Showing 42001 words to 45000 words out of 298130 words

Chapter 15 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

yi mashi zai warware shiyasa yafara tunanowa, Hankalin shi na akan wayarta yaci gaba cewa"muna kama da daddynmu Ni da sister Wina, Idan bazan manta ba, Mahaifin mu Attajirin mai kuWine... " muryarta a ruWe tace"Zaka Iya Tuna sunan shi? Ko sunan Mommyn ku? Da sunan Country din da kuke rayuwa? A ?agare ta furta maganar.

Shiru ya danyi, Yana kallon Screen din wayarta da yake daddanawa.

"Bansan asalin sunan shi ba, amma kamar yana da nick name da ake kiran shi da shi, Ni kamar Big Boss Ne Namanta, mommyn mu kuma sunanta umm......" duk yadda yaso ya tuna sunanta ya kasa.

Cike da zumuWi ta dafe kafadarshi"bro, Kayi ?o?ari ka tuna dan Allah, Koda bayanzu ba, waWannan bayanan da su zamuyi amfani wurin gano su wanene Azzaluman da suka sadaukar da mu" Jinjina mata kai yayi"zanyi ?o?ari na tuna, amma ko Yanzu naga daddyna wallahi zan gane shi saboda kamanninmu sun 6aci da shi Yana da Kyau, hatta ?irar jikina kalar nashi ne da sumar kaina, bani da banbanci da shi sai dai na girman jiki da shekaru"

?aga hannayenta sama tayi"Ya Allah Ka bayyana mana bayin Allah nan, Da mahaifin Unaizah Jan wuya, da dukkan waWanda suka sadaukar da mu, wallahi muna kwaWayin Ganin su ko don mu tarwatsa zukatansu" addu'o'i ta dinga yi yana amsa mata da ameen.

"Da ace zan Iya tuna Phone number din mommyna da mun jaraba kiranta, saboda na ta6a haddace layukan wayarta dana Daddyna amma nasan zaiyi wuya mu same su.

Cikin sanyin Murya Ya ?are maganar,
Unaisah tace"Sajeed, koda ka tuna layin wayarta wallahi ba lallai tana amfani da shi ba, tun da mugayene babu Allah aransu, kamar yadda Iyayen Unaizah suka hana tasan komai nasu, kuma zai Iya kasancewa Hakane"

"Kin faWi gaskiya, amma duk da haka zan jaraba rubutawa mu gani," ya fada tare da daddana wayar Ya rubuta number dayake tunanin ta mommynsa ce, duk suka ?ura ido suna jiran ganin in zata shiga, Muryar na'ura ce ta sanar da su cewa Number da suke kokarin kira badaidai take ba, dafe kai yai da hannu Waya"nayi mistake sister bazan iya tuna ainihin yanda number din yake ba" fuskarshi yamutse yayi maganar.

Ganin Yana rubuta wata number ne yasa tace mashi"wannan fa"?
"Layin wayatane zan kira" natsuwa sukayi suna jiran jin in zai shiga, Har saida gabansu Ya faWi Jin Wayar Na yin ringing, duk da basu da tabbacin Idan Number dai dai Ya sanyata, kallon juna su ka yi da alamun mamaki, Har kiran ya katse ba'a Waga shi ba, Suka sake kira nan ma ba'a yi picking ba....

"Mu bari zuwa Anjima sai Mu ?ara Kira, Allah yasa layin dai dai muka Kira," acewar Unaisah
Sajeed Ya amsa mata da ameen.


*d'MOM SARAH>?
?*


Su biyu ne zaune Asaman wasu Hadaddun kujerun sha?atawa dake a bakin Swimming pool Area na gidan, Daga tsakiyar su table ne mai Wauke da Mugs guda Biyu na coffee suna sha suna fira, Hajiya Layla ta sanya arab gown ta yafa mayafi akanta, yayin da ita kuma Hajiya Sara ta dauki wankan kimono robe, babu mayafi akanta zallar gashin kanta ne ta saki har saman gadon bayanta launin Ja.

"Har yau ina mamakin Yadda Kike rayuwa da Mijin ki, mutun babu fara'a babu annuri, gaskiya Ina jinjina maki" Hajiya layla ce tayi maganar.

