Showing 201001 words to 204000 words out of 298130 words

Chapter 68 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

furta magana,

Cikin karyayyar murya Aneelerh tace"dan Allah taj kayi hakuri mu manta da abun da ya wuce, Benazir tayi nadama, neman ku take ruwa ajallo don ta nemi yafiyarku, wallahi taj ta riga ta gane kuskurenta" tana magana tana marairaice mashi fuska don ya tausaya masu"ka dubi girman Allah ka kuma duba darajar yarinyar dake atsakaninku ko dan saboda ita yakamata ka sassauta mata, Allah ma muna yi mashi laifi ya yafe mana balle mu da muke ?an adama, taj ita kanta bada son ranta ta gudu ba kamar yadda na faWa maka asiri akayi mata, yakamata kayi nazari kada ka yanke hukunci cikin fushi, nasan Benazir bata kyauta maku ba, amma ka duba pls, tana fa sonku shiga akayi tsakaninku saboda babu yadda za'ay uwa ta haifi Wan sunna tayi watsi da shi......"

babu alamun taj zai fahimci maganar ta, idanunsa sun kaWa jawur bakomai yake tunano ba face lokacin da ta Wauki cikin unaisah hauka ne kadai batayi ba saboda ta tsani ciki, har fadi take zai bata mata shape din jikin ta, bayan haka tasha yin yun?urin zubda shi Allah bai nufa ba.

"Pls, koda bazaka yafe mata ba, dan Allah ka amince Unaisah ta gana da mahaifiyarta..." kafin ta ?are maganar yace

"Aneelerh kin riga da kinsan ?iyayyar da unaisah take ma benazir, tunkafin ta mallaki hankalin ta, unaisah bata bu?atar mamanta, Nima kuma bana bukatarta...." hankalinsu ba karamin tashi yayi ba, Ga samu ga rashi, kallon chief Aneelerh tayi ya kasa kunne yana sauraron su.

"Dan Allah ka taimaka mana ka sanya baki a maganar nan!...." ta fada hawaye na bin fuskarta.

Duk yadda taj yaso hana chief magana sai da ya sanya baki

"Taj, I won't come between you and your ex-wife, Unaisah ita ce damuwata! Bana so ta rasa gatan da uwa take ba Wan ta! duk irin tsanar da tayi mata wlh tana bukatar soyayyar mahaifiyarta fiye da taka!" ya Wan dakata da maganar yana kallon taj, wanda ya nutsu yana sauraron shi.

"kai kanka ba zaka so unaisah ta rasa albarkar mahaifiyarta ba, shin zaka so unaisah tabar duniya ba tare data gana da mahaifiyarta ba? Ya jefa mashi tambayar cikin tausasa harshe shiru taj yayi

"Zaka so ne ta mutu da bakin cikin mahaifiyarta? Taj Ka riga da kasan mahimmanci uwa a addinance, ko da kuwa ta banza ce, bana so mahaifiyar yarinyar nan ta mutu a sanadin rashin ganin yarta da batai ba, kuma bana so unaisah ta rasa soyayyar mahaifiyarta, ba zakai mata kwaWayin ta samu ladar dake a cikin kyautatama iyaye ba? Ka gama da iyayen ka lafiya ita bakaso ta gama da nata iyayen lafiya ne"?

cikin kwantar da murya chief ya cigaba dayi mashi nasiha, su Aneelerh duk sun nutsu sun kasa kunne suna sauraron shi, mutumin Ya kara shiga ransu, yadda yake magana cikin hikma da ilmi ba karamin sace mashi zuciya yai ba.

Jikin shi yayi sanyi sosai, kalaman chief sun ratsa zuciyar shi, aranshi yana ji koda bazai yafewa Benazir ba, zai yi kokarin haWa Unaisah da maman ta, Benazir taci albarkacin chief wlh da ko kallo bata ishe su ba. Koda kuwa zuciyarta zata buga ta mutu ne....."

GyaWa kai yayi cikin sanyin murya yace"Na amince, wallahi taci albarkacinku, bazan iya watsa maku ?asa a ido ba, Ina matu?ar ganin ?imarku da darajarku, kuma bana fata Allah Ya nuna min ranar da zan bijire ma bukatarku..." ya faWa yana kallon chief da Aneelerh, har cikin ran su sunji dadin maganar shi.

Hanky chief Ya zaro daga pocket dinsa Ya mi?a ma taj don ya share hawayen shi, da sauri Ya kar6a yai masa godiya kafin ya share fuskarshi

"Yanzu za'a iya bamu aronta muje da ita asibitin"?

