Showing 3001 words to 6000 words out of 298130 words

Chapter 2 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

Wagowa ta Wanyi ta kalli chief dake a gefenta, face mask din fuskarshi Ya hana ta ganshi da kyau, sai dai kyawawan idanuwanshi.

Tana faman zazzare idanuwanta haWi da ?yaf?yaftasu ta nufi sheikh iman, ta Waura hannunta asaman nashi daya mi?a mata.

"Unaisah ko"? ?aga mashi kai tayi alamar Eh.

"Meyasa kina ji muna magana ki ka yi shiru baki tanka mana ba kamar wata mai laifi, ai ba wani abu bane don kinzo duba Wan uwanki"

Shiru tayi bata ce komai ba, duk ta kama kanta kamar wadda tayiwa sarki ?arya.

"Zonan surukata" prime minister ne ya kirata, da sauri ta wurga eye balls dinta kan fuskarshi rass taji gabanta Yai mugun faWuwa, har saida ta zaro ido waje ta saki baki tana kallon ikon Allah, duk sun fahimci dalilin ruWawarta.

da sauri ta kalli Boss man ta kuma kalli Salsabeel dake atsaye fuskarshi Wauke da murmushi
"Baki ji Yana magana ba? Kije ku gaisah" acewar Salsabeel
Zuwa tayi gaban prime minister ta tsaya muryarta adabarbarce ta furta"Ina kwana,"

Murmushi yasakar mata Ya Waura tafin hannunshi saman sumar kanta
"Ba ki yi breakfast bane? Ko baki duba time ba, Naji kina fadin Ina kwana bayan rana tayi" cikin kulawa yayi mata maganar.

Muryarta kamar ta salihar baiwa ta furta"mantawa nayi,'

"Okey, surukata Ina fata kina lafiya"?

"Lafiyalou"

"Naji dadin haWuwa dake, ke fa"?

?aga mashi kai tayi"nima"

"Unaisah" Boss ne ya kira sunanta, ta juya tana kallonshi.

"Sunan shi prime minister, uncle na chief namu, kuma shine ya kira sheikh Imam don Ya duba lafiyar Wan uwanki"

Da sauri ta maida kallonta ga prime minister, farin cikin yasa taji hawaye sun cika mata idanuwanta, miryarta na rawa ta furta.

"Mun.... gode, Ubangiji Allah yasaka maka da gidan Aljanna, kamar yadda ka sanya mu farin ciki kaima Allah Ya faranta maka, In sha Allah duk idan nayi sallah zanyi maka addu'a'.

Murmushi kowan nan su yasaki, musamman prime minister har cikin ranshi yaji daWin kalamanta.

"Nagode surukata,"
Juyawa tayi da sauri ta dubi sheikh imam.

"Baba mungode, Allah ya saka maka da mafificin Alkhairinsa" addu'o'i ta dinga yiwa sheikh imam, Fuskarshi Wauke da murmushi Ya shafa sumarta da hannun shi tare da cewa"Nagode da addu'arki agare ni, kina da kaifin basira, kuma kina da hankali, Iyayenki sun baki Tarbiya, Allah yayi maki albarka tare da sauran ?an uwanki" amsa mashi tayi da ameen, ha?i?a taji daWin kalaman sheikh imam, ?an hawayen da take 6oyewa cikin idanuwanta tuni sun fara gangarowa kan kuncinta.

"Unaisah, saura chief namu, yakamata kiyi mashi godiya" Boss Man ne ya faWa yana nuna mata shi, tamkar mai jin shakkar shi ta juya tare da Waura idanuwanta kanshi, Yana daga tsaye ya goya hannayenshi on his broad chest, harta Waga ?afa zata nufe shi Big guy yai hanzarin dakatar da ita ta hanyar yi mata Magana.

Nufota yayi adai dai bayan ta ya dakata tare da du?o da kanshi saitin kafaWarta Yayi mata raWa.

"You don't need to thank him, saboda baya so, but be kind to him. If you give me the chance, I'll guide you.

Cikin sanyin murya ta amsa amshi da toh.
"Good Girl," Ya ambaci hakan tare da Wago da kanshi, babu wanda yaji me suke tattaunawa.

