Showing 288001 words to 291000 words out of 298130 words

Chapter 97 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

kuka ba, ba zai yi maku maganin komai ba saima ya kara jaza maku wani ciwon, ku tayashi da addu'a in sha Allah zai dawo ko dan saboda ku..." sun yi shiru suna sauraron shi.

"Allah Ya kare mana shi aduk inda yake, Allah Ya karkato mana da tunanin shi ya dawo gida .." cikin sanyin murya suka amsa mashi da Ameen

Mi?ewa Parveen Tayi boss yace"ina zuwa"?

hannunta dafe da cikinta tace"fitsari ne Ya matse ni" ta fada tare da kama hanyar ta nufi dakin su,

"Nima fitsarin nake ji, tun Wazu ya matse ni" murya na rawa jamimah tayi maganar tare da mikewa daga kan sofa ta watsa da gudu ta nufi dakin su.

"Time din sallah azhar har ya wuce, Ku tashi ku tafi Waki, ku yi wanka ku yi sallah kafin ku fito zanyi magana a shirya maku lunch din ku nasan kuna jin yunwa" cikin kulawa ya faWa yana duban su.

Bata jin zata iya cin abinci in har Danish bai dawo ba, cike da rashin kuzari ta mi?e idanun ta akan daddynta dake kallon ta bakomai ne ke daure mashi kai da ita ba face haukan da tayi Wazu ya rasa gane meke a tsakaninta da Danish!.

Ta Wan tsargu da kallon da yake yi mata, in a weak voice tace"Zan shiga daki, bansan ko zan dawo na iske ka ba, ka gaida min aunty Danejo" bata tsaya taji amsar shi ba, ta juya ta nufi dakin su tana tafiya a harharWe kamar zata kife ?asa har sai da ta shige dakin tukunna ya Wauke ido daga kallon ta.

Knocking door room dinta da akayi ne yasa tayi sauri fitowa waist Winta daure da towel, hannun ta ru?e da wani short towel da take tsane sumar kanta da shi.

Cikin kunnanta ta tsinkayi muryar Batool daga waje tana fadin

"Aunty Ummi ni ce, Mun dawo, ki buWe min ?ofa..." wani irin sanyi ne taji ya ratsa zuciyarta, taji dadin jin muryar Batool saboda a halin da take a ciki tana bukatar wanda zai kwantar mata da hankalin ta.


"Batool, ki jira ni, Ina shiryawa ne"

"Toh"

Cikin kankanin lokaci ta kammawa shiryaw cikin abaya ba?a mai kyan gaske, ta yi rolling headscarf, ta nufi door room din tana buWewa Batool tayi sauri faWawa kan kirjinta, tayi mata wata irin runguma kamar zata koma cikin ta wani irin faduwar gaba taji saboda kunnnata sun jiyo mata shesshekar kukan batool, dama tun da ta rungume ta taji aranta ba lafiya ba.

AruWe ta furta"My Babe, meya faru? Baki da lafiya ne"? Ta faWa tare da tallabo fuskar Batool da hannunta, hankalinta ya ?ara tashi da ganin yadda fuskarta ta yi jawur ta jike da ruwan hawaye

Jijjiga kafaWarta tayi"meke damunki ne? Wani abu ya faru ne? Fadamin mana waya ta6a min ke"? Ta fada akagare da son jin amsarta.

La66anta na rawa ta labarta mata abunda ya faru a head quarter dangane da batan Danish.

Hankalinta Ya tashi matu?a muryarta na rawa ta furta"inna lillahi wa inna ilaihirraji"un Amma banji dadin abun da big guy yayi mashi ba, bai kyauta ba Allah, da hankalinshi da komai sai kace baisan wanene Danish din ba..." rai a6ace tay maganar.


"Yanzu Ina su Unaisah din"?


"Duk suna adakin su, gaba Waya basa jin dadin jikin su saboda abunda ya faru, munyi kuka har mun gaji"


tsantsar tausayinsu ne Ya kamata ga damuwar bacewar Danish tana jin shi kamar kaninta saboda kaunar da takeyi ma su
Da tafukan hannayenta ta share ma batool hawayen dake sintiri kan fuskarta.

