Showing 162001 words to 165000 words out of 194140 words

Chapter 55 - BABU SO Miya kawo Kishi Book complete by M shakur.doc

M Shakur   

26 Oct 2025

3187

Mommy irin wannan
maganar? .
 Ya bazan faWa mataba Anaam. Kin san ko
suwaye su aunty Safarah? Wlhy rashin faWar shine mafi munin kuskure dan hatta ke da kanki sai sun sabauta rayuwarki, Wan sauran zuminci kuma da muke tattali su Sarar mana da shi. Ita kanta Fadwa Win taimakonta nayi, dan wata ?ungiya garesu ?an baza'a zauna da kishiya ba, inma an zauna da ita saita koma tamkar babu ita a wajen miji, kina tunanin a hankali bajan ra'ayinta zasu cigaba dayi ba harta koma cikinsu. Koba komai ita Win jininmu ce, yana da ?yau muyi duk yanda ya dace domin ta dawo hayyacinta. Yaya baya son yanke hukunci cikin fushi, amma tunda kikaga yau yakai da marinta to idan takaisa ma?ura komai zai iya lalacewa .
(Aysha kenan, dan ma bakisan akan sani ta zubar da ciki ba akan makircin kakarku) Anaam ta faWa a zuciya, a fili kam saita kai zaune tana mai dafe kanta.....
A Sangaren Fadwa kam Mommy na yanke waya kiran Gwaggo Halima na shigo mata.

Sabon kuka ta Sarke da shi tana zayyana mata
abinda ya faru, harda kiran Mommy datai
amma ta yanke mata waya...
 Kan ubancan, mi Nafi ke nufi Share! ya
mareki ya mari banza?. A to lallai idan tace wannan layin zamubi ni da ita bazatai mana ?yau ba. Ai dama su Malika sun tabbatar min abinda yafi hakama zai iya faruwa saboda Nafi maciji ce da fuskar tana. Aiko zan tabbatar mata Share! bai mareki a banzaba dan wlhy saina rama miki . Ta yanke wayar.
&Sai da Gwaggo ta gama sauraren Mommy data isa sashenta a rikice tsaf sannan ta saki murmushi irin nasu na tso!in makirai. Domin kuwa anzo gaSar da ta jima tana jira kenan. Kallon Mommy tai da dafa kafaWarta.  Nafisa Halima zata iya fiye da haka domin wannan ?ar tata. Jikina ya fara sanyi da al'amarinta tun lokacin zubewar cikin Fadwa. Karki manta itace ta fara kawo shawarar a sami malamin dazai aiki akan Mustapha da yarinyarnan ta wajen Usman. Abinda yasa na?i yarda a lokacin na tabbatar idan muka biye mata wataran zata haWo wani abin a bama Share! yaci a zuwan dan ana son rabashi da Zuwaira ne. Ki tuna Halima ?udace, domin samun biyan bukatarta rai ba'a bakin komai yake ba.

Tunda kuma ta haWa kai dasu Malika to komai zai iya faruwa da Mustapha ciki harda rabashi da ke kanki uwarsa, dan kuwa ke shaidace, nice na haWa auren Halima da Sadiqu, amma gashi nan babu mai cin dukiyarsa daga ita sai ?a?anta sai wanda ta zaSa a dangi. Gasu Muhammadu nan ?an uwanta tasan yanda zata samesu gefe ta kalallame ta dawo wajenmu tana nuna mana tana tare damu. Kin dai san duk son da Halima zatamana bai kai ya na ?an uwanta ba tunda ba haihuwarsu nayi ba. Kuma kodan wannan dukiyar dake zagaye da Mustapha ai Halima bataso zaunawa ba tunda tasan yanda ta mallake Sadiqu dolene itama ?arta ta mallaki Mustapha yanda koke kanki bai isa yaji maganarki ba, danni tawa mai sau?ice kwana nawa ya rage ALLAH na tuba .
Kalaman Gwaggo ba karamin hautsuna zuciyar Mommy sukai ba. Gaba Waya tama rasa ina zata kama ta ri?e a wannan gaSar. Shigowar kiran Gwaggo Halima ya saka tunaninta katsewa. Ta dubi Gwaggo,  Itace fa take kirana .
 ?aga muji mizata faWa, nasan dai ?ar tata ta kirata itama ai .
Dagawa Mommy tayi, ta saka hansfree yanda itama Gwaggo zata iya ji. Daga can Gwaggo

