Showing 84001 words to 87000 words out of 194140 words

Chapter 29 - BABU SO Miya kawo Kishi Book complete by M shakur.doc

M Shakur   

26 Oct 2025

3270

kitchen ta nufa kanta tsaye mamakin da gaske Anam ta wuce gida na cinta, dan yanzu tai kiran wayarta Husnah ta Waga tace barci takeyi. Suka gaisa da iya cikin girmama juna.
? ? ?  Maman Abu yau duk mun makara kenan ba'ai breakfast da wuri ba ko? .
? ?  A'a tun Wazun na dafa shayi aka soya ?wai, amma hajiya tace a sauyawa Alhaji bazaici ba . Cikin Wan waro ido waje Aysha tace,  Kina nufin Yaya bai karyaba har yanzu? Sha Waya saura fa .
? ?  Eh ai yanzu hajiyar ta dawo daga wajensa ma .? ? ?
??  Lallai ma Aunty Fadwa, shine ita bazata zauna ta haWa masaba kuma ta bar miki. Na kula har yanzu bata gama sanin wanene Yaya ba.
? ? ? ? ?  Maman Abu dai batace komai ba, dan ita kanta yau ta jinjina wautar Fadwa Win duk da tun jiya take mamaki akan duk abinda ya faru. A yanda ta santa da soyayyar Shareff tun suna gida batai zaton zatazo gidan aure tai sakaci haka ba, tunda dai komai na mace Fadwa ta iya nan kuma mahaifiyarsu (Gwaggo Halima) batai sakaciba gaskiya musamman ma akan Fadwa data kasance mace babba. Fatan dai ba raye-raye a wayar nan dake Wauke mata hankali tazo ta cigaba dayi anan Win ba, dan tara ?awayen data saba tun acan taga har anan kullum cikin zarya suke.
? ? ? ? Da taimakon Aysha aikin ya kammala yanda tasan Shareff zaici a kwanciyar hankali. Suka Wiba nasu ta shirya na Shareff Win da Fadwa. Tana ?o?arin fita Fadwa ta fito cikin kwalliya sai zabga ?amshi takeyi. Gaisheta Aysha tayi. Ta amsa cikin raba hankalinta biyu tana buWe abincin. Da murmushi ta kalli Aysha. Aysha ta mayar mata batare da tace komai ba.  ALLAH ya kaini ran aurenki shatu. Dama inata zullumi nakai abincin nan ya gane banice nayi ba . Ita dai Aysha dariya tayi kawai. Fadwa zata Wauka tray ta amsa da cewa.  Bara na Wauka sai na gaishesa daga nan .
? ? ?? A tare suka nufi sashen nasa, sun samesa a falo zaune yana waya. Aysha da tasan bai cika damuwa da zaman dining cin abinci ba sai ta dire tray Win saman centre table. Fadwa kam gefensa takai zaune dan haka ya Wan kalleta idanu ?asa-?asa dan kwalliya na Waukar hankalinsa matu?a ga mace, Fadwa kuwa gwanace wajen iya tsarawa nan Sangaren ta ciri tuta dan batajin ganda kamar girki da sauran ayyuka da latsa waya ke hanata nutsuwar yinsu yanda ya dace. Ya ajiye wayar daya kammala yana kallonta da ?yau, sai kuma ya Wauke kansa ya maida ga Aysha dake gaishesa.
? ? ??  Kin tashi lfy? .
? ?  Lafiya lau Yaya, ya gajiyar tafiya? .
 Alhmdllhi .
Ya faWa a ta?aice. Harta yun?ura zata tashi ya dakatar da ita.  Ku har kun karya ne? .
? ? ?  Yanzu zanje na karya Yaya .
?an jimm yay kamar bazaice komai ba. Dan har ya Wauke idonsa a kanta sai kuma ya sake juyowa.
 Har yanzu tana kwance ne? .