"Ki daina zubda hawayenki, bana so pls, ni nasan zai dawo ne in sha Allah, mu tayashi da addu"a" ta fadi hakanne saboda tasan bazai iya jure rashin Unaisah ba, tun shekaran jiya data ga abunda ke tsakaninsu tasan ba karamin abu ne zai iya raba su ba.


"Aunty Ummi ko sallah banyi ba.."

"Okay, ki shiga ciki ki yi, bari naje gurin yan uwan naki, nasan zasu neme ni" a hanzarce ta fuce daga dakin, sam ta manta bata gyara gadon ba, saukin ma ta bar bargon a toilet.

_________________________________
'?

*ANEELERH=ؓ?*

a Zaune take kan gadonta jikinta sanye da riga bubu, ta yi shiru tana kallon baby junaid dake zaune gefen ta hannun shi ru?e da plate din wainar fulawa wanda zahra ta soya mashi ita, sai tsantsani yake saboda dadin da tayi mashi dama ya iya kwaWayi, kadan yake balla ya Wan dangwala yaji saiya tura a cikin karamin bakin shi

Shekaran jiya izuwa yau ya ?ara samun lafiya walwalar shi ta dawo tun da yaga Angel dinsa ta cika shi da farin ciki, ko bacci yake yana ambaton sunanta, tun da suka dawo gida ya addabeta akan ta kira Angel awaya tace mata tazo yana son ganin ta, dakyar take samu ta shawo kan shi, sai dai har yanzu bakowa yake yarda ya Wauke shi ba, daga momynsa sai zahra da mami amma su abie kam ?iwuya yake yi masu abun yana daure mata kai, har mahboob bai cika yarda ya dauke shi ba.

Tayi zurfi acikin tunaninta Muryar shi ta katse ta

"Mommy, wannan sauran wainar dana rage na Angel ne, wa zai kai mata? ko ni zakisa mahboob yakaini a mota in kai mata..."ya faWa yana nuna mata rabin wainar da ya rage a plate din

Murmushi tasakar mashi"na fada maka ba Angel bace, bana so wani yaji kana kiran sunan Angel, ita yarinyar da ka gani sunan ta Azeezaty suna kama ne da Angel din mu"

yamutsa fuska yai tare da ma?e mata kafada"wallahi wayo zaki min, Angel dina ne ita ay har tambayarta nayi tace mun eh itane ko" ya faWa da shagwa6a yana hade fuska.

?ura ma juna ido sukayi batasan ya zatay da shi ba tana son ta tambaye shi meya faru amma tana jin fargaban kada akoma yar gidan jiya, zai iya birkice mata tun da ta fahimci baison maganar kwata kwata.

"Mommy kina kallona ko zaki ci wainar ne in Wan maki" ya fada yana kokarin 6allo mata da sauri ta furta"a koshe nake my baby boy, na fiso ka ci ka koshi..." farfari yayi mata da idanun shi

"Yaushe zaka koma school"?

Ma?e mata kafaWa yai"shaina ?ara samun lafiya" yar dariya tayi "junaid na ganoka gudun school kake, Allah next week zan maida ka, ay naga kaji sauki jikin ka ya murmure" yamutsa mata fuska yai tare da zumbura mata baki

"Allah in kinasho in koma ki sani makarantar su Azeezaty, sai mu runka yin wasa da ita"

ya faWa tare da 6allo wainar da ya rage ma Angel ya tura abaki yana ci, murmushi tayi tare yin kasa da muryar ta"babyna" ya amsa mata naam

Takai hannu ta shafa sumar kan shi.

"Zaka iya tuna abun da ya faru ranar da muka je gidan Hajiya adama"? Dakyar ta kare maganar ganin yadda ya ware idanun shi da karfi, Jikin shi ya fara kerma kamar mazari.

da sauri ta janya plate din wainar ta daura kan table, ta saukowa daga kan gadon ta zukunna agaban kafafuwan shi kamar mai neman gafara.

"Dan Allah junaid ka fada min, kaga ni mommynka ne, duk duniya baka da tamkar ni, idan ma kana jin tsoron ka fadi ne wasu suji nayi maka alkawarin bazan bari kowa yaji ba daga ni sai kai...."

tatta6e fuskarshi yayi ruwan hawaye suka taru acikin idanun shi labbanshi suka kama kerma taji faduwar gaba da ganin yanayin shi sai dai bata jin zata iya hakura a wannan karan, saboda tayi matukar ?agara da son jin meya faru da su aranar!.


