Showing 96001 words to 99000 words out of 298130 words

Chapter 33 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

firgici da ruWani yasa har batasan sa'adda ta saki wayar hannunta ba, gaba Waya ta kife kan flloor, Jikinta ya kama kerma kerma tana faman zazzare eyes din ta akan fuskar shi yadda kasan twin brother din ta.

saboda ruWu tunani su ka yi ko dai Nazli ce ta koma inda danish yake atsaye hakanne yasa sukayi Saurin kai idonsu inda take atsaye don suga idan tana nan, Ganinta yasa suka ?ara rikicewa.

Security adivisor ya kasa samun nutsuwa saboda al'ajabin da ya kama shi, Muryar shi na rawa rawa yana tangyadi cikin harshen turan ci yace" dama prime minister yana da wani Wane da ba mu san da shi ba, ko kuwa ?aninsa ne? Ko dai giyar dana sha ce takai mun karo? Pls ku yi min bayani yadda zan fahimta.

Senate lateef ne ya bashi amsa da cewa"ba su haWa ala?ar komai ba, kama ce kawai" babu alamun za su gasgata maganar shi.

"Abun da Waure kai, amma ya ya akai su ke bala'in kama har haka? Kamar an yi photo copy din fuskar Hateem, ko ma ince Nazli" his exellency Deen ne yayi maganar, Yazrin sam takasa samun nutsuwa Sai kallon shi take yi ko ?yaftawa babu, wato danish ya girgiza su da kyawun shi, Hankulan su Faryat ya tashi haikam tsabar yadda su ke kallon shi kamar za su haWiye shi, yadda kasan irin kura taga naman nan.

Ha?i?a sun rudu da prisoners, babu wanda bai yi mamakin sanyin kyan su ba, da al'ajabin kamanceceniyar su da ?an uwan su yadda kasan ya'yan cikin wasu daga cikin su tsabar yadda kamannin su ya bayyana da juna...

Ganin kallon nasu ba mai ?arewa ba ne gashi sunbar yara atsaitsaye, da sauri Ziyad ya ce

"Lokaci yana tafiya, yakamata acigaba da shagali"

kafin Ya ?are maganar sautin wa?a mai ratsa zuciya ya karaWe cikin hall din, ?aya bayan Waya Suka juya suna nufar wurin zaman su kowa da abun da yake sa?awa a cikin zuciyar shi.

Hateem kamar jira yake yi a samu maslaha, jiki na rawa ya nufi danish ya ru?o hannun shi acikin nashi, burin shi su haWa ido don su kalli juna dakyau amma ya?i bashi damar hakan, murmushi ne dauke akan fuskar sharafudeen sai faman kallon su ya ke yi, yaji dadin ganin hateem a irin wannan yanayin.

Da zolaya yace irin wannan kallo haka? Ka da fa ka lashe mana yaro" ?ar dariya hateem yayi,

Chief owais da ke kallon su ba karamin kwanciyar hankali ya samu ba ganin ya faranta ran uncle din sa

"Uncle ka tafi da shi, zaman shi anan bazai yiwu ba, saboda baya son hayaniya, kuma baya son ana kallon sa, From now until nightfall, I entrust him to your care" wani irin farin ciki ne ya ?ara lullu6e prime minister, kamar wanda akayima albishir da gidan Aljanna, cikin sanyin murya yake fadin"nagode owais, wlh ka gama min komai, bazan ta6a manta alkhairin ka a gare ni ba, Allah ya faranta maka kamar yadda ka faranta min" addu'o'i ya dinga zuba mashi, bai manta da sheikh imam ba wanda ke atsaye tun dazu murmushine akan fuskar shi.

"shukran jazeelan Ya sheikh, Allah ne kadai zai iya biyan ka, saboda babu wasu kalmomi da zan iya yin amfani da su wurin yi maka godiya" ya faWa yana ru?o hannun sheikh imam gaba Waya wani irin annurin farin ciki ne akan fuskokin su.

