Showing 114001 words to 117000 words out of 194140 words

Chapter 39 - BABU SO Miya kawo Kishi Book complete by M shakur.doc

M Shakur   

26 Oct 2025

3273

ne da dama baida wasa sam, badan haka ba da ya jima da zama mijin hajiya a gidansa saboda azabar Gwaggo Halima. Hatta da yaransa suna matu?ar shakkarsa, kuskuren da aka samu kawai shine siyasa ta kwashe kaso mafi yawa na hankalinsa har takai a yanzu bai iya saka idanu a kansu. Gwaggo Halima ta nutsu a gidanta cikin matu?ar tashin hankali da ba?in ciki, tasan ko giyar wake tasha bazata taSa gangancin rabuwa da uban ?a?anta ba, domin yin hakan a gareta ba ?aramin nakasu bane, shiyyasa ta nutsu a gida zuciyarta na mata zafi da raWaWi musamman na?in jin Fadwa har a waya dan Abbansu yayi seizing wayar tata duk dan kar suyi waya, ya kuma hana har ?anenta zuwa gidan Fadwan wannan shine dalilin da yasa a ?an gidan su babu kowa a kusa da ita sai su aunty Malika dake matsayin ?anne ga Abban nata.

? ? ? ? Yau ma dai kamar kullum tun bayan kai Anaam gidan Shareff da tujarar Mommy aka tashi gidan. Sai dai babu wanda ya kulata sai Gwaggo ce da tazo wuya ta fito tai mata tatas a tsakar gidan saboda ita kam dai haukar Mommy Win ya fara kaita ma?ura. Tun Mommy na ?o?arin son nunama Gwaggo irin Waci da zafin da takeji a zuciyarta har tayi shiru ta koma kuka...
? ? ?  Gwaggo baki san irin zafin da nake ji bane a zuciyata wlhy, ji nake kamar na tsinema Shareff na huta. Ni yaron nan zai wula?anta a idon duniya ya nuna ubansa ne ya isa da shi bani ba!! .
? ? ?  Ai taimakonki yay, saboda yin biyayya ga mahaifin nasa ne ya janyowa igiyoyin aurenki cigaba da wanzu har yanzu a gidan nan shi da Usman. Ban san mike damun kankiba Nafisa, ina wayonki ina hankalinki ne? Kinbi kin ruWa kanki akan Wan abu ?an?ani da maganinsa ke'a hanunki cikin sau?i.....
? ? ? ? ?  Gwaggo taya zakice cikin sau?i? Da'a sau?ine Shareff zai kai iyanzu bai saki yarinyar nan ba har zuciyata ta cigaba da ?una? .
??  Kinbi hanyar da bazai saketa Winneba ai. Idan kin shirya cin nasara akan Wanki sai ki nutsu ki dawo hayyacinki ta ?are maganar da mi?ewa ta fice tabar Mommy da binta da kallo cikin rashin fahimtar kalamanta........