Ruko hannun shi tayi cikin sigar lallashi da wayau da dabara ta karya murya tare da marairaice mashi fuska duk don ya tausaya mata ya fada mata, magiya ta dinga yi mashi yayi shiru yana kallonta da tsantsar tashin hankali akan fuskarshi.

can dai ta Wan bugu cikin shi da wayau tace"Ni dama na sani Ana guduwa tayi junaid, sai da nace mata kada ta tafi tabarmu amma shine ta tafi, ni bansan laifin da nayi mata...."

bata ?are maganar ba, sakamakon abinda kunnuwanta suka jiyo mata daga bakin junaid

Cikin shesshekar kuka yace"mommy bafa guduwa tayi ba, Allah dodone Ya kashe ta a cikin gidan nan, ni na ganshi da idona kuma itane tace in gudu in 6oye"

kamar an dasa mata aya ta tsaya cak tana kokarin tariyo maganar shi acikin zuciyarta lokaci Waya ta saki dariya tana fadin"haba junaid, abun naka hada zolaya, karya fa babu kyau, In ba zaka fadamin gaskiya ba ay basai ka shirga min karya ba..."

girgiza mata kai yai babu alamun wasa akan fuskarshi ya furta"wallahi mommy dagaske nake faWe maki, dodone Ya cinye ana adakinta, tana ta kuka hada jini a jikin ta..."

yadda kasan kanzon kurege haka take sauraron shi sai tikar dariya takeyi irin ya raina mata wayon nan shi kuwa ya ha?i?ance yana faWa mata iya gaskiyar shi sai ma ta maida maganar tashi abun nishadi.

"Mommy ki daina dariya, ba abun dariya bane wlh dagaske nake maki" wani kallon rainin wayau ta wurga mashi kafin tace"junaid bana hanaka yin rantsuwa akan karya ba..."

kuka ne Ya ci karfin shi wannan karan ta Wan ji faduwar gaba duk da bata yarda da maganar ba ta dauki abun shiririta arude ta ke lallashin shi cikin shesshekar kuka yace"mom.. my ba karya bane, ki daina min dariya, ni banaso dodon daya kashe ana ya kashe mu mommy, dan Allah mu gudu mubar gidan nan ni wlh tsoro nake ji..."

bata san sa'adda ta rungume shi a kirjinta ba, hankalinta yayi mugun tashi saboda kukan da junaid yake yi mata tasan halin kayanta ba karamin abune zaisa junaid yin kuka ba irin haka, tabbas wani mummunan abu ya faru da ya yi silar zaucewarshi sai dai zuciyarta taki yarda da maganar shi, gani take bame yiyuwa bane.

_______________________________
'?

A ?alla ta fi karfin mintuna a tsaye tana kallon Unaisah dake a kwance kan darduma ta nannaWe kafafunta cikin hijab, idanunta suna a rufe gam sai yan siraran hawayen da ke sintiri kan fuskarta tayi kukan tayi addu'ar amma har yanzu zuciyarta taki sarara mata daga radadin da take mata, gani take kamar ta rasa Danish.

aranta tana ji in har kurkukun ya koma tabbas zata bishi ne ko da hakan zaiyi silar rasa ranta don ji take bazata iya rayuwa batare da shi ba.

"Unaisah!" ummi ce ta kira sunan ta, tayi shiru tamkar bata ji ta ba

"Nasan kina ji na, ni bansan ya zanyi dake ba, duk irin kokarin da nayi gurin kwantar maki da hankali kinki daina kukan nan, ga abincin ki dana sa akawo maki shima kinki ci, to wai kukan da kike shi zaisa ya dawo ne? Tun da kinyi addu'ar sai kibar ma Allah komai In sha Allah zai dawo...." cikin sigar lallashi ta faWa tare da zukunnawa gaban prayer mat din

"Dan Allah ki tashi ki ci abincin ki..." da wata irin karyayyar murya ta furta"aunty Ummi, ba zaki gane ba, ni kadai nasan halin da nake a ciki, zuciyata bata min dadi ji nake kamar zan rasa raina ne, yaya Omar ya 6ata min rai, shine silar komai, wallahi Aunty ummi naji zafin kalaman daya gaya ma Danish, duk da baida ilmi ko jahili akayi ma gori sai yaji ba dadi"

jikin Ummi ba karamin sanyi yayi ba, ga wani irin tsantsar tausayin Unaisah daya kamata, tasan bai wuci hada soyayyarshi ke azabtar da ita ba.

