Showing 15001 words to 18000 words out of 194140 words

Chapter 6 - BABU SO Miya kawo Kishi Book complete by M shakur.doc

M Shakur   

26 Oct 2025

3201

da bai san wace aunty take magana ba akai kamar yanda itama Fadwa da gaba Waya takaici ya turni?e takai kallonta wajen. Wuff ta kwashi kusan rabin naman daya tsole mata ido ta maida a plate Winta. Lokacin da yake juyowa fuska a tsuke harta mi?e a table Win ta koma na kusa da su da guy Win da duk hankalinsa ke kansu yake.
? ?? Plate Win abincin nasa ya kalla sai kuma ya kalleta. Kauda kansa yay gefe saboda murmushin dake neman suSuce masa. Ya Wan jinjina kansa dayin ?wafa. Fadwa dai kallonsa kawai take mamakin tsaurin idon yarinyar nan na nema sha?ureta.
? ? ?? Saurayin da gaba Waya komai na Anam ya gama tafiya da imaninsa shima fuskarsa Wauke da mayataccen murmushi yake kallonta. Ya sake sakin murmushi ganin duk laumar abincin da zata kai sai da yankan nama. Cikin murya ?asa-?asa yanda ita kaWai zataji yace,  In ?ara siya miki wani gimbiya? .
? ? ? ? Kai ta Wago ta kallesa, sai kuma ta saci kallon Shareff. Ido suka haWa, ya zuba mata hararar da hanjin cikinta suka kaWa, amma saita fuske cikin dakewa. ?asa tai da idanunta Tana ?o?arin sake kai abincin bakinta kamar bata gansa ba, saurayin ya sake Wan matsota cikin ran?wafowa har tana jin hucin numfashinsa yace,  Queen Please .
? ? ? Wani irin cije baki Shareff yayi da ?arfi, sai kuma ya mi?e gaba Wayansa. Gabansu ya iso ya Wauka wayarta da saurayin ke ?o?arin Wauka. A kausashe yace,  Tashi muje .
? ?? Kamar bazata Wago ba sai kuma dai ta Wago tana kallonsa.  Ni banfa gama ba, ba yanzu muka fara ba, ga budurwarka ma bataci nata ba .
? ?  I will slap you in baki tashi ba .
Mi?ewar tayi fuska a kumbure. Ya nuna mata hanyar waje, ko kallon saurayin baiyi ba yayma waiter nuni tazo. KuWinsu ya bata, tareda wasu yace ta masa takeaway na naman rago. Fadwa da ko lauma Waya bataiba dama ta mi?e tsam da wayarta a hannu ta fice, bayansu yabi, sai dai kafin ya fito Fadwa ta tsaida napep ta shige abunta, Anam ko jikin mota ya sameta ta haWe fuska tamau. komai baice mata ba ya buWe ya shiga, a dai-dai nan aka kawo masa takeaway Win da ya saka akayo. Jin ya kunna motar tai saurin buWewa itama ta shiga. Sai lokacin ya lura babu Fadwa, motar ya sake buWewa ya fito yana dube-dube.
Wata sha?iyyar dariya Anam ta ?yal?yale da ita harda kwanciya, tana ganin zai dawo ta haWiye kayarta da gyara zama ta fuske...
A dake yace,  Malama dawo nan .
Ido ta Wan waro tamkar bata san mike faruwa ba.  Yaya Auntyn kuma fa, ba fitsari taje bane? .
Kallon banzar daya watso mata ya sata buWe murfin ta fita tana danne dariya da ?yar, ?asa-?asa take faWin,  Ai daga yau daga kai har ita kun shiga uku da ni. Sai tasan ita ?aramar ?ar iska ce ......

