta ru?e dana baby junaid, sakin hannunta yai da gudu ya tunkari zahra Ya faWa jikinta yana fadin"aunty zahra Ina tsarabar da kika ce zakiyi min jiya! Shine ma baki tada ni daga bacci ba"

Janyo shi Aneelerh tayi tana fadin"meye haka? Ba ka ga bacci take yi ba"? Zahra dake sauraronsu tayi shiru batare da ta motsa ba ashe idonta biyu.

Da shagwa6a baby junaid yace"mommy ay itane tace zata min tsaraba, Ni ta tashi ta bani abuna kamin taci gaba da baccin..." bai kare maganar ba, ta rufe bakinsa da tafin hannunta.

"Yi shiru kada ta farka, mu tafi zuwa anjima sai mu dawo" ma?e mata kafaWa yayi"nidai ba inda zani Allah, sai ta bani abuna" kwace hannunsa yai daga na Aneelerh Ya fada kan zahra yana kiciniyar tada ta daga bacci, duk yadda taso tayi pretending sai da takasa tana faman fitar da numfashi mai Wan huci ta sanya hannu ta janye junaid kafin ta mike zaune ta tu6e hijab din jikinta ta jefar da shi gefe Waya

Har saida gaban aneerlah Ya fadi ganin jirwayen hawaye akan fuskar zahra, idanunta sun kumbura suntum da su, da alama tasha kuka har ta gaji.

Waro idanu waje baby junaid Yayi "mommy mun shiga uku, aunty zahra kuka tayi wani ya buge ta . " bai kare maganar ba, zahra tai saurin sanya hannu ta dan buge bakinsa"kada na kuskura nasake ji kayi magana," ta6e mata baki yai alamar zai yi kuka da sauri ta janyoshi tare da manna shi kan kirjinta, wani sabon kukan ne ta kuma fashewa da shi.

Hankalin Aneelerh ba karamin tashi yayi ba, tuni yanayin fuskarta Ya canza, matsawo tayi kusa da zahra ta zauna, cikin sanyin murya tace"ni dama tun jiya da kika dawo gida hankalina bai kwanta da yanayin ki ba, saboda na lura da yadda kike kokarin danne damuwarki saboda kada mu gane! Meyasa zahra eyeh? Adan tsawace ta fada tana dubanta
"Ki fadamin me ya faru dake


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login