Showing 204001 words to 207000 words out of 298130 words

Chapter 69 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

mata, tuni murnar da take yi ta koma ciki.

"Sister kinyi shiru baki ce komai ba? Meke damunki"? Cike da tashin hankali batool tayi maganar, su Parveen duk sun kura mata ido suna kallonta, jemimah tace"le6enki ma ya kumbura kamar yankan tumatur"

"Unaisah! Lafiyarki kuwa"? Acewar ummi ta faWa tana kare mata kallon ?urulla

Adabarbace ta furta"am.. Umm.." sam ta kasa ?arasa maganar, idanunta azazzare take kallon su.

gani take kamar sun san komai daya faru da ita adaren jiya, da sauri ta mi?e jikinta na kerma tace" aunty ummi babu komai, ba abunda ke damuna, lafiyana lou..." bata ?are maganar ba, kamar mara gaskiya ta nufi hanyar fita daga dining room din zuciyarta cike fal da tashin hankali
Gaba daya sun lura da tashin hankalin dake akan fuskarta
Deeja na dariya tace"wallahi Allah kumatunta sun kumbura suntum kamar alkubus, wama ya sani ko bugun tsiya akai mata..." bata kare maganar ba, Haris ya toshe bakin ta..
Mi?ewa ummi tayi sam hankalin ta bai kwanta da yanayin unaisah ba, mi?ewa batool tayi da niyar tabi bayansu, da sauri ummi ta dakatar da ita"ki zauna ku karasa cin abincin, zanji da ita" jiki asanyaye ta amsa mata da toh..
Da sauri ummi ta nufi dakin su Unaisah, tana shiga tajiyo sautin kakarin amanta a toilet kamar zata fasa makoshin ta.

Knocking ?ofar toilet din tay"unaisah ina son magana dake"

Fitowa tayi fuskarta sharkaf da hawaye, hannun ta ruke da Wan pant din ta.

"Meke damunki ne"? tana faman jan numfashi tace"bakomai aunty ummi..." katse ta ummi tayi"kada kiyi min karya, yana??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????yinki ya riga ya nuna baki da koshin lafiya, kawai ki fadamin meke damunki! Idan ba haka ba hankalina ba zai kwanta ba..." cikin nuna damuwa tayi maganar, shiru tayi jim tana tunanin ko dai ta fada mata watakil ta taimaka mata....

Mi?a mata pant din hannunta tayi, waro ido ummi tayi"me zanyi da shi" matse shi tayi, tana faman no?e kai tace"jiya da tsakar dare na tashi da matsanancin ciwon mara, kamar bazan rayu ba, bayan na shigo toilet na duba sai naga jini ne ya dawo min"

cike da jin tausayinta ummi ta ruko hannunta suka zauna gefen gadon.

"Sannu unaisah, wallahi daga gani kin ji jiki ba kaWan ba, meyasa a daren baki neme ni ba? Ay da na taimaka maki, halan ko magani baki sha ba"?

"Ban shaba ba aunty ummi, saboda naji saukin ciwon, kuma lokacin dana farka da safe banga jinin ba ya dauke! Aunty ummi dama Yana haka"? Waga mata kai ummi tay alamar eh"kada hakan ya dameki, nima sometimes yana yi min haka yaje ya dawo, in har bai wuce kwanaki goma shabiyar ba, to still jinin ne, amma da zarar kinji ya dauke duf babu shi sai kiyi wankan tsarki ki cigaba da sallah" ajiyar zuciya unaisah ta sauke, sam tagaza fada mata abun da ya faru jiya.

"Me kike son nuna min a jikin pant din . " cike da jin kunyarta tace"wani abune da nake gani kamar kunu gayanan kyankyamin shi nake ji .."

kiris Ya rage ummi ta fashe da dariya ganin yadda ta kwa6e fuska tana gwale la66anta.

"Nuna min in gani .." buWe mata pant din tayi.

Shiru ummi tayi jim alamar tana nazartar abunda ta gani, tabbas sperm ne amma meya kawo shi? Cos Bata tunanin unaisah ta fara feelings...rayawa tayi aranta watakil ba abun da take tunani ba ne

"Unaisah, dole fa sai kinyi takatsantsan, kamar yadda nayi maki bayani zan ?ara jan kunnanki, daga yanzu kada ki kuskura ki ?ara ba wani namiji damar da zai ta6a jikin ki, ko da ru?e hannunki ne! In ba haka ba ke zakija ma kanki zunubi, saboda duk wasu hukunce hukunce na musulunci sun hauki, Idan kika aikata mai kyau za'a rubutaki, haka zalika idan kika aikata zunubi za'a rubuta maki. .."nan dai tayi mata takaitaccen bayanin dalilin dake kawo hakan dallah dallah yadda tasan zata fahimta, hankalin unaisah ba karamin tashi yayi ba.

