Showing 63001 words to 66000 words out of 298130 words

Chapter 22 - KURKUKUN KADDARA (TAKUN KARSHE) BY BOSS BATURE.doc

murza mashi mararshi da hannayenta, gaba Waya tagama susutar dashi wata irin zuface tasoma wanko fuskarshi
Muryarshi da matsananciyar kalasa sautinta ke fita
"Bazan iya sabama mahaliccina ba faryat, Ina jin tsoron Allah, kiyi ha?uri, Nima inajin abun da kike ji amma bazan iya ba, Kina bani wahala faryat, kema kuma kina cutar dakanki, saboda kina sona, Kina son kasancewa dani, amma kin haramta ma kanki aurena akan wani dalili naki mara ma'ana, Meyasa bazaki tausaya mana ba daga ni har ke? Faryat ki cika mana burinmu na ganin mun raya soyayyarmu, kada ki bari shaidan Yaci galaba akanki, ki fi karfin zuciyarki faryat, ki zauna kiyi tunani... " da?yar ya ?are maganar muryarshi na sar?ewa ya daddage ya 6an6are hannayenta daga ru?on da tayi mashi, da sauri ya ru?o handle din ?ofar ya fuce daga dakin

A jikin kofar Ya jingina kanshi hawaye masu Wumi suka shiga zarya akan kuncinsa.

Sautin shesshe?ar kukan faryat ne ya cika kunnuwansa, baisan ya zaiyi da ita ba, yasan da irin mugun sha'awar dake gareta sai dai shi bazai amince mata su aikata sabo ba, saboda babu Wa'a ga abokin halitta wurin sa6ama mahalicci Allah! Bazai juri sauraron kukanta ba, zuciyarshi karaya take yi, da sauri Ya sauko down stairs Cikin takun sauri Ya Nufi part din baba Obinna, zuciyarshi na cigaba da tafarfasa, Abakin kofar dakinsa Ya tsaya da yin tafiyar Ya zaro hanky, Ya goge kwallarsa, Kafin ya daidaita nutsuwarsa, sallama yayi mashi.

Daga Ciki Ya jiyo muryar baba obie

"Shigo daga ciki" BuWe kofar yai tare da shiga Ciki, adai dai lokacin Baba Obie, Yana zaune saman darduma hannun shi ru?e da cazbaha.

Ba zato ba tsammani, Yaji saukar Jazz saman bayanshi, gaba Waya ya rungume shi tare da cusa fuskarshi saitin kafadarsa, Hakan ba ?aramin Waga mashi hankali yayi ba, saboda a duk lokacin da jazz yayi mashi irin wannan rungumar to an 6ata masa raine," Yana Iya jiyo sautin fitar numfashinsa, dakatawa yayi da jan cazbahar, Ya ru?o hannun Jazz Ya zagayo da shi ta gabanshi, tare da rungume shi ya kwantar da kansa saman kirjinsa tamkar Wansa na cikinsa ko jikansa.

Cikin sigar lallashi yake bubbuga bayansa batare daya furta masa ?ala ba, har saida Yaji alamun Ya fara samun nutsuwa tukunna Ya soma magana
"Waya ta6a min shalelena"? Muryarshi adisashe Ya furta"Baba ka ta ya ni da addu'a, ita kadai nake bukata daga gare ka" ya fada batare daya raba jikin shi daga na Obie ba.

"Jazz kasan bana son damuwarka, Ka fada min koma menene nayi maka alkawarin indai baifi karfina ba wallahi zanyi maka shi," babu wasa a kalamansa
Jazz yayi fatan ace zai iya fada mashi abunda ke damunshi amma bazai iyaba, Yasan muddin baba obie yaji zancen Yana son faryat sai ya aura mashi ita, koda kuwa Iyayenta basa so, shi kuma abunda yake gudu tada husuma, saboda ba lallai hajiya saratu da Pravin su amince mashi ya aureta ba, komai zai iya faru.

Shafa bayanshi baba obie yaci gaba dayi yana fadin"Ina sauraronka, Fadamin meke damunka rabin raina"

?agowa yayi da fuskarshi wadda tuni ta ji?e sharkar da hawaye, cikin rauni na murya yace"baba, Bana jin daWin yadda wasu suke guduna saboda rashin asalina, meyasa sauran mutane ba kamar kai da daddy mubarak suke ba"? Zuciyar baba obie ba karamin karaya tayi ba, nan take ya gane gori akayi masa, bawan Allah tsantsar tausayinsa ne yakama shi.

