Showing 285001 words to 288000 words out of 298130 words

Chapter 96 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

argue with him, He doesn't know anything, We need to persuade him gently." cikin tausasa murya ya faWa yana kallon fuskar Big guy tamkar baisan suna magana ba Ya haWe rai ba annuri ko kaWan akan fuskar shi.

Dafa kafaWar shi COO yai"Allah Ya huci zuciyar ka Yalla6ai, mu kan mu bamu ji dadin abun da yayi ba amma yakamata muyi mashi Uziri saboda baisan komai ba..."

bai kare maganar ba Unaisah ta fashe da matsanancin kuka, kamar jira su Batool su ke ta fara kuka suma suka fashe da kukan gaba daya sautin shesshekar kukan su Ya karade kunnuwan jami'an dake agurin, tsabar tashin hankaline Yasa suka fashe da kuka dama tun da suka fito daga dakin tambayar zuciyarsu araunace take saboda raunin da aka fama masu

ga kuma wani tashin hankalin da suke kallo duk da basu san meya faru ba amma sun fahimci Danish ne yayi wani abu badai dai ba.

"OMAR, pls ya isa haka! Ka sake shi, nayi magana da Salsabeel awaya ya faWa min yana acikin head quarter din yanzu zai shigo"

idanun shi jawur Ya dubi Taj a fusace Yace"Taj I won't let him go. He must return and answer the chief's questions, ya 6ata min rai ya rasa wazai disga sai chief din mu? Tsaran wasan shi ne? duk kokarin da ya ke yi akan su shi baya gani ne? Ni bana son mutun mara Wa'a irin shi ..."

Ya fada tare da cije le6en shi ya maida dubanshi ga Danish wanda tu??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ni Jikin shi Ya fara kakarwa wata irin zufar 6acin rai ce ta fara tsatstsafo mashi, Numfashin shi ya fara hauhawa yana fita cikin sauri, lokaci daya temperature din jikin shi ya Wau wani irin zafi, idanun shi suka rune zuwa Ja.

"Yaya Omar dan Allah Ka sake shi, nayi maka alkawarin zan shawo kan shi" cikin shesshekar kuka Unaisah tayi maganar

Haris yace"dan Allah Ya Omar ka ?yale Danish, Idan laifi yayi maku ku yi hakuri zamu fahimtar da shi" magiya suka dinga yi mashi akan ya yi hakuri Ya saki Danish

Adaidai Lokacin da Salsabeel Ya faWo arean da suke yana faman wurga idanu don ya gano inda suke kwatsam idanun shi suka sauka akan gungun jami'an da su ka kewaye su.

Gaban shi ne yayi wani irin faduwa aguje ya nufe shi har yana bangaje jami'an dake sintiri kamar mahaukaci haka suke kallon shi

Yana ?arasawa ya sanya karfi ya raba tsakanin big guy da Danish Yana faman haki ya dubi Danish wani irin faduwar gaba yaji ganin sa6ar majici akan wuyan shi babu wanda Ya lura da sabar sai shi da Allah ?addara zai ganta, wahalallan Yawu ya haWiya la66anshi na rawa ya furta"Danish, please...don't. Please, Danish, try to control your anger.."

gaba Waya jami'an sun ruWe da ganin yadda Salsabeel ke lallashin shi, Musamman Big guy ranshi ya ?ara 6aci a faWa ce yace"meya sa ka ke bashi hakuri"?

Salsabeel bai tanka mashi ba saboda tashin hankalin da yake tunkaro su batare da su sun sani ba, In har evil heart dinshi ta motsa zai rikiWa ne ya canza halitta, ya tarwatsa head quarter din gaba Wayanta ba ?amar 6arna zai yi ma su ba.

Da hannu ya dafe saitin zuciyar Danish, Ya marairaice mashi fuska tare da girgiza mashi kai alamar A'a...

gaba daya jami'an sun kasa fahimtar me Salsabeel Ya ke nufi!


Wani irin dogon numfashi Danish Yaja cikin zafin nama Ya bangaje hannun Salsabeel daga kan kirjin shi yana faman fitar da huci mai zafi ya mi?i hanya, aguje su Unaisah suka bi bayan shi suna kwala mashi kira ko kallo ba su ishe shi ba, bai sha wahalar gano kofar da suka shigo Soc din ba Ya fu ce daga ciki Ya nufi main enterance gate na head quarter din.