"Kuma idan kika bari Namiji yana wasa dake yana tattabaki, you can get pregnant, a yadda kike ?aramar nan har ranki zaki iya rasa wa...." ummi bata kare maganar ba Unaisah ta daura hannayenta biyu akai la66anta na kerma ta furta inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un...." da biyu ummi ta fadi hakan saboda taja mata kunne.
Tayi mamakin ganin Yadda jikinta ke kerma, da gudu ta fada toilet taja kofa ta datse.. " lamarin ya daurewa ummi kai, arude ta mike tana kwala mata kira"unaisah! Unaisah? Lafiyarki kuwa? Meya faru? ko dai maganar dana fada ce? To meye na damuwa"? Shiru bata amsa ba, bugun kofar ummi ta dinga yi kamar zata balle ta"ki bude min kofa, keda baki jira kin karasa jin me zance ba, meye na tada hankali kamar baki da gaskiya"? Ta faWa tana kumshe dariya a bakinta saboda ta bata dariya.

"Unaisah, ki fito muyi magana, watakil baki fahimci me nake nufi ba, zan yi maki bayani..." cikin disasshiyar murya ta furta"aunty ummi ki tafi dan Allah, cikina ne Ya katsa, idan na gama zan same ki a daki muyi magana" ajiyar zuciya ta sauke"shikenan zan jiraki"

Sai da taji alamun ummi ta fita daga dakin, kafin ta fito fuskarta sharkaf da hawaye baiwar Allah, hankalinta yayi matu?ar tashi, ta raza da jin kalaman ummi, fargabanta kada ta samu ciki!

Wani irin ciwon kaine Ya farmata, ga wani bacci da ta fara ji mai hade da kasala, Pant din da ta bari kan floor ta Wauko ta koma toilet din,

Wankan tsarki tayi tare da alwala, daga bisani ta fito sanye da towel, da wata irin kasala ta dauko wasu kayan tasa tare da hijab ta zura a jikin ta.


Bayan ta kammala sallah ta zauna kan darduma ta Waga hannayenta tana addu'a hawaye na sintiri kan kuncinta, ko da ta gama bata motsa daga kan dardumar ba.

Bakomai ne Ya faWo mata aranta ba face Danish, ko ya ci abin ci? taga bata ganshi a dining ba, har cikin ranta ta damu da shi, bata son yana ke6e kan shi a Waki, batasan meke damunshi ba...

"Sister dina!" muryar batool ce ta katse zancen zucinta, da sauri ta mike tare da juyawa ta kalle ta.., sam babu walwala atare da ita, duk ta damu da yar uwartata

"Dan Allah ki fadamin meke damunki" ?a?aro murmushi tayi akan fuskarta

"Calm down your mind! Ni Ba abunda ke damuna, lafiyana lou, ciwon ciki nayi jira da daddare naci wahala sister, amma yanzu da sauki jikin nawa..." huggin dinta Batool tayi sai taji wani sanyi ya ratsa zuciyarta.

"Ni kadai na kwana jiya adaki"

tausayinta ne Ya kara kama Batool

"Da na sani jiya na tayaki kwana, amma kodan saboda ke zan dawo kwana dakin nan"


Murmushi unaisah tayi"kada ki damu, ay naji sauki ma"
Kallon dakin Batool tayi"duk yayi datti bari na taimaka maki"
"Nagode sister," ta fada tare da zama kan mirror chair tana jiran batool ta kammala gyaran.

"Sister an kaiwa danish abinci a dakin sa"?

"Eh, Haris Ya kai ma shi, ni bansan meke damun shi ba, kema kin lura da yanayin shi na?in shiga cikin mu"? Ta faWa a yayin da takai hannu tajanyo zanin gadon da yayi uban squeezing kamar an ?watoshi daga bakin kura.

"Batool na lura, abun yana damu na, nayi masa faWa ya?i dainawa to ya zanyi da shi? ta faWa da damuwa akan fuskarta"ko da yake halinsa ne ko a prison bai fiye shiga cikin mu ba, yafi son yaganshi kwance kan gado" daurewa kawai takeyi sam bata son batool ta fahimci halin da take a ciki.