Boss Man Yace"Unaisah zoki wuce ki tafi Waki ki yi sallah, Yanzu za'a kawo maku lunch Winku" amsa mashi tayi da toh, kafin ta nufi ?ofar room Win ta fuce da sauri.

Kafin wani ya kuma yin magana acikinsu, Danish dake akwance Yaja dogon Numfashi, Yatsun ?afarshi suka soma yin kerma da na hannayensa nan take suka fahimci ya farka daga bacci, wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskar prime minister.

Salsabeel Yace"Ya farka, Yakamata akawo mashi abincin Yanzun"

"Wani kalar abinci zai Iya ci"? big guy ne ya tambaya.


"Abinci mai ruwa zaifi yi mashi sau?in wuce wa ta ma?oshi, don bazai Iya tauna abu mai tauri ba"

"Okey, bari naje na kawo mashi" big guy ya faWa tare da juyawa a hanzarce ya fuce daga Wakin.

Fitarshi keda wuya, Wayar Chief ta fara Ringing, gaba Waya suka Wago suna kallon shi
Prime minister yace"Wanene ke kiranka"
Curo wayar yayi daga aljihu Ya duba screen din kafin Ya bashi amsa da cewa"Dad Lateef ne"

"Okey, idan kana bu?atar ka shirya kafin mu tafi can gidan ka tafi Waki, in sha Allah kafin ka dawo na kammala bashi abincin mu sai mu fara zuwa gida"

Chief ya furta"okey," kafin ya juya ya nufi room door din, bayan fitarsa

Sheikh Imam Yace"atare zamu tafi gidan baban naku, Inason in gaishe da aminina da sauran mutanan gidan"

Prime minister Yace"Toh,"

Shigowa Wakin Big guy yai hannayen shi a ru?e da tray madaidaici, kan carpet din gefen gadon Ya daurashi, kafin Ya haye saman gadon Yayi ma salsabeel alamar yazo Ya taimaka mashi, atare suka WaWWago da Danish suka jinginar da bayanshi jikin headboard din gadon bayan sun sanya mashi pillow, Yalwatacciyar sumar kanshi ta sauko kan shoulders dinshi.

"Baba, ko zaku je gidana ka huta, kafin in kammala bashi abinci, in yaso daga baya zamu zo tare da Chief owais, sai mu wuce gidan baban"

Jinjina kai Sheikh Imam Yayi, Hakan yayi nima inaso in canza kayan jikina, Wa zai kai ni gidan"?

Big guy yace"Aikina ne wannan" ya faWa tare da saukowa daga kan gadon, Yace da sheikh su tafi Ya sauke shi a mota, Sallama sheikh Yayi ma Prime minister kafin fitarshi saida Ya faWa cewa idan sunga wani abu badai dai ba dangane da Danish su kira shi awaya su sanar da shi.

Prime minister Ya amsa mashi da toh haWi da yi mashi godiya, bayan fitarsu, wayar boss tayi ringing, da sauri ya zaro daga aljihu, sunan chief ne ya bayyana akan screen din da sauri yai Ya kara wayar a kunnanshi.

Bayan sun kammala yin wayar Ya dubi Salsabeel.

"Chief Yace ka koma gida wurinsu khadeeja" Amsa mashi yayi da toh,
"Yalla6ai zan wuce, In sha zuwa gobe zan shigo in ?ara duba jikinshi" cikin girmamawa yayi maganar Yana duban Prime minister
Fuskarshi asake yace"Allah yakaimu Lafiya, Amma nayi tunanin kaima agidan nan kake zaune"
Salsabeel Yace"a'a, gidanmu daban, Ina kula da sauran ?an uwanmu ne"
"Akwai sauran Yaran kenan bayan wanda ke acikin gidan nan"?
"Eh yalla6ai"
"Allah ya tayaku ru?o, Sai Allah Yakaimu"

"Ameen" ya fada tare da kallon boss yayi mashi sallama.

"chief yayi magana da Jami'in da zai yi driving dinka, Yana awaje Yana jiranka"
Amsa yayi da toh, kafin Yasakai Ya fuce daga Wakin.

Ya rage saura prime minister da Boss man sai Danish da ke asaman gadon.