"Kiyi hakuri Unaisah, In sha Allah Danish zai dawo, Allah shi zai tsare sa aduk inda yake, mu taya shi da addu'a ni inaji araina ko dan saboda kaunar da yake yi maki zai dawo"

dakyar ta buWe idanunta wadanda suka kada jajawur ta dubi ummi duk da halin da take a ciki tayi mamakin kalmar kaunar data furta.

fahimtar hakan yasa ummi tay saurin furta"naga kamar yafi kaunarki a cikin yan uwanki, kema haka shiyasa nace haka, kada ki Wauka ko ina sanya maku ido ne"

shiru tayi bata tanka mata ba.

"ni abun da nake tunani watakil ya ke6e kanshine awani guri don ya gusar da bacin ranshi in ba haka ba Danish ay ba za ace ya 6ace ba, mutumin da ba shi kadai bane tsaf zai iya kawo kan shi gidan nan..."

bata kare maganar ba ta dakata tana kallon Unaisah ganin yadda ta zabura ta mi?e tsaya kamar zata fadi saboda rashin kwarin jikin ta

"Ina zuwa"?

"Yanzu zan dawo aunty ummi, wani abu zan duba" tana fadan hakan tasa kai ta fuce daga dakin cike da sa ran hasashen ta zai zama gaskiya, maganar da ummi tayi ta tuna mata da wani abu daya ta6a faruwa.

________________=؋?Chief Owais=ت?

Kwance yake akan gadon shi, yar singlet da short ne ajikin shi, damuwa ta hana shi ta6uka komai, ya dade bai shiga tashin hankalin daya shiga a yau ba, wayarsa dake akan bedside drawers sai ringing ta ke yi daga kiran ya katse wani ke shigowa sautin ya cika kunnuwan shi, amma baya jin zai iya picking din su yasan bai wuci Na hannun damansa bane suke kira don suji ko an ga Danish.

Shaf ya manta da bakin da za su yi, saida tunanin Ya faWo mashi aran shi kafin ya mike ya janyo wayar shi tare da duba screen din My dad shine sunan daya gani saida ya fara daidaita nutsuwarsa kafin yai picking call din

"My Son, Ya kake Ya aiki, ka manta da daddyn ka ko"?

Duk da halin da yake aciki sai da yaji nutsuwa ta shige shi jin muryar daddynsa

lumshe idanun shi yayi cikin sanyin murya ya furta"lafiyalou daddyna, ni na isa in manta da bugun zuciyata? Mutumin da nake kwana in wuni da tunanin shi araina saboda kaunar da nake masa"

Sautin dariyar mai girma sharafuddeen ce ta ratsa kunnan shi cike da nishadi yace"My Son kasan duk wata hanya da zaka kare kanka agurina, ka faranta raina, but meke damunka ne? Naji muryarka kamar baka jin dadi..."

Shiru yayi jim dama yasan zai yi wuya in daddyn nasa bai gane wani abu ba, dayawan lokutta ta muryar shi kadai yake gane halin da yake a ciki.

"Babu komai, yanzu na tashi daga bacci ne, shiyasa kaji voice dina wani iri"

"Hmm owais kenan, har ni zaka boye ma damuwarka"?

"Daddy, ka yi hakuri zan iya kiranka anjima mu yi magana"?

"Okay, in ba baka kira ba, Ni zan kiraka, ko inzo gidan naka da kaina kasan bana wasa da lafiyarka" yar dariya chief yayi saboda yaji dadin maganar shi ba wani jimawa sukayi ba sukai sallama

layin Omar ya danna ma kira kusan sau uku tana ringin bai Waga ba sai a kira na hudu yayi picking.

Kara wayar yayi a kunnan shi"Omar, kana Ina"?