Unaisah da ke ta sauraron su aranta Allah Allah take Danish ya amince da bu?atar chief yabi prime minister don tasan halin shi da kafiya ba kowa ke iya tankwara shi ba.

Kafin ta ?are zancen zucin nata ba, da mamaki taga danish yabi prime minister hannun su ru?e cikin na juna suka nufi hanyar fita daga hall din ko irin ya waigo ya kalle su baiyi ba, ajiyar zuciya ta sauke, sarai ta fahimci masu satar kallon ta.

gimbiya mujeedat sai bin su da kallo take yi, tarasa ma wani irin tunani zatayi game da bawon Allan nan mai tsantsar kama da Nazli, kasa jurewa tayi da sauri ta bi bayan su, ita ma Yazrin ta bi su, Nazli ce kaWai ba tayi yunkurin bin su ba, kwata kwata babu annuri akan fuskarta, Ita bakomai ne damuwarta ba face abu biyu, na farko yaron da ke kama da ita! arayuwarta ta tsani ace wani yana kama da ita, saboda izzarta, tafi so mai nata ya kasance ita kadai ke da shi, bayan wannan sai Unaisah! Hankalin ta bai kwanta da ita ba, saboda wani kallo da taga sun jefa wa juna a tsakanin ta da chief owais nan take taji bata son ganin yarinyar, Nazli tana da zafin kishi, izzarta ce ke hanata bayyanawa.

Fuskarta babu annuri ta kai hannu ta dauki wayarta dake kan floor, da wani irin takun qasaita ta juya tabar wurin su.

Mom turai da ke ta kallon su tun Wazu take son tunkararsu ganin babu dama ne yasa ta yi shiru tana kallon bada?alar da ake yi, yanzu kuwa da ta samu dama, Da sauri ta nufi wurin Azeeza saboda sun bata tausayi da suna kuka, hanky ta zaro daga purse dinta, ta zu?unna agaban ta tare da sanya shi kan fuskarta ta shiga share mata hawaye

Cikin kulawa tace "Stop crying kin ji ko? everything is over now, we are welcoming you to our family" wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyoyinsu har sun fara Wan sakin jikin su.

A hankali Sir mubarak Ya nufi Jemimah dake a ma?ale da Angel ta cukuikuiye mata rigarta zukunna yayi agabanta, ya ru?o hannayenta a cikin nashi yana rarrashinta ganin har yanzu tana shesshekar kuka.

"Sorry baby girl, share hawayen ki...."

muryarta na rawa ta furta"wlh baku son mu, shiyasa ku ke korar mu, ni dai gida zan koma Allah" a fadace ta faWa tana faman zabga masu harara, ?an kumatunta sunyi jawur da su.

Ba zato ba tsammani Taji Sir mubarak Ya dauketa dungurum Ya daurata kan kirjin shi, wu?i wu?i tayi da idanunta.

"Sai mu ga da wasu kafafun zaki koma gida, ay tun da ki ka shigo wurin nan sai mun ci abinci dake, idan kuma mutun yace zaiyi min rigima zan sanya bindiga ne in har be mashi tsakiyar kan shi"

Ya fada Yana daura yatsan shi akanta, Murmushi kowan nan su ya dan saki.

"Bismillah ku shiga daga ciki mu zauna, ko baku gaji da tsayuwa bane"

Zaki ne yayi maganar Yana nuna masu cikin hall din, su kansu so suke su zauna kafafuwansu har sun fara ru?ewa kawai suna fargaban shiga ne.

Ganin hakan yasa zaki matsawa ya ru?o hannun Sajeed Dana Naufal Ya shiga da su cikin hall din, Da sauri Dr Jazz Ya matsa Cikin su ya ru?o hannun javed dana haris yayi ciki da su.

Bayan mom turai ta gama sharewa azeeza hawayenta, ru?o hannun ta tayi suka nufi table din su.

babu wanda yayi tsammanin Hajiya malikat zata tanka, don tunda aka fara rikicin bata sanya baki ba, sai yanzu data matso kusa da su ta Wan saki fuskarta tana fadin"naga kowa dan uwansa yake dauka nima bari na dauki nawa" ta fada tare da ru?o hannun Unaisah, ta haWa dana batool dake a gefenta"mu shiga ciki ?an mata," wani irin farin ciki ne ya lullu6e su, da sauri suka bi bayan ta, chief owais dake atsaye ya goya hannayensa kan kirjinsa sai kallon su ya ke yi, hankalin ya kwanta babu sauran damuwa.