? ?? Ta fahimci Anam yake nufi. Dan haka ta girgiza kanta.  Tun Wazun ta tashi ta wuce gida .
? ?? Fadwa da sai yanzu ta saka musu baki, tace,  Gida kuma? Rijiyar zaki wai? .
??  Eh aunty, tana idar da sallar asuba kusan 6:30 nama zata da wasa take na shareta sai dana tashi naga da gaske ta tafi shine na kirata Husna tace min tanama barci .
? ? ?? DaWine ya sauka har cikin ?asan zuciyar Fadwa, ko banza shirinta na jiya yayi aiki tunda Anam ta bar mata gida a kan gaSa. Amma saboda mazuran da yay jiya sai ta nuna rashin jin daWinta a yanzu har hakan ya bama Aysha mamaki dan tasan dai ba shiri suke da Anam ba. Zaman nan da akai tare dan ya zama dolene kawai. Shiko mai gayya komai bai ce ba. Sai ma umarni ya bata akan ta tashi ta bashi abinci. Cikin shau?in farin cikin tafiyar Anam ta mi?e ta fara haWa masa tea. Aysha kuma ta mi?e ta fice ta basu waje.
? ?? Kusan itace ma ta basa abincin a baki tana zuba masa hirar wahalar da taci lokacin da ta samu miscarriage. A ransa yana jin rashin daWin rasa Wan tayinsa, amma ya barma ALLAH tunda dama shine ya bashi bada wayonsa ba. A fuska kam tausayintane sosai sai dai baice komaiba. Rashin maganar tasa yasa ta sake yarda da maganar su Sima lallai da gaske baya bu?atar cikin a yanzu daman. Ta godema ALLAH data farga da wuri ta Wauka mataki gashi yanzu farin cikin dake neman kufce mata na dawowa gareta.
? ? ? ? Basufi awa Waya da yin breakfast Win ba ya mi?e ya shiga bedroom, babu jimawa ya fito cikin shirin fita. Kallonsa take da mamaki.  Soulmate badai fita ba ko? . Yi yay kamar baijita ba, ya kai zaune da Waukar wayarsa Waya, danne-dannensa yay yakai kunne alamar kira, hakan ya sata yin shiru tana kallonsa har ya kammala. Sake dubansa tai a shagwaSe.  Dan ALLAH Soulmate fita zakai wai? . Wayar daya gama ya ajiye gefensa, batare daya kalleta ba ya bata amsa.  Dama munyi dake bazan fita ba? . Baki ta tura da dawowa kusa da shi ta zauna ta narke masa a jiki. Zata fara shagwaSa sallamar Khaleel ta dakatar da ita. Kai tsaye ya bashi umarnin ya shigo, maimakon ta tashi a jikin nasa saita sake narkewa har Khaleel ya shigo. Kallo Waya yay musu ya Wauke kansa tunda indai taSarar Fadwa ce ba yau ya fara gani ba.
? ? ?? Shareff daya fahimta bata da alamar tashi Win, ya dubeta yana Wan tsuke fuska.  Gyara mana .
?? Baki ta ?ara tura masa, sai kuma ta tashi fuska a murtuke tabar falon ko amsa gaisuwar Khaleel batai ba dan har yanzu haushinsa na jiya na ranta ya mata addu'ar kishiya. Baibi takanta ba shi dai ya gaida Yayansa. Suka mike a tare suka fice dan motarsa Khaleel Win ya amso wajen wanki da yakai tun sassafe. Khaleel ne ke driving Win, yana gefensa suna hira da gaba Waya ma akan company ne. Sai Wai-Wai data shafi zamansa a gidansa wanda duk shine ke masa tambaya akan wasu abubuwan.