"Yalla6ai zan taimaka maka mu bashi abincin"
Prime minister yace"Okey,"
Boss man ne ya Wauki tray din abincin Ya Waura shi daga gefen gadon, Ya Wauki robar madara Ya cire murfin a cup ya tsiyaya madarar, kafin Ya mi?a ma prime minister yasa hannu ya kar6a haWi da furta mashi thanks.

Abaki ya kanga ma Danish sai dai ya?i buWe bakin ya rufe shi gam.

Ajiye robar milk din boss yayi, tare dakai hannu ya ru?o la66ansa ya buWe mashi baki da?yar, a hankali milk din take shiga bakinshi hankalin prime minister ya kwanta ganin yana swallowing dinta, duka ya shanye, murmushi yasaki yana kallon boss man yace"naji dadi daya sha, ka ?ara mashi da yogurt"

Martanin murmushin Boss yayi mashi kafin ya kar6i cup din ya zuba mashi yogurt ya mi?a ma hateem, cikin ikon Allah danish ya shanye, sai da ya tabbatar daya cika mashi cikin shi tukunna yace.

"Bari nabarshi haka, kada naci ka mashi ciki," Hateem ne ya faWi hakan idanunsa akan fuskar Danish wani irin kallon so da ?auna yake jefa mashi.

Sauke tray din boss yayi kan carpet, kafin ya Wago yana kallon hateem daya ?urawa danish ido kamar mai karanto wani abu akan fuskarshi, tun Wazu yake ta son ya tambayeshi wani abu sai dai ya kasa, gani yake kamar raini ne yayi magana da mutun mai babban mu?ami irin Hateem.

Daurewa yayi muryarshi da alamun jin shakkar furta maganar yace"yalla6ai..." kallon da prime minister yayi mashi ne yasa shi saurin haWiyar maganar.

Murmushi ya sakar mashi tare da cewa "I'm listening to you, and I heard you mention my name. Why did you go silent? Is there something you want to tell me?"

Sunnar dakai ?asa Tajo yayi"bakomai subul da baka nayi wurin furta sunan"

"Ban yarda ba, please tell me what you want to talk to me about. Kada kaji nauyin yi min magana, I'm a human being like everyone else."

Da sauri boss ya Wago da ido ya kalleshi, ha?i?a yana matu?ar mamakin sau?in kan prime minister Hateem, tun da yake arayuwarshi bai ta6a tsammanin akwai wata rana wadda zato zo har ya sami damar ganawa da shugaban ?asar Nigeria sai gashi cikin ikon Allah ya haWu da mutun bai ru?e da babban mu?ami na shugaban ?asar canada ?asar da tana Waya cikin Manyan ?asashen duniya da suke da tarin jama'a da wadatar arzi?i...

Yayi zurfi acikin tunaninshi muryar prime minister ta katse shi"kayi shiru baka ce komai ba,"
Sosa ?eya ya Wanyi da hannunshi kafin ya furta"am....dama yalla6ai tambayace nakeso nayi maka idan ka bani dama, amma dan Allah kada ka Wauka da wata manufa"
Da fara'a akan fuskar Hateem Yace"kada hakan ya dame ka, Nifa Wan siyasane, tambayoyi har marasa kan gado ?an jarida sunayi min kuma in basu amsa dai dai dasu, ballanta kuma kai dana yaba da hankalin ka, duk mutumin da Owais ya yarda dashi toh nima na yarda dashi, don haka kada kaji komai na baka damar yi min kowace irin tambaya ce"

Ajiyar zuciya boss man ya sauke, har cikin ranshi yaji dadin kalaman prime minister, kuma ya ?ara jin ?aunar mutumin aranshi.
Sai dai duk da haka nauyin shi yake yi, da?yar ya iya buWe baki yace"yalla6ai, naji kamar ance baka ta6a haihuwar Wa namiji ba, ?a'?an biyu duka mata ne shin dagaske ne"? Boss Na ?are maganar yayi saurin kau da idonshi gefe Waya saboda kunyar tambayar da yayi mashi

Shiru prime minister ya Wanyi, na ?an mintuna yana maimaita maganar taj acikin zuciyarshi, yayin da yake kallon fuskar danish

"Am sorry Sir, idan tambayata ta 6ata maka rai" acewar Tajj.

Calmly Hateem Ya soma magana ba tare da ya kau idon shi daga kan fuskar Danish ba.