&&&&

? ? ? ?? A kallo Waya zaka fahimci tsananin Sacin ran dake tattare da ita. Tunda Gwaggo Halima ta kirata ta sanar mata abinda ya faru take kiran wayarsa amma ya?i shiga. Kasa daurewa tai ta dawo falo tare da tura Hussaina gate zaman jiran shigowarsa. Mintuna goma kuwa ba'aiba cikakku da zaman Hussaina a gate sai ga motarsa ta shigo. Anam ce ta fara fitowa, Hussaina ta bita da kallo harta shige sashen Mom. Shima dake binta da kallon fitowa yay hanunsa Wauke da ledar takeaway. Hussaina ta taso da sauri tana washe baki dai-dai yana sama motar lock da key ta waje.
? ? ?  Yaya sannu da zuwa .
Batare daya kalleta ba ya amsa mata. Idonta akan ledar hannunsa ta kuma faWin,  Yaya Dama Mommy ce tace kaje tana nemanka . A yanzu kam idanunsa ya Wago yana kallonta. Sai dai baice komaiba tsahon sakkani ya janye. Ganin zai bar wajen takai hannu ga ledar.  Bara na Wauka maka to . Harararta yay, babu shiri taja baya tana tura baki gaba. Baibi takantaba ya nufi sashen Mom. Fawwaz kawai ya samu a falon zaune yana kallon cartoon. Yaron ya taso da gudu ya nufosa. Ledar ya ajiye gefe fuskarsa Wauke da murmushi ya Wagashi sama.  Oh my Friend ya kake? .
? ? ?  Lafiya lau Yayanmu. Good morning .
? ? ? Kumatunsa ya Wan ja yana murmushi. Kafin ya Wan kalla falon.  Gentlemen ina Mom ne? .
? ? ?  Tana Waki da aunty Rahma tazo .
 Okay! To kace ina gaisheta.
? ?? Kai ya jinjina masa. Sai kuma ya kai bakinsa kusa da kunnen Shareef Win, cikin raWa yace,  Aunty Anam kuma yanzu ta dawo sai fushi takeyi .
? ? ? ? ? Idanu ya Wan waro waje kamar yanda yaron yayi,  Haba dai? .
??  ALLAH kuwa. Ko kulani ma batayiba ina gaisheta da nuna mata Cartoon Wina .  Ayya am sorry my dear, maybe bata da lafiyane. Amsa wannan ka kai mata sai kuci tare . Duk da ledar ta masa nauyi da Wan gudunsa ya nufa Wakin cike da murna yana ?wala kiran  Aunty Anam! Aunty Anam!! .
? ? ? ? Idanu yaWan lumshe a hankali da harWe hannayensa duk biyu a ?irji yana murmushi har yaron ya shige ciki. Haka yake shi mutum ne mai tsananin son yara. Bai shirya aure yanzu ba, amma saboda son da yakema yara ya sashi amsar tayin su Mommy dan ta matsu taga yay aure ya rasa dalili?.

? ? ? ? Shigowarsa falon yasa Hussaina saurin yin shiru ta haWiye sauran gulmar da take faWama Mommy. Sai dai kuma yama riga yajita, kallon daya watsa mata yasa tai saurin barin falon tana tura baki gaba.
? ??  Shareff kai dawa kaje gidan Halima!! . Mommy ta faWa a fusace tunkan yace mata komai. ?an jimm yayi na wasu sakanni, sai kuma ya Wago yaWan dubeta.  Mommy ni ban shiga gidanba ma balle naje da wani . Harara ta watsa masa.  Wlhy Al-Mustapha ka kiyayeni a gidannan. Idan kace zamu saka ?afar wando Waya da kai bazakajita da daWi ba! Yanzu na kiraka nace kasata a napep ta dawo shine danka rainani ka Wauketa kukaje wajen wadda ke shirin zama matarka har kana mata wala?anci a gabanta ko?! Ita kuma shegiyan yarinyar mai kama da ifiritin aljanu haihuwar bakwaini tana mata rashin kunya, to idanma wani abune a ranta tun wuri ta fiddashi dan har abada bazan haWa zuri'a da Usman ba, sunga ta rasa miji a can shine zasu kwasota su kawo nan talla...... . Murmushin yay da tasowa ya dawo kusa da ita, sai dai a ?asan carpet ya zauna ya Wora kansa jikin ?afarta, hanunta ya ri?o cikin nasa murya a sanyaye,  First-luv Please cool down, yaronki bashi da wata mata bayan zaSinki, idan ma hakane a ransu ai bani kaWai bane Wa a gidan ko?!.....
? ? ? ?  Ko kai kaWaine bazaka aureta ba, kuma ko yanzu dan kayi aure idanma hakane a ransu Maheer ma yafi ?arfin nan sai dai suje can su nema mata miji dan ko Khaleel saina hana uwarsa yarda .
? ? ?? Murmushi ya saki mai faWi da lumshe idanunsa. Yayinda kunensa ke cigaba da sauraren banbamin masifar Mommy. A haka su Aysha suka shigo suka samesu. Gaisuwar da suke masa ce ta sashi buWe ido da tashi daga jikin Mommy yana kallonsu. Kafinma yace wani abu Hassan yay saurin faWin,  Yaya daga aikan Gwaggo muke fa . Komai baiceba ya mi?e ya fita a falon.