Halima dake a wuya muryarta a sha?e ta fara
magana batare da ko gaisuwa ba.  Yanzu
Fadwa ke kirana Share! ya mareta, tace kuma
ta kiraki ta sanar miki amma bakice komaiba
kin yanke waya. Kome hakan ke nufi kenan? . A harzuke Mommy ta maida mata murtani.
 Abinda duk zuciyarki ta baki Halima. Nifa
bazan Soye miki ba na gaji da yawan kai ?arar
Fadwa. Ita kullum bazata iya ha?uri da miji ba
saita kawo kararsa. Ko haka taga wani a
cikinmu nayi? Sannan kin tambayetama mita
masan ya mareta? Taya zata kai masa ?awaye
Wakinsa na sirri su gyara saboda rashin sanin
ciwon kai. Ni yamun dai-dai, kinga gobe idan
??
ta sake saiya mata dukan tsiyama ba mari ba.
Sannan Halima ki sani, dukkan ?ulle-?ullen
da kukeyi ke da su Malika naji kuma na
sani......
 To idan kinji kin sani Win sai yaya Nafi? Kin
goya bayan Wanki akan marin da yay yarinyata ma, to wlhy ki sani da hannuna zan rama mata marin da yay mata, idan shi Win mahaukacine zan maidosa hankalinsa kuwa. Kuma karki manta duk wani ?ulli da tuggunki a tafin hanunna suke, ko dama wanzami baya son jarfa ne, yanda kika mallakemin Wan uwa kike tunanin ke naki Wan bazai mallaku ba. Hhhhh Nafi idan kikace wannan layin zamubi

ni da ke akan Share! da Fadwa wlhy muje
zuwa Wan halak ka fasa....
 Halima idan kin isa ke tujararriyace mu
zuba Win dan ALLAH, ni dake za'aga mai iko akan wannan auren. Shiyyasa dama ni tun farko ban so wannan haWin ba kika katsatstsare ke da Gwaggo sai anyisa. Bayan nasa ?arki bata da tarbiyya ko mis?ala zarratin..
 Matsalarkuce kuma wannan, ni nagama dake kuma muje zuwa Wan halak ka fasa . Gwaggo Halima ta faWa da yanke wayar. Wani jijjiga Mommy tai zata maka wayar da ?asa Gwaggo ta ri?eta.
 Kefa daWina dake baki da hankali idan ranki ya Saci, ki nutsu, har mi akai kai Halima ne ma. Ai wannan ya?in namune gaba Waya, shiyyasa naita nuna miki ki kwantar da hankalinki akan haukan da kike na tsinema Mustapha a banza saboda farin cikin Halima da ?arta. To gashi nan tun ba'aje ko'inaba sun fara nuna miki halinsu .
Kukan takaici da ba?in ciki Mommy ta fashe da shi...........
Ashe haka duniya take ?afar kazace. Aminai biyu ya hakane ? Yanzune fa wasan na ainahi zai fara, dan za'ai yunwa muga cikin

kowa .
Next Chapter
Leave a comment
[11/18, 10:04 PM] +234 706 492 2404: 70
BABU SO
Chapter: 70 Share:
Report
BABU SO View: 283 Words: 2K
Chapter 70 70
........Wasa farin girki wai amarya da tu?a

tuwon tiya goma. Ashe rikici a waya tsakanin Mommy da Gwaggo Halima somin taSi ne. Dan kuwa ba'a rufa awa guda cikakkiya ba sai ga Gwaggo Halima tazo gidan. Hakan yayi dai- dai da dawowar Daddy daga wajen aiki gidan shima. Yay sagade yana kallon Gwaggo
Halima data ?araso garesa tana huci.  Halima lafiya kuwa da magribar nan? .  Inafa lafiya Yaya, Share! ya buWe ?wanji ya
shashsheka ma Fadwa mari amma saboda
son zuciya irin na matarka ta goya bayansa
saboda itace ta haifesa .
Da mamaki sosai yace,  Mari fa dai? Ya
ALLAH mike damun Share! haka? Wannan ba
maganar nan bace shiga ciki nafara zuwa salla
kafin su Abubakar su dawo .
A maimakon sashen Mommy ko Gwaggo da
da idan tazo gidan take shiga yau sai ta nufi sashen Mom.....
________________&
Rashin fitowarsa har aka kira sallar magrib yasaka Anaam kasa zaune ta kasa tsaye. Tana son zuwa dubashi tanajin tsoro. Gani take kamar itama Win marin nata zaiyi. Harga ALLAH tana matu?ar tsoron duka a rayuwarta. Koda wani taga ana duka firgicewa take. Ballema har abada bazata taSa iya