? ? ? Sun fara shiga sashen Daddy inda suka sami iyayen nasu uku zaune suna shan hira. Dan in har Abie na gari to bazaka taSa rabasu ba sai dai in sun fita aiki, yau kuma babu aikin shiyyasa har breakfast tare sukayi. Bayan ya gaisheasu su duka suke masa fatan alkairi akan abinda yaje yayo cikin kulawa. Yaji daWin addu'oin iyayen nasa dan su duka yana matu?ar jinsu a ransa. Ya Wan jima anan tare da su suna hira har Khaleel ya fice ya barsu, sai da aka kira sallar zuhur suka fito suka nufi massallaci. A lokacin Anam nacan cike da farin ciki. Dan bata jima da tashi a barci ba Fawwaz ke sanar mata su Mamie sunzo. Da farko bata yarda ba su Husna harda Mom nata mata dariya. Ganin haka yasa ta mike ta nufi gidansu, tun a gate maigadi ya sanar mata, aiko da gudu ta shiga tana ?wala kiran Mamie!! Abie!!. A lokacin Abie na can tare da su Shareff zasuje massallaci.
? ?? Bayan an idar da salla koda ya shigo gidan sashin Mom ya fara shiga, suka gaisa har da ?annensa sannan ya shiga wajen aunty Amarya. Daga can sai sashen Gwaggo data tsaresa yaci birabisko data dafa. Baici ba, amma yace ta saka masa a kula zaije dashi gida yaci. Taji daWin hakan har cikin ranta, ya fito yana murmushin tsokanarsa da take. Sashen Mommynsa ya nufa inda anan ne ya zauna sukasha hirarsu har take kawo masa ?arar Maheer da yay biris kamar ba shirin aurensa ake ba. Ha?uri ya bata da tabbatar mata zai kira Maheer Win a satin nan zai taho gida insha ALLAH. Taji daWin hakan har a ranta. Yay mata sallama akan zaije gida sai zuwa dare zai sake le?owa.
? ? ?? Daga nan gidan su Anam ya shiga. Inda ya sameta nanu?e da Mamie da Abie tana zuba surutu tana cin abinci. Suko sun biye mata sai dariya suke cike da farin cikin kasancewa da abarsu. Shigowarsa baisa ta daina surutunta ba. Sai dai ta?i yarda ta kallesa ko sau Waya dan tunda taji sallamarsa tai gefe da kanta. Shima kallo guda yay mata ya Wauke kansa, ya maida hankalinsa gasu Abie. Tayin abinci Mamie ta masa babu musu yace zaici. Kasa ha?uri Anam tai sai da ta kallesa. Ya wulla mata harara ta tura masa baki da ?ya?y?yafta idanu. Fuska ya sake tsukewa cike da gargaWi a gareta ta taSe baki. Duk abinda suke Abie na lure da su sai dai yayi kamar baya gani har Mamie ta dawo da abincin. Mace ce da sam bata da son jiki, yau da safe suka iso ?asar amma bata zauna jiran wani ya basu abincin rana ba bayan na safe da suka samu Mom ta shirya musu. Tayi girkinta kodan farin cikin Anam, dan abinda tafi sone ta girka. Abincin ya faraci a nutse suna hirar China da su Mamie, itako ta daina hirar tana cin abincinta a shiririce tana saurarensu, sai dai sai balla ma Shareff harara take ta gefen ido.
? ? ? ? Sai da aka kira la'asar suka fita da Abie massallaci. daga can ya wuce gida dan tun Wazun yake ganin kiran Fadwa na shigo masa ya?i ya Waga, saima wayar da yasa a silent.........
'