___________________

? ? ? ? A yau da Anam ke cika kwanaki biyar a gidan ya kamata ta fara shirin fita aiki, amma mutuniyarku barcinta take sharSa saboda jin daWin Wan sanyi-sanyin safiyar dan bata isashen barcin dare daboda zafi. Da zarar an Wauke wuta bazata sake rintsawaba. Dan ?ar fan Win da Mom ta bata Fawwaz ya joganeta jiya ta?i Waukar caji. Gaba Waya Mom ta shafa'a da batun fara fitar Anam Win yau itama, shiyyasa batai tunanin tadata ba tanata ?o?arin shirya su Fawwaz karsu makara tafiya makaranta suma. Sai daga baya ta tuna taje ta kakkaSeta da ?yar..

? ? ? ? Kamar kullum cikin shirin fita office ya fito. Shareff mutum ne mai himma, bashi da wasa akan aikinsa shiyyasa a kullum cikin haSaka kamfani yake. Zamansa tsayayyen mutum yasa ma'aikatan ke tsananin shakkarsa da kiyaye dokokin kamfani, dan shi babu ruwansa yana ganin baka serious zai sallameka ne acewarsa a kwai dubu masu bu?atar gurbinka zaune a gida. Sashen Mommy ya fara shiga, ?anensa nata ?o?arin karyawa suma. Cikin girmamawa duk suka gaidashi. Amsawa yay yana ?o?arin kaiwa zaune a Waya daga kujerun falon dan bazaka taSa ganinsa cikinsu yana cin abinciba. Mommy dake tsaye itama a dining Win tana haWa masa tea ta ?araso garesa. Tunkan ta ?araso ya mi?e fuskarsa Wauke da murmushi ya amsa mug Win.  Good morning First-luv .
? ? ?  Morning dear, how are you? .
 Alhamdulillahi .
? ??  Haka ake so ai. A saka maka Irish Win? .
? ?  No Mommy wannan Win ma is ok for me. Yau na makara gashi inada meeting eight thirty .
? ? ? ?  To aiko gara ka hanzarta tunda gashi eight Win gab yake dayi .