Kafin karasawar shi big guy ya kira layin Waya daga cikin jami'an dake tsaron gate din Ya basu Umarni karsu kuskura su bar shi Ya fita.

Lokacin daya karaso Yana tafiya kamar baya acikin hayyacin shi, hankulan jami'an dake sintiri gaba daya ya dawo kan shi, fisatattun jami'an dake tsaron gate din suna ganin shi suka gane shi ne matashin da aka basu umarni karsu bari ya fita, aikuwa azafafe suka yi mashi ?awanya kamar zasu rufe shi da bugu.

Yan uwanshi sai kuka suke suna ambaton sunan shi hadi da yi mashi magiya akan ka da ya tafi ya bar su, babban abunda suke ma fargaba in ya fita ina zai dosa?

Dakyar chief ya iya lallashin zuciyarshi cike da rashin ?warin jiki ya fito daga Wakin Ya nufi su big guy dake atsaitsaye curko curko sun kasa kunne suna sauraron Bayanin da Salsabeel ya ke yi masu dangane da Danish


"Ga chief nan" taj ne Ya fada kusan atare suka kai duban su gare shi, damuwa ce karara akan fuskar shi.

Bawan Allah da buWar bakinsa sai cewa"Ina Danish? Ina sauran yaran"? Kafin wani daga cikin su Ya bashi amsa sautin ringing wayar big guy ya katse hanzarin su
Da sauri Ya kara wayar a kunnan shi.

"Sir, Yaron nan fa Ya fita! Mun yi kokarin mu dakatar da shi amma mun kasa, gaba Waya ya watsar da jami'an da sukai kokarin hana shi fita..." a kidime Big guy ya furta"what? Ya fita! Garin yaya hakan ta fadu"?

Wani irin faduwar gabane Ya Warsu a zuciyoyin su, sunyi matukar mamakin jin hakan shin tayaya akaima har ya iya fin karfin jami'ansu Ya fuce daga head quarter din?

"Yaran suna nan, amma Waya daga cikin ?an matan mai launin ido ruwan toka ta kubce mana, yanzu haka wasu daga cikin jami'an mu sun bi bayan su"

Tashin hankalin da ba'a saka mashi rana, Salsabeel bai tsaya yaji karashen zancen ba, Ya watsa aguje Ya fuce, Agaggauce Senior agents din suka rufa mashi baya, ya rage saura big guy da chief atsaye suna fuskantar juna

"Meya faru Omar? Meyasa Ya tafi? Wani ya 6ata masa rai ne ko abunda ya faru tsakanin mu ne"?

Dakyar big guy yai karfin halin zayyana mashi abunda ya faru bayan fitowar Danish

Girgiza kai yayi cikin sanyin murya yace"meyasa Omar? Meyasa zaka yi mashi haka? Kamanta wanene shi? Yaron da bai san komai ba yanzu daka bata mi shi rai ina kake tunanin zai dosa? Wa ya sani agarin nan"? Yanayin yadda chief ke yi mashi magana araunace ba karamin karya mashi zuciya yayi ba.

"Duk abun da nayi nayi ne saboda kai, kasan irin kaunar da nake maka, zan iya jure komai amma wlh muddin wani yayi kokarin bata maka rai bazan kyale shi ba, koma wanene.."

"Nasani Umar, amma ni baka kyauta min ba, yakamata kayi amfani da hankalin ka, rayuwar shi abun tausayi ce, tabbas raina ya 6aci da abun da yayi min amma wlh ko kusa ban ji haushin shi ba, saima son shi da ya ?ara ninkuwa acikin zuciyata, yakamata mu yi mashi Uziri bai kamata mu ga laifin shi ba yaron da har yanzu suna iya control dinshi..." bai ?are maganar ba ya juya cikin takun sauri Ya nufi hanyar fita daga Soc din da sauri big guy yabi bayan shi


*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE=?%?
'?*

*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*_________________________________
'?