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS=?G?
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA=?G?
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O? [10/31, 11:58 AM] Marsy=??: *_Typing=???_*




*_d'
=?%?BABU SO....!!d'
=?%?_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce>??
*_BABU SO=?I?
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_32_*



...........Itama Aysha a ranar ta dawo gida da dare, shine ma ya kawota tare da Fadwa. Anam najin sanda suka shigo gaida Mamie ta ma?ale a Waki har suka fita bata le?o ba. Washe gari Mom tazo da mai gyaran jiki. Ba hajiyan bace zatai mata da kanta, ma'aikatan ta ne, amma saboda Mom tai al?awarin shigowa kullum ayi a gabanta insha ALLAH. Ita dai Anam bata damu da wannan zancen gyara ba tun amsar da Mom ta bata a waccan ranar, dan haka koda suka korata a falo da zasuyi magana ko'a jikinta tama nufi can cikin gida wajen Aysha dake fushi da ita ta barsu. Da wannan damar su Mamie sukasha hirarsu dan Hajiyar Sudan tasan Mamie Win sukan haWu idan ta shigo Nigeria.
? ? ??

_________________

? ? ?? Tun daga wannan ranar aka farama Anam gyaran jikin mai inganci. Yayinda a cikin gida aketa shirin biki gadan-gadan babu wasa. Ita da Shareff dai haWuwa ta gagara. Da zaran taji ya shigo gidan zata bar falo idan har tana zaune ne ma. To yanzu ma gyaran da ake mata babu dare ba rana yasa bama zaman falon take sosai ba saboda dokar Hajiyar sudan. Randa Maheer ango ne dai ya iso ta kasa ha?uri sai da ta fito cike da farin ciki suka gaisa. Sai dai yanayinsa ya saka mata sanyin jiki dan duk ya Wan rame gashi babu fara'a tattare da shi.
? ? Washe garin da Maheer ya dawo biki na saura kwanaki goma sha biyar da daddare Shareff yazo gidan ya samu iyayensa a falon Daddy. Sune sukace yazo sunada magana da shi. Bai wani damu ba dan duk zatonsa maganar dai bata wuce akan Maheer ba daya kasa kwantar da hankalinsa akan auren nasa.
Bayan ya gaishesu Daddy ya fara bayani kai tsaye kamar haka.  Shareff mun kiraka nanne matsayinka na Babba ga duk yaran gidan nan. Da farko dai akan maganar auren ?an uwanka ne, Maheer ya samemu jiya akan yanada wadda yake so ba wannan da ake shirin masa aure da ita ba, sai dai mahaifiyarku tace bazai aureta ba, hasalima ta haramta masa auren yarinyar. Munyi-munyi da shi ya?i ya sanar mana wacece, sai dai ya ro?emu mu ro?a masa ita ta amince masa dan ALLAH. To kai tsaye dai mun amsa wannan ro?o nasa, sai dai munce yayi ha?uri a Waura wannan Win tunda an riga an gama magana karmu kasance ?ananun mutane, munga rauni a tare da shi, duk da baiyi jayayya damu ba. Dan haka munaso ka kasance da shi dan hankalinsa ya sake kwanciya. Sai auren Aysha da shima aka Waga kamar yanda dangin ango suka bu?ata, duk da dai bakama san da zancen ba dama mun bari sai ka dawo a sanar maka .
Numfashi Shareff ya sauke a hankaki, kansa a ?asa cike da girmamawa yace,  Insha ALLAH Daddy zanyi hakan, ita kuma ALLAH ya zaSa abinda yafi alkairi, duk yanda kukayi dai-dai ne ai .
 Amin ya rabbi. Magana ta gaba kuma akan ?anwarkane itama Mamana .
Gabansa ne ya faWi, amma sai ya cije bai nuna alama ba, sai ma ruwa daya Wauka ya Salle murfinsa ya kai baki.. Daddy ya cigaba da faWin,  Wasu dalilai sun sa mun yanke shawarar aurar da ita itama rana Waya da na Maheer ga wani bawan ALLAH da muke da tabbacin zai ri?e mana amanarta da izinin ALLAH. Itama an gama tsaida komai....
Gaba Waya ya watso ruwan daya gumtsa har yana fesama Abbah dake a kusa da shi.  Subahanalillahi Abba ya faWa yana yana ri?o ruwan dake neman subucewa a hanun Shareff Win. Daddy da Abie kam sannu suka shiga masa dan bayan fesar da ruwan tarine mai ?arfe ya sar?esa. Idanunsa da sukai masifar kaWawa da ja cikin ?an?anin lokaci ya Wago yana kallon Daddy.
Sannu Daddyn ya ?ara masa hakan ya sashi maida idanun ya risinar. Daddy ya cigaba da faWin  Karka damu munyi bincike mai zurfi a kansa kafin yanke wannan hukunci, sannan munada dalilai masu ?arfi akan hakan. A matsayinka na babba saika sanya albarka a lamarin duk da yazo a ?urarren lokaci ko .
Kansa ya ?ara Wagowa da Wan haWiyar yawu yana murmushin ya?e.  ALLAH ya sanya alkairi . Ya faWa a takaice yana maida kansa ya dukar. Da amin suka amsa masa, daga haka suka cigaba da bayanin abinda yasa suka kira san. Bai bar wajensu ba sai kusan goma da rabi, ko'ina bai shigaba dan yasan duk sunyi barci ma yanzu ya shiga mota jiri na kwasarsa ya bar gidan....