"Toh, ni ma dai bari na dauki nawa ?an matan" hajiya madina ce tayi maganar da fara'a akan fuskarta ta ruko hannun Parveen da na hannah, ta nufi wurin zaman su da su, gaba daya sun koma ciki, hatta su Hajiya saratu kowa Ya koma mazaunin su wasu suna daga tsaye har yanzu hankalin wasun su bai kwanta da yaran ba, Abunne ya daure masu kai sun gaza samun sukuni a fakaice su ke satar kallon su.

Tuni Daddy sharafudden yayiwa sheikh Imam mazauni a wurin su, umarni aka bawa servers din dake awurin akan su kawo masu abin da zasu ci, nan fa suka fara aikin jera masu abinci kala kala da abin sha sha?e da table...

Wata irin nauyayyar zuciya jemimah take ta faman saukewa, mom turai da sir mubarak sun tasa su agaba sai faman tarairayarsu su ke yi, kamar ?a'?an cikin su.

"Me ku ke son ci"? Cikin kulawa tayi masu maganar.

Jemimah ce tai kokarin bude baki tace"komai ma muna ci" murmushi mom turai tayi, ba karamin burgeta su ke yi ba,

"Ko kin lura yaran nan suna kama da ke? Kamar ?annan Jazz saboda sunyi kama da shi kan shi" murmushi tayi tana kallon Sir mubarak da yayi maganar.

"Nima nayi mamakin kamannin mu" ta fada idanunta akan fuskar Jemimah da azeeza, wadan da tuni suka fara cin abincin da aka kawo masu.

6angaren Su Hajiya saratu kuwa, sun kasa sun tsare sai jifar Parvin take yi da wani kallo mai wuyar fassaruwa, dama su biyune hajiya madina takai su tebur din su, ita da hannah wadda jikin ta keta kerma
"Baki da lafiya ne"? Hajiya laurane ta jefa mata tambayar fuskarta a yamutse, girgiza kai Hanna tayi, ta6e baki tayi"to meye kike ta kermar jiki! Tun da kun riga da kun samu wurin zama, ay sai ku saki jiki kuma ku kwashi arziki" ta fada tana hura hanci.

"Please ni ban kawo su nan da agaya masu magana ba!" Hajiya madina ce ta fada tana mai nuna 6acin aranta, kafin ta mayar da dubanta ga su parveen

"Ku ci abinci mana" da sakin fuska tayi masu magana, parvenn kamar jira takeyi aikuwa ta dauki glass of juice ta fara sha, tana shanyewa ta soma cin fruit salat, bayan ta gama ta koma tana cin spring rolls, Wan zaro idanu hajiya saratu tayi tana kallon ikon Allah, yadda kasan irin kwancen yunwar nan,
Hajiya laurat tace"ba banza ba naga tayi kama dake ashe itama din acici ce" ta fada da zolaya tana yar dariya, parveen dai ko kallo basu ishe ta ba, ta dage damtse komai ci take, har kwara hannah a hankali take dan cakura tana ci
"Wai ni ka Wai ce nake mamakin kamannin yaran nan da family din nan"? Hajiya madina ce tayi maganar,
Hajiya saratu tace"hmmm, ay ni abun ya gama Waure min kai, har yanzu zuciyata ta gaza samun nutsuwa, na ruWe musamman dana ga yaron nan mai kama da hateem" lumshe ido Hajiya laurat tayi tunawa da surar shi don ba karamin tafiya yayi da imaninta ba.

