Showing 57001 words to 60000 words out of 298130 words

Chapter 20 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

suke, Hajiya laurat ta rafka salati tana fadin"wa nake gani kamar Harriet ?ar aikin gidan baba obie" ta kira ta ne da ainihin sunan ta, gaba Waya suka Wago suna kallonta, Hadimar data rakota Harta Juya ta nufi hanyar komawa gidan, Jiki asanyaye turai take tafiya tana tunkarar su.

Wani irin Matsiyacin kallo Hajiya laurat da Hajiya saratu suke watsa mata.

Tuni tasha jinin jikinta, da hannu Hajiya laurat ta nunata"ke! meya kawo ki nan? Ko kinga sa'ar Yin ki ne"

Shiru tayi bata tanka mata ba, Hajiya saratu ta kwashe da dariya Tana fadin"shisshigine da kutsu irin na Wan talaka, malama wani tsautsayinne ya kawo ki wurinmu? Ko aiko ki akayi don ki yi mana hidima ne"?

Cike da sha?iyanci her excellency Muhibbat tace"jibarta kamar wata mutuniyar kirki, ita kanta ta raina kanta shiyasa take jin shakkar shiga cikin mu, Ni wlh bansan me mubarak Ya gani a jikinta da har Ya aureta ba, in banda hasken fatarta da gashin da take da shi, Mace kullum kamar ana Wibar namanta ana miya da shi, babu ?iba babu tsawo, Duk arzi?in da take ci," Dariya suka sanya, mutun ukune basu tanka mata ba, Gimbiya mujeedat da hajiya malikat sai Hajiya madina. Sauran sune hatsabiban.
Hajiya Jamila tace"ai auran nata da yayi bana Allah da annabi bane wama yasani kota asirce shine, saboda Sir mubarak yafi ?arfinta nesa ba kusa ba, Babban gorone, Shiyasa ta nace mashi don aci arzi?i, don Ma Allah Yasa bata ta6a haihuwa da shi ba, sai dai taci ta zubda.... " Hankalin turai ba ?aramin tashi yayi ba, Jin cin mutuncin da suke Yi mata, Tuni hawaye sun soma wanke fuskarta.
Hakan ba ?aramin daWi yayima hajiya laurat ba, Ita dama burinta takala Ya ?untata.

"Nifa Har yanzu ban daina zargin Yaron nan nata shege bane, tun da bashi da uba, ahaka tazo da shi aiki gidanmu daga ?asar england, matar nan muguwar munafuka ce, babu Allah aranta, Allah kadai Yasan ma?ar?ashiyar da take kulla mana" zaro ido waje Hajiya turai tayi jin abunda Saratu take fadi, Maganar ta ?ona mata ranta, zuciyarta har wani tafarfasa take Yi sam takasa buWe baki ta dakatar da su, sai dai binsu da take Yi da idanu.

"Gobe kada in kuskura Inga ?eyarki awurin taron shagalin dinner din da za'ayi na Hateem, Idan ba haka ba agaban idon kowa zan watsa maki ruwan lemu akan fuskarki" Hajiya laurat ce ta fada tana nuna ta da cup din hannunta.

"Dake da wannan Wayar munafukan meye ma sunanta"? Da sauri hajiya saratu tace"hajjaty" hajiya laurat tace"yawwa ita nake nufi, uwar iyayi, mai shafa turaren ?an bori, ku biyun nan bamu bu?atarku a family din nan don kawai ba yadda zamuyi daku ne amma very soon zamu yi maku korar kare" ta faWa tana sakar mata shu'umin murmushi.

Fashewa Turai tayi da kuka mai cin rai, kamar an ru?e mata ?afafuwanta takasa tafiya tabar wurin su.

Gyaran murya Gimbiya Malikat tayi masu, gaba Waya suka kalleta.

"Ba girmanku bane, kun bani Kunya, ni banga amfanin maganar da kuke gaya mata ba, ku kama mutunci ku mana" rai 6ace ta furta maganar, babu wasa a fuskarta.

Sai lokacin Gimbiya Mujeedat ta buWe baki cikin nutsastsiyar muryarta ta furta Sunan turai.

Baiwar Allah muryarta na rawa ta amsa mata da na'am.