Cigaba da yin magana yayi"Na tsani kaina baba, Rashin asalina Yana neman Yaja min na rasa abunda nakeso, kowa ya buWi baki sai yace ni Wan mai aikine bani da asali, Har shege ake kirana baba" da?yar ya kare maganar wani irin kukane Yaci karfinsa da sauri Baba obie Ya janyoshi zuwa jikinshi sosai Ya rungune shi, Yana lallashin shi.

"Toh toh ya isa ka yi shiru, Bana son Kana sanya damuwa aranka, Kukan Ya isa haka, kowani Wan adam da ka gani a duniyar nan da irin tashi ?addarar, babu wanda Allah baya jarabta, inaso ka rungumi wannan amatsayin ?addararka, Kada ka ta6a bari wani Yasa ka canza tunaninka, Allah Shi yake son ganin rayuwarka haka, Kuma shine zai nema maka mafita" nasiha mai ratsa zuciya baba obie Yaci gaba dayi mashi har saida yaji ya daina kukan tukunna Ya raba shi daga jikinshi
Cikin kulawa yace dashi"Yanzu fada min wanene Ya tsokane ka"?
Shiru yayi batare dayace komai ba, baba obie ya fahimci bayason ya sanar da shi, hakan yasanshi cewa"Ko da yake basai ka fadamin ba, ni da kaina zan binciko wanene, kuma zan hukuntashi" ya fada yana daure fuskarshi alamar ranshi ya 6aci.

"Baba," Kallon shi obie yayi ina sauraronka
"Kamar yadda nasaba fadamaka,Yau ma zan maimaita maka, Ni dai inason family Winka, Ina alfahari daku, nayi fatan ace nima ina Waya daga cikin jikokin ka sai dai Allah bai nufa"

Wani irin annurin farin cikine Ya bayyana akan fuskar baba obie.

"Jazz baka Wauke ni kamar yadda na dauke ka ba, ko da yake ba laifinka bane, laifin wadanda suke yi maka gorine, sune sukasa kake jin kanka bare afamily dina, amma inaso kasani, baba obie baya yi maka kallon bare, inasonka jazz kamar yadda nakeson jikokina, Kamar yadda kake fatan ka zama daya daga zuri'ata nima haka nake fatan ka kasance" yayin da baba obie ke yin maganar, wani irin sanyi da daWi ne ke tsuma zuciyar jazz, har abada bazai ta6a mantawa da halaccinsu agare shi ba.

Ganin Ya faranta masa raine yasa baba obie cewa"namanta ban tambayeka ba, Ya jikin naka"?

Fuskarshi dauke da murmushi Yace"naji sauki, nagode na kulawarka agareni"
Jinjina kai baba obie yai"gobe idan Allah yakaimu, Ina fata zaka halacci Dinner din Hateem"

Jim ya Wanyi harga Allah baison zuwa kodan gudun a ci mutuncinsa, amma saboda yana son ya faranta ma baba obie yasa shi cewa "In sha Allah tare dani za'a buWe taro"

Murmushi baba obie yai masa"Naji dadin jin hakan rabin raina.

Jan shi da fira baba obie yai, kamar wani abokinsa, tuni jazz ya saki jikin shi.


*=؋? UMMIN AMERICAd'*


Duk Yinin Yau Bata fito daga Waki ba, ta killace kanta tun safe bata jin daWin zuciyarta, duk ta ?untata kanta, tayi jiran zuwansu unaisah su shigo don su We6e mata kewa sai dai shiru babu alamarsu, tuntana sa ran ganin su har ta fidda ranta, ta ?undundune kanta cikin lallausar bargonta, Sallah ce kaWai take tada ta daga saman gado
Har ta fara nutsawa cikin baccinta kwatsam wayarta dake ajiye kan nightstand ta soma yin ruri, da wata irin kasala ta Wago da kanta, sumar kanta duk ta hargitse babu gyara, laluba Hannu tayi ta kamo wayar batare data duba sunan mai kiranta ba tayi picking tare da kara wayar a kunnanta.

Sautin Muryar NATASHA ne ya Daki Dodon Kunnanta"nayi fushi Kin manta dani ko"? ta faWa cikin harshen turan ci.

Muryarta da kasala Ta furta"ba haka bane Natasha, Kina araina, dake nake kwana dake nake tashi"

"Ban yarda da kalamanki ba Ummi, Idan Dagaske kinyi kewata meyasa baki kirani ba? Sai da na kira ki ni da na damu dake ko"?