Adai dai lokacin Batool ta fara kakka6e zanin gadon, Kwatsam ba zato ba tsammani unaisah ta hango zoben da ya faWo ta cikin bedsheet din..saukowa tayi daga kan kujerar, ta nufi inda Yake ta zu?unna tana kallon shi, zoben azurfa ne sai kyalli yake a hankali tasa yatsanta daya ta Wago da zoben, hankalin batool kwata kwata baya akanta, sai surutu takeyi mata....
?ura ido tayi sosai akan zoben, was wasi ta fara yi kamar wanda prime minister ya ba danishW'
Anya kuwa shi ne?S' kokwanto ta shiga yi, tayaya akai zoben ya shigo dakin su idan na shi ne ...? yunkurawa tayi a sukwane ta mike, batare da sanin batool ba, ta fuce daga dakin.

"Sister jiya kafin mu kwanta aunty ummi ta kunna min kallo a laptop din ta...." dakatawa tayi da yin maganar ganin babu kowa adakin.

"Unaisah! Unaisah! "ranta ne Ya bata kodai ta shiga toilet, hakan yasa taci gaba da gyara mata dakin......."

________________________________
'?

Prisoners shield=ؔ?

Fitowa yai daga toilet, jikinshi a sanye da bathrobe, baijima da tashi daga bacci ba Ya shiga wanka, yayi wani fresh dashi, sumar kanshi ta lullu6e bayan shi.

Walking slowly Ya nufi dressing mirror, zuciyarshi cike fal da tunanin Angel dinsa, yayi maraicin ganin ta idanunsa sun kwaWaita da son ganin ta, tun safe baici komai ba, abincin da haris ya kawo mashi yana nan ajiye kan table ko buWesa baiyi ba.

Har ya yunkura zai zauna kan mirror chair, sautin knocking din kofar Ya dakatar da shi . ....

Cike da zumudi Ya nufi kofar, fatan shi Allah Yasa Angel dinsa ce,
BuWe ?ofar yayi a hankali, tun daga kasa Ya fara kallon ta, ko takalma babu a kafarta kamar an korota,
Gown din jikinta tayi mashi kyau sauke idanunsa yayi akan fuskarta har saida gaban shi Ya faWi, ganin yadda ta kumbura gashi babu fara'a ko kaWan ta haWe rai, ido cikin ido suke kallon juna har na tsawon mintuna biyar kafin sanyayyar muryarshi ta katse mata shirun ta

"Mu shiga ciki" yayi mamakin ganin batayi mashi musu ba, ta nufi ciki da sauri yabi bayanta, a tsakiyar dakin suka dakata


"Meke damunki? Idanunki sun kumbura kamar kinyi kuka, faWamin waya ta6a min ke"

Lumshe idanunta tayi kafin ta buWe su a hankali.

Takawa tayi har zuwa gabanshi ta tsaya suka fuskanci juna

"My man, Ina zoben da prime minister Ya baka"? Cike da fargaba Ta furta maganar ita kanta tsoron amsar da zai bata take ji saboda bata son zargin da take yi ya tabbata.

da sauri Danish Ya Wago da yatsun hannun shi Ya kallesu kwata kwata babu zobe

aruWe ya furta"ban gan shi ba, bansan a ina ya faWi ba, bari na duba toilet watakil na manta shi a ciki"

Juyawa yayi da sauri ya nufi toilet ya shige ciki.

tana atsaye cikin jin kunar rai, take kallon shi har ya 6ace ma ganinta, wani irin kululun bakin ciki ne Ya tokare makoshinta, hankalin ta yayi mugun tashi, zuciyarta ta karaya jikinta yayi sanyi, ta gaza yarda da abunda take zargi!!

dagaske danish ne ya aikata mata rashin imanin nan? babu tausayi babu imani Yana ganin tana fama da azabar radadin ciwo ahaka Yayi abun da yakeso yayi? Tunawa tayi da lokacin daya wurgar da ita kan gado, Ya sa hannu Ya hambareta har kanta Ya daki pillow, abun ya tsaya mata aranta.


Fitowa yayi daga toilet din, ya Wago suka hada ido, wani irin faduwa gaban shi yayi ganin kallon tuhuman da take jefa mashi, tuni yasha jinin jikin shi

"My man, kaga zoben"? La66anta na kerma ta furta maganar
Girgiza mata kai yayi"ban gan shi ba, bansan a ina Ya faWi ba..."

