Showing 228001 words to 231000 words out of 298130 words

Chapter 77 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

razana dakyar ya iya bude baki yace"ni damuwata yanzu ina Ana? Ga junaid ya bayyana saura ita baiwar Allah, bamusan meya faru da ita ba! Bamu san awani hali take a ciki ba..." bai kare maganar ba, Abie yace"in har wani abunne ya faru da su, zai iya yiwuwa itama ta boye awani wuri kamar yarda ta 6oye junaid..." jin wannan maganar yasa mahboob ruko hannun zahra yace mata tazo suje su kara nemo ta, da sauri suka fuce daga dakin bedroom dinta suka shiga, suka fara nemanta sako da lungu har karkashin gadon ta, da cikin wardrobe dinta amma basu ganta ba, sun duba ko'ina tun suna sa ran zasu ganta har suka fidda rai, kafin su fito daga dakin sai da mahbbob ya shiga toilet dinta Ya kashe shower din da aka bari a kunne da faucet, ruwa harya fara taruwa sosai har cikin dakin ta ya fara gangarowa, basu bar dakin ba sai da mahboob ya taimaka ma zahra suka gyara mata shi, kafin suka fito da sauri suka nufi sauran dakunan suna duddubawa, duk wani wurin sirri da mutun zai iya 6uya saida suka duba ko zasu ganta sai dai kash bata nan, ceilling ne kadai basu tsaga sun bincika ba don sunsan ba tayadda za'ay ta iya shiga ciki ta buya.
Badan sunso ba dole suka hakura da nemanta, jikinsu yayi mugun yin sanyi, zuciyarsu ta karaya, gani suke kamar ba zasu kara ganin Ana ba.


Anila taso takai baby junaid asibiti adaren saboda aduba mata lafiyar shi amma abie ya hanata yace mata ta cigaba da yi mashi addu'a in sha Allah zai samu lafiya, taruwa sukayi akan shi Waya bayan Waya kowannansu saida yayi mashi addu'a suka tottofa mashi a jikin shi, har indomie zahra ta dafa mashi ta kawo masu a plate amma ya?i ci, ta koma kitchen ta haWo mashi tea dakyar anila ta samu yasha tea din, jikin shi ya danyi sauki, zuciyar shi dai ce take bugawa da karfi, duk yadda taso ya bata hadin kai suyi magana don taji meke damunshi ya?i mata magana kamar kurma sai dai yabi ta da ido, don dole ta hakura, gashi ya hanata sukuni ya manne mata kamar anta da jini, ko da zata shiga toilet ta karasa alwala sai dai ta shiga da shi, bayan ta fito ta goya shi abayanta ahaka tayi sallah =ؔ?

___________________________________
'?

*ALHAJI MUSA=ت?*

Da sassafe ya shigo katafaren falon gidan, jallabiya ce a jikin shi grey colour, ta Wanyi tighting arms dinsa, kamar kullum fuskarsa a daure ba fara'a, ya zuba hannayenshi cikin aljihun jallabiyar.

Cikin takun izza yake tafiya yan aikin gidan dake kai komo suna yin aikace aikacen gyara falo dakai abinci dining suna ganin shi, suka fara gaishe da shi, ko kallo basu ishe shi ba, kaitsaye ya nufi dining room ya tsaya bakin glass door din yana kallon zungureran table din dake a kewaye da kujeru ancika shi da kayan breakfast, wani abu da ya Waure mashi kai babu kowa a kan kujerun yayi mamaki sam ya manta da abunda ya faru jiya, saboda bayan ya gama balbalin bala'in shi gidan ya bari gaba daya bai ?ara dawowa ba, sai yanzu daya shigo da safen nan,baisan awani hali mutanan gidan suka kwana ba.