Murmushi hajiya sara tayi"bana damuwa da hakan, Saboda nature din shi ne, Sai ka Iya zama da shi zaka gane wanene shi, Yana da sau?in kai, fiye da tunaninki" ta6e baki Hajiya laila tayi"ahakan"? Jinjina mata kai tayi"?warai kuwa, saboda Yana kyautata min, kuma yana nuna min so, tun lokacin dana aure shi bai ta6a canza min ba, nasan yana da wuyar sha'ani sai dai ba kamar yadda kika zata ba, ban ta6a neman abu a wurin shi na rasa ba, ko baida shi zaiyi min ne balle ma Yana da shi din, Baya son 6acin raina, Sannan yana bani kulawa, wani lokacin idan muna atare sai in dinga jin kamar ma bamu daWe da yin aure ba saboda yadda yake tarairata...."

tun da hajiya sarah tafara kora ma hajiya layla bayani take ta faman yamutsa fuska, ba haka taso taji daga gare ta ba, tun Wazu take ?o?arin bugun cikinta don taji ya take ha?urin zama da Alhaji musa sai dai wani abu data fahinta dangane da Hajiya sarah irin matan nan ne masu shegen wayau, ba su bari aji sirrin mijin su, baka ta6a jin aibun mijinta abakinta sai dai Alkhairinsa.

Mug din coffee ta dauka ta kur6a zuciyarta ajagule, bayan ta ajiye mug din tace"amma a ganinki abunda Alhaji musa yake yima Mijina ya dace? A matsayin shi na yayanshi ya dinga juyashi son ranshi"?

Girgiza kai Hajiya sarah tayi"Ni kaina ban goyi bayan hakan ba, ko lokacin da ya bashi umarnin yazo daku joss sai da nayi kokarin dakatar dashi sai yace min indaina sanya mashi baki akan abin da ya shafi danginshi, gaskiya banji daWi ba, amma abunda ke Waure min kai, meyasa shi Alhaji ubaid Win Yake yi mashi biyayya? Bayan shine ke babba"?
?aure fuska Hajiya layla tayi tamkar bazata tanka mata ba tace"may be ko dan arzi?in Shi bai kai na musan ba shiyasa yake li?e ma shi, kinsan idan mutun nada arzi?i ko shine ?arami agida babba yake komawa"
"Bana tunanin haka, amma dan Allah ki yi ha?uri da halin mijina" ta faWi hakanne don ta fahimci ran Hajiya layla a6ace yake da abunda Alhaji musa yayi masu.
"Bazan 6oye maki ba, ina jin haushin Yadda Mijinki Yake juya mijina, wannan ba Wabi'ar arziki bace, Yana da girman kai da izza, nazo gidan nan ne bada son raina ba, Alhaji Ubaid shine Ya takura min akan muzo, da wallahi ko ?eyata bazaku gani ba" a fusace ta faWa tana haWe rai, jin wannan maganar yasa Hajiya sarah ta sassauta muryarta"Allah Ya Huci zuciyarki, nasan bai kyautaba.... " Kwa6e fuska Layla tai batare da ta kuma cewa komai ba.

"Na lura kamar ranki Ya 6aci" acewar Sarah,
Murmushin ya?e Layla tasakar mata"komai ya wuce ai, Tun da na faWi ta cikina, kinsan ni ban iya 6oye damuwata ba"
Martananin murmushin sarah tayi mata, tsawon mintuna babu wanda ya ?ara yin magana acikinsu sai dai su kalli juna suyi murmushi.
Sai daga bisani Layla tace"Inataso in tambayeki Omar ?in mu tsawon lokaci ban sanya shi a idanuwana ba"
Hajiya sarah tace"Ni kaina bansan meya ru?e shi A america ba, baya son zama nigeria saboda daddyn shi da basa jituwa, Amma yana kokarin kirana awaya wannan karanne ma ya dau lokaci nima kona kira shi bana samun shi, sai idan shine Ya tuntu6e ni"

Har layla ta buWe baki zatayi magana Ta hango Zeenatu dake tunkarosu sai sauri take Yi, Riga da wandon jean ne a jikinta, Kanta babu mayafi, Yau ne karo na farko Da hajiya layla tafara ganin zeenatu tana yawo babu mayafi a jikinta.

"Dama zeenatu tana yawo babu hijab ba mayafi a jikinta" jin haka yasa sarah ta dubi inda hajiya layla take kallo ita kanta mamakine Ya kamata.