Murmushin takaici ta sakar mashi, kafin tace"Ni na ganshi"! da mamaki Ya kalle ta, hannu ta zura cikin aljihun gown din, ta zaro zoben ta mi?a mashi

"A ina kika gan shi"? ya faWa tare da matsowa kusa da ita, ya mi?a hannu zai karba, daddagewa tayi da iya karfinta na karshe ta ware yatsu biyar ta wanka mashi zazzafan mari kan kun cin shi, tashin hankalin da ba asaka mashi rana! lamarin ya gigita shi da sauri ya dafe kun shi, jikinsa na 6ari ya Wago amatu?ar ruWe ya kalli fuskarta...la66ansa na kerma ya furta"my.. Angel? Kina cikin hayyacin ki kuwa? Ni kika mara"?

Harara ta watsa mashi da kakkausar murya ta furta"idan akwai abun da yafi mari zanyi maka shi! Mugu Azzalumi, fasiki Wan iska... " waro idanunshi waje yayi tamkar kwayar zata fado ?asa He was completely confused

"Danish me nayi maka dana cancanci haka daga gareka? Danish kaida kanka? Sai yanzu na gane dalilin dayasa ka tsareni jiya akan in faWa maka idan na fara period, dama abunda kake jira kenan, Ina fata yanzu hankalin ka Ya kwanta, tunda ka samu abunda kakeso ...." rushewa tayi da matsanancin kuka mai cin rai, bawan Allah Yama rasa bakin magana, har yanzu baisan kan me take magana ba, ko kaWan baiji zafin marin da tayi mashi na, babban tashin hankalin shi miya faru da ita a daren jiyaS'

"Kiyi min bayanin meya faru dake"? Tsawa ta daka mashi kamar zata rufe shi da bugu tace"kana nufin kamanta abunda kayi min? Saboda ba damuwarka bace in rayu ko in mutu ko"? Ta fada tana cije la66anta da hawaye suka ji?a su.

"Idan ka manta bari na tuna maka, jiya ka shiga dakinmu da daddare...." zayyana mashi komai tayi tunkafin ta karasa gabansa yayi wani irin mugun bugu na tashin hankali, mi?a mashi zoben tayi"a jikin zanin gadonmu na tsince shi, ina fata yanzu ka tuna komai....."

Runtse idanunshi yayi, wani irin ?unci yaji aran shi, jikin shi ya hau yin kakarwa kamar wanda Sanyi ya kama . shirun da yayi ne ya ?ara tabbatar mata da zarginta akanshi.....amsar shi kawai take jira.. Duk da bata bukatar wannan

"Bani bane! Bazan Iya cutar dake ba Angel! bansan ya akai zobe na Yaje dakin ku ba..."

wasu zafafan hawayene suka wanke fuskarshi, wlh yafi ta jin radadin abunda akai mata, yaji zafi kamar ya fasa ihu! Wai Angel dinsa ce wani yayi ma wannan aika aikar?

"Danish baka ta6a min karya ba sai yau, baka da wata hujja da zaka kare kanka awurina, zoben ka ba ?afa gare shi ba, balle kace shi yakai kan shi dakina...Danish meyasa kayi min haka? Ko amafarki ban ta6a tunanin zakai min haka ba? A zato na kai garkuwane agareni mai bani kariya a duk lokacin da wani yayi yunkurin cutar dani sai gashi kai da kanka ka cutar dani, saboda idonka Ya makance burinka kawai ka samu abunda kake so ko"?

Dafe kanshi yayi da hannu Waya saboda wani irin sara masa da yai, ?afafunsa sungaza daukarsa baisan sa'adda Ya zube kan gwiwowinsa ba.

