Showing 222001 words to 225000 words out of 298130 words

Chapter 75 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

ko sallama batayi ba saboda idon ta ya rufe, yaronta kaWai takason gani muryarta na rawa ta furta"Ana! Ana! Ana...! Shiru ba'a amsa mata ba, a kan sofa ta wurgar da handbag dinta, ta nufi bedroom dinta da sauri don taga ko baby junaid na anan tana shiga ta iske dakin wayan babu kowa, fitowa tayi a fujajen ta nufi kitchen"Ana! Ana! Wai ina kika shiga ne?...." tana shiga kitchen ta taras babu kowa ranta ne ya bata kodai yana adakin Ana suna bacci"? Hakan yasa ta juya da sauri ta nufi hanyar dakin Anah

"Aunty Anila..." zahra ce ta kira sunanta, shigowarta kenan ta hango Aneelerh ta nufi dakin Ana da sauri tabi bayanta, kafin ta karaso Aneelah ta ture kofar dakin, cike dasa ran zata gansu kwance kan gado, zura kafarta keda wuya idanunta suka sauka akan gadon Ana babu kowa akai, dakin gaba Wayanshi a haukace yake kamar anyi dambe a cikin shi, fululluka har biyu ta gani kan floor, ga zanin gado a yamutse yayi uban squeezing, wani abu da ya ?ara rikirkita Anila, dressing mirror din dakin data gani ya kife ?asa, Wa'iyazubilla wani irin jiri jiri ta fara gani a cikin idanunta da wani irin azababban faduwar gaba ta ?arasa shiga ciki kamar wadda aka zare wa laka, zahra tana abiye da bayanta sai faman zare idanu sukeyi cike da tashin hankali, tun daga kan yanayin dakin suka fahimci wani mugun abunne ya faruW'


"Mun shiga uku Aunty Anila! Meya faru da dakin Ana? Ta ina? Ina baby junaid..."? AruWe zahra take magana ita Anila gaba daya rudani Ya hana ta furta kalma, jikinta na kerma tasa hannu tayi knocking toilet door din dakin cike da sa ran Ana zata amsa mata, almost 3 times tana kwankwasa kofar toilet din babu alamun za'a tanka mata ko za'a buWe kofar, da iya karfinta na karshe ta bangaje kofar da kafadarta nan take door din ta buWe a slow ta bada wani sauti kiiiiiiiiii!

Da wani irin faduwar gaba ta zura kafarta cikin toilet din, A hankali take bin ko'ina da kallo, bata ga kowa ba, sai shower da tagani a kunne ruwa yana ta kwararowa ya malale kan floor, ga faucet ma a kunne ruwan dake 6ul6ulowa ta cikin shi Ya cika sink din harya fara gangarowa ?asa.

Hankali atashe Anila da zahra suke karewa toilet din kallo..
Muryar Anila na rawa ta furta"Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un! Zahra na shiga uku? Bangan su ba! Banga baby junaid ba! Ina Ana takai shi? Ina suka shiga!...


Ru?o hannunta Zahra tayi"Auntyna ki kwantar da hankalinki, muje mu duba sauran dakunan watakil taje gyara dakin wani a cikin mu, ko kuma sun fita backyard.

Da sauri suka fito daga dakin, adai dai lokacin Su mami sun shigo suna zaune a falon suka hango zahra da Anila zasu gifta ta falon
Muryar Mami ce ta katse su"Kai Ina zuwa haka? Kusan atare suka juyo muryar Anila na rawa ta ce"mami ba mu ga Ana da baby junaid ba, su muke nema..." jin wannan maganar Yasa ummi da su Abie suka mike tsaye
Ummi tace"kun duba ko'ina"? Zahra tace"yanzu zamu karasa dubawa..." ta fada tare da ru?o hannun Anila suka nufi hanyar dakunan su Abie...

Abu kamar wasa sai da takaiga ko'ina na gidan sun duba sa?o da lungu amma ba su gan su ba, nan fa hankulan mutanan gidan Ya tashi, hatta su abie saida suka tayasu neman Ana, kowan nan su Ya hada uban gumi kan fuskarshi, sai da suka tabbatar babu su agidan sannan suka dawo falo suka tsaya cirko cirko.