Agogon hannunsa ya duba don yaga ko time na yin breakfast dinne baiyi ba sai kuma yaga lokaci yayi
Ta6e baki yayi kafin ya dago ya kalli yan aikin, Tani ya hango da hannu yai mata alamar tazo, jikinta na bari ta nufe shi"yalla6ai gani"
"ya akai banga mutanan gidan ba? Ko baku fada masu an shirya masu breakfast ba"?
"Wallahi mun yi masu magana, ita zeenatu tace mun bazata ci ba, nayi nayi da ita taki kula ni, shi kuma shureim da naje dakin shi na iske shi kudundune cikin bargo kamar baida lafiya nayi mashi maganar breakfast yace min baijin yunwa in tafi kawai..."

bata kare maganar ba, rai a6ace ya Waga mata hannu da sauri taja baki tayi shiru duk tabi tasha jinin jikin ta, wucewa yayi azafafe Ya nufi upstairs, ya ture kofar dakin zeenatu ya shiga daga ciki, tana a zaune kan prayer mat, hannunta ruke da al'kur'ani tana karantawa sam bata ji motsin shigowar shi ba.

"Zeenatu"! Kakkausar muryarshi ce ta daki kunnanta, bata kula shi ba, tamkar bataji kiran da yayi mata ba, hakan ba karamun fusatashi yayi ba, kwatsam taji ya dauke kur'anin dake a hannunta, azabure ta mike idanunta sharkaf da hawaye ta furta"Daddy, give me my Qur'an..." ko kula ta baiyi ba ya rufe kur'anin ya nufi bookshelf din dakin ya daura shi asama kafin ya juyo ya kalle ta"fushi kike dani? Rai a6ace tace"daddy ba iya fushi nake da kai ba, haushin ka nake ji, dan Allah ka kyaleni in cigaba da karatuna ko na samun saukin abunda ke damuna..." fashewa tayi da kuka gaban hijab din jikin ta ya jike sharkaf da ruwan hawayen ta

"You don't want my happiness, Daddy. You don't want peace kullum burinka ka 6ata min rai, a haka kake son inyi alfahari dakai amatsayin mahaifina!"

ta faWa tana zare mashi blue eyes dinta wadanda suka kaWa jawur, ko kadan baiyi mamakin kalaman data furta mashi ba, ya riga da yasan meke damunta, wato saboda ya bata ma shureim rai jiya shiyasa take fushi da shi.

Matsawa yayi kusa da ita da sauri taja da baya tana girgiza mashi kai, wani irin fargaba da tsoron shi ne suka kamata tayi zaton zaiyi mata wani abune. Batai aune ba taji ya dam?i arm dinta ya janyota kan broad chest dinsa yayi hugging dinta.

softly yace"fadamin laifin me nayi maki? Meyasa kike fushi da daddynki? Cikin shesshekar kuka tace"ka 6ata ma ya shureim rai, jiya banji dadin kalaman daka gaya masa ba, daddy ya shureim baiyi maka laifin komai ba, amma ka rufe shi da fada harka shake wuyan rigar shi, baka dubi girman shi ba..." dakyar ta ?are maganar, shafa bayanta yayi cikin sigar lallashi yace"yanzu me kike so nayi? Don in wanke laifina"? Ya faWa tare da dago da fuskarta suka haWa ido sai taji yayi mata kwarjini da sauri ta kau da idonta gefe murya na rawa tace"kaje ka bashi hakuri, idan yace ya yafe maka nima zan daina fushi dakai" Waure fuska alhaji Musa yayi jin abunda tace wai shi zaije yaba shureim hakuri, girman kanshi ba zai barshi ba, amma dayake shu'umun kanshi ne sai yace mata"okey, mu sauka down, muje kici abinci" ma?e mashi kafada tayi"bazan iya ci ba, in ba atare da ya shureim ba"

"It's okey, muje sai in bashi hakurin" tace toh, ya ruko hannunta suka sauko downstairs.

A dining room ta tsaya kamar yadda ya bata umarni, Shi kuma Ya nufi dakin shureim time din daya shiga da sallama abakin shi, bai taras da kowa ba adakin, sautin ?arar zubar ruwa yajiyo daga bathroom, alamar yana aciki yana wanka, zama yayi gefen gadon shi yana jiran fitowarshi,
Almost 15 mins yana jiran shi, har ya mike zai tafi don bayason jira arayuwarshi sai dai ajira shi, jin motsin buWe toilet door dinne yasa shi dakatawa ya tsaya yana kallon shureim dake fitowa waist dinsa daure da towel, gefen fuskarshi yayi jawur kamar jini ya kwanta, hada sahun yatsun Alhaji musa shatunsu ya fito rudu rudu, sai yaji ba dadi aran shi, ganin irin illar daya yi mashi kuma yayi imanin zafin marin da yayi mashine ya haifar mashi da rashin lafiya a jikin shi kamar yadda yaji Tani tace bashi da lafiya.