"Zo ki zauna kusa dani" ta fada tana nuna mata gefenta.

rai a6ace Laurat da muhibbat suka mi?e tsaye suna fadin Allah Ya kiyaye su haWa kafada da ita, Indai turai zata zauna sai dai su su tafi" ko kallon su mujeedat batayi ba.
Muryar turai da shesshe?ar kuka tace"bazan Iya zama ba Aunty mujeedat, bana so na shiga tsakaninku, ni zan tafi kawai, dama yaya mubarak ne Yace in zo wurinki don inyi maki bangajiyar tafiyar da ku ka yi, don haka zan tafi tun da naganki..... " tana ?arasa maganar, ta juyawa da sauri ta nufi hanyar fita daga garden din.

Zuciyar Gimbiya mujeedat ta sosu, ranta ya 6aci da kalaman da Su laurat sukayi ma Turai.
Yun?urawa tayi tare da mi?ewa tsaye tana gyara rigarta,
Har suna hada baki wurin tambayarta ina zataje?
Batare da dube su ba tace"zan shiga cikine, nagode da ziyara sai mun haWu gobe idan Allah yakaimu" Ta fada tare da kallon Gimbiya malikat tace"mu shiga daga ciki," mi?ewa hajiya malika tayi suka ru?e hannun juna atare suka nufi cikin gidan.

Bayan tafiyar su, Tsoki Hajiya laurat taja tana fadin"wannan munafukar matar duk itace taja mana, Muna zaman mu lafiya, ta tarwatsa mana farin cikin mu"
Hajiya Jamila tace"Halin talakan kenan, Yanzu gashi tasa Ran gimbiya mujeedat Ya 6aci"
Hajiya saratu tace"banji dadi ba wallahi, amma nasan ta inda zan rama, Allah yakaimu gobe lafiya, Idan har matarcan ta kuskura ta zo dinner din ya hateem jikinta zai gaya mata sai nayi mata abun da bata ta6a tsammani ba" ta faWa tana faman haWe fuskarta, Sun jima a garden din kafin daga bisani kowaccensu ta shiga motarta suka nufi gidajensu.

Baiwar Allah Hajiya turai tana azaune cikin motar Sir mubarak, tasha kuka tamkar ranta zai fita tayi danasanin zuwa gidan prime minister, kalaman su sun ?ona mata rai, musamman da hajiya saratu ta ambaci jazz da sunan shegene, tayi alkawarin bazata fadama sir mubarak abunda suka gaya mata ba, don kuwa idan yaji sai sun yabama aya zakinta.

_______________________
'?

Baka jin sautin komai a falon tamkar babu mutane acikinsa, alhalin nan kuwa Suna zaune kowa Ya hakimce abun sa, tsabar miskilanci ne Yasa basa iya buWe baki su tanka ma Junan su, Kowannan su da abunda Ya Wauke mashi hankali, fitowa Dr jazz yayi daga bedroom dinsa ya kimtsa kanshi cikin shadda launin blue sky abunka ga farar fata ta ?ara fiddo mashi da hasken shi, ga wani daddaWan ?amshin turarensa dake fesowa, Ya gyara sumar kanshi hannun shi Waya ru?e da key din motarsa, wani irin annurin farin cikine akan kyakkyawar fuskarshi ga dukkan alamu akwai wani abu daya faranta mashi rai.

kafin Ya ?arasa cikin falon, Idanunsa suka hango ma sa Matasan Samarin Family din dake zaune saman sofas Har sai da gabanshi Ya faWi da idanunsa suka yi mashi tozali da su, Baisan da zuwansu ba, aranshi ya ayyana to fa ashe yau muna da manyan ba?i a gidan na mu ba, meyasa Ibad bai faWa min sunzo gidan nan ba? Ya ?arasa zancen zucin nashi cike da jin fagabar tunkararsu, Ya kasa motsa ?afafuwanshi Ya tsaya atsaye kamar wanda aka yi mashi Iyaka da shiga falon, Waya bayan Waya ya soma bin su da kallo, Zaki Yana a azaune saman 2 seater Yayin da Apple Laptop dinsa ke akan Table din gabansa, Gaba Waya ya tattara hankalin shi akanta yayin da yake operating dinta atsanake, Short ne a jikin shi tare da Denim shirt tabi shape dinsa, Kau da idanunsa yai daga kan Zaki Ya mayar da su kan Wani Matashin saurayi fari Sol, fatarshi ko ?warzane babu, Ga wata nannaWaWWiyar sumar kai dark brown, kai daga ganinsa wani shege ne mai ji da naira, Allah yayi shi da kyau mai jan Hankali, Jallabiya ce a jikin shi launin grey, ta zauna mashi sosai, bakowa bane wannan face Captain YASEER Wan gidan His Excellency Abdul Razak da Her Excellency Muhibbat shuwa arab ne kamannin shi sak dana su Chief Owais, banbancin su launin fatane dana Ido, hannun shi ru?e da Expensive phone dinsa da yake daddanawa da zira ziran yatsun hannunsa, yayin da Justice Nadeem Wan gidan His excellency Deen Yake a kishingide kan doguwar Sofa, Ya zagayo da hannun shi Waya saman forehead dinsa, idanunsa suna a lumshe tamkar mai yin bacci.