? ? ? Koda ya fito sashen Mommy wajen aunty Amarya ya shiga suka gaisa kamar yanda ya saba duk safiyar duniya zai shiga ya gaida kowa na gidan. Daga nan kuma babu mai sake ganinsa sai wata safiyar, sai dai duk ranakun juma'a da laraba zai sayo fruit bayan ya tashi aiki ya shiga kowane sashe yakai musu, hakama duk ?arshen wata zai sayi kayan tea dasu sabulai omo MacLean kayan dai bu?ata kananu yakai kowane sashe. Tun Mommy najin haushi da masa faWa har dai ta tattara ta zuba masa ido amma hakan na damunta da Sata ranta saboda zugar Gwaggo. Sashen Gwaggo ya nufa itama ya gaisheta dan itace a tsakiyar Mom da aunty amarya. Yasanta da son su zauna hira dan haka ya ma?ale daga ?ofa suka gaisa duk da tayin kunun gyaWa da take masa kuma ransa naso.
? ? ?  Gwaggo na makara, amma zubamin zanje da shi office nasha. Bara na gaida? Mom a kaimin mota .
? ? Kafinma tace wani abu ya fice da sauri zuwa sashen Mom idonsa akan agogon dake a tsintsiyar hanunsa. Gaisuwar su Fawwaz ya fara amsawa dake fita da gudu zuwa school bus Winsu. Kafin ya ?arasa cikin falon su gaisa da Mom. Itama nan koda tai masa tayin abinci cayay Alhmdllhi ya fito da hanzari. A jikin motarsa ya samu Ladi mai aikin Gwaggo Wauke da ?aramin basket. Tunkafin ya ?araso ya buWe motar da key tai ?ar ?ara.  Ranka ya daWe gashi inji Gwaggo . Baice komaiba ya amsa basket ya ajiye a gefen mai zaman banza, fitowar Daddy ta dakatar da shi daga yun?urin shiga motar da yay niyya ya nufi Daddyn Win duk da sun gaisa bayan fitowarsu massalaci da asuba, tare kuma suka fita motsa jiki....
? ? ??  Babana har an fito? .
??  Eh Daddy nama so makara dan inada meeting .
? ?  To ai yau da gobe sai ALLAH ko . Daddy ya faWa dai-dai da fitowar Anam daga sashen Mom. Tsaf take shirya cikin kayan NYSE da sukaima jikinta cif kamar ka saceta ka gudu. Ta naWa yololon veil Winta tare da Wora p-cap Win samansa, saita goya bag Winta mai suffar teddy data zuba komai a ciki. Tayi ?yau sosai sai zuba ?amshi take mai daWi. Fuskarta ?awace da murmushi ta nufo inda suke, sai da ta sauke hular daga kanta tace,  Good Morning Daddy .
? ??  Good Morning Maman Daddy. how are you? .
? ?  I'm fine Daddy, sai dai zafi da dare barci babu daWi .
? ? ? ??  Ayya mamana ba'akwai fan a Wakin naku ba? .
?  Akwai Daddy, idan suka Wauke nepa Winne fa, fan Win da Mom ta bani ya?i Waukan cagi jiya .
? ?? Kanta ya Wan shafa da faWin,  Am sorry insha ALLAH za'a saya miki wata to koda an Wauke wutan, koma ac za'a sayo dai? .
? ? ? ?ar dariya tayi da satar kallon? Shareff da tun zuwanta wajen ya haWe fuska yana danna waya kamar bai san da zuwan nata ba. Shima Daddyn dariya yay da duban Shareff Win,  Kun gaisa da Yayan naki ko? .
? ? ? ? Baki taWan tura gaba da Sata fuska, sannan tace,  Good morning .
? ??? Duk da sarai yajita bai amsaba, sai duban Daddy yay yana tura wayarsa a aljihu da faWin,  Daddy bara na wuce ina ?ara makara .
? ? Daddy yace,  Ato shikenan sai kije ya saukeki tunda hanyarsa ce .
? ? ?? Idanu ta waro da ?yau tana ?ya?y?yafta su.  Daddy Abie yace driver zai dinga kaini .
? ??  No na dakatar da shi ai. Duk motocin gidan nan ace sai an Wauka miki wani driver. Idan Shareff zai fita sai ya dinga tafiya dake, idan ya tashi aiki kuma ya Wakkoki ba shike nan ba .
? ? ? ?? Zatai magana ya girgiza mata kai alamar kartace komai. Shirun kuwa tai, sai dai kamar zatai kuka takeji. Sam bata bu?atar haWa sabgarta da shi. Duk miskilancin Khaleel tafi jin daWin zama da shi, shiko Maheer dama mutum ne mai sau?in kai da faran-faran, shiyyasa da akace mata bayanan taji duk babu daWi.
? ? ? Ganin shima baice komai ba Daddy ya dubesa  To ALLAH ya bada sa'a. Sai ka wuce da Mamana ko .? Kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ya Wan rissinar da kansa ?asa da fadin.  Mu yini lafiya . Jinjina masa kai shima Daddyn yayi.  ALLAH yasa. Mamana bishi ALLAH ya bada sa'a .  Amin Daddy ta faWa dabin bayan Shareff da tuni yay gaba abinsa kamar ta make masa ?eya..........
'

_>?-?>??maza ki make to dan ALLAH_.