Kwata kwata shureim bai lura da Alhaji musa ba, cikin rashin kwarin jiki ya nufi dressing mirror.

"Shureim"!Ya kira sunan shi, Waure fuska yayi batare daya kalli inda yake ba, duk da yayi mamakin jin Muryarshi a cikin kunnanshi aranshi ya ayyana kome yazo yi dakin shi?ya dai san ba hakuri yazo bashi ba abune mawuyaci.

"Da kai fa nake magana"! ya faWa fuskarshi adaure, da farko yaso ya shareshi don yaga iya gudun ruwan shi amma sai ya fasa saboda mutunne shi mai matukar ladabi da biyayya yana ganin girman nagaba da shi bayan haka akwai na annabawa wato hakuri.

Juyowa yayi suka fuskanci juna
Muryar shi kasa kasa ya furta"Uncle, barka da safiya? Ka tashi lafiya"? ya dan yi mamakin tarbar da shureim yayi masa, amma bai nuna a fuska ba,
"ka zauna inason magana dakai" kasa kasa ya amsa da toh, kafin ya juya ya shiga wurin closet dinsa, jim kaWan ya fito sanye da jallabiya fara, a kan couch suka zauna shureim ya kau da idanun shi gefe Waya yana jiran jin dame yazo!

"Shureim dangane da abun da ya faru jiya bana a cikin hayyacina, kasan inada bad temper idan raina ya 6aci bana iya controlling kaina..." yanayin yadda yayi maganar ya Waurewa shureim kai har saida Ya juyo dakai ya kalle shi don ya tabbatar idan dagaske uncle musa ne ke yi mashi magana ba wani daban ba.

haWa ido su kayi da juna da sauri dr. Shureim ya kau da idon shi gefe Waya, hakan bai dame shi ba yaci gaba da magana cikin tausasa harshe"inaso komai ya wuce shureim, ni bana son duk wani abu da zaisa mu samu sa6ani atsakanin mu..." sai da yai wannan maganar shureim ya dube shi dakyau yace"uncle ni wannan duk ba damuwata bace, bana ru?e mutun a zuciyata, tabbas banji dadin kalaman daka jife ni da su ba, sun bata min rai, saboda ban ta6a tsammanin zaka iya furta min su ba, da ace wani na waje ne ya gaya min su bazan ji komai ba, amma kai da kanka uncle why? Saboda na fita da zeenatu yar uwata? Ko dan saboda rungumar da nayi mata wanda nikaina bada son raina nayi ba.." idanun shi cike tab da kwalla ya fada yana kallon cikin idon shi"saboda zafin kalaman daka furta min jiya ko bacci banyi ba, da bakin cikin su na kwana azuciyata" mood din fuskar Alhaji musa Ya canza sosai, kalaman shureim sun karya mashi zuciya sai yaji duk ba dadi.
Ru?o hannun shi yayi a cikin nashi ya ru?e su gam na Wan wani lokaci kafin ya fara magana a tsanake"Allah ya huci zuciyarka shureim, na gane kuskurena kuma in sha Allah zan gyara.."ya faWa yana Wan jinjina kan shi.

"Da akwai wata tambaya da kayi min ajiya, dangane da kullan da ni ke yiwa zeenatu, kace ka fara kokwanto akaina! Shureim ina son jin dalilin dayasa kace haka? Wani irin kokwantone kake yi akaina..." ba tare da jin shakkar shi ba yace"ban yarda da kullan da kake yi mata ba, raina yana bani kamar akwai wani abu da kake 6oyewa shiyasa nake kokwanto akanka, ka hanata cigaba da karatu, ka hanata yin kawance da kowa, sannan ka hana ta fita, kamar baka son kowa ya ganta, ita kanta zeenatun ta fara korafi kan kullan da kake yi.

Shiru Alhaji musa yayi tamkar bazai yi magana ba, can kuma ya saki Murmushin gefen fuska kafin yace"zan fada maka dalilin dayasa nake kullanta, in har hakan zai goge zargin da kakeyi akaina.." ya fada yana kallon shi.