Ziyad ne kaWai yake a zaune saman lallausan Carpet din dake a shimfiWe tsakiyar Sofa set din falon, faffaWan farantin da aka kawo masu fresh fruit acikinsa ya tasa a gaba yana shan kayan marmari, duk acikin su Ziyad yafi su sau?in kai kasancewarshi Wan jarida da son labari, A yanzu haka da yake a zaune cikinsu A takure yake jin kanshi sun?i sakar mashi fuska su yi fira kowa Ya kama harkar gabanshi shiyasa ya sauko kan carpet yaci gaba da shan kayan marmari.

?amshin turarensu Ya gauraye Falon, Jazz dake kallon su ba ?aramin burge shi su ke yi ba, ba tun yau ba Yana son Yaga jikokin Baba Obie sun haWu suna sada zumunci aranshi sai yaji inama ace shima Jikan Baba obie ne da Allah ne kaWai Yasan irin Farin cikin da zaiyi a duniyar nan.

Ganin basu lura da shigowarshi falon bane yasa shi yin saurin tafiya cikin sanWa Ya nufi ?ofa Ya fuce daga ciki Yana faman sauke ajiyar zuciya, da sauri Ya nufi Harabar Ajiye motocinsu, Ya buWe motarshi Ya shiga daga Ciki, tare dayi mata key, zuciyarshi acike fal da tunaninta, fatan shi Allah yasa wannan karan ta kula shi.
Yana driving fuskarshi dauke da annurin farin ciki, A haka Ya nufi Gidan baba obie.

Ganin shirun nasu bamai ?arewa bane, Yasa shi mi?ewa, Ya nufi Zaki Ya sanya hannu ya Wauke laptop din da yake dannawa, Ya juya Ya nufi Captain Yaseer Ya kar6e wayarshi, kafin Ya tunkari justice Nadeem Ya sanya hannu Ya kamo Hancinshi Yaja Shi da karfi har sai da Justice Nadeem Ya buWe idanunshi dake dauke da bacci Fuskarshi adaure yake kallon Ziyad.

Harara Ziyad Ya watsa masu Ranshi a6ace yace"wai meke damunku ne? Kullum muka haWu kamar wasu kurame babu mai magana kowa ya kama harkar gabansa? Haka ake zumunci? Ni banga amfanin kirana wurin nan donmu haWu ba.... " gaba Waya sun Waura idanunsu kan fuskarshi babu alamun zasu tanka mashi.

Guntun tsoki Yaja"kun wani zuba mun idanu kuna kallona wato ni ga shashasha"
Yamutsa fuska Zaki yayi tare da mi?a mashi hannu yace"Bani laptop dina ziyad"
"Ta ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~??arfi ce zoka kwata" A faWace Ya faWa Yana haWe mashi fuska.

Murmushi gefen fuska Zaki Ya sakar mashi.

"Meye damuwarka"? Ya tambaya yana faman lumshe idanunsa.

"Damuwata shine ku bani aron hankalin ku muyi fira kan abunda ya shafi rayuwarmu, daga gobe fa shikenan kowannanku zai koma inda Yake rayuwarsa, yawanci ba akasar nan kuke zaune ba why ba zamu kula juna yadda ya dace ba? Bamu da tabbacin ko zamu sake haduwa da junanmu"

Yanayin yadda yayi masu maganar Ya ta6a zuciyoyinsu,

In a calm voice Zaki Ya furta"In sha Allah zamu sake haWuwa, Yanzu dai ka yi ha?uri, Ka zauna mu yi fira"

Ta6e baki Ziyad yayi, kafin Ya koma Ya zauna, Batare daya mi?a masu Kayansu daya kar6a ba.