"Ka fama min raunin da yake kwance acikin zuciyata, tsawon shekaru da suka gabata, bana son tuna haukan da nayi, da hawayen dana zubar, da kuma ?unci da raWaWin dana fuskanta saboda rashin da nayi na abun da na ?wallafawa rai........" tuni yanayin fuskarshi ya canza zuwa matsananciyar damuwa, yayin da yake yin maganar farin ruwane kwance acikin fararen idanuwanshi.
Hatta tajj dake sauraronshi, Jikinshi yayi mugun yin sanyi tunkafin Ya ?arasa jin zancen nashi
Numfasawa prime minister yayi before saying"I've lost so much that I still haven't forgotten him. I loved him more than I love my children now, and I've never stopped missing him. I know if I tell you that, you'll think it's crazy." He said it with a smile on his face.

("nayi babban rashi da har yau bana manta shi, inason shi fiye da ?a'?an da nake dasu a yanzu, kuma har yau ban ta6a cire shi araina ba, nasan idan na faWa maka zaka ji abun wani iri" ya faWa fuskarshi da murmushi.)


"Bayan gimbiya mujeedat ta yi haihuwa ta biyu ta haifi Yazrin, a ?alla ta Wauki shekaru bata sake haihuwa ba, tunda Allah ya bani ?an mata har biyu, sai na ?wallafa rai ga son samun Wa Namiji har tsakar dare inayin nafilfili akan Allah ya bani Wa namiji, cikin ikon Allah a lokacin da banyi tsammani ba, Allah ya kar6i addu'ata, Matata ta samu ciki a daren ranar ko runtsawa banyi ba.. though I wasn't sure if it was a girl or a boy, nidai kawai nasanyawa raina namiji ne.." dakatawa yaWan yi da yin maganar, tajj ya natsu yana sauraronshi, tun yana daga tsaye har dai yakai ga janyo kujerar gaban mirror ya ajiyeta daga gefen gadon ya zauna yana kallon prime minister.
Cigaba da magana yayi"tun kafin a haife shi na fidda mashi suna, na tsara mashi kalar rayuwar jin daWin da zaiyi, hatta makarantar da zan sanya shi da komai ma na rayuwarshi sai da na rubuta a diary din dana ajiye domin shi kawai, ita kanta gimbiyata mamaki ta dinga yi ganin yadda na haukace akan son abunda ke acikinta, har fadi take yi na fahimci kafi sonshi akan sauran yaran dana haifa maka, idan ta fadi hakan sai dai nayi murmushi, ba ita kadai ba hatta family dina na Canada dana Nigeria sai da suka shaida ?aunar dana ke yi mashi, duk rana ta Allah saina kirasu awaya nace su tayani da addu'a Allah ya sauki matana lafiya, saida na addabi kowa da zancen cikinta, mahaifina har tsakar dare nake tada shi daga bacci ince mashi ya tashi yayi nafila ya taya matana da addu'a......" shiru ya Wanyi idanuwanshi akan agogon hannunshi.

Tajj duk ya ?agara da sonjin ?arashen zancen.

"Ban ta6a kawowa raina cewa yaron zaizo duniya amace ko zai mutu bayan an haife shi, kana Naka Allah Yana nashi, sai gashi an haife shi babu rai, wallahi bazan iya misalta haukan da nayi ba a asibitin da ta haihu, likitan daya fara furta mun zancen an haifi yarona babu rai da hannu biyu na cakumi wuyan rigarshi na sha?e shi tamkar zan kashe shi da?yar dangina suka raba ni dashi, na dinga yi masu sambatu ina fadin karya sukeyi min ni yarona bai mutu ba da ranshi, daga ni har mahaifiyarshi ba'a bari munganshi ba, ita bata acikin hayyacinta bacci takeyi, ni kuma an hana in ganshi gudun kada in haukace masu saboda sun fahimci na mutu akan ?aunarsa, tun bayan 2 weeks da faruwar lamarin, Ina kwance gadon asibiti Ina jinyar zuciyata, duk na fita hayyacina sai sambatu nake yi ina fadin ina yarona baba kana gani za'a raba ni dashi, ni nasan Wana bai mutu ba, baba ina jin bugun zuciyarshi acikin zuciyata, ire iren kalaman da nake fadi masu ba ?aramin raunata masu zuciya nayi ba, babu wanda bai zubar min da kwalla ba, haka suka dinga lallashina sunayi min nasiha, da?yar suka shawo kaina har suka samu na ha?ura nabarma Allah komai sai gashi yanzu tamkar ba'ayi ba" Prime minister Hateem ya ?are maganar yayin da hawaye ke ?o?arin gangarowa saman kuncinshi, da sauri boss man yayi saurin share mashi hawayen don bazai juri ganin babban mutun kamar prime minister yana zubar da hawayensa akan idonsa.