_________________________________

? ? ? ?? Gaba Waya yau bashi da ra'ayin fita ko'ina, sai dai hakan bai hanashi yin wasu ?an ayyuka ba ta cikin system Winsa. Zuwa yanzu babu kowa a sashen nasa, itama Fadwa tunda ta fita bata dawo ba. Shi kuma bai nema kowaccensu ba yanata harkokin gabansa har akai kiran sallar zuhur. Shigarsa bedroom Winsa domin Wauro alwala ya sashi jan tsaki, dan yana nan a yanda suka tashi barci suka barshi. Har cikin rai abin ya sosa masa zuciya, yana da mace har biyu a cikin gida amma sashensa ya gagara samun shara. Ba yau ya saba ganin hakan ba, sai dai bazai yarda itama Anaam ta zama haka Win ba tunda yaga Fadwa ta fara gyara nata halayen itakuma. Jiya itace tai masa gyara, bazai yuwu kuma yau tayi ba bayan ba itace ta kwana a Wakin ba.
? ? ? Koda ya fito sai da ya le?a sashin Fadwa dan tabbatar data tashi yin salla kamar yanda musulinci ya koyar da duk magidanci na ?warai. Da mai-aikinta data dawo ya fara cin karo a falo, ta zube har ?asa tana gaidashi. Hannu kawai ya Waga mata ya nufi bedroom Win Fadwa Win. Kwance ya sameta tana ramuwar barcin data hana kanta yi daren jiya, ya Wan kafeta da ido na wasu sakanni kafin ya tasheta. ?agowa tai da ?yar tana kallonsa cikin rufewar idon barci..
? ??  Tashi kiyi salla sai ki koma ki kwanta .
?? Da ?yar ta iya amsa masa da to, yasan kaWan daga aikinta yana fita ta koma, dan haka ya cigaba da tsaiwa a kanta har sai da ta tashi ta shiga toilet sannan ya fito. Sashen Anaam ya nufa, itama dai bai sameta a falo ba sai bedroom, saSanin Fadwa ita kwancen kawai take amma ba barci take ba. Taji shigowar tasa amma ta?i Wagowa ko sau Waya balle ta nuna tasan da wanzuwarsa. Tun a kallo Waya ya fahimci ba barci take ba, sai dai idanunta sun nuna taci kuka duk da suna a rufe dan ta cire glass Win.
? ? ?  Ki tashi kiyi salla .
? Bata tanka masa ba, kuma bata motsaba ya juya yay ficewarsa. Idanunta ta buWe ta raka bayansa da harara tana laSe baki. Sai da yaja kusan mintuna uku da fita sannan ta tashi domin gabatar da sallar, a ranta tana addu'ar zuwan jininta a nan kusa.
? ? ? ? Bayan ta idar da sallar saman sallayar ta cigaba da zama tana sharar hawaye, bu?atar kasancewarta da iyayenta ce ke damunta. Abinda Shareff Win yay mata Wazun a dalilin makircin Fadwa har yanzu yana cizon mata rai. Ta san tun farko dama ya tsaneta, taya bazai goya bayan matar son sa ba koda ace itace mai gaskiya. Itako ta Wauka alwashin baza'ai nisa ba balle har su sami galabar ?untata shi da matarsa, a yau Win nan za'ayi mai yuwuwa ita ba shashasha bace...