Fuskar mami A yamutse ta furta"to ina suka shiga ne? Ko dai sun fita daga gidan ne? Ummi tace"nima abun da nake tunani kenan, watakil ta fita da shi"


Abie ne Yace"bari nayi magana da baba mai gadi, in ma fitar su kayi zamuji a wurin shi, A hanzarce Ya fuce daga falon Uncle dan Iya yabi bayan shi da sauri.

Baiwar Allah Aneelarh, tafi kowa jin jiki, kwata kwata babu nutsuwa atare da ita gaba Waya ta gama sarewa, tana zaune kan sofa, hannayenta biyu daddafe da kanta, tsantsar tashin hankaline da fargaba akan fuskarta.

Zahra dake a gefenta itama damuwarce akan fuskarta, ta dafa kafaWar Anila tana kokarin kwantar mata da hankali, ganin yadda ta canza fuskarta tayi jawur cheeks dinta har kerma suke, dama abunda take ta zullumi kenan, tunkafin barinsu gidan hankalinta bai kwanta da yanayin da taga Anah ba! shiyasa take ta jin faduwar gaba dama sau dayawa in wani abu zai faru da bawa Allah na bashi haske kan al'amarin.

Mai gadi na zaune kan kujera Ya kure sautin radio dinshi, sam baiji Kiran da su Abie suke kwala mashi ba, har saida suka karaso gaban kujerar tukunna ya lura da su, da sauri Ya kashe radio din Ya mi?e yana kallon su

"Bayan fitar mu daga gidan nan! Wani ya ?ara fita ne"? Abie ne ya jafa mashi tambayar, girgiza kai yayi"yalla6ai babu wanda Ya fita..." can kuma yace au na tuna Mahboob ya dawo tare da junaidu, bayan shigar shi ina zaune sai ga mahbob ya fito ya shiga mota ya fuce, bayan shi babu wanda Ya ?ara fita...." bai kare maganar ba Uncle Wan iya ya tari numfashi shi da cewa"kana nufin baga ka lokacin da Ana ta fita da junaid ba..." girgiza kai baba mai gadi yayi yace"a'a gaskiya ni banga gifcinsu ba, Ina zaune na kasa na tsare ko sauro bai isa Ya haura gate din nan batare dana kama shi ba..." hankali atashe Abie da uncle dan iya suka kalli Juna.

"Yalla6ai wani abu ya faru ne"? Baba mai gadi ne yayi tambayar ganin kamar damuwa akan fuskokinsu...
Abie ne ya zayyana mashi abunda ke faru, baba mai gadi yace"ikon Allah! Amma yalla6ai kun duba ko'ina? Saboda wallahi ni banga fitarsu ba, Allah shine shaidata, ko gyangyadin bacci banyi ba, lokacin sallah kadai ke tada ni, kuma sallar ma abakin gate din nayita...." ba su tsaya jin karashen maganar shi ba, da sauri suka koma falon gidan, su mami na ganinsu suka mike har suna hada baki wurin tambayar abunda me ganin yace Abie ne ya kora masu jawabi.

Kaf a kunnan Anila lokaci Waya ta rushe da kuka tana fadin"inna lillahi wa'inna ilahirraji"un..." daga kan sofa ta sauko kan floor ta zauna dirshan, taci gaba da kuka"wallahi saida raina ya bani wani abu zai faru da su, tun lokacin da muka bar gidan nan naketa jin faduwar gaba, ashe wani abu ne zai faru da junaid dina, na shiga uku mami ku taimaka mun! Ku nemo min Ana ta kawo junaid dina.."!! Da sauri Zahra ta rungumota a kirjinta, ta cigaba da lallashinta..ita kanta zahran kukan ne ke shirin kubce mata.

"Haba Anila meye abun kuka? Kamar dai bakiyi tawakkali ba? Wayace maki wani abu ya faru da su? Uncle Wan iyane ya fara mata magana cikin tausasa harshe.

Ummi tace"ni abunda nake tunani kodai Mahboob ne Ya fita da su yakamata akira shi aji" da sauri Abie ya zaro waya ya danna ma mahboob kira yana dagawa ko sallamar shi abie bai amsa ba yace"mahboob kana ina"?

On the other hand mahboob yace"ina akan hanyar dawowa gida..."

"Ana tana atare dakai"?