"Ban amince a fita da ita daga gidan nan ba, sai dai Idan mara lafiyar za'a kawo nan ta zauna"! Acewar chief, yarfa hannu Aneelerh tayi, tuni murnar da suke ta koma ciki, muryar ta kamar zata fashe da kuka tace"dan Allah ka taimaka mana! Ka dubi girman Allah ku bamu ita, mu kai ma mamanta, Benazir ba zata iya zuwa nan ba..." saukowa tayi daga kan kujerar ta zukunna kan gwiwowin ta, da sauri ta yace tashi ta zauna, jiki asanyaye ta koma ta zauna.

"Aneelerh kina ganin unaisah zata yarda idan taji cewa wurin mahaifiyarta zaku kaita? kin riga da kinsan irin tsanar da tayi mata, tun kafin ta mallaki hankalin ta...." dafe kai Aneelerh tayi, sam ta manta da wannan zancen ita dai burinta kawai Angel taga mamanta

"Ya zamuyi taj? Wallahi nasan mawuyacin abune Unaisah ta bamu hadin kai"

Taj yace"ko nayi rantsuwa ba zanyi kaffara ba, Unaisah ba zata amince da ita ba don ta yanzu..."

"Kana nufin ta san komai game da yadda mahaifiyarta ta gudu bayan ta haife ta?"

"Ta sani yalla6ai"!

"Ya salam, kunyi babban kuskure da kuka sanar da ita, saboda kun dasa mata ?iyayyar mahaifiyarta, tun da kuruciyarta, kuma yaro yana da ru?on abu a zuciya....."

Shiru taj yayi shi kanshi yasan yayi kuskuren sanar da Angel, duk da ba a hayyacinsa ya faWa mata ba, a lokacin da take cikin azabtar da shi da rashin jinta, har ya taushe mata fuska da pillow, aranar ne ya sanar da ita, don ta tausaya mashi tasan cewa shi kadai ne gatan da take da shi......."

Shiru sukayi tsit na wani lokaci, Kowa da abunda Yake sa?awa aran shi

Unaisah dake zaune tana shan lemu sai kallon su take Yi, ta rasa me suke tattaunawa, tsawon lokacin nan basu gama ba, gashi ta ?osa ta sake huggin din auntyn ta.

"Ko da zan baku unaisah! Zan gindaya maku sharudda, saboda a halin Yanzu bincike mukeyi kan case dinsu, Rayuwarsu tana a cikin hatsari, babu bu?atar kowa yasan suna araye, daga ita har taj din!" hankali atashe zahra da Aneelerh suka kalli fuskar chief da yayi maganar.

"Dalilin dayasa tun farko na kira ku gefe Waya, don in gargaWe ku akan kada ku kuskura kuyi gangancin da wani zaisan suna araye!!...." babu wasa akan fuskarshi yayi maganar.

"Idan har kukai kuskuran da wani Ya sani, ku kuka da kanku! zaifi kuyi takatsantsan yadda mukai maganar anan to mu binne komai anan"!

ya faWa tare da kwankwasa table din gabansa.

Zahra ba karamin tsorata tayi ba, Jikin ta har ya fara kerma, dama da biyu chief ya tsoratar da su don su dauki maganar serious kada su 6ata masu dokar aikin su.

Murya na rawa Aneelerh tace"in sha Allah ba zamu bari wani ya sani ba,..." la66an zahra na kerma tace"wallahi nima bazan yi kuskuran sanarma wani ba, nayi maku alkawari..." Aneelerh tace"zahra bata da matsala, zata rufa mana asiri, ba zata bari wani ya sani ba, amma ni damuwana tayaya zamuje da unaisah asibitin"?

"Unaisah ba zata bamu matsala ba, Zan ja mata kunne akan kada ta fadama kowa ina araye! Ita ma kuma kada ta bayyana kanta koda wani ya nuna ya santa! abun da yakamata shine zaku je da ita amatsayin yarinyar da kuka ce zaku kawo masu, kada abari kowa yasan itace yarta ta ainihi!"

gaba Waya sunyi amanna da maganar Taj,

"Itama unaisah za'a fada mata cewa zataje duba mara lafiyane wadda yarta ta 6ace mai kama da ita, ta hakane kadai zamu samu yardarta, inyaso daga baya idan suka sha?u da juna ta yadda ba zata iya jurar rashinta ba, sai afaWa mata gaskiya" sai da taj yakai Aya Aneelerh tace"amma anya ba za'a samu matsala ba? Benazir idan tana sambatu sunanka dana Angel take fadi saboda mun riga mun fada mata sunan yarta, bayan haka Alhaji ubaid yasan unaisah, itama tasan shi! Kana ganin idan ta ganshi bazata nuna ta sanshi ba? Ko ta tambayi meye alakarshi da mara lafiyar....."