Hajiya muhibbat tace"na girgiza da ganin shi, lokacin da mujeeda ta cire masa mask din fuskarshi araina sai da nace wannan kyau haka kamar Wan sarkin aljanu? Dariya su kayi gaba dayan su

"Ay tun da nayi mashi kallo Waya na kau da ido, saboda wannan kyan nashi kadai ya isa yasa mace fadawa ga halaka" acewar Hajiya laurat

"Ina kananun Yaran nan ?an mata masu kama da tagwaye, wlh yadda kukasan Hajja turai tayi kakin su, ?aramar fuskarta da komai kalar nasu ne, sai kuma wani mai kama da hajjaty kamar anyi photo copy din fuskarta acewar Hajiya mudeena.

"Nima na lura da su, amma fa ni duk ba wannan ba, Yarinyar nan ta burge ni, kwarin gwiwarta ya tafi da imani na....".hajiya muhibbat ce ta yi maganar tana kallon can cikin hall din inda su unaisah su ke

Duk wannan suratan da su ke yi, akan kunnan su Parveen sai dai sam basa ganewa hankalin ta na kan abinci ci, hajiya saratu sai faman satar kallon ta ta ke yi afakaice, tun parven bata lura ba har dai ta gano ta, da zarar ta Wago suke haWa ido da juna.

_________________________=؞?

Gyaran murya Zaki yayi masu, a tare su ka dago suna kallon shi,

"Kunyi shiru baku faWa mana sunayen ku ba"

Murmushi sajeed ya Wanyi

"Ni sunana sajeed, shi kuma Wan uwana Sunansa Naufal"

"Masha Allah, It's a pleasure to meet you both, I hope you will feel at ease with us, sannan ku dauka tamkar ?an uwan ku ne mu" jinjina mashi kai su ka yi alamar eh.

"Okey, Yanzu ina so ku bani mamaki, ku cinye wannan abincin da nasa aka kawo maku" dariya su ka yi gaba Wayan su, har cikin ransu sunji dadin tarbar da zaki yayi masu.

Nan fa suka saki jiki suka soma cin abinci.

?agowa zaki yayi tare da kallon Su captain, yayi mamakin ganin yadda suke dogon wuya suna le?en table din su unaisah.

Da zolaya yace"kun dai ji kunya wlh, ina ajin naku yake"?

dariya ziyad yayi yana fadin"wlh yarinyar ce ta tafi da imanina, ni ka gane bawai sonta nake ba, wannan ay tafi karfin Wan jarida, kawai dai kamar nasan fuskarta, sai dai narasa gane a ina nasanta, abun ya shige min akaina...."

Da?yar captain Yaseer Ya janye idonsa daga kan fuskar Unaisah.

"Nifa ina ji zan canza she?a ne, wlh ko da dukiyata zata ?are ne akan neman waccan yarinyar saina jaraba sa'ata..." justice na murmushi yace"karka soma wlh, domin kuwa iskace zata wahalar da mai karan kara, ay ni tun daga kan kallon dana ga chief yanayi mata raina ya bani cewar da akwai wata a?asa"

Kwa6e fuska captain yayi"kana nufin yana sonta"? Dage mashi gira Justice yai.

Yatsina fuska yayi"again, bayan ya kwace nazli, ga kuma wata, mata biyu kenan zai aura!"

"Ni duk ba wannan ba ma, ganin yaron nan mai suffar lu'u lu'u yaWan girgiza ni, wai ku bakuyi mamaki ba? Ziyad ne ya fada.

"Ay mamakinne yasa ka ji munyi shiru da zancen shi, domin kuwa kwakwalwa zata iya daina aiki" dariya su ka yi jin abun da Justice yake fadi.

"Gaskiya nayi mamaki ace wai yaron nan a daji aka tsince shi, ay hankalima bazai dauka ba, kai daga ganin zubin halittarsa Wan wani ne, shiyasa nifa gaba Waya na ruWe da lamarinsu, kaina a duhu yake, kamanninsa sun 6aci da Uncle Hateem kamar yayi kakinsa kuma gaskiya ina kishi da shi Allah" captain ne ya fada.