Da mamaki mahboob yace"ana kuma abie? Ba tana agida ba? Ko bata nan ne"?
Katse kiran Abie yayi, tare da kallon su mami dake kallon shi
"Baya atare da su..." sautin kukan Anila ne Ya ?ara karaWe kunnuwansu...
Mami tace"amma abun da daure kai! Ina Ana taje da shi? Ke zahra kira layin Ana muji..." sai yanzu dabarar kiranta yazo masu arai, cikin shesshekar kuka Anila tace"ko kun kira akashe zaku same ta, tun muna agidan hajiya adama inata kira baya shiga.." Zahra tace"bari dai a akara kira watakil ta kunna wayar" ta fada tare da zaro waya ta danna ma Anah kira, nan take aka sanar da ita wayar akashe take, nan fa hankalinsu Ya ?ara tashi, Cire hula abie yayi zufa ta ko'ina ta fara tsastsafo mashi ta kan goshin shi, idanun mami tuni sun rune sun koma Ja, al'amarin yayi matu?ar Waga hankulan su

fashewa zahra tayi da kuka tana fadin"Allah yasa Ana ba guduwa tayi da baby junaid ba! Raina yana bani itace ta gudu da shi..." cikin shesshekar kuka Anila tace"ni bana zargin Ana, bazata ta6a daukar min babay junaid ba, na yarda da ita sai dai idan wani abunne ya faru da su duka biyun."

Ummi tace"Anila raba kanki da Wan adam ba abun yarda bane, na jikinki ma zai iya cutar dakai balle ita da take yar aiki bare, Allah kadai yasan meya faru! Ina suka shiga"?

Girgiza kai mami tayi hawaye nabin kuncinta tace"dan Allah ku daina waWannan maganganun, dukkan mu babu wanda yasan meya faru da su? Ko ina suka shiga, bai kamata mu yanke mata hukunci batare da mun san ainihin abunda ya faru ba, dududu ba yanzu muka dawo ba, mu Wanyi hakuri kafin dare yayi watakil ta dawo da shi, mu kyautata mata zato dan Allah..." dakyar ta kare maganar daurewa kawai takeyi

Ita dai ummi hankalinta bai kwanta da Ana ba, tafi zargin itace ta gudu da junaid, dama tun lokacin da ta fada masu tana yin mummunan mafarki tafara zarginta, yanzu gashi ta 6ace babu ita ba junaid, wama yasani ko yar kungiyar asiri ce shiyasa ta sace shi har baba mai gadi baisan da fitar su ba.

Ta dai bar abun a zuciyarta gudun kada ta daga masu hankali

"Anya baba mai gadi gaskiya ya fadi? Taya za'ay su fita batare da sanin shi ba? Ga shi mun duba ko'ina babu su babu alamar su! In har bata kofar gate suka fita ba ay babu wata kofa da mutun zai iya fita daga gidan nan in ba dai 6acewa tayi da shi ba kamar yadda naga yan kungiyar asiri sunayi"

Maganar ummi ba karamin firgitar da su tayi ba, cak Anila ta dakata da yin shesshekar kukan Idanunta jawur ta dubi ummi"bangane me kike nufi ba ummi! Dan Allah ki fahimtar dani!" kafin ummi ta buWe baki, Uncle dan Iya ya wurga mata harara, Rai a6ace yace"baki da hankali ne? Ko so kike zuciyarta ta buga ne? meya kawo wannan maganar? Maimakon ki kwantar mata da hankali saima kara dagula mata tunani kike kokarinyi! Wallahi kar in kuskura in kara jin bakinki!!" faWa sosai yakama yi mata kamar zai rufeta da bugu, har saida Abie ya dakatar da shi kafin suka samu yayi shiru.

Mi?ewa Anila tayi, zuciyarta ta karaya, jikinta yayi mugun sanyi, ga wani azababben zazza6i da ciwon kai mai raWaWi da tafara ji, gaba Waya suka bita da kallo ganin ta mi?i hanyar fita daga falo kamar bata a cikin hayyacin ta.

da sauri Abie yabi bayanta ya dam?i hannunta fashe wa tayi da kuka tamkar ranta zai fita tadinga kokarin ?wace kanta tana sambatu cikin fitar hayyaci ta furta"wayyo Allahna abie, dan Allah ka sake ni inje in nemo baby junaid dina, bana so na rasa shi, bana so acutar min da shi, kabarni abie, Junaid shi kadai ne jinin uzair da nake da shi, idan na rasa shi bansan inda zan tsoma raina ba..."