Calmly chief yace"wannan ba matsala bane, idan har zamu bada unaisah dole asibitin ya kasance a karkashin kulawar jami'an mu, zamuyi magana da likitocin dake kula da mommyn nata, zamu sa ahana kowa shiga dakinta, daga ita Unaisah din sai grandma dinta, ko itama tasan ta ne"?


Girgiza kai tay yai"a'a hajiya layla bata san angel ba, bana tunanin ko a hoto ta ta6a sanin ta, saboda babu zumunci atsakanin ta da taj...."

Taj yace"abun zaizo mana da sauki saboda kaf dangin Benazir ba wanda yasan Angel sai kakanta, bayan haka bana tunanin sambatun da maman nata takeyi zai tona asirin wacece ita, duk da Angel tana da kaifin basira but zata ruWe ne saboda tasan ba ita kadai bace mai suna angel after that koda ta furta sunan taj ba lallai tai tunanin ni take nufi ba"! ajiyar zuciya Aneeelerh da zahra suka sauke a lokaci Waya.

"Amma da zarar ta dawo hayyacin ta, Aneelerh ki sanar da ita cewa yarta ce, sannan kiyi kokarin jan kunnanta akan kada tace zata furta wata kalma da zaisa unaisah ta gane itace mahaifiyarta...." amsawa sukayi da toh

Chief ya Waura da cewa"Ko da zamu baku ita, ba yanzu ba, sai zuwa dare zansa akawo ta asibitin, She will be under the care of our officers because we won't be careless with her life..." cike da gamsuwa suka amsa mashi da toh, sunjima suna tattaunawa, a karshe taj shi Ya ce zai yi magana da unaisah dangane da zancen zuwanta asibitin bayan haka sun yanke shawarar canza mata suna duk dan kada a gane itace.

Godiya su Aneelerh suka dinga yiwa chief kamar zasuyi mashi sujjada, har saida taj yace su daina baison ana yi mashi godiya kafin suka dakata har cikin ransu sunji dadin hadin kan da suka samu a wurin shi........"


Unaisah kamar jira take su kammala maganar, tana ganin sun nufo wurin ta, jiki na 6ari ta mi?e ta nufesu, murmushin farin ciki suka saki, da sauri Aneeelerh ta Wauketa kamar karamar yarinya ta rungumeta a jikin ta, zahra sai jin dadi take yau gata ga yarinyar data kwallafa rai akai.

Su uku suka zauna kan sofas din, taj da chief suna zaune can inda suka baro.

Aneelerh ta kasa janye idanunta daga kan Angel, tayi mamakin girman ta, ga wata madarar kyau da tayi komai nata ya canza mata, sai faman sakar ma juna murmushi suke yi.

"Aunty aneelerh, daddy Ya faWa min kin haifa min baby boy, Yana Ina?

"Angel, ?anin ki junaid Yana a school, bawan Allah, Kullum burinshi yaga Angel, Yana matukar sonki Angel, tun yana jariri nake nuna mashi hotunanki, Yasan komai dangane dake ganinki ne kadai bai ta6a yi ba...." marairaice fuska tay kamar zata fashe da kuka

"Ina son ganin shi..." da sauri zahra ta lalubo hoton junaid awayarta ta mika ma Unaisah, yatsun hannunta har kerma sukeyi wurin karbar wayar, ta kura mashi ido tana kallon Wan kyakkyawan yaron aunty aneenerh, wani irin farin cikine Ya bayyana akan fuskarta, hada videos dinsa ta kalla.

"Aunty Aneelerh, fuskarshi kamar anyi photo copy din fuskarki, dake yake kama, Wallahi harna ?osa mu haWu da Wan ?anina, In rungume shi a jikina in ji Wumin shi, Ya Allah nagode maka da ka nuna min wannan ranar, ga ni ga aunty na, ga Wan kanina da zan gani wayyo dadi...." zahara dake kallon ta ji take kamar ta rungumeta, Yarinyar tajima da sace zuciyarta, tun ranar da suka hadu awurin dinner din hateem ashe da rabon su sake haduwa matsayin yar uwar mijin auntynta......