"Sai dai idan wani abunne Yaja hankalinta har ta manta bata sanya mayafin ba"

Sai faman sakar masu murmushi take yi, Cikin girmamawa ta gaishe da su atare suka amsa mata.

Mom sara tace"daughter Kin dubi jikin ki kafin ki fito daga Waki"? da sauri takai hannu ta shafa kanta taji babu mayafi, duk tabi ta ruWe tana faman zazzare idanu, kunyar duniya ta kamata.
"Mom, wlh bansan babu mayafi ba, ashe haka na fito, namanta da hijab din saman gado, Bari na koma in dauko"
Gaba Waya suka sanya dariya
Layla tace"Ki kwantar da hankalin ki, ai ba wani abu bane don kinyi yawo a cikin gidanku babu mayafi, amma dai yakamata kina kulawa tunda kin girma" ta fada tana kallon kirjinta da suke aciki kamar zasu fasa rigar, dukar dakai ?asa zeenatu tayi wani irin kunyarsu take ji
"Bari na koma in dauko mayafin"
Har zata juya Mom sara tace"ke zonan" da sauri ta dubeta, Da ido hajiya sarah ta nuna mata wayar hannunta"me kike yi da ita"?
"Oh namanta, Ita na kawo maki, Ana kirana da ba?uwar number a lokacin ina a toilet, ban samu damar yin picking ba shine na kawo maki ki duba mai kiranki"
A ruWe Sarah tace"kamar ya ana kirana? Wayar wacece"?
"Tawa ce"
"Sai kuma kice ni ake kira"!
"Mommy ai ni bana amfani da ita, tun da na kar6eta a hannun ki nace maki zan ba yaya shureim ya tura min hutunan su to su kadai nake kallo, ni banma lura da sim awayar ba"
Mi?a mata hannu sarah tayi"bani wayar" bayan ta kar6a ta soma bincika layin dake akan wayar don ita kanta batasan akwai sim ba, sai yanzu da zeenatu take fada mata.

"Layin Mtn ne akan wayar, amma wannan number da aka kira ki da ita bansan wanene ba, ki koma ciki, Idan na shigo zan duba mai kiran naki"

Amsawa tayi da toh, da sauri ta juya ta nufi cikin gidan cike da fargaban kada Yaya shureim yaganta da ?ananun kaya.

Har saida ta 6ace ma ganinsu tukunna suka kau da idanunsu daga kallonta.
"Zeenatu tana burgeni, Idan ina kallonta sai in runka tunawa da Yarinyar Benazir"
Sarah dake kallonta tace"yarinyar da baki damu da ita ba? A yadda naji labari baki ta6a ganinta ba saboda baki zumunci dasu"
"Hakane, Amma ayanzu da zan ganta babu abun zai hana in rungumeta, saboda nayi danasanin watsin danayi dasu"
Sarah tace"kinyi babban kuskure, Baki kyautaba, Sai kace ba jininki ba, Ai ni da jikatace wallahi koda ban son mahaifinta saina ?aunace ta, laifin wani baya shafar wani"

Shiru Layla tayi batare da ta sake cewa komai ba, Ita kadai tasan takaicin da take ji duk idan ta tuna yadda ta?i Tajuddeen da Yarinyar shi......

Bayan zeenatu ta shiga gidan, Cikin sanWa take tafiya gudun kada Dr shureim Yaganta ahaka, babu kowa hanyar data biyo sai lalla6awa take yi kamar wata 6arauniya, adai dai lokacin dr shureim ya fito daga bedroom din shi sanye da jallabiya, Babu rawanin larabawan da yake naWawa akanshi zallar sumar kanshice har saman wuyanshi ta nannaWe gwanin ban sha'awa.