manta dukan dayay musu ba ita da Aysha. Da sauri ta juyo jin motsin buWe ?ofa. Sukaima juna kallon cikin ido ita da shi, ita ta fara janye nata tana sauke ajiyar zuciya dajin shakkar
kallon fuskarsa dake a matu?ar tsuke.  Ki tashi kiyi salla .
Ya faWa a ta?aice da juyawa zai fita. Harya kama handle Win ?ofar zai fita ya tsaya cak, juyowa yay a hankali yana kallonta saboda ganin yanayinta. Sai dai baice komaiba ya juya ya fita. Numfashi ta saki a hankali da mi?ewa ta shiga toilet domin Wauro alwala.
Bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i, kai tsaye kuma sashenta ya zarto. Tunda ta idar da salla ta kasa tashi a wajen, babu abinda ke mata kaikawo, haka kawai marin nan na Wazun da yay ma Fadwa ya matu?ar tsaya mata a rai, duk da kuwa ?ararsa kawai taji bawai yinsa akan idonta ba. Harya ?araso gabanta bata san da shigowarsa ba, ya kai tsugunne gabanta, tare da Wago haSarta. Cikin idanunsa ta zuba raunannun nata da babu gilashi, bata ganinsa fes yanda ya kamata, amma hakan bai hanata tsaidasu a
tsakkiyar nasan ba...  Mike damunki? .
?o?arin janye idanunta tai a cikin nasa ya hana hakan, taso kauda kanta gefe nanma ya

hana, saita ?ara tsu?e fuska da tura baki. A karon farko ya saki murmushi, tare da kai yatsansa ya Walli lips Win nata.  K wai baki san shekarunki sun girmi wannan taSaran ba Autar mata? .
Hanunsa ta ture zata tashi, yay saurin
dam?ota yana dariya, jikinsa ta faWa, dan
haka suka zube ?asa gaba Wayansu. ?afarsa
Waya ya kwanta, tare da jawota ya kwantar a
cinyarsa ita kuma. Ya tokarar da Wayar ta
jingina kanta.  Nayi laifi ne wai? .
Hanunsa dake kan cikinta ta kamo, ta saka
babban Wan yatsan a bakinta ta ciza.  Wai wai
shiii! Wace mugunta ce muka wannan? .
Dariya ta ?yal?yale da shi.  Noorie muguntafa
babu ?yau sam sam . Ka Wan ta murguWa
masa baki  Punishment Win mai yawo ne ai .  Shi kuma punishment Win mai rashin kunya
fa? yaya ya kamata ya kasance? .  Sai an binciko a littafin shara'a .
Ta faWa tana ?o?arin mikewa ta gudu. Ri?ota yay yana ?aramar dariya.  Sarkin wayo ai ni tuni na binciko. Yanzu kuma zan ?addamar da shi .
 Wayyo yaya! Wayyo ni yunwafa nakeji, tun safe banci komai ba.
 Nima ita nakeji ai . Ya ?are maganar da manne lips Winsu waje guda. Ko sau Waya batai ?o?arin hanashi ba, saima gudunmawa

data fara bashi, burinta kawai taga ya huce
daga fushinsa. Cikin ?an?anin lokaci ta gama
hautsina masa kwanyar kansa, tun yana binta
a salon jarumta harya fita a hayyacinsa ya
Wauka wata hanya da ban da karatun da ya
kasance mai girma ga Anaam. A yanzu kam ita
ya nema gigitawa, yayinda shi tuni ya fita
hayyacinsa har baya gane ita Winfa ?anwarsa
ce. Sunyi matu?ar shagala a farantama
junansu ring Win wayarsa ya shammacesu. Da
?yar Anaam ta iya janye jikinta dake rawa
gefe. Shima nashin rawar yake fiyema da tata,
sai dai jarumtar ?an mazan ta Soye haka, ya
rimtse ido da ?arfi ya sake buWewa saboda
ganin mai kiran. Ko'a turu a kwantosa bai isa
Waga wayar nan ba, dan babu makawa sai
Daddy ya gane halin da yake a ciki. Haka ya
barta harta tsinke wani kiran ya ?ara shigowa.
Yanzun ma kasa Wagawar yay har saida ta
yanke, da ?yar ya samu iya Wan dai-daita
kansa bayan wasu mintuna sannan yay kiran
Daddyn Back.
Koda Daddy yaji muryarsa a sha?e a zatonsa
duk Sacin rai ne, dan kuwa yasan wanene Share! idan yay fushi.  Ka sameni a gida yanzun nan kai da Fadwa . Bai jira cewarsaba ya yanke kiran. Shima Win baice komaiba ya koma kwance tare da mirginawa jikin Anaam