Kafin ya Waura da cewa"Dalilin dayasa nake kullan zeenatu, is that I'm a famous politician with many enemies who want to harm me. Zeenatu is my weakness, bayan haka itace ?a Waya tak da nake da ita akusa dani, in har ban bata kariya ba, rayuwarta tana a cikin hatsari saboda akwai masu bin diddiginta, bana so inyi ganganci da rayuwarta, makiyana sun sha turo min sako akan zasu halaka zeenatu, shureim taya bazan killace ta agida ba"? Maganar Uncle musa tayi tasiri a cikin zuciyar shureim jikinshi yayi sanyi zuciyarshi ta karaya, hankalin shi ya tashi da jin abunda ke faruwa da rayuwar zeenatu!

"May be zeenatu ta manta bata fada maka ba, lokacin da tana zuwa high school, kusan kullum in zataje makaranta sai an samu wadanda suka kai mata farmaki, don ma Allah yasa akwai bodyguards da suke kula min da ita ay da tuni zeenatu babu ita araye" ya faWa tare da dukar da kan shi ?asa ya marairaice fuska kamar ba Alhaji musa ba.

Cikin sanyin murya Dr shureim Ya furta"Uncle, hankalina ya tashi da jin maganar nan, yanzu na fahimci dalilin dayasa kake kullanta, ni kaina bazanso abun da zai cutar da ita ba, amma kullan yayi yawa tun da har ta fara takura, bai kamata saboda wasu ahanata jin dadin rayuwarta ba, bayan haka Allah shi yake tsare bawansa aduk inda yake, kuntata rayuwarta agida bashi bane mafita ba, wlh duk tsaron dake agidan nan bazai hana a cutar da ita ba, amma idan muka cigaba dayi mata addu'a, in sha Allah makiyanka ba zasu ta6a yin nasara akanta ba!" wasa wasa dr shureim ya 6uge dayi mashi nasiha har saida ya tabbatar Ya samu nutsuwa Kafin yayi shiru yana jiran jin me zaice..

"Shureim nagode da shawararka, zanyi tunani akai in sha Allah, sannan akwai magana da nakeson yi dakai idan na samu lokaci..." bai kare maganar ba, wayar shureim ta fara ringing,
"Zan Waga kira"
"Okey, pls ka sameni a dining, zeenatu tana jiranka, tace bazata iya cin abinci in ba atare dakai ba..." jinjina kai shureim yayi bayan fitar Alhaji musa ya nufi gaban mirror ya dauki phone dinsa Ya duba sunan mai kira, mommyn su ce da sauri yayi picking ya kara a kunnanshi
Tunkafin yayi sallama muryar hajiya layla ta katse shi"shureim wai lafiya tun jiya inata kira bana samunka ko wani abu ya faru ne?

Cikin sanyin murya yace"a'a mommy, kiyi hakuri, wayar tana a kashe ne ban jima da kunnata ba"

Yanayin muryarshi ya sa ta tunanin kodai ba lafiya gidan?

"Ya jikin Benazir din? Ko har dr Ya sallame ku"

"Abun da yasa na kira ke nan, don in tuna maka, karfe 11 da rabi za'a sallame mu"

Agogo Ya kalla karfe 9, ajiyar zuciya ya sauke"In sha Allah yanzu zan shigo asibitin" amsa mashi tayi da toh, da sauri ya karasa shiryawa cikin shigar larabawa, ya Wauki facemask ya zura a aljihun shi da niyar in sun fita zai sanya ma fuskarshi, don baison mommyn su taga tabon marin da Alhaji musa yayi mashi yasan muddin tagani sai ta tada 6alli.

Adai dai lokacin daya fito daga dakin, sai ga Hajiya sarah ta kimtsa cikin riga da skirt na atampa, ta kashe daurin kallabi mayafinta akan kafada ta daura shi, ta ruke purse dinta a hannu, kasa karasawa tayi gare shi ganin tabon dake akan fuskarshi cos tun jiya da abin ya faru kowa ya shiga dakin shi basu kara haduwa ba, taji nauyin hada ido da shi duk saitaji ba dadi.

"Aunty, barka da safiya, kin tashi lafiya" fuskarshi dauke da murmushi ya nufe ta.

