Showing 3001 words to 6000 words out of 194140 words

Chapter 2 - BABU SO Miya kawo Kishi Book complete by M shakur.doc

M Shakur   

26 Oct 2025

3331

shuWawa shi da Humaira ALLAH bai basu haihuwa da wuriba har ALLAH yayma mahaifiyarsu Juwairiyya da Asiya rasuwa a ?asar saudia sunje aikin hajji, mutuwar tasu ta samu asaline dalilin accident daya wanzu a cikin harami a wannan shekarar. Sun shiga tashin hankali sosai, wanda har yay sanadin kawunsa ya samu ciwo shima yabar duniya. Girma ya dawo hanun Usman, dan kuwa ragamar rayuwar ?annensa biyu ta dawo garesa, wato dai Humaira data zama matarsa da Mimi. A wannan gaSar ?an uwansa sun kirashi sun masa gaisuwa, yaji daWi har cikin ransa.
? ? ?? Bayan ya aurar da Mimi ga wani abokinsa dake anan Malaysia shima dai Wan Nigeria ne babu jimawa ALLAH yayma Hajara (Mama) mahaifiyar su Muhammad ?an uwansa rasuwa itama. Har Nigeria yazo tare da matarsa da ?anwarsa Mimi dake fama da ?aramin ciki, hakan da yayi sai ya sanyaya jikin ?an uwan nasa dan kuwa su ko auran Mimi duk da ya basu hakkinsu ?in zuwa sukai, hakama rasuwar mahaifiyarsa da kawunsa da uwar matarsa a waya kawai sukai masa ta'aziyya. Ya nuna musu hakan ba komai bane su manta kawai.
? ? ? ? ?an shirin da suka samu a tsakaninsu a wannan karon ya samu damar sanin duk iyalansu, dan kuwa a baya basu taSa yarda yasan fuskokin matansu ba ma balle adadin ?a?ansu ba. Muhammad matansa biyu. uwargidansa Wasila Wiyar ?anwar gwaggo nada yara huWu a lokacin, babban shine Al-Mustapha da yaci sunan MD Shareff mahaifinsu suna kiransa da *_Shareff_*. Sai Maheer, Binta, Ishaq da ?aramin ciki da take kan laulayinsa. Wasila da yara ke kira Mommy a gidan ba wani sanin Usman taiba amma ta mugun tsanarsa saboda huWubar Gwaggo, ?insa take tamkar itace ?an uban nasa ba mijinta ba. a gefe tana matu?ar jin kishin yana rayuwa a ?asar waje a ganinta kodai yaya ya fisu nasibin rayuwa. Ta shiga matu?ar takaicin ganin su Muhammad sun fara sakkowa akan ?in Wan uwansu da sukeyi, dan haka ta shirya sake haddasa sabuwar ?iyayya a tsakaninsu kamar yanda Gwaggo ke Waurata akan hanya. Sai amaryarsa Ubaida da suke kira (Aunty Amarya) nada ciki tsoho itama haihuwa yau ko gobe, mace ce mai son jama'a da ha?uri, duk da ?iyayyar iyayen miji da take fuskanta da iskancin kishiya ta zama mai ha?uri da kawaici a gidan. Sai matar Abubakar Mariya da suke kira Mom. Itama mace ce mai dattako da mutunci. Ba wani daWin iyayen mijin nata takejiba saboda Gwaggo itace ke juya Mama, bata son kowa yay farin ciki a gidan sai Wiyar ?ar uwarta. Amma haka taita kawaici da shanye haWata fitinar da aka dingayi da uwar mijin tasu har ALLAH ya rabasu lafiya da ita. Itama dai yaranta biyu duk maza. sai dai tana da ciki Wan watanni biyar. Umar dai ya?i aure, hasalima ya zama fanWararre a cikinsu sai addu'a. Tuni yana kudancin ?asar sai ya gadama yake waiwayen kano tun daga karatu, su kansu ?an uwan ba'a komai suke sakashi a lissafinsu ba. Rasuwar ma baizo ba sai bayan kwana bakwai duk da mahaifiyarsu ce. Kamar yanda ?an uwansa suka gabatar masa iyalansu shima haka ya gabatar da tasa matar a garesu. ?ya?y?yawar bafulatana mai tarin ilimin zamani dana addini. Ga tarbiyya da mutunta mutane.
? ?? Babu laifin zaune babu na tsaye Mommy ta tsinci kanta da tsanar Humairah wanda babu makawa kishine kawai da hassada ke cin ranta, dan kuwa ko ba'a faWaba Humairah ta fisu komai na rayuwa. Kasa biye ?iyayyarta tai ta dinga nunata ga Humairah datai kamarma bata fahimta ba, dan mace ce data iya zama da mutane matu?a, sai dai koda wasa ta?i bada fuskar da Mommy Win zata kawo mata raini.
? ?? Rasuwar Mama yasaka ba?in halin Gwaggo fitowa muraran gasu Muhammad. Dan kuwa sun fahimci Gwaggo itace ke tunzura mahaifiyarsu aikata wasu abubuwan ashe. Duk da tana nuna itace uwa a garesu kamar da can, a yanzu hakan baya hana ta nuna musu bata haifesu ba ko wani abu makamancin haka. Sannan a kullum burinta taga babu zaman lafiya tsakaninsu da ?an uwansu biyu kacal da ALLAH ya basu, kai hatta lalacewar Umar sun fahimci Gwaggo nada kamasho dan kuwa dai shi da Muhammad sune ?an Wakinta, a yanzu kuma Shareff ma a hanunta yake yaron gaba Waya ya tashi a taSare ga rashin kunya da rashin mutunci. A kullum cikin jibgar ?a?an anguwa yake da musu ?wacen abu idan ya gani gashi baya son karatu sam.
? ? ? Abubakar da yaran gidan suke kira da Abbah ne ya fara nusar da Yayan nasa Muhammad da suke kira Daddy abinda ke shirin faruwa, yana tsoron su sake samun bara gurbi bayan Umar a zuri'arsu. Sannan koba komai Shareff shine babba a ?a?ansu lalacewarsa na nufin rugujewar sauran ?anensa. Sosai Daddy ya fahimci Abbah, suka zauna shawarar matakin da zasu Wauka akan yaronsu duk da gida Waya suke da Gwaggon sashenta daban itama inda suke zaune da Mama kafin rasuwarta. Suna a wannan halin Usman yazo Nigeria domin fara ginin wani fili daya saya, a ganinsa ya ?yautu ya mallaki muhalli a ?asar haihuwarsa. Zuwansa ya musu daWi, dan basu Soye masa komai game da halin da Shareff ke neman shiga ba a hanun Gwaggo. Ya jimanta al'amarin tare da sanar musu subar komai a hanunsa shi zai Wauke Shareff