Tana cikin yin magana ta sar?e kwatsam ta yanke jiki zata faWi da sauri abie ya kwanto da ita kan kirjin shi, sai lokaci mami ta fashe da kuka kalaman Anila sun karya mata zuciya, zahra ma kukan takeyi haka itama ummi gida ya zama kamar na masu zaman makoki, adai dai lokacin mahboob ya shigo falon ko sallama baiyi ba sautin koke kokensu Ya cika kunnuwanshi, hankali atashe ya karasa shiga ciki yana faman raba idanu akansu, arude yake fadin mami! Ummi! Zahra! Me..me ya faru? Daddy..bai kaiga kiran sunan abie ba yai arba da anila wadda ke rungume jikin abie, kamar ba numfashi atare da ita, tsabar kiWima Yasa mahboob sakin key din hannun shi ya faWi ?asa.

La66ansa na kerma ya furta"dan Allah kuyi min bayani meya faru kuke kuka? Meke damun Aunty Aneelerh?

dakyar Zahra ta shanye kukanta muryarta a disashe ta kwashe komai ta sanar da maboob da buWar bakinsa sai cewa yayi"ban yarda ba, wallahi bazai yiwu ba! Ni da kaina na Wauko yaron nan daga school kafin ma mu iso gida bacci ya dauke shi, bayan nayi parking din motata na goyo shi abayana na shigo da shi cikin gidan banga kowa ba a falo, raina ya bani watakil kun tafin unguwar da naji kunce zaku je, sai na wuce da shi dakin Ana, bayan nayi knocking din kofar ta buWe min naga idanunta jawur kamar daga bacci ta tashi, har na tambayeta ina mutanan gidan tace min ai kun tafi tun Wazu, sai na mi?a mata junaid nace ta kwantar da shi idan ya tashi daga bacci ta yi mashi wanka ta bashi abinci, ta amsa min da toh, ta tambaye ni ni bazan ci abincin bane nace mata sauri nake zan tafi kallon match idan na fita zan tsaya agidan su abokina zanci acan, mukayi sallama da ita na juya cikin sauri har nakusa fita falon naji ta kwala min kira na jiyo na kalle ta, a lokacin ta rungume junaid dake bacci a kirjinta, ganin tana kallona da murmushi akan fuskarta yasa nace mata lafiya? Ko akwai wani abu da take son fadamin ne? Ta girgiza min kai tace a'a wai nayi mata kyau ne, bance mata komai ba, na dai Waga mata hannu na mayar mata da martanin murmushin da tayi min kafin nasakai na fuce daga gidan...." gaba Waya su mami sun kasa kunne suna sauraron mahboob dake basu labarin rabuwar shi da Ana har yakai karshe.

"Tayaya za ku ce min ba ku gan su ba fisabilillahi? Idanunshi cike tab da kwalla yayi maganr, duk da bai tabbatar da abunda suka fada mashi ba, amma zuciyarshi ta karaya dama tunda ya damka ma Ana amanar junaid ya fita daga gidan yake ta jin wani iri, idanunshi suka dinga tariyo mashi murmushin da ta sakar mashi.


Zahara tace"wallahi mahboob babu su, ko'ina mun duba, ba Ana ba baby junaid, ni abunda ya daure min kai, dakin Ana da muka gani a haukace babu gyara, duk an jefar da pillows ?asa dressing mirror dinta ya kife ?asa, daga gani wani abunne ya faru, maganar zahra ta ?ara jefasu a rudani...."