Ya rurru?e ?afafunta da hannayen shi, hawaye na fita ya furta"Unaish ki yarda dani! Ban ta6a maki karya ba, bani bane! Bansan wanene yayi maki aika aikar nan ba! Garkuwarki bazai ta6a cutar dake ba, ni aikina shine baki kariya kamar yadda kika faWa" ya faWa yana fitar da huci mai zafin gaske

"ki tausayama rayuwata, kada ki yanke min hukunci akan laifin da bani na aikata ba! nayi maki alkawarin zan gano koma wanene yayi miki hakan ..." cikin rauni na murya ya ?are maganar, yana kallon cikin idanunta.

cike da jin tsanar shi ta sa kafa ta buge hannayenshi daya ruke kafarta da su, ta soma ja da baya tana fadin"wallahi bana son ganinka! Ka fita araina Danish! Na tsaneka! Ka 6ata komai, kullum burina in faranta maka rai ashe kai ba haka bane awurinka, abin da baka sani ba ni nema nake na nema mana hanyar da zamu mallaki juna na har iya tsawon rayuwarmu, sai dai kash gajen hakurin ka da son zuciyarka sun ja makaW'

wurga mashi zoben tayi kan kirjin shi, da gudu ta juya ta fuce daga dakin.

Jiki amace ya kwanta kan floor, hawaye suka cigaba da sintiri kan kuncinshi, ga wani azababben ciwon kai da yake ji, tuni zazza6i Ya lullu6e jikin shi, Waukar zoben yayi a hannunshi Ya kura mashi ido yana kallon shi, ya rasa ya akai zoben yaje dakin su?wa ya kai shi? Wanene Ya cutar mashi da Angel dinsa?

sambatu ya fara yi"bani bane! Bazan iya cutar dake ba! Ni garkuwa ne agareki mai baki kariya, kada ki juya min baya, bana jin zan iya rayuwa batare dake ba, Angel kada ki fushi dani bani baneW'W'W'


Gaba Waya kalamansa acikin kunnanta, tana a durkushe bakin kofar dakinsa tana kuka kamar ranta zai fita, ganin lamarin take kamar a mafarki! wai Danish dinta ne yayi mata haka? Wlh ya karya mata zuciya! Ya kunsa mata kiyayyarshi, duk irin burin da taci na son ganin sun rayu a karkashin inuwa Waya ya ruguza komai....

Jin motsin mutun yasa tayi saurin share hawayen ta, jiki ba kwari ta mi?e daddynta ta hango yana shigowa, da alama Ita Yake nema...
Sai da ta fara daidaita nutsuwarta kafin ta sauko down ta nufe shi, sam baiji takun tafiyarta ba, sai dai Yaji ta faWa kan bayan shi ta rungumeshi, bata san sa'adda ta sake fashewa da wani kukan ba, duk yadda taso ta shanye shi takasa har saida Taj yaji, gaba daya yabi ya rikice, kafin yayi yunkurin ruko ta da gudu tabar jikin shi, ta nufi dakinsu ta shiga, a lokacin Batool ta jima da fita, kan gado ta haye ta kifa kanta jikin pillow ta cigaba da kuka kamar ranta zai fita.

da gudu Taj Ya faWo dakin, Ya hau har saman gadon, jikin shi har kerma yakeyi tsabar rudu da tashin hankali, janyota yayi da karfi ya rungumeta sosai a kirjin shi, muryar shi na rawa ya furta

"Unaisah! my Angel! Meya faru? Waya ta6a mun ke? baki da lafiya ne?

fuskarta tayi sharkaf da hawaye, hatta temperature din jikinta ya dauki zafi rau.


"My Angel meke damunki? Dan Allah kiyi min bayani? Ko baki da lafiyane?" sai da tayi kukan mai isarta kafin ta raba jikinta daga nashi ta sauko daga kan gadon, ta nufi toilet ta shige, jim kaWan ta fito da alamun ruwa akan fuskarta...tsayawa tayi nesa da shi tana faman sauke ajiyar zuciya.


"Zonan Unaisah" Ya kirata fuskarshi babu walwala, kamar babu laka a jikin ta ta karasa tare da zukunnawa ta zauna kasan gadon, saukowa yayi ya zauna suka fuskanci juna
Ya ruko hannayenta a cikin nashi"fada min meke damunki? Meyasa kike kuka?

Shiru tayi jimm har cikin ranta bata jin zata iya tona mashi asiri, koda zuciyarta zata buga saboda bakin cikinsa, ta ?wammace tabar abun aranta.

"daddy dan Allah kada ka tambayeni meke damuna, ka tayani da addu'a, in sha Allah zanji sau?i.."

ta faWa tare kwantar da kanta saman kafadarshi, Waura hannun shi yayi akan bayanta yana dan shafa shi cikin sigar lallashi yace"kiyi hakuri duk da bansan meke damunki ba, tun da kin nuna bakison in tambayeki dole in hakura, amma dan Allah kada ki sanya damuwa aranki!


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login