Sautin ringing Win wayarta ne ya farkar da ita daga dogon baccin daya Wauke ta, tana a kudundune cikin lallausan duvet dinta.

da wata irin malalaciyar kasala ta fara ?o?arin buWe idanunta da su kai mata nauyi saboda baccin da tasha ga wani irin tsami da jikin ta yayi mata, lalube ta fara yi tana shasshafa bedmattress din don taji idan yana nan har ta ?are lalubawa bata ji mutum akan gadon ba, hakan na nufin ya jima da tafiya.

Tunawa da yanayin da take a ciki yasa tay saurin ware idanunta cike da fargaba ta dubi jikin ta zir take ba sutura, lumshe idanunta tayi cike da jin shaukin shi take Wan jan numfashi, yayin da ?wa?walwarta ke tariyo mata abun da ya faru tsakanin ta da shi a lokacin da suke tsaka da jin daWin su.

A hankali ta mi?e zaune ta ja duvet din ta lullu6a kirjin ta da shi, kafin ta jingina bayan ta jikin headboard, sumar kanta ta yamutse saboda dam?ar da tasha a hannun big boss, ko ina na jikin ta zafi ya ke mata.

idanunta sun kumbura sun kaWa jajawur, haka la66anta ma sun kumbura don ba karamin tsotsa suka sha ba, ta galabaita sosai har wani jirin kasala take ji a jikin ta.

Kifa kanta tayi kan gwiwowinta tunawa da nasihar da mahaifinta ke yawan yi mata.

"Ke kadai Allah Ya bani mamana, tun kina ?aramarki bani da burin daya wuce in inganta rayuwarki ki zama hafizar alkur'ani mai ilimin addini da zamani saboda inyi alfahari dake sannan ki zama abun kwatantace, Alhamdulillah cikin ikon Allah sai gashi kin cika min burina ko'ina zancenki ake duk in na shiga cikin jama'a sun dinga yabonki suna fadin ?ata malama ce hafiza mai cikar kamala da kamun kai ga kyautatama al'umma da son taimako, kowa yabon ki yakeyi, burin kowace mace tayi koyi da Aishatu bintu imam malik mace Waya tamkar da dubu, Ummi nasihar da zan maki ko bayan ba raina kiji tsoron Allah, kada ki canza daga yadda nasanki, abun da zaki min wanda zaki biyani shi ne Ki karemun martabana da kimata a idon duniya, kada kiyi abun da zai zubda min mutuncina Aishana"

Rushewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, a duk lokacin da ta tuna nasihar mahaifinta zuciyarta ba ?aramar karaya ta ke yi ba, tana jin tsanar rayuwar data Waukarwa kanta, tana mai danasanin abun da yayi silar rabuwarta da mahaifinta, saboda bata da abu mafi soyuwa da ya wuce shi a duniyar nan, kai duk wani gata da ya zata samu agurin ubanta ta samu ninkin baninkin sa.

tana jin raWaWin karya al?awarin mahaifinta da ta yi na kare mashi martabarsa.

kifa kanta tayi jikin pillow, ita kadai baiwar Allah babu mai lallashin ta.


Ba halin ta bane, ba laifin ta ba ne, tana da ilmi tasan zina ba kyau ta kuma san hukuncin wanda ke aikatata amma meyasa takasa dainawa ko da tayi nufin ta tuba ta koma ga Allah? Tasha yun?urin yin hakan amma aduk lokacin da big boss ya bu?ace ta bata iya bijire ma shi.

Ta yi kuka tamkar ranta zai fita kamar ?ar dambe ta dun?ule hannayenta ta dinga bugun mattress kamar zatai hauka ta tsani abunda take aikatawa bata so ta mutu batare da yafiyar mahaifinta ba, kuma batason ta mutu tana aikata sabon Allah tana matukar jin tsoron makomarta.

Ringing Win wayarta ne ya dawo da ita hayyacin ta, fuskarta sharkaf da hawaye ta janyo wayar daga kan drawer ta duba sunan me kiranta.

Maji daWina shine sunan daya bayyana akan screen din, kasa picking call din tayi saboda fushin da zuciyarta ke yi.