data juya masa baya ya rungumota da Waura
kansa a gefen wuyanta yana shinshina, ga
sanyin tiles na ratsasu dan harya huda
sallayar tana iya jinsa a jikinta shima haka.. Jin saukar hanunsa a ?irjinta tai saurin
ri?ewa.  Yaya kirankafa Daddy yakeyi . Iska ya Wan hura mata cikin kunne da ture hanunta ya Waura a inda yay niyya tun farko.  Koratama kikeyi kenan? .
 Eh mana, Daddy ba abin wasa bane ai,
umarninsa yana sama da muradanmu . Sassanyan murmushi ya saki da sake
?an?ameta a jikinsa, a hankali ya furta *_Ina ?aunarki da yawa_* . Sosai tsigar jikinta ta yamutsa saboda yanda yay furucin a cikin wani irin wahalallen sauti. Taja numfashi mai kauri da cije gefen lips Winta sakamakon saukar kiss Winsa saman wuyanta. Bata iya ta Wago ta kallesa ba harya fice daga Wakin. Ta sauke sassanyar ajiyar zuciya da sake kananneWe jikinta waje guda wani abu mai girma na tsikarar ?asan zuciyarta....
A sashen Fadwa kan duk da yaji a ransa itace takai ?ararsa wajen su Daddy bai mata magana ba, umarnin kawai ta samesa a mota ya bata ya juya ya fita abinsa. Taja wasu mintuna kafin ta fito dan har ya kunna mota

ma.
Tafiya suke amma kowanne fuskarsa na gefe,
ita tana kallon mutane shi kuma titi har suka iso. baiyi mamakin samun Gwaggo Halima ba, Fadwa ta nufeta ta rungumeta tana sakin kuka. Lallashinta ta shigayi tana shafa bayanta da fuskarta wai tana neman tabon marin. Abin sai ya girmi kan kowa amma babu wanda yay magana sai Mommy ce taja tsaki da taSe baki. Share! kam zama yay ?asa a tsakkiyar ?afafun Abie da Abba. Kansa a ?asa batare daya kalla kowa ba ya gaishesu. Haka kawai yakejin tsananin kunyar Abie da Mommynsa fiye da kowa a wajen.
Abba da yaga mulmular da Gwaggo Halima kema Fadwa na neman yin yawa ya magana a kausashe.  K Fadwa tashi ki zauna da ?yau bama son shashanci .
Tashin tai zaune, sai a sannan kuma take
gaidasu. Iya su mazan kawai suka amsa.
mommy da Gwaggo babu wanda ya tanka.
Gwaggo Halima tai ?aramar ?wafa da ayyana
(Zanyi maganinku) a zuciyarta.. Abie ne ya
buWe taron da addu'a, kafin ya maida
hankalinsa ga Share! cikin serious matu?a.  Al-Mustapha miya haWaka da matarka
harda mari? Bayan wannan ba Wabi'ar dakaga wani a cikinmu nayi a gidan nan bane? .

?asa Share! ya ?arayi da kansa, cikin
matu?ar girmamawa.  Kuyi ha?uri Abie nayi
kuskuren aikata hakan, sai dai saida na
umarceta ta tashi tabar inda nake dan bana
son yanke hukunci cikin fushi, amma ta?i yin
hakan har takai nayi marin .
 Amma banda abinka Babana ai kai
babbane, da ta?i tashi sai kai ka tashi ka bata
waje tunda kasan baka iya controling kanka a
yanayin fushin. Su mata ha?uri ake dasu a
kowane hali, domin hangenka da nasu sam ba
Waya bane ba, sai dai sunada sau?in sha'ani
kuma ba koda yaushe ake cizawa a kansu ba .  Hakane Abie, insha ALLAHU hakan bazata
sake faruwa ba......
 Tama sake faruwar mana. Wlhy da kaina zan
rama mata mara mutunci kawai. Kai yanzu
dan baka da kunya Share! har kanada hanun
Wagawa ka daki Fadwa a gidanka? .  Yaya Halima! Ya kamata kiyi shiru abi
komai a sannu .
 Wane kuma sannu Abubakar, bayan kanaji
yana lallaSashi saboda ba ?arsa aka mara ba . Murmushi Abie yay da girgiza kansa. Cikin
dattako da nutsuwar da kowa ya sansa da ita ya fuskanci Gwaggo Halima.  Ba haka bane Yaya Halima. Da Share! da Fadwa da Anaam duka su Win ?a?anmu ne, bazamu taSa sakaci da cutuwar Wayansu ba ai. Da kinyi ha?uri zan

kai inda kike bu?ata nima ai .
Baki ta taSe da juya kai gefe. Nanma
Murmushin Abie ya saki kawai ya sake maida
hankali kan Share! da ransa ya Saci.  Babana
ina jinka miya haWaku takai ga mari? .  Ban taSa fatan dan na samu matsala da
wata a cikinsu sai munzo gabanku ba. Amma
tunda ita tafi zaSar hakan a koda yaushe fine.
Fita nai a gida tun safe ina wajen matsalar can
data taso a company, na dawo kawai na samu
ta cikamin sashe da ?awayenta wai suna min
gyara. A yanda suke komai kai tsaye ya
tabbatar min ba yau ce rana ta farkon hakan
ba. Korarsu kawai nai na ?yaleta domin ita
tasan bana son yanke hukunci cikin fushi,
amma saita biyoni bayan nace ta ?yaleni a
yun?urin farko da tai. Taya zata kawomin
wasu ?an iska sashe, ta san adadin abubuwan
dana ajiye masu muhimmanci a ciki? Ko
bamma ajiye komaiba ita bazatai tunani da
hankalinta rashin dacewar kai wani can Win .  Inafa zata san abinda ya dace tunda a nuna
mata barbaWa magani shine kawai zaman aure .
A harzu?e Gwaggo Halima ta dubi Mommy
mai maganar.  Nafi wlhy ki iya bakinki domin
zai kaiki ya baroki allura ta tono galma .
 Yo ta tono mana dan ubanta, abu mai sau?i

bayan ta tono ita galmar ta turbuWata cikin
?ansa yanda ko mayen ?arfe ?aryarsa sake
ganinta .
Aifa nan take falon ya harmutse da hayaniya
tsakanin Mommy da Gwaggo Halima. Mamaki al'ajab sukabi suka sanya Share! cikin madaukakin imani. Yau kuma aminai biyune kema juna tujara haka akan abinda suke ganin shine mafi ?ololuwar alkairi a garesu idan suka ?ulla. Kai duniya ina zaki kaimu ne haka?. Da ?yar su Daddy suka samu sukai shiru. Gwaggo kam tayi kamar bata a falon tai mu?utt da cuno baki gaba ita a dole takai ma?urar Sacin ran abinda su Mommyn ke aikatawa. Acan ?asan ranta kuwa dariya taketa kwasa. Yanzu kam Abba ne ya amshe da zancen yana mai fuskantar Fadwa.
 K shashashar inace da zaki bama ?awaye damar shiga Wakin mijinki? Haka kikaga iyayenki na mana? Wace irin mace ce ke da baki kishin mijinki? Ai wannan jama kanki rainine ma wajen su ?awayen naki da shi kansa mijinkin. To saurara ki jini, daga rana mai kama irin tayau, hakan ta sake faruwa ni da kaina zan hukuntaki sannan shima nasa ya hukuntaki tunda koba aure tsakaninku
Yayanki ne.. Kinaji na da ?yau? .
Hawaye ta ta share tana jinjina kanta.  Zan

kiyaye Abba insha ALLAHU. Amma Abba dama fa haushina yakeji, dan dama a kwanakin nan banda wulakantani babu abinda yakeyi saboda ya ?ara aure. Baya ganin kowa a gidan sai ita ?ar gwal.....
 Shiyyasa kuka dage boka da matsubbata ke
da uwarki domin sabautamin Wa. Su Malika na
kawo miki barbaWe-barbaWe kina faman zuba
masa dare da rana. To wlhy babu lallai babu
dole tun kan ai nisa sai ya datse igiyar auren
tunda bake kaWaice mace ba a duniya......  Dan ALLAH Nafisa idan baki sakashi ya
datse igiyar aurensu ba baki cika uwarsa ba,
kuma shi din bai haifuba a cikinki...  Haka kikace? .
 Eh na faWa. bandama ?addara mi Fadwa
zatai da wani Share! can. Ko dama kun ?ulla
a haWasu aure dan ku dinga maidamin yarinya
baiwarku .
 Hahaha yo baiwa kuma ta nawa Halima.
Sai dai wata kuma dan ita kam ta riga ta gama zama labari .
?ara hargitsewa falon yay, da ?yar yanzu kam Abie da Abba suka sakasu yin shiru, dan Daddy dai ya mugun sha?a zuciyarsa har wani zallo takeyi, gata tokare a ma?oshinsa kamar yay amanta ya huta.............
End of book

End of book
Leave a comment
Post
omments
No Comments posted yet
C*_Typing=???_*




*_d'
=?%?BABU SO....!!d'
=?%?_*
_(Miya kawo kishi?)_



Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login