Shiru tayi na Wan wani lokaci har sai da Natasha Ta furta Naji kinyi shiru tukunna taja numfashi tana faman sauke ajiyar zuciya tace"bansan yadda zanyi maki bayani ba NATASHA, ni kaWai nasan halin da nake aciki, ina cikin damuwa, Ina cikin kaWaici, Rayuwata a ?untace take natasha, bani da wani ?an ci, ba wanda Ya damu dani, tun safe bana jin daWin jikina babu wanda ya le?o Waki na don Yaga awani hali nake aciki.... "Muryarta na rawa ta ?are maganar, tamkar zata fashe da kuka, hakan Ba ?aramin Waga Hankalin Natasha Yayi ba, Jin sautin miryar aminiyarta da alamun matsananciyar damuwa..
Cikin saurin mirya ta furta"Ummi, muyi magana ta video Call, Inason naganki ko hankalina Ya kwanta"

"Toh, amma kafin nan zan shiga toilet, ?an mintuna kaWan Idan na fito zan kiraki" natasha ta amsa mata da toh, bayan ta yi rejecting Kiran, ta daura wayar kan drawer, kafin Ta sanya hannu ta yaye bargon data lullu6a da shi, Jallabiya ce a jikinta launin dark ash, saukowa tayi daga kan gadon ta nufi toilet, After Some minutes ta fito fuskarta da alamun lemar ruwa, Laptop dinta dake ajiye kan desk ta dauko ta koma kan gado ta zauna daga tsakiya ta ajiyeta agabanta, kafin ta buWe ta soma sarrafata, Natasha ta kira video Call nan take ta Waga, kallon juna suka soma yi tamkar suna a wuri Waya, Natasha tana a kishingiWe saman beach chair dake a ga6ar teku, babu suturar mutunci a jikinta, dama ita bata cika son sanya suturar da zata rufe mata tsiraicinta ba, tafi sha'awar ta sanya pant da bra.

cikin harshen turanci suke yin magana.
"Yanayin fuskarki Ya tabbatarmin da bakyajin dadin Ummi, Ki faWamin meke damunki? Waya ta6a min ke"?

Yamutsa fuska Ummi tayi tamkar batason furta maganar tace"kamar ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????yadda na faWa maki bana jin daWin jikina, narasa gane meke damuna, amma ina da tabbacin hada kaWaici, ban ta6a ?untataba Irin na Yau, Jin kaina nake tamkar Ina a prison"

Cikin kulawa Natasha tace"meyasa ba zaki janye aikin da Commender Ya baki ba? Ummi dama ni nasan bazaki Iya jurewa ba, tuntuni naso In gargaWeki saboda ba zaki Iya ba, mu da muka saba da yawo kullum sai mun fita wurin abokan harkar mu, taya zaki Iya jure rayuwar kulle"? Ta faWa tana mai dubanta,
Dafe kai Ummi tayi da hannu Waya"Har yanzu banyi danasanin kar6ar aikin kula da yaran nan ba, Saboda Inaji araina akwai wani alkhairi atattare da zamana da su, shiyasa bana danasani, ni kawai abunda ke damuna rayuwar kullance ke banaso, Yana ?untata Rayuwana, hada ?arin Yaran da suke Webe min kewa basu zo wurina ba yau, ni kuma nakasa tashi naje gare su" fuskarta a yamutse tayi maganar
"Har Yanzu ba zaki fahimce ni ba Ummi, Ni inaso na kwatarmaki ?an cinki ne, Inason farin cikin ki, Kina bu?atar abokan Harka, kefa ba irin matan da za'a ?untata ba ne...' tunkan Natasha ta ?are maganarta, ummi tayi saurin tarar numfashinta da cewa

"Akwai labari mai daWi, nasan idan na fada maki zakiyi mamaki"

Ta faWi hakan ne don batason Natasha taci gaba da yi mata zancen Ajiye aikin da take Yi.

"Na?osa naji labarin nan fadamin mana" ta fada tana sakin murmushin sha?iyanci.

"Mutumin Ya ziyarce ni Har cikin gidan da nake,"

Waro idanu waje natasha tayi da mamaki ta furta kina nufin Big Boss? Ya ziyarce ki? ?aga mata gira ummi tayi alamar eh.