Text message ne ya shigo on the top of the screen din wayar, cikin zuciya ta soma karanta abunda ya rubuta mata

_"ummi, na tafi ba tare da nayi maki sallama ba, ki yi hakuri da hakan nasan zaki tashi da kewana, anyi min kiran gaggawane, ba dan nagaji da jin Wumin jikin ki ba, bazan iya misalta daWin da kika jiyar dani ba, kin bani cikakkiyar gamsuwa da zan iya Waukar kwanaki ban nemi matana ba, bazan iya biyanki ba Ummi, ki fadamin me zanyi maki don in faranta maki"_

Runtse idanunta tayi gam, siraran hawaye suka dinga shararowa kan kuncin ta..

"Ya Allah Ka cire min jarabar son bawan nan naka, Ina neman tsari da shi...."

bata kare maganar ba kwatsam taji dirar motoci acikin gidan, a firgice ta jefar da wayar ta faWa kan mattress ta duro daga kan gadon, tafin hannunta a tallabe da bargon ta faWa toilet taja ?ofa ta datse, tana faman zare idanunta, sam ta manta da su Batool tasan bai wuci sune suka dawo gidan ba, abunda take jima fargaba kada wani ya shigo Wakinta tasan in har suka ga gadonta sai sun zargi wani abu saboda ya 6aci ba kaWan ba.

Cikin Takun sauri Chief Ya faWo Falon Ya nufi upstairs, agurguje taj da big guy suka biyo bayan shi, kwata kwata babu kwanciyar hankali akan fuskokin su damuwace ?arara saboda jami'an da suka tura su nemo Danish kusan awanni har yanzu ba wani labari, har tracking layin sa sukai a karshe suka gano location din da wayar take agida yabar ta baije da ita head quarter din ba, wannan dalilin ne yasa suka yanke shawarar su dawo gidan, watakil su gan shi.

bai nufi ko'ina ba sai bedroom din Danish Yana isa bakin kofar yayi knocking Win ta cike da fargaban kada su ki ganin shi.


Jin shiru ba'a buWe kofar bane yasa shi tureta da hannun shi ya faWa ciki Yana haki saboda gudun daya sha, bazai iya tuna when last yayi irin shi ba.

da matsanancin faduwar gaba yake bin dakin da kallo wayam babu kowa adakin dafe kan shi yayi da hannu Waya idanunshi sun kaWa jawur babban tashin hankalin shi Ina Danish yaje? ya zai yi da yan uwan shi? Me zai fada ma Uncle hateem idan ya kira yana son yin magana da shi"?

"baya aciki ko"? muryar boss ce ta katse mashi zancen zucin shi
Big guy duk ya rasa kuzarin shi Ya daura ma kanshi alhakin 6atan Danish saboda shi ne silar daya ja har ya yi zuciya Ya tafi, sai yanzu ya ke danasanin bata mashi rai da yayi ganin yadda ya Waga hankalin chief Owais.

"Taj bansan ya zanyi ba, baya nan, ya tafi, ya zanyi da raina, bana so na rasa yaron nan wallahi danasan abun da zai faru zuwan mu headquarter da ban tursasa mashi akan yabi mu ba..."

dakyar yake magana saboda damuwar data cika zuciyar shi.

jikinsu yayi mugun yin sanyi.

Cikin raunin jiki ya dubi big guy"Omar, kaga abunda kaja min ko? Idan har yaron nan bai dawo gida nan ba, bazan yafe maka ba..." gaba Waya ya rikice masu.


"Sir kayi hakuri, na kar6i laifina, kuma nayi danasanin 6ata mashi rai da nayi, bada son raina ba ya 6ata min rai ne amma nayi maka alkawarin zanje in nemo shi duk in da ya shiga agarin nan..."

yana faWan hakan ya juya azafafe ya haura kan stairs ranshi ya 6aci da furucin Chief, kalmar daya furta mashi Wazu daya ce Son danish na kara ninkuwa azuciyar shi yaji haushinta bayan irin cin mutuncin da yaron yayi mashi amma ko kadan ransa bai 6aci ba, shi arayuwarshi bayason wanda zai shiga tsakaninsa da chief, yana matu?ar jin kishin yaga chief yana nunama wani so fiye da shi hakan na kona masa rai yafi so koda yaushe ya zamana na hannun daman shi.