? ? ? Yawaitar ?amshin turarensa a Wakin ya tabbatar mata shigowarsa, amma sai tai kamar bata jiba duk da taji sallamar da yayi ciki-ciki. Ta gabanta yazo ya gitta ya zauna a bakin gado ta kusa da ita kaWan, dan ?afarsa Waya ma akan sallayar take. Ido ya Wan tsura mata na wasu sakanni, tayi kicin-kicin da fuska tamkar bata san da shigowarsa ba...
? ??  K kina ganin ba'a isa ace miki kinyi ba daidaiba kenan? To bari na faWa miki matata ba abin rainawarki bace, a baya kunyi abinda kuke so k da ita, amma a yanzu bazan Wauka raina juna daga kowaccenku ba. Dole ne duk mai bu?atar son zama lafiya da ni ta zauna da ?ar uwarta lafiya a gidan nan kuma cikin girmamawa da daraja juna! .
? ?? Yanda yay maganar a kausashe ya sata jin zuciyarta a wuya, hawaye ne suka shiga rige-rige sakko mata saman fuska,  Ni bance ina bu?atar zaman gidan ba ai, balle naima wata ?ar iska biyayy.....
? ? Bummm ya buge mata baki da bayan hannu. Ba ?aramin zafi ne ya ratsata ba, ta dafe bakin tana kallonsa da idanunta da sukai jazur ta cikin glass, sai dai babu hawaye yanzu a cikinsu sai tsantsar ba?in ciki da ?unar zuciya. Ya mi?e tsaye yana nunata da yatsa.  Idan kin isa mara kunya a gidan nan ki sake yima matata ko kallon banza kiga yanda zanyi dake mara kunyar banza
? ? ?? Hawayen da take ri?ewa suka Salle mata, ganin zai fice bata amayar dana cikintaba ta mi?e zumbur,  Idan na zauna kenan har za'ayi yadda za'ayin dani, inda kun kwantar da hankalinku ni dama banzo wannan gidan naku da niyyar zama ba, matar taka kuma wlhy tasa a ranta bashi taci, dan ni naci uwarta iya wasan data Wau layin muyi, dan bata kai matsayin mace ba a wajena. Itace jaka da har take tunanin mijin nata wani abin a SO ne, ni baka cikin irin mazan dazan iya SO Yaya balle muradin zama a shi gidan, ?addara ce ta kawoni nan badan rasa masoya ba. Zan kuma barsa a yanzun nan bari na har abada, dan ALLAH kuyi kwaWon juna ku cinye......
? ? ? ?? A wani irin mugun fusace ya juyo gareta, dan har ya saka kafarsa Waya zai fice a Wakin batare daya kulata ba, sai dai kalamanta na ?arshe-?arshe sun masa saukar mashi ne a tsakkiyar ?irji. Ko War bataji da yanayin nasa ba dan itama zuciyar tata irin tasance kuma a wuya take fiye da tasan. Kallonta yake da jajayen idanunsa da suke neman wargaza duk wani ?warin gwiwar ta amma ta dake.........
'? ? ?