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS=?G?
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA=?G?
09134848107




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O?



*_d'
=?%?BABU SO....!!d'
=?%?_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce>??

*_07_*


.........Tunda suka tafi tsakanin shi da ita babu wanda yayma Wan uwansa magana. Yanata tu?insa da amsa wayoyi itako tana buga game a wayarta cike da nishaWi har suka iso. Motar ta buWe tai ficewarta tana taSe baki, sai da ta rufe masa ?ofar batare data kallesaba tace,  Jazakallahu khairan tai gaba abinta. Fusgar motar yay da ?arfi yay gaba har yana tada ?ura. Hakan yasata faWin,  Kaji dashi in kayane dai .

? ? ? ? Koda ya tashi a aiki baibi takanta ba yay wucewarsa gida. Tun Anam na jira da marmari har ranta ya fara ?una gashi bata sayi layin Nigeria ba har yanzun. Sosai ranta yake a Sace ga yunwa dake bala'in cin hanjinta dan bawani abun kirki taci da safeba ta fito, da rana ko inibi data taho dashi a bag kawai tasha da strawberry. Ganin yamma na ?ara mata, gashi bata san yanda zata kira wani a gidan ba tunda babu waya ta fito domin samun abun hawa ko zata iya ganewa. Ga wani irin zafi dake ratsata duk da rana ta risina kasancewar anyi la'asar, sai dai ita zafi takeji matu?a kodan inda ta fito akwai ac ne.
? ? ? ? Ta tare abin hawa yafi sau huWu amma ta rasa yanda zata musu misalin anguwar, wasuma basa gane jagulalliyar hausarta da yaren malay ya cinye, turancin ma idan tayi wasu suce basaji wasu suce basu fahimci kwatancenta ba. Kanta ta dafe ?walla na cika mata ido dajin wani irin tsanarsa a cikin ranta, tabbas bata ?aunar wula?anci shiyyasa bata wula?anta kowa, kai bama ta tashi taga iyayenta na wula?anta wani ba kowa abin girmamawarsu ne koda bai kaisu wani matsayi na duniya ba. Hannu takai a hankali ta share ?wallar idanunta tana maijin kewar iyayenta da ?aunarsu, waWannan matsalolin na Waya daga cikin abinda ta guda a zuwanta hidimar ?asa Nigeria, amma su Mamie suka kasa fahimtarta.......
? ? ? ? Harya gota ta ya dawo baya da mamakin kodai gizo idonsa ke masa. Dai-dai saitin da take yay parking da sauke gilashin motar. Tabbas itace inhar bai ruWeba, dan yanda yarinyar ta shiga ransa bayajin zai manta fuskarta koda a barci ya tashi.
? ??  Beauty! .
? Ya faWa cikin tsantseni da taraddadin wasiwasi.
? ? ? ? ?? Duk da tajisa tunma tsayuwarsa hakan baisa ta Wago ba. Sai ma sake haWe fuska da tai ta Wauke kai gefe fiye da yanda ya sameta. Murmushi ya saki dan yanda tai Win ya tabbatar masa ita Wince. BuWe motar yay cike da farin ciki ya fito.  A gafarce ni. Assalamu alaiki ?ya?y?yawa . Duk da bata saki fuska ba ta amsa masa. Ya koma ta gabanta cikin sake raunana murya.  Inaji a jikina ke rabonace Beauty. Ranar Yayanki ko saurayinki ne ban saniba ya gudumin dake gashi yau ALLAH ya haWamu daga ni sai k . Karon farko ta Wan Wago ta dubesa, ya sakar mata murmushi.  Dan ALLAH kar kice baki ganeni ba .
? ??  Bamma taSa ganinka ba .
Ta faWa da ?o?arin barin wajen. Sauri bin bayanta yay.  Please dan ALLAH karkimin haka. Ni ne wanda muka taSa haWuwa a GJ restaurant da daddare . Sarai ta ganesa tun kiranta Beauty da yay dan muryarsa bata bace mata ba. Amma sai ta sake Sata fuska aWan fusace tace,  Bani bace Please kabar bina .
? ? ??  Kiyi ha?uri bazan iya daina binki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login