"Amma ya akai ya iya shigowa gidan Jami'an Isod, bayan kin faWamin acikin sharuddan da suka baki, babu shige babu fuce basu bu?atar wani naki yazo inda kike, har zuwa lokacin da kika kammala Yi masu aikin su" ta faWa a kagare da son jin ?arashen xancen.
Dariyar sha?iyancin Ummi tasaki tamkar babu damuwa aranta"kinsan mutumin na dabanne, ni kaina bansan tayaya akai ya shigo gidan ba, Har tambayarshi nayi sai yace min idan na yarda dashi indaina tambayarsa.... " dariya natasha tayi cike da nishaWi tace"Namijin Duniya, Nayi kewarshi ummi, kullum cikin begen ganinsa nake yi, yayi min nisa yanzu, ba kamar lokacin da nake yi mashi rainon babynsa Pretty ba, tun da Ya kar6i Yarinyar sai nayi dagaske nake ganin shi, ko wayana baya picking... " kafin Natasha ta ?are maganar Ummi tayi hanzarin tarar numfashinta da cewa"wai ina yarinyar take ne? Na jima ina son na tambayeki ita, nayi missing dinta, tun ranar dana fara Yin tozali da ita naji kaunarta ta shiga raina, duk da bata jin magana amma tana da kyau"
Natasha tace"hmmm, Ummi Ya raba ni da ita, tsawon watanni, duk idan na tambayeshi ina baby Pretty na sai yace min ya mayar da ita wurin mamanta, har alfarma na nema awurin shi akan ya amince min inbiyo shi nigeria saboda ina son ganinta amma Ya hanani.... "muryarta na rawa ta ?are maganar idanunta sun cicciko tab da kwalla.

"Ummi Inason yarinyar nan, Ina ?aunarta, nayi fatan ace ni na haifeta ko dan saboda mu kasance atare har abada, mun sha?u da juna, na saba da ita, Amma yayi min yankan ?auna.... " tunda tafara magana ummi ta natsu tana kallon fuskar Natasha ta cikin screen din laptop tamkar suna awuri Waya.

"Ummi nasan zaki Iya taimaka mani, tunda Yana kaunarki, Yasha fadamin ke kadaice kike Iya sarrafashi son ranki, please kiyi amfani da damar da kika da ita, Ki lalla6a shi Ya dawo min da baby pretty" cikin sanyin Murya ta ?are maganar, Ummi dake kallonta tuni tausayinta Ya kamata, bata ta6a ganin Natasha tana zubar da kwallarta akan wani Wan adam ba sai akan babyn da take mutuwar so, tasan da irin kaunar da take yima yarinyar a lokacin baya.

Cikin kwantar da murya ummi ta furta"Am sorry, Kinsan bana son ganin hawayenki, zan Iya yin komai akanki, saboda halaccin ki agare ni, Kin wuce ?awa a wurina sai dai ?ar uwa, saboda kin kaunace ni a lokacin da kowa yake guduna, abun da nakeso dake ki kwantar da hankalin ki, zanyi kokarin ganin na shawo kanshi don ya dawo maki da babyn ki"
Murmushin farin ciki natasha tasaki tana fadin"thank u ummi, nasan zaki iya yin komai saboda farin cikina, shiyasa nake ?ara kaunarki, ina nan ina shirye shiryen zuwa Nigeria saboda ke"

Martanin murmushin ummi ta mayar mata,
"Ina handsome boy din nan, namanta ban tambaye ki shi ba"

"Bashi da lafiya, Yana a kwance"
Yamutsa fuska Natasha tayi"najiye mashi ba dadi, Allah Ya bashi lafiya, har yau ban manta da fuskar shi ba"
Murmushi Ummi tayi mata" dama ke ay bakya mantawa da abu mai kyau, naga kin kirani da layinki Na england, hakan na nufin kin koma gidanki"?
?aga mata gira tayi alamar eh. Jinjina kai ummi tayi, shiru sukayi na wani lokaci yayin da suke kallon juna batare da ?yaftawa ba.
"Kin tsareni da ido Kina kallona, Kamar akwai wani abu da kikeson fadamin" acewar natasha ta faWa tana Wage mata gira.
Dariya Ummi tayi, Harta BuWe baki da niyar furta magana, Sautin knocking ?ofar da akayine Yasa ta fasa yi mata maganar,
"Zan Kiraki Anjima Ki kula min da kan ki"
"Bangaji da jin muryarki ba ummi, amma shikenan zan jira zuwa anjiman inma kin manta baki kirani ba, Ni zan Kira ki, ki kula min da kanki and pls ki daina sanya damuwa aranki" a hankali ummi ta furta mata"toh, nagode da kulawarki agare ni" bayan sunyi sallama, Ta kashe video Call din, ta sauko tare da laptop din a hannunta, ta nufi desk ta Waurata, kafin ta shiga wurin closet dinta, mayafi ta daura akanta.