Tunda yayi tozali da bayanta Ya ?ura mata ido yana kallonta, kwata kwata ranshi bai bashi cewar zeenatu ce ba, saboda bai ta6a ganinta da ?ananun kaya a jikinta ba, sun matseta duk da bata da ?iba kayan sun mata kyau.
Da sauri Yabi bayanta Kamar yadda take Yin tafiya cikin sanWa shima haka Yabita da sanWar har cimmata,
"Zeenatu"! Kaitsaye kiran ya daki kunnata, A firgice ta juyo idanuwanta azare take kallon shi, wata irin zabura tayi da niyar ta watsa da gudu sai dai kafin tayi hakan yayi sauri ru?o waist Winta ya dawo da ita jikin bango, Ya dafe da hannu Waya yana binta da kallon mamaki.
Da sauri ta daddafe kirjinta da hannu biyu don kada yagan mata abunta, ta kasa jurar hada ido da shi, Kunyar shi duk ta kamata, Juya mashi baya tayi tana fuskantar Bango, muryarta da shagwa6a ta furta"ni fa bansan babu mayafi na fito ba,"
Koda tayi maganar hankalinshi na akan bayanta data juya mashi, sumar kanta yabi da kallo, ?amshin turarenta sai shigar mashi hanci yake yi
Jin yayi shiru bai tanka mata bane yasa ta juyo don ganin me yake yi, karaf suka haWa ido cikin na juna, kallon juna suka cigaba dayi kamar zasu haWiye kawunansu tsabar so da ?auna, Bai ta6a yi mata kyau irin na yau ba saboda sumar kanshi daya bari babu Arab turban dinsa, haka shima tayi mashi kyau yau daya ganta da ?ananun kaya.

da?yar Ya iya tattara natsuwarshi Ya furta"Kin yi min kyau" murmushi tasaki tana faman ?yaf?yafta mashi blue eyes din ta.
?aura hannun shi yayi saman sumar kanta, lallausar gaske Ya shafata a hankali har wani lumshe mashi ido take Yi
Can ?asan ma?oshi ya furta"na fara tunanin yi ma Uncle maganar auran mu saboda na?osa na mallake ki, ko dan ki haifa min fatima" shi kanshi baisan ya furta hakan ba, gaba daya yafara zaucewa da kyawun zeenatu
Runtse idanunta tayi da sauri tare da Waura tafukan hannayenta ta rufe fuskarta alamar taji kunyar kalamin shi
"Yaya shureim ni kunyarka nake ji, dan Allah kabarni in tafi Wakina"
"Ki daina jin kunyata, Ni da nake burin ki zama abokiyar rayuwata" wani irin daWine ya ziyarci zuciyarta jin kalamin daya furta mata.
Tunda yafara kallonta bai bari ya daura idonshi akan dukiyar fulanin ta ba sai da taja numfashi suka motsa tukunna hankalin shi ya karkata akan su.
Yajima yana mamakin cukowarsu kamar bana yarinya ba, jin numfashinshi saman fatar kirjinta yasa tayi sauri buWe fuskarta da idanunta gaba Waya lissafi na neman kwance mashi kamar zai cafko su haka yake ji ya du?ufa yana kallonsu ko kyaftawa baiyi.
"Yaya shureim menene haka? Dan Allah ka daina kallona, Ka bari sai munyi aure" Ta fada tana bubbuga mashi ?afafuwanta, Wagowa yai da idonshi ya kalleta launinsu harya fara canzawa
Matsar da fuskanshi yayi saitin tata ya daura tsinin hancin shi akan nata, nan take ta soma jin wani irin yanayi atattare da ita, Numfashinta harya fara canzawa, Bugun zuciyarta ya ?aru, duk ta ?agara da son jin shi a jikinta, tayi tunanin zaiyi mata irin abunda taga daddynta da mommynta sunayi wato kisssing din junansu.

Kamar tasan abunda ya ke shirin yi mata kenan, saboda baya a hayyacinsa a bu?ace yake da ita, Yana kokarin haWe bakinsu, Kwatsam Benazir Ta biyo hanyar da suke da sauri take Tafiya sautin takalmanta ne suka ja hankulansu, a gigice Zeenatu ta bangaje dr shureim ta watsa da gudu ta nufi bedroom dinta.

"A'u'zu billahi minasshaidanirrajim"

acikin zuciyarshi ya furta hakan.

*Daga Al?alamin Boss Bature=؋?
'?*




*Littafin kurkukun ?addara 500 ne, dukanshi Book One two and 3 Idan kin shirya biya ga Details da zaki tura*

3196407426

First bank

Bature Hafsat Muhammad,

*bayan kin tura zaki bada transaction reciept ko screenshot na debit alert a matsayin shaida*

*Something Is About to Happen*
_______________________________ '?


jikin shi da kasala Ya juyo Yana duban Benazir dake tunkaro shi ga dukkan alamu bata ga Zeenatu ba.