Dafa kafadar chief yai da hannun shi"dan Allah ka kwantar da hankalin ka, bana so kana sanya damuwa aranka, in sha Allah Danish zai dawo ..." lallashin shi ya cigaba da yi, bawan Allah gaba Waya ya rasa ?warin gwiwar shi.

"Nima Zan bi Omar, Zamuje mu binciko shi"

Numsafawa yai kafin ya dubi Taj da rinannun idanun shi

"Ina sauran Yaran? Sun shigo?"

bai ?are maganar ba, suka jiyo sautin tafiyar su da sauri taj ya dubi kofar shigowa falon, Waya bayan Waya suke shigowa kamar yan gudun hijra saboda jigatar da su ka yi, fuskokin su sharkaf da hawaye sun sha kuka bayin Allah har sun gaji sun gode ma Allah, Unaisah tafi su jin jiki har wani jiri take gani acikin idanunta, sun ruke hannun Juna ita da Batool suma sauran sun rurruka hannayen junan su.

"Sun shigo,"

"Pls, Calm them down, I don't want them to worry about losing their brother, ka cigaba da lallashin su, Sannan ashirya masu lunch dinsu"

"Sir kaima kana bukatar hutu, ka koma daki ka kwanta ka huta zanyi magana akawo maka lunch din ka" girgiza kai yai"wallahi bazan iya cin komai ba in har Danish bai dawo gidan nan ba"

Taj yayi mamakin kalaman shi, bai ta6a zaton son da chief yake ma Danish yakai har haka ba, aranshi ya ayyana watakil ko dan saboda sabon da sukai da junan su cikin kwanakin nan.

"Da ka daure.."bai kare maganar ba ya katse shi"Boss ka tafi kawai, Ka kula da sauran yaran, Ka kira auntynsu ka fada mata halin da suke a ciki"

Cike da jin tausayin shi ya amsa mashi da toh.

Lokacin da ya sauko down, A kan sofas Ya hango su zazzaune sun yi shiru kamar masu zaman makoki, tsayar da idanun shi yayi akan Unaisah da ta kwantar da kanta saman kafadar Batool, tayi matukar bashi tausayi, bakomai yake tunawa ba face lokacin data bi bayan Danish ta haura kan titi mota takusa hankadeta ba dan Allah yasa Jami'an su sun yi gaggawar Kai mata agaji ba da tuni rai yai halinsa saboda ta furgice idanunta sun makance bata ji bata gani danish kawai take nema ido rufe, har wani zazza6i take ji ajikin ta mai azabar zafi, ga ciwon kai daya fara takura mata, ta rasa meke mata dadi duniyar nan, ita damuwarta ina Danish ya shiga? Baisan kowa ba agarin abuja, abun da take jima fargaba kada yace zai koma Gidan kurkukun kaddara duk in zuciyarta ta raya mata hakan sai taji matsanancin faduwar gaba ga tashin hankali da firgici.

kwata kwata babu wanda Ya lura da Taj a cikin su saboda damuwar data rufe idanun su.


Har saida yayi masu gyaran murya tukunna suka kalle shi in ka cire Unaisah wadda ta rufe idanunta hawaye sai suntiri suke yi kan kuncin ta.

Jiki asanyaye ya zauna yana dubansu

"Unaisah! " dakyar ta buWe idanunta da suka rune zuwa ja ta kalle shi

"Meyasa baki jin maganata? Bana hanaki yin kukan nan ba? Ko shi zaisa ya dawo ne"? Yawu mai Waci ta hadiya tamkar bata son yin maganar tace"daddy, bana jin dadin jikina ne"

"Ba dole jikinki yaki dadi ba, duk kinbi kin daga hankalinki uhyum! Sai kace ba kisan tawakkali ba Unaisah! Ce maki akai Ya bace ba zaki kara ganin shi ba ne? ya fada yana kallon fuskarta, shiru tayi tana sauraron shi tasan ba lallai ya fahimce ta ba tun da shi a zaton shi sabo ne kadai atsakanin su.

Sassauta muryar shi yayi cikin sigar lallashi yace"kuyi hakuri nima na damu da rashin shi, amma bai kamata ku zauna kuyita


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login