&Ranar laraba aka saka amaryar Maheer a lalle, ga Anam dai babu abinda ya danganci hakan sai ba?i da suka fara cika gida. Sai a ranar alhamis ne da safe Abie da Mamie da Aunty Mimi da Abba da Daddy suka zaunar da ita. Bayan gama mata nasiha suka koma lallashinta, sai dai gaba Waya bata fahimtar wani fari ko ba?i a zantukan nasu, dan da alama brain nata ta raba tafiya da ?wa?walwarta wajen yin aiki. har suka gama lallashinta taron ya tashi babu alamar numfashinta na fita daga gangar jikinta, a da kamar bata damu da auren ba, sai a ?wanakin nan kuma jikinta ke mata matu?ar sanyi, rauninta na bayyana a zahiri. Bata samu damar fashewa da kuka ba sai da Aunty Mimi ta kamota suka komo ciki dan da suna a falon Abie ne.
Mamie dai kasa tsayawa tai, sai aunty Mimi ce ke lallashinta amma kuka ya gagara tsayawa. Gaba daya ta birkice cikin ?an?anin lokaci har takai idanunta sun fara daina gani da ?yau. Hankalin su Mamie ya tashi, amma basu yarda kowa ya sani ba wani abokin Abie amintaccensa doctor ne na ido yazo ya dubata. Ya tabbatar musu damuwace ta kawo hakan, dan haka ya basu shawarar ai mata allurar barci ta huta. Wannan shine dalilin hana yin kamun amarya a yau da aka shirya sai dai anyi Wan shagali duk da ba kowa yasan minene ya hana Win ba. A take ?ananun magana suka baje gida musamman ga su Mommy.
Duk da sun kasa gane kan zancen sunji farin ciki, har Gwaggo ta kasa ha?uri sai da tabi diddigin jin ba'asi, jin amarya Anam ce babu lafiya sai gata itada Mommy da Fadwa wai duba Anam Win lamarin zam-mamaki. Suna fita kuwa suka sanya dariya. Dan dama tun jiya suke dariya da ?ananun maganar rashin kawo lefen Anam gidan, acewarsu wane aurene haka kamar auren sadaka. Duk da zancen nasu ya koma kunen su Mamie harda su Daddy ma babu wanda yace komai.
Suna tsaka da wannan farin ciki Dr Jamal ya kira Fadwa yace tazo gida. Sagale tai tana kallon wayar dan ya yanke, kamar zata share sai kuma dai ganin da number Win Shareff ya kirata ta yanke hukuncin zuwa duk da kuwa a cikin tashin hankali suke da shi a kwanakin nan. Tadai danne ne kowa bai sani ba sai kawayenta su Sima dake ?ara tunzurata da tabbatar mata itace mai gaskiya.
Tasan bama suba duk wanda zataima bayani dole zai bata gaskiya. Dan kuwa ita dai babu abinda tai masa a kwanakin nan ya Worama kansa wani irin ba?in rai da yafi halinsa data sani. A gaba Waya satin nan baya fita aiki kullum yana gida kwance, da farko ta fara lallaSashi da son jin minene matsalarsa? sai ya dinga daka mata tsawa da faWin karta damesa, ta shanye na farko dana biyu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login