Girgiza kai mahboob yayi cikin tashin hankali ya watsa da gudu ya nufi dakin Ana, don ya gane ma idon shi kafin fitowar shi Abie ya kwantar da aneelerh kan doguwar sofa, mami ta Wauko robar ruwa a fridge mai sanyi ta buWe murfin ta yayyafa mata akan fuskarta, dogon numfashi taja tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, a hankali ta buWe idanunta waWanda suka kaWa jawur ta dubi fuskokin su, biji biji take ganin su da?yar ta iya motsa la66anta da suke bushe ?amas ta furta"mami ina junaid Wina? Ana ta dawo min da shi"

shiru sukayi fargaban halin da zata shiga ya hana wani ya bata amsar tambayarta...
Abie ne yai karfin halin furta"kiyi hakuri Anila, basu dawo ba, amma yanzu zamu tafi neman su, in sha Allah zamu dawo maki da yaronki..." runtse idanunta tayi wasu irin zafafan hawaye suka wanke fuskarta...fitowa mahboob yayi daga dakin Ana yana tafiya kafafun shi suna harWewa saboda rashin kwanciyar hankali, dawowa cikin falon yayi ya tsaya yana kallon fuskokin su.

"Zahra kun kira layin Ana Win"? Waga mashi kai tay"mun kira akashe" tsoki Ya buga tare da ru?e qugun shi kafin wani ya kara magana a cikin su, sautin kiran sallar magrib Ya karaWe kunnuwan su
Uncle Wan iya yace"dan Allah ku kwantar da hankalinku, in sha Allh zasu bayyana cikin koshin lafiya, yanzu ku je kuyi sallah kuyi masu addu'a duk inda suke Allah Ya kare mana su, in sha Allah idan muka fita zamu bi gidajen makwabta mu duba watakil adace ko sun shiga ciki"


__________________________________
'?


*=؋?UNAISAH ANGEL=ؓ?*


Wunin ranar Unaisah bata jin dadin jikin ta, kamar mai fama da zazzabi tun da idanunta sukayi tozali da zeenatu bata ?ara samun nutsuwa ba, Yarinyar ta tsaya mata aranta tunanin zeenatu yayi mata ?atutu a cikin zuciyarta, ta rasa meyasa take ta faWo mata aranta, har takai ga da zarar ta rufe idanunta fuskar Zeenatu take gani.

Tana akwance kan darduma wani guntun baccine Ya Wauketa bayan ta kammala sallar magrib, gaba daya ta kudundune kanta cikin hijab....

Benazir tana zaune gefen gadonta tana ta kallon ta, yayin da hajiya layla ke azaune kan sofa..

"Benazir..." dagowa tayi tare da kallon mami data ambaci sunan ta, kallon kallo suka shiga jefawa junansu, tuni benazir tasha jinin jikinta, dama tun dazu da abun nan ya faru na zuwan zeenatu ta lura da irin kallon da mami takeyi mata ga wani annurin farin ciki da take gani atare da ita...

"Ya jikin naki? Wazu naga kamar kin samu lafiya.."

shiru tayi jim tana tunanin ta yadda zata 6ullowa mommyn nasu don bata shirya bayyana masu ta samu lafiya ba, tana da dalilinta nayin haka..


Jin tayi shiru yasa mami ta sake furta"dake fa nake magana? Hannu tasa ta Wan sosa gashin kanta tare da kyafkyafta idanunta irin yadda masu tabin hankali sukeyi sam ta kasa buWe baki tayi magana, hajiya layla ta kura mata ido tana kallon ta, ta Wan rude da yanayin ta aranta ta ayyana ko dai har yanzu da sauranta"?

"Mami ina baby na? Ban ganta ba? ta faWa tare da saukowa daga kan gadon ta fara Waga pillow tana nemanta, hada kokarin yaye zanin gado duk don tayi pretending kada hajiya layla ta gane ta samu lafiya.

Shesshekar kukan karya ta farayi hada yarfa hannu ta juyo ta kalli hajiya layla da ta saki baki sototo tana kallon ta.

"Mami kodai wani ya sace min ita ne? na duba banganta ba.." abun ya Waurewa hajiya layla kai, yanzu fa take zaune tana kallon yarinyar amma farat Waya ta nuna bata ganta ba.

Jinjina kai tayi aranta ta ayyana lallai haryanzu da sauranta, ganin yadda tabi ta ruWe ne yasa mami yin saurin kiran sunan ta, a hautsine ta juyo tare da kallon ta
"Gata nan a kwance kan darduma.." girgiza kai tayi"mami ba itace ba, wannan ?atuwa ce, babyna karama ce" waro ido waje mami tayi can kuma tayi tunani kodai don taganta nannaWe cikin hijabine, mikewa hajiya layla tayi taje gaban prayer mat din, a hankali ta cire ma Unaisah hijabin


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login