Sajeed dake sauraran su murmushi ne dauke akan fuskarshi, Naufal Kuwa gaba Waya ya rasa nutsuwarsa saboda kallon da hajjaty take mashi, Da zarar Ya Wago da idanun shi karaf suke sauka acikin nata, saboda shi ta baro wurin da take ta dawo kusa da table din dake fuskantar nasu ta zauna tana ta kallon shi, ko kyaftawa babu.

Cikin muryar raWa yace da sajeed "waccan matar sai kallo na take yi kamar zata haWiye ni, ta?i bari naci abinci cikin kwanciyar hankali, bansan me na tsare mata ba, ni fa duk na tsorata" da sauri sajeed ya saci kallon inda naufal ke nuna masa ganin hajjaty yasa shi yi ma naufal rada"ka kwantar da hankalin ka, saboda kana kama da ita ne shiyasa take kallon ka" ya fada yana ?ar dariya, shi dai naufal hankalin shi ya?i kwanciya, kamar anyi mashi dole ya kalle ta.

Hakanan take jin shi a zuciyarta, komai nashi sak kalar na yaron ta, bazata ta6a mantawa da suffar shi ba, abinne ya daga hankalinta, ya kuma tada mata tsohon Ciwon dake kwance a cikin zuciyarta, bakomai take tunawa ba face yaronta da ta rasa tun farkon zuwan su nigeria wannan wani labari ne wanda sai nan gaba kaWan zamu ji shi...>?z?

Dr jazz sai Rawar kai yake yi da su Haris, kamar kannansa, Ya tasa su agaba shi da ibad sai fira suke jan su da shi.

"A cikin ku wanene Haris"? yai tambayar yana duban su, da yake yana fuskantar su, da sauri Javed Ya nuna haris," Wan zaro idanu Dr jazz yayi"masha Allah, kaine haris kenan"? Jinjina mashi kai haris yayi alamar eh, da biyu ya tambaye shi saboda yasha jin labarin shi awurin deeja, tana yawon yin sambatun sunan shi idan haukan ta ya motsa.

Ru?o hannun shi yayi a cikin nashi yana fadin"kun burgeni, ina kaunarku, ganin ku kawai da nayi kun kwanta min arai na" murmushi kowan nan su ya saki.

"Wlh nima Na kamu da kaunarsu, dan Allah ku dawo gidan mu da zama, dama ni bani da abokai a nigeria" ibad ne yayi maganar da yar shagwa6ar shi.

"Kun ?i sakin jiki damu, ko dan baku san mu bane" kallon juna haris da javed su ka yi, sufa basu saba mu'amala cikin mutane ba.


"Okey, yanzu bismillah mu fara cin abinci"

Atare suka soma cin abincinsu, jefi jefi Dr jazz yake satar kallon Haris Aranshi ya ayyana duk ranar da khadeeja ta yi tozali da shi ba karamin hauka zatayi ba.

"Yaya jazz, wadancan twins din sunyi kama da mommy da kai," ya faWa yana nuna su azeeza.

Murmushi jazz yasaki shi kanshi ya kamu da kaunsarsu, tun dazu yake ta faman satar kallon su, ji yake tamkar kannansa na jini.

"Please Ya jazz mu yi wa daddy magana, akai mana su gidan mu, ni wlh bana so suna kuka, kaga mom saratu da waccen tsigai din ko ina ruwansu da rayuwarsu, ni fa shiyasa bana son zuwa nigeria saboda su, ko gajiya da masifa basayi, ina ruwan su da ?addarar rayuwarsu? Su ne suka tsara ma kan su ne? Ni fa kaganni ya jazz ba ruwana da shiga sabgar wani ko in wulakanta sa, wai don basu da asali, sai kace an gaya masu daga sama suka fado, mutun dai ay sai an haife sa yake xuwa duniya ba daga sama aka wurgo saba, balle ace da rashin asali aka haife su," Rai a6ace ibad yakeyin maganar da zallar shagwaba.

Su haris sun saki baki suna kallon shi, komai nashi burge su ya ke yi, ganin suna kallon shi ne yasa shi dakatawa da maganar yana yar dariya yace"na cika ku da surutu ko"? Girgiza mashi


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login