On the other hand big guy yace"na tafi neman bugun zuciyarka saboda bana so in rasa ka" shiru yayi jimm yana maimaita maganar big guy harya fahimci ranshi ya 6aci saboda yayi mashi karya, location dinshi ya nuna yana agidan kamar ko ya sani yana akwance kan gadon bai jima da tashi daga bacci ba.

"Omar zamuyi magana, nasan meke damunka, pls don't forget to get the soldiers ready and go to the airport, jirgin su commender yakusa yin landing nan da minti talatin "

"Consider it done, sir, amma ya yakamata kaima ka shirya mu tafi airport din atare, zasu fi jin dadin tarbar da zamuyi ma su"


"Just do what I say" ya umarta, bai bari big guy ya kara magana ba yayi rejecting call din don baya jin zai iya fita daga gidan a halin da yake a ciki.

*Unaisah Angel*

Bayan fitowarta daga dakinsu bata nufi ko'ina ba sai upstairs tana tafiya jiki duk ba kwari ta tura kofar Wakin ta shiga daga ciki bata ga kowa ba.


Gadon shi tabi da kallo sai ta dinga ganin kamar zata gan shi kwance yana bacci, kau da idanunta tayi ta juya ta nufi toilet dinsa.

A hankali ta daura tafukan hannayen ta, ta tura ?ofar ta buWe ta, dira ?afarta ke da wuya taci karo da abunda yayi silar razanar da ita ta daddage ta fasa kara tana ambaton sunan Allah ta dafe kanta da tafukan hannayenta, hadi da runtse idanunta jikinta ya fara kakarwa, wani irin faduwar gaba taji tamkar ana dakan sakwara a kirjin ta.

dukkan ilahirin jikinta rawa yake kamar mazari tayi matu?ar firgita da abunda idanunta suka gane mata, tayi matukar razana, yatsun hannunta na kerma ta bude kofar Wakin garin saurin ta fita cikin rashin sa'a tayi tuntu6e da ?asan hijab dinta dake ja da kasa gaba Waya ta wuntsila ta yi kundunbale ta kife ?asa hankalinta yayi mugin tashi jikinta yadau zafi rau wata irin zufar tashin hankali ce ta fara tsastsafo mata.

Tana ta kokarin mikewa donta gudu taji motsin buWe ?ofar tuni tasha jinin jikin ta, ta ?ame a durkushe ta kasa Wagowa yayin da ?wa?walwarta ke tariyo mata Halittar da tagani a cikin toilet dinsa kamar Wolf (kerkeci) jibgegen gaske.

?amshin turaren Chief ne Ya ziyar ci kofofin hancin ta, Kafin DaddaWar muryarsa ta katse zancen zucin ta

"Unaisah? Are you Okay"? Ay tana jin muryarshi ta yi wani irin yunkuri da iya karfinta na karshe ta zabura ta mi?e, gaba Waya ta faWa kan broad chest dinsa ta ?an?ame shi, cikin shesshekar murya take faWa mashi abunda ta gani a cikin toilet din tare da yi mashi nuni da yatsan ta.

Sam ya kasa fahimtar me take nufi, sai kallonta yake yadda ta kankame jikinshi ta hanashi motsawa daga gani ta tsorata ba kadan ba.

"Unaisah, what's wrong? Who's in the toilet?"

Batare data Wago ba ta furta"dodo ne a toilet din sa,"

"Okay, zanje na duba, ki jira anan" ya fada tare da ruko hannayenta a hankali ya banbare su daga kan waist dinsa.

yayi mamakin uwar zufar daya gani akan fuskarta kamar an yayyafa mata ruwa ga zafin da jikinta ya Wauka yaji shi har jikin shi da ta rungume shi sai faman jan numfashi take tafin hannunta Waya dafe da saitin zuciyarta.


"Ki kwantar da hankalin ki, Ina atare dake, ba abun zai faru..."

yawu ta haWiya tana faman zare idanunta acikin nashi ta amsa mashi da toh.

har ya Waga ?afa zai nufi toilet din Yaji ta dam?o upper arm dinsa, slowly yakai duban shi gare ta.

Girgiza mashi kai tay a tsorace tace"Don't go alone, I don't want anything to harm you"

murmushin gefen fuska ya sakar mata har cikin ranshi yaji dadin nuna damuwa da ta yi akan shi hakan ba karamin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login