Waga Murya ta yi Wanene"?
Daga waje tajiyo Muryar Batool Tana fadin"aunty Ummi ni ce" wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyarta jin muryar Batool.

"Ki shigo daga ciki," turo ?ofar batool tayi tare da shigowa ciki, tana bin dakin da kallo kafin ta Waura idanunta akan fuskar Ummi, Murmushi suka sakarma juna
"Nayi fushi Batool, sai yanzu zaki tuna dani? Nayi tsammanin kece mutun na farko da zaki zo gare ni idan kika ji shiru ban fito ba, amma sai naji shiru babu ke babu unaisah" tafaWa tana haWe mata fuska alamar ranta Ya 6aci.
"Aunty ummi am sorry, Kina araina, tun Wazu nake taso in shigo wurin ki'
Mi?a mata hannu Ummi tayi da sauri Batool ta ?arasa gabanta tare da faWawa kan chest dinta, sosai Ummi tai hugging dinta.

"Nayi missing dinki My babe, kun barni a daki ni kaWai inata kewarku, Ina unaisah ne"! Ta faWa batare data raba jikinta daga na batool ba.

"Nima bansan inda take ba, Wazu muka rabu"
"Okey,ina fata kina lafiya, " Wago dakai Batool tayi"Lafiyata lou, amma ke kamar baki da lafiya"
Shafa gefen fuskarta ummi tayi"bana jin dadi, amma kada hakan Ya dame ki, ganinki da nayi ya faranta raina" ta ?are maganar tare da ru?o mayafin Pakistan din batool"kayan sunyi maki kyau sai naga kinyi min kama da wata Old friend Wina da muka rabu da dadaWewa, kamar ita ta haifeki, Itama doguwace fara, Mom dinta balarabiya ce"
Murmushi batool tayi"amma ni da Unaisah nake kama"

Girgiza kai Ummi tayi"No, baki kama da Unaisah kun dai yi yanayi da ita"

Kwa6e fuska Batool tayi saboda ita tafison ace tana kama da Unaisah, ummi ta fahimci hakan sai tayi saurin cewa"wasa nake maki, dama don in ga reaction dinki ne, gaskiya kuna kama da ita sosaima kamar twins" jin hakan yasa batool sakin dariyar farin ciki, ummi dake kallonta batayi mamakin hakan ba ta riga data fahimci tsantsar ?aunar da suke ma junansu.

"Mu zauna ki tayani fira, Ko baki gaji da tsayuwa bane"

"Aunty ummi, nasan kina jin yunwa, ki tafo muje falo zan sama maki abunda zaki ci" wani irin kallon ?auna ummi keyi mata ba ?aramin dadi take ji ba idan Batool ta nuna damuwa akanta.
Ru?o hannunta ummi tayi acikin nata atare suka fito daga dakin.

Sautin Muryoyinsu Naufal ne Yajawo Hankalin Ummi Ga kallon su, tun Dazu suna a falo, Tare da Boss Man, Sun tasa shi gaba sai surutu suke zuba mashi.

Jin takun Takalmansu Yasa su dagowa suka kalli su Ummi dake saukowa down stairs, Har suna haWa baki wurin ambaton sunanta Aunty Ummi.
Saukowa Jamimah da azeeza su ka yi daga kan sofan da suke zaune, da gudu suka nufe ta, Hannah da Parveen ma suke mi?e suka nufe, wani irin daWi taji aranta,
?aya bayan Waya ta soma rungumarsu a jikinta,
"Aunty Ummi, Yanzu kika tashi daga bacci"? Azeeza ce tayi mata tambayar
Girgiza mata kai tayi alamar a'a
Parveen tace"Ko dai baki lafiya" Harara Ummi ta jefa ma Parveen tare da cewa"kun damu dani ne? Meyasa ba ku zo bedroom Wina kun duba ni ba? Shiru sukayi sai jamimah ce tai kokarin cewa"mantawa mu ka yi" Jan kumatunta Ummi tayi da hannu"Aku sarkin Wumi, Na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login