"Yayana nakaina, me kake yi anan"? Tana murmushi tayi mashi maganar

Sam ya kasa buWe baki Ya bata amsa, sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi.

"Lafiya? Ya akai naga idanunka sun yi ja"? AruWe ta jefa mashi tambayar tana duban shi.
Shafa sumar kanshi yai da hannu Waya kafin ya furta"bakomai, Yanzu na tashi daga bacci,"

"Amma dai daga gani baccin bai isheka ba, cos gaba Waya kamar ma baka a hayyacinka"

?a?aro murmushi yayi akan fuskarshi batare dayace mata komai ba.

"Yayana, Maganar zuwa gidan su Aneeleeh ne Ya kawo ni, wallahi duk na damu da rashin samun layin Abie din su, har number dinsa na kar6a awurin daddy na jaraba kiran layin da wayar mom amma shiru ba'a Wagawa" muryarta tamkar zata fashe da kuka tayi maganar.

"Bana so mubar abuja batare da mun je gidan su ba"

"In sha Allah zamu je, Zanyi maki ?o?arin hakan, abun da yakamata mu yi shine mu tura mashi da text message, may be layin nashi baya akan waya duk ranar da ya sanya shi zai ga sakon mu ne"

"Hakane, tun da akwai layin awayarka ka tura mashi da sakon"
Ba tare da 6ata lokaci ba, Dr. Shureim Ya zaro wayarshi, ya soma daddanata
"Me zan rubuta mashi"? Ya tambaya yana kallonta.
"Ka faWa mashi Benazir ce ?awar Aneelerh, Matar Tajuddeen" Ya furta Okey, bayan ya gama rubutu text din Ya turama masa, Kafin daga bisani ya Wago da ido, Ganin takura mashi ido yasa shi yi mata gyaran murya"lafiya kike kallona"? murmushi tasaki tare da fadin"yayana fada min gaskiya, meya jefa ka cikin yanayin nan" ta fada tana Wage mashi gira, nan take ya fahimci jikin shi ya nuna halin da yake aciki, shafa kirjin shi yai da hannu tamkar zai gyara ma6allin gaban jallabiyarsa Duk yabi ya dabarbace wata irin kunya ce ta kama shi.

"ina Zeenatu"? Ta jefa mashi tambayar tana bin shi da kallon ?urulla.

Galla mata harara yayi"Bansani ba, ?ar sa Ido, Kije dakinta ki neme ta, wato dai bazaki canza halinki ba, Har yanzu kina nan da rashin jin maganarki, ' kafin ta kara furta mashi magana yayi saurin wuce ta Ya nufi bedroom dinshi, Yana shiga ya jefar da wayarshi kan gado da wata irin kasala Ya faWa saman gadon Yana fuskantar ceilling, wani irin yanayi yake jin kanshi mara misaltuwa.

Lumshe idanunshi yayi yayin da acan cikin zuciyarshi yake tariyo wani abu daya ta6a faruwa arayuwarshi
Har abada bazai ta6a mantawa da wannan daren ba, wanda yake yi mashi la?abi da DESTINED NIGHT, abun da ya faru a daren Ya tsaya mashi aranshi Ya kafa tarihin da har abada bazai ta6a gogewa aranshi ba.

?o?arin canza akalar tunanin nashi yayi gudun kada ya fama raunin dake a zuciyarshi.

Sunan Allah yaci gaba da ambato har saida yaji zuciyarshi tayi mashi sanyi tukunna Ya samu damar mi?ewa Ya nufi toilet don Ya tsarkake jikin shi.

__________________Boss Bature

A hankali dankareriyar Motarsu Ta kunno kai ta cikin Katafaren Gate din shiga gidan dake a tsare da Security Officers, motace Yar Ubansu mai numfashi tsadaddiyar Gaske, Su biyune a back seat Na motar, Alhaji musa dake a hakimce Ya kishingiWa saman seat din ta motar, Wankan boyal ne a jikin shi launin milk sun zauna mashi, daga gefen shi Alhaji Ubaid ne Cikin shiga ta shadda fara, dawowarsu kenan daga taron da suka halarta wanda akayi a head quarter na party din su.

Tun kafin Security guard din dake driving dinsu yayi parking, idanun Alhaji musa masu dauke da bacci suka hango mashi Hajiya sarah


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login