"Bro, Ni bansan ta yadda zan fara firar bane, ko zaka taimaka mana da abun da zamu tattauna akai"? Captain ne Ya faWa Tamkar baison furta maganar, justice Nadeem dake a kishingiWe tuni Ya gyara zama saman Sofa Yana duban su

"Me zai hana Mu yi magana dangane da matayen da muke da burin aure"? Acewar ziyad.

kallon Harara Captain Ya watsa mashi"mu yi magana kan abu mai mahimmanci, Idan ba haka ba zan ja baki na nayi shiru"!

"Aure shi yafi komai mahimmanci domin kuwa Sunna ce mai karfi ta Manzon Allah SAW, Allah Ya bamu komai da zamu bu?ata, Kowannanmu Yana da aikin yi, Aure shi ya rage mana yakamata ku yi tunani yanzu fa lokaci ne da zamu more rayuwarmu, mu ma yi aure mu hayayyafa kamar yadda Iyayen mu suka yi.... " Ziyad ne ya kora masu jawabi.

"Look, Ni aure baya a gabana yanzu, har yau banga macen data kwanta min arai na ba, tun lokacin dana rasa wadda nake da burin aure naji matan ma sun fitarmin araina"

Justice Nadeem dake kallon Captain Ya saki murmushi tare da cewa"Ai ba ita kadai bace mace a family dinmu ba, Kai ma kaso ka wahalar da kanka, Ai ni tun lokacin dana fahimci macace mai izza da ji da kai, na sanyama zuciyata salama, saboda bana son macen da namiji bai isa yayi iko da ita ba, ba zata yi dadin zaman aure ba, kwara wadda zaka Iya juyawa son ranka ba wadda zaka dinga jin fargaban tunkararta ba"

Ziyad yace"ka faWi gaskiya mutumina, ita fa gaba Waya namiji ma baya agabanta, bata da burin yin aure, kai ma mai yaja maka yin dakon soyayyarta? Bayan Ga matasan ?an mata nan masu jini a jika a family namu.... " kafin Ziyad ya ?are maganar, Zaki yai gyaran murya tare da cewa"wai kuna Nufin Nazli"? ?aga mashi gira Nadeem yai, matashin murmushi ya saki kafin yace"Kuna nufin bakusan ala?ar dake a tsakaninta da chief Owais namu ba"? Atare suka haWa baki wurin furta meke nan"?

Jim ya Wanyi kafin Ya furta"Uncle Hateem, Ya riga daya mallaka mashi ita, bata da wani miji daya wuce shi a duniyar nan, tun kafin tazo duniya, wannan al?awarine dake atsakanin Uncle sharafudeen da uncle Hateem, zasu haWa auran ?a'?ansu... " da mamaki suke kallon shi
Ziyad yace"amma ni banta6a ganin alamun suna kula junansu da sunan soyayya ba, Ko ranar Birthday din grandfa da suka haWu ko kallo ba su wa junansu ba"
"Dama taya za'ai su kula juna?bayan kowannansu Yana ji da kanshi daga ita har shi Owais din, duk abunda take ta?ama da shi shima Yana da shi, gaskiya Uncle sharafudeen da Hateem basu yi tunani mai kyau ba, bayan sanin cewa Izza A jinin su take, tayaya Nazli zata yi mashi biyayya amatsayin matarshi? Justice Nadeem ne yayi maganar.

Captain da ke sauraransa fuskarshi babu annuri babu walwala ya furta"da ace nasan da zancen nan da tuntuni na cireta araina, dama ni ba Iyawa zanyi da ita ba, owais din shi yafi dacewa da ita, suje can su ?arata," Ya faWa tare da jingine kanshi jikin Sofa.