"Angel ga zahra, itace ta Wauko min hotonki awurin dinner, Wiyar uncle dina ce..." sai lokacin Angel ta dubi zahra dakyau, nan take ta gane fuskarta, da sauri taje ta rungume zahra, fuskar kowan nan su da murmushi....
"Angel ina tayaki murnar ganin auntynki, Nima nayi murnar ganinki, wallah ba zan iya misalta farin cikin da nake a ciki ba, naji dadi dana zama silar haduwarku...." ta ?are maganr tare da raba jikinta daga na Unaisah, share mata hawaye tayi da tafukan hannayenta"ki daina kuka kinji, Allah yakamata muyiwa godiya daya sake hadaku, naga ma kamar baki da lafiya, fuskarki ta kumbura, Jikinki da zafi..." cikin kulawa da nuna tausayawa tayi mata maganr
Cikin sanyin murya tace"lafiyana lou, babu abunda ke damuna, farin cikin ganin auntyna ne" ta fada tare da kallon Aneelerh dake kallon ta.

Wayar Aneeleerh ce ta fara ringing, ta Wauko bag din data bari kasan sofa ta zaro wayar

"Tun bayan da chief ya kiraku wayarki take ta ringing, banaso na katse maku tattaunawarku shiyasa ban kawo maki ita ba..." murmushi aneelerh tayi aranta ta ayyana har yanzu tana nan da wayonta, ga hankali

Ko da ta duba screen din wayar missed calls ta gani sunkai ashirin, daga wurin mutun uku hajiya layla da dr shurem dana mami din su..
Unaisah zan amsa kira" amsa wa tay da toh, mikewa aneelerh tayi ta nufi gefe Waya, tabar zahra zaune tare da Unaisah kamar wasu kawaye haka suka fara fira

Hajiya layla ta fara danna wa kira, bayan sun gaisa hajiya layla tace"Aneelerh ya ake ciki? Naji shiru baki kirani ba, ko dai iyayen yarinyar basu bamu ita bane? Wallahi jiya ko baccin kirki Benazir batayi ba, tana ta sambatu tana ambaton sunan yarta .."
"Ki cigaba da kwantar mata da hankali, nayi magana da iyayen yarinyar sun bamu ita, amma sai zuwa anjima zata zo asibitin"

Muryar Hajiya layla da alamun farin ciki ta furta"Alhamdulillah!....wallahi naji dadi Aneenerh, dan Allah kuyi mana godiya wurin iyayanta..."

Murmushi Aneelerh tayi"in sha Allah zanyi masu" sallama sukai da juna, ta sauke ajiyar zuciya, idanunta akan su unaisah, wani irin sonta ne ke kara baibaye zuciyarta,

Layin mami ta kira, ko sallama Aneelerh bata kaiga yi ba, mami ta katse ta da cewe"Aneelerh sai yanzu zaki kirani? Baki ga missed call dina bane? Kunsa inata zullumi, na kasa tsaye na kasa zaune..."

"Allah sarki mami, Yanzu na dauko wayar, banga call din ki ba"

"Toh ya ake ciki ne"?

"Mami, mun ga yarinyar, dagaske ba unaisah bace, zahra tayi kuskuren fada mata sunan ta, ashe ita wannan sunanta Azeezaty, suna bala'en kama da unaisah, amma iyayen yarinyar sun bamu aron ta har zuwa time da benazir zataji sau?i"

"Toh Aneelerh, har naji sanyi wlh, yanzu zakuje asibitin ne"?

"Mu zamu tafi, ita kuma yarinyar sai zuwa anjima da dare za'a kaita"

"Allah yakaimu lafiya" ameen mami, daga haka sukai sallama da juna, komawa tayi wurin su unaisah suka cigaba da yin firar yaushe rabo, chief tuni ya shige gidan saboda yana son ya fita office, zama taj yai a wurinsu suka dinga sanya juna nishadi, ana tuna rayuwar baya, har wuraren ?arfe 9 na safe kafin su Aneelerh suka mike zasu tafi, Angel kamar tay masu kuka taso su shiga ciki suka ce a'a sai zuwa na gaba suna sauri ne, dakyar taj ya lallashe ta yace ta koma gida, zaije ya rakasu, tana ji tana gani ya tafi da su aneelerh, a motarshi yakaisu cikin estate din inda suka bar motarsu, sai da ya tabbatar sun tafi kafin ya dawo.