"Nayi kuskure dana yi maka tambayar nan, ka gafarceni yalla6ai, ni kaina jikina yayi sanyi kuma banji daWin yanayin da na jefa ka ba, da ace nasan maganata zata fama maka raunin dake acikin zuciyarka wallahi daban furtata ba" cikin sanyin murya murya Boss man Yayi maganar.

Cikin karyayyar murya yace"kada ka damu, ay yanzu komai ya riga daya wuce,"

?arfin hali taj yayi wurin furta"yalla6ai ko zan Iya sanin sunan baby boy din da ka rasa"

He smiled a little before saying, "Sunanshi *OMAIR BIN HATEEM OBINNA* wannan shine sunan da nayi niyar sanya mashi, Allah bai nufa ba"

Maimaita sunan taj yayi"suna mai daWi, ubangiji Allah ya baka mafiyin abunda ka rasa, In sha Allah zan tayaka da addu'a"
"Nagode sosai"

"Yalla6ai, zan fada maka wani abu, ni tunda nake arayuwata ban ta6a ganin mutun mai babban mu?ami mara girman kai irin ka, A yanzu haka da muke yin magana sai nake jin tamkar a mafarki ne

Murmushin gefen fuska prime minister ya saki jin abunda taj yace.

"Ba kai kaWai ba, mutane dayawa suna mamakin halina, ni ta inda na banbanta da sauran, ba??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ni da girman kai, kuma bana Waukar kaina wani, duk idan na tuna cewa mu dukkanmu bayin Allah ne, kuma babu wanda yafi wani awurinshi sai wanda yafi jin tsoronshi sai in ?ara jin ni ba wani bane, idan na shiga cikin takalawa sai in manta wanene ni, zan saki jiki dasu muyi mu'amala tamkar bani da ko sisi, haka zalika idan na shiga cikin masu kuWi sai inji dai dai nake da su, yanzu haka da nake atare dakai, kallon aboki nake yi maka" zaro ido taj yayi fuskar shi da alamun mamaki.

"Ni kuma yalla6ai"

?aga mashi kai hateem yayi alamar eh, wani irin farin cikine ya lullu6e Taj sai faman sakin murmushi yake yi jin prime minister ya kira shi da sunan aboki.
A hankali Hateem Ya mayar da idanuwanshi kan fuskar Danish, ya mi?a hannu ya shafi gefen fuskarshi.

"Allah ya jarabceni da ?aunarka, Ina fata ka zama alkhairi arayuwata, zan cigaba da yi maka addu'a Allah Ya baka lafiya, bana so in koma ?asar canada batare da ka buWe idanuwanka kayi tozali dani ba" cikin sanyin mirya ya ?are maganar, ba zato ba tsammani yaji saukar yatsun hannun danish acikin nashi wata irin cakuma yayi ma hannun prime minister ya ?an?ame shi, hankalin Taj ba ?aramin tashi yayi ba, har ya yun?ura zai raba hannun Danish daga ru?on da yayi ma Hateem, da sauri ya girgiza mashi kai alamar a'a, komawa yayi ya zauna still hankalin shi bai kwanta ba, idanun shi akan hannayensu dake harWe cikin na juna, lamarin yayi mugun Waure mashi kai ganin mutumin da ko yatsan shi bai iya Wagawa amma yayi ?arfin halin ru?e hannun mai girma Hateem.

Tun da ya kafe hannun Danish dake a ru?e da nashi da ido, bai ko ?yafta ba, wani irin yanayi yake ji atattare dashi mara misaltuwa, ga wani bugu da zuciyarshi take yi mashi, gaba Waya ya shagala da kallon hannayensu na tsawon awa batare daya ankara da gudun da lokaci ke yi ba

Motsin buWe ?ofar Wakinne Yaja hankalin boss ga


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login