Shiru suka yi na Wan wani lokaci, babu wanda Ya furta magana sai daga bisani Justice nadeem Ya furta"Zaki Ina budurwarka ta Canada Kyakkyawar balarabiyar nan"

Da zolaya ya faWa yana duban shi.
Kallo ya jefa mashi mai kama da harara kafin Ya furta"ta koma gidan su"
Zaro ido justice Nadeem yayi"me? Kana nufin tabar gidanka"
?aga mashi gira yai alamar eh,
"But why"?
Bai cika son tada maganarta ba, saboda hakan Yana fama mashi raunin dake a zuciyarshi.
Cikin sanyin murya ya furta"bansan meyasa ba, rana Waya ta haukace min ta soma kokarin juya min ba, badan naso ba nabarta ta dawo Nigeria"
Justice Yace"banji dadi ba, me zai hana ka nemi gidansu inyaso saika gabatar da kanka wurin Iyayenta"?
Murmushin takaicin Zaki yayi"tana da aure har da ?arta, ban ta6a fada maka bane"
Jin wannan maganar Yasa Captain ware manyan idanunshi, hatta Ziyad dake sauraransu saida Ya zaro ido da alamun mamakin kalaman Zaki
A ruWe justice Nadeem ya maimaita maganarshi"tana da aure har da ?a? Amma ta zauna a gidanka tsawon shekaru tamkar ma'aurata? Kafin Ya ?are maganar Captain Yace"tayaya hakan zai yiwu? Nima fa nasan Matar duk lokacin da zanje canada a gidan ka nake taras da ita, nayi tsammanin ?ar aikin ka ce, shiyasa ban ta6a kawo ma raina wani abu ba,"

Girgiza kai Zaki yayi"ba ?ar aikina bace, Taimakon ta nayi, na ru?e ta agidana saboda ta nuna min bata da kowa bayan mun fara sha?uwa take bani labarinta, Hankalina Ya tashi jin cewa tana da aure, amma agidana mijinta ya tura mata da sakon saki, ganin hakan yasa muka cigaba da yin rayuwarmu, naso ta amince min in aure ta saboda bani da burin daya wuce na mallake ta, nasan tana sona sai dai tafi ?aunar takomama mijinta saboda ?arta da tabar mashi"

Gaba Waya sun lura da canzawarshi, hakan Ya ?ara tabbatar masu da irin kaunar da yake yi mata.

Mi?ewa yayi da sauri Ya nufi bedroom dinshi, Da sauri justice Yabi bayanshi, Yana Shiga Ya zura hannayenshi cikin aljihun short dinshi, Yayin da zuciyarshi ke cigaba da tafarfasa

"Bana so hakan Ya dame ka, Yarinyar nan ko tana so ko bata so, Kai ne mijinta, Saboda kafi cutuwa, Tsawon shekara goma sha shidda kuna rayuwa agida Waya tamkar ma'aurata? Ka raineta ka kashe mata ma?udan kudi, Idan har ta butulce maka Allah ma bazai barta ba"

Justice ne yayi maganar, yana daga tsaye abayanshi
"Duk abunda nayi mata nayi ne don Allah..." kafin Ya ?are maganar justice yace"nasan don Allah kayi mata amma wallahi bazan bari ta karya maka zuciya ba, tun da nake da kai baka ta6a nuna kana son wata ?a mace ba, sai akanta, don haka dole ta aure ka, shi kuma mijinta Ya ha?ura ya nemi wata, nasan ma yayi auranshi tun da jimawa"
Juyawo Zaki yayi idanunsa akan justice Yace"nagode da kulawarka agare ni, amma mubar maganar, saboda hakan bamai yiwuwa bane, Ni bazan tursasa mata akan ta so ni ba, ta Wauke ni tamkar yayanta tana girmamani, tun da nake da ita ban ta6a nuna mata inasonta da aure ba itama haka "
"Ita ai ba makauniya bace, in ba kaiba wani namijine zai dauki dawainiyar baligar mace kamarta almost 16years, idan bazan manta ba, lokacin da naje gidanka a canada, ina lura da duk wani motsinku, Idan ka shiga daki da dare zaka kwanta tana binka bata fitowa har saita tabbatar da kayi bacci take fitowa, kaima kuma haka, sannan baka Iya cin abinci idan ba atare da ita ba, itama haka, kana nufin wani abu bai ta6a shiga tsakaninku ba"? ya faWa yana bin sa da kallon tuhuma.

"Nadeem, Ba abunda kake tunani bane, nasan nayi kuskure na ajiye macen da ba muharramata ba a gidana, amma wallahi ban ta6a shigarta ba..... " muryarshi na rawa ya ?are maganar, wani irin yanayi yake jin kanshi tunawa da rayuwarshi da ita.

Numfashi yaja kafin yaci gaba dacewa"Ta saba min da kanta, komai ita take yi min, bansan menene so ba sai akanta, ban fara muradin yin aure ba sai akanta, ashe ita din ba


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login