________________________________
'?

Fitowa dr shureim yayi daga bedroom dinsa, Ya kimtsa tsaf cikin shigar su ta larabawa, hannun sa ruke da wayarshi, har ya fara tafiya kiran Aneelerh ya katse mashi hanzarin shi, da sauri yai picking tare da kara wayar a kunnansa

"Assalamu alaikum Aneelerh, barka da safiya, fatan kun wayi gari lafiya"

On the other hand Aneelerh tace"lafiyalou Alhamdulillah, Ya shureim.."

"Tun Wazu nake ta kiran layin ki don inji Ya ake ciki game da yarinyar an dace ko kuwa"?

"Yaya shureim, mu hadu asibitin zanyi maka bayanin komai" amsa mata yayi da toh, kafin sukai sallama, a tsanake Ya nufi falo, tunkafin Ya isa ya hango mutanan gidan a dining sun hallara sunayin breakfast,
"Shureim har ka kammala shiryawa"? alhaji ubaid ne yai masa maganar
"Eh daddy..." ya faWa tare da gaishe da su, Alhaji musa yace"ba zakayi breakfast din bane"?
"Idan naje can zanyi..."
"Okey,
Hajiya sarah tace"in sha Allah idan na taso daga office zanbiyo asibitin.."
"Allah ya kawo ku lafiya..." satar kallon zeenatu yayi, hannunta ruke da cup tana shan tea, murmushi ta sakar mashi tare da kashe mashi ido Waya...lamarinta ya fara bashi tsoro yarinya kamar mai iskokai?

"Zeenatu ba zaki bini mu tafi ba"?
"Ina zamuje"?

"Asibiti wurin auntynki benazir.." ma?e mashi kafada tayi"bana jin dadi, bazan iya zuwa ba, ka tafi kawai..." da mamaki hajiya sarah take kallon ta

"Zeenatu! Kin kuwa saurari abun da yace maki dakyau? Asibitinne ke bazaki je ba? Dallah tashi ki bi shi ku tafi, idan kika zauna gidan me zaki yi ke kadai? Daddynki ma fita zaiyi..." bata kare maganar ba, Alhaji musa ya katse ta da cewa"ba ki ji tace bata da lafiya ba?
Rai a6ace hajiya sarah tace"amma ay lafiyarta qalou, ni banga wani alamun rashin lafiya atare da ita ba..."

Alhaji ubaid yace"shureim ka tafi kawai, Kada ku takura mata, tun da ba koshin lafiya gare ta ba, ni bana so ma taje asibitin taita kuka kamar jiya da mukai ta fama da ita...." jiki asanyaye dr shureim Ya mi?e idanunsa akan fuskar zeenatu, itama kallon nashi take Yi, ji take kamar ta tashi tabi shi sai dai ta kasa kamar ana ruke kafafunta, a hankali Ya juya yana tafiya kamar babu kuzari a jikin shi, bakomai yake tariyowa ba face kalamanta! Meyasa zeenatu ta canza daga jiya zuwa yau? Ya jefawa kansa tambayar da baida amsarta!!

________________________________
'?


*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne dukanshi za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08103884440*_________________________________
'?


Bayan komawar Unaisah cikin parlour, a dining room ta hango ?an uwan ta, har sun fara yin breakfast sunyi neman ta har sun gaji ba su ganta ba, suna jin takun tafiyarta gaba Waya suka dago suna kallon ta.....

"Sister! Ina kika shiga muna ta neman ki"? Batool ce tayi mata maganar, bata tanka masu ba, sai faman sakin murmushi takeyi kamar wadda akayiwa albishir da gidan Allah, yau ranta fari fess, cike da zumudi taja kujera ta zauna tana kallon su Waya bayan Waya, tasan in har ta sanar da su Azeeza game da zuwan auntyn ta aneelerh ba karamin dadi zasu ji ba saboda tasha basu labarinta agidan kurkukun ?addara,

abunda bata sani ba tun da ta zauna suke ta kallon ta


"Aunty ummi Ina kwana.. " wani kallo ummi tabi ta da shi, har saida tasha jinin jikin ta

Kafin ummi ta furta kalma Sajeed Ya riga ta cewa"Sister baki da lafiya ne? ko kinyi kuka ne"? lokaci Waya yanayin fuskarta ya canza! Kwata kwata ta manta da abun da ya faru daren jiya, saboda murnar zuwan Aunty Anila, maganar sajeed ce ta tuna


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login