Tuni taji idanunta sun ciko tab da kwalla cikin sanyin murya tace"shureim ka yi hakuri da abunda ya faru jiya, wlh bakin cikine Ya hana in leko dakin ka, banji dadin ganin yadda tabon marin ya bata gefen fuskarka..."
Cikin sauri yace"pls komai ya riga daya wuce, kada ki damu kanki, lafiya kalou, ay uncle dinma yazo har daki ya bani hakuri harma mun sasanta kanmu" kallon shi kawai takeyi gwanin ban tausayi, ta dade bata ga mutumin mai saukin kai da hakuri irin dr shureim ba.
Ganin tayi tsaye tana kallon shine yasa shi furta"nayi waya da mommy ta fadamin karfe goma za'a sallame su, yakamata muyi sauri muyi breakfast sai mu wuce..." girgiza kai tayi da sauri ta share kwallar data zubo mata, tabi bayan shureim suka nufi dining
___________________________________
'?

Around karfe 10 na safe, Unaisah tana a zaune kan kujerar gaban gadon Benazir, har ta kammala shirin ta cikin abaya maroon colour, tayi rolling veil akan ta, baiwar Allah jikinta yayi sanyi, zuciyarta batayi mata dadi, sam bata son rabuwa da Benazir ta kamu da kaunarta, duk yadda take zumudin son tafiya don taga yan uwanta, saida taji ba dadi, sabo kenan turken wawa...

Gaba Waya ta shiga zurfin tunanin rabuwa da ita, benazir dake zaune gefen gadon ta ?ura mata ido tana kallon ta ko kyaftawa batayi, ta fahimci kamar wani abu yana damun yarinyar, ita kan ta faduwar gaba take ji kuma ranta yana bata kamar wani abu zai faru

"Babyna me kike tunani"! Cikin kun nanta ta tsinkayi muryar Benazir, wadda tayi silar dawo da ita daga duniyar tunanin data lula..

Numfasawa tayi a hankali take kallonta, tuni taji hawaye sun cika tab da idonta, hajiya layla tana a tsaye bakin kofar toilet tana kallon su fuskarta duk ayamutse, damuwarta halin da Benazir zata shiga idan aka raba ta da yarinyar, ita kanta ta shaku da yarinyar tana son ta, sai dai ba yadda suka iya dole su yi hakuri su rungumi kaddara.

Tattausar murmushi Unaisah ta sakar mata, tare da mi?a mata kwayar maganin dake a hannun ta"mamana ki sha maganin ki," dakyar ta ?are maganar tamkar zata fashe da kuka saboda tasan maganin bacci ne dr jazz ya bata don ta ba benazir tasha, duk don su samu tayi bacci ko sun tafi da unaisah....

Baiwar Allah Benazir kamar tasan me suke kokarin yi gabanta sai faduwa yakeyi, buWe baki tayi unaisah ta sanya mata kwayar maganin, ta kanga mata glass din ruwan hannunta ta shanye shi, ?an mintuna ?alilan Benazir ta fara gyangyaWi idanunta suka fara kokarin rurrufewa wani irin karfi maganin ke gare shi dr jazz ya iya aika aika...cikin karyayyar murya ta furta"babyna, kada ki tafi ki barni, inaji ajikina kamar tafiya zakiyi..." Wan zaro ido unaisah tayi da sauri tace"ki daina wannan maganar mamana, ina atare dake babu inda zanje" dafe kai benazir tayi da hannu Waya, dakyar take buWe idanun ta masu Wauke da matsanancin bacci ta ?urama unaisah ido cikin sanyin murya tace"dan Allah ki yafe min Angel, nasan ban kyauta maki ba, amma kada kice zakiyi fushi dani, kada ki tafi ki bar ni, wallahi ina sonki, Allah shine shaida ta bada son raina na tafi nabar ki ba, nayi maki alkawarin zan baki gatan da kika rasa na rashin uwa atare dake, zan tarairaye ki in baki kulawa Angel" a matu?ar ruWe Unaisah ke kallon Benazir, kalamanta sun ta6a mata zuciya, sun fama mata ciwon dake a zuciyar ta, amma sai tayi tunanin watakil tana sambatune akan yarta da ta rasa.

Kukane Ya kwacema Hajiya layla da sauri ta toshe bakinta da tafukan hannayenta saboda batason ta Waga masu


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login