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS=?G?
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA=?G?
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O?



*_d'
=?%?BABU SO....!!d'
=?%?_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce>??
*_BABU SO=?I?
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_48_*


........Hannunsa daya Waga kamar zai mareta ya dun?ule, yanda ilahirin fuskarsa ta canja kammani ya matu?ar girgiza zuciyar Anaam amma ta sake aro jarumatar dole ta baibaye tata fuskar da zuciya da shi.
? ?  Ita ?addarar data kawoki, ita zata dawwamar dake a cikin gidan sai dai ki haWiyi zuciya ki mutu! idan kuma k kin isa mara kunya ce ?afarki ta taka ko gate mugani stupid girl .
? ? Kafin ta samu damar cewa wani abu ya fice a Wakin, hawaye ne suka cigaba da rige-rigen sakkowa a kumatunta, zubewa tai a saman gadon ta rufe fuskarta da tafukan hanunta. Taja tsahon mintuna tana kukan kafin kiran daya shigo wayarta ya katse mata shi. Amrah ce, kamar bazata Wauka ba sai kuma ta Waga takai kunne batare da tayi magana ba. Daga can Amrah tamkar mai tsoron ajita ta fara faWin,  Kina jina Anaam? . A ta?aice tace mata eh kawai.
? ? ?  Ke kaWai ce? .
Cike da ?osawa tace,  K dalla faWi abinda zaki faWa .
??  Mtsoww! K daWina dake masifa. Ina yarinyar na ?awar Fadwa da muka gansu ranar da aka kai lefen Yaya Maheer? .
? ? ? ??  Amrah dan ALLAH ki barni wane shirmene wannan? .
 K Please karki kashemin waya maganace mai muhimmanci wlhy. Ina dai kin ganeta .
? ?  Muje na gane, kamar Bibah suke kiranta .
? ? ? ?  Yes! Exactly ita fa. Kin san yanzu ana tsaka da rigima a gidan nan kin san Mommyn su Yaya Shareff tana nan har yanzu tanata rikicin sai an raba aurenku, na fito daga gida zanje zan shiga cikin gidan kawai naga Bibah Win tare da Gwaggo da Maman Bibah a lungun mai shop Win nan, shine fa na lallaSa naje kamar zan sayi abu a shagon, ki duba WhatsApp Winki na turo miki voice recording Win dana musu dan naga yanzu ma kin fini gane wani hausan .
? ? ? Kamar Anaam zata gwaleta sai kuma tace mata  Okay a ta?aice ta yanke wayar. Daga can Amrah bata damuba dan ta saba da halin Anaam tun suna yara, sai dai a yanzu ma ta fahimci kamar a cikin damuwa take dan muryarta da alamar tayi kuka.
? ? ? Taso share zancen Amrah Win amma sai yayta tsunkulin zuciyarta. Data Winta ta buWe tare da shiga in box Win Amrah Win. Maganar ya Wanyi ?asa sosai, da alama ba gab take da su ba. Earpiece ta saka yanda zataji da ?yau. Maman Bibah ce ta fara magana cikin alamun Sacin rai.
? ? _ Amma ba haka kikai min al?awari ba, kin tabbatar min idan shirinki na zubar da cikin nan na Fadwa ya tabbata da Shareff ya dawo zakiyi duk yanda zaki ya aure Bibah, sai kawai naji wai ga wadda ya aura, kin kuma ?i saurareni tun ranar Waurin auren nan, na kira ta waya Gwaggo da kinji muryata sai ki kashe .
? ? ? Da Wan zafin rai Gwaggo ta amshe da faWin,  Haba Luba, wace magana kikeyi haka. Kina zaton zan faWi abinda bazan cika bane, ai ni na fara miki tayin haWa Bibah da Mustapha saboda ganin dacewarsu, na kuma tabbatar miki kasancewar Fadwa a gidan bazai hanata shiga ba duk da ?ar uwa take a gurinta itama. To amma su Muhammadu sukai wannan sar?a-sar?ar da kema kin san gwagwarmayar da aketayi na hana faruwarta. Ba yin kammu bane, kuma bamu san sun Waura auren nan ba. Amma ki kwantar da hankalinki, ni bana rama alkairi da sharri, Bibah kamar ta shiga gidan Mustapha ne ta gama. Yanzu dai kuje gida zanyi duk yanda zan a satin nan na le?i gidan naku kinga wani zai iya ganinmu anan, kuma za'a iya zargin wani abu shiyyasa ma nace kada ku ?araso gida mu haWu anan .
? ? ? Mamaki, al'ajabi, ruWani duk suka dirga a zuciyar Anaam lokaci guda, ba komai ta fahinta a zancen ba, sai dai maganar zubar da cikin Fadwa da su Bibah suka bata shawarar yi ta fahimci cewar Gwaggo ce ta sakasu su bama Fadwa shawaran kenan, sannan Bibah ma son Shareff take kuma Gwaggo ta mata al?awarin samunsa matsayin miji duk da da wadda ta haifi mahaifin Fadwa, da maman Mommyn Shareff, da Kakar Bibah wadda ta haifi Mamanta da Gwaggo uwarsu Waya ubansu Waya. Kai kai kai wannan makirar tsohuwa da abin mamaki take, ta ?yal?yale da dariya dake tabbatar da ?unar zuciyarta a bayyane. Cikin bushewar zuciya da cin alwashi ta jinjina kanta.? ?
? ? ? ?  Yes bazan tafi ba, amma Yaya badan kurarinka ba, sai dan koyama matarka da Mommy da aunty Halima hankali har da kai kanka a dalilin tsohuwar banza Gwaggo, yanzu na ?ara fahimtar matar nan itace take ?ulla komai dake a family Win nan tabbas. Zan tabbatar mata *Karen bana! Shike maganin zomon bana* kuwa..

? ? ? Bayan sallar la'asar sai gasu Amrah, tayi farin ciki da zuwansu matu?a, musamman Ikram mai shegen surutu da bakinta baya shiru. Suka shiga buWe kulolin abinci dake a falon wanda ita bama tasan da su ba, sai dai kai tsaye ta gane Fadwa ce ta kawosu tana ciki. Koda suka tambayeta ita ta dafa? Kai tsaye tace musu matar gidan. Amrah dai kasa Soye mamakinta tai sai da tace,  Wai kina nufin Fadwa? .
? ? ?  Bayan ita akwai wata matar ne a gidan? . Ta faWa batare data kalli Amrah Win ba. Harararta Amrah tai da faWin,  Banza kefa idan kina kan dokin zuciya ba'a maganar arzi?i dake . Shiru Anaam Win tamata hankalinta na kan hotunan su Gwaggo da Amrah ta dauka. Dukansu ta tura cikin wayarta, daga haka suka cigaba da hira.
? ? ? An fara kiran sallar magrib Shareff ya shigo, fuskarsa murtik da alama har yanzu ransa a Sace yake. Ikram ta she?a da gudu garesa dama tun Wazun take tambayar yana ina Anaam ta mata shiru. ?aurewar fuskar ya Wan sassauta yana shafa kan Amrah.
? ?  Autah yaushe kuka zo? .
Hanunsa cikin nata tana murmushi tace,  Yaya tun around Four. Inata tambayar aunty Anaam kana ina? Ta?i amsani .
? ? ?? Kallonsa ya kai ga Anaam Win, anyi sa'a itama ta Wago nata idanun a lokacin. Janyewa tai cikin salo tana Wan taSe baki, shima sai ya janye nasan yana ayyana (Zanyi maganinki ne) a ransa. Gaishe sa su Amrah sukai, ya amsa musu yana ficewa da basu umarnin tashi suyi salla. Bai dawo gidan ba sai da aka idar da sallar isha'i. Kai tsaye nan ya zarto domin maida su Ikram gida. Anaam jitai kamar karsu tafi, tai musu rakkiya har wajen motarsa, sai da taga ficewarsu sannan ta nufi komawa suka kusa cin karo da Fadwa.
? ? ? Kallon kallo sukema juna, Fadwa ta saki siririyar dariya tanama Anaam kallon sama da ?asa.  Amarya! Amarya! Ta ango ba?ya laifi ko kin kashe Wan masu gidaaa hhhhh. Uhhm kamar haka ake kirarin ko? . Tai maganar cikin sigar tambayar rainin wayo ga Anaam dake kallonta ita dai. Dariya Fadwa ta sake kwashewa da shi  Oh sorry amarya, ALLAH kina bani tausayi, dan ban taSa gamo da amarya irinki ba ko'a hikayoyin marubuta. Dama tsiyar auren cushe kenan fa . Ta ?arayin ?ar dariya da matsowa gaban Anaam dake kallonta uwa ta samu tv ko bata fahimtar yaren da take magana da shi. Cikin yin ?asa- ?asa da murya murmushi shimfiWe a fiskarta ta cigaba da faWin,  Zan baki shawara ?yauta dana tabbatar zatai miki amfani ?ar turawa, karki bari ki zubar da ?uruciyarki da lokutanki masu muhimmanci a inda ko kallonki ba'a da bukatar yi, gara ki taimaki kanki, ki tattara komatsanki kibi tsoffinki ku koma inda kuka fito koda baki gama serves Win ba, koda yake dama mun san bashi akazo yiba neman miji akazo. Bokanku ya iya aiki tunda gashi kin samu ta hanyar cushe, sai dai kuma akwai matsala mai yawa dan basu jehoki gurbin daya dace ba, gara ki sani tun yanzu, wannan gidan sai ya zame miki tamkar kurkuku mafi muni da ?untata a rayuwarki, kina da zaSin taimakon kanki ko cigaba da zaman cin kwakwa, AL-Mustapha Muhammad Shareff anyisa ne domin Fadwa Sadiq Dakata kawai . Ta kare maganar da ?yafta mata ido.
? ? ?? A karon farko Anaam ta saki murmushi tana girgiza kai.  Hauka maganinka ALLAH, ke kuma sanyin da wannan yanayin yazo miki. ALLAH ya ?ara afuwa . Tai gaba abinta.
? ?  Ubanki ne mahaukaci ?ar iska .
Anaam ta cigaba da tafiyarta tana dariya batare data waiwayita ba. A falo ta zube maganganun Fadwa na dawo mata Wai-Wai cikin amsa kuwwa. Tabbas bata da burin yin dogon zango a zaman gidan nan, sai dai ya zame mata dole zaman a yanzu kodan kawo ?arshen makircin Gwaggo, na biyu zata cika burin iyayenta akan zumincinsu da suketa ?o?arin ganin sun toshe duk wata hanya da zata wargazashi. Na uku Fadwa, dolene ta koyama Fadwa hankali ta kuma tabbatar mata sufa *Mata suna suka tara* lokaci shi zai nuna *Zarah*. Na huWu Mommy, na karshe Shareff, zata tabbatar masa da cewar ita Win ba kanwar lasa bace, daga shi har matarsa sai ta goge musu hadda a cikin gidan nan...
? ? ? Ta saki murmushi a karon farko bayan ta kammala rubuta dukkan abinda ta gama lissafawa a cikin wayarta sannan ta mike. A dai-dai nan ya shigo falon da sallama ciki-ciki. Itama ciki-cikin ta amsa masa tana ?ara tsume fuska. Shima dai tasa fuskar a tsuke take, ya ajiye ledar hanunsa yana kallonta tamkar mai harara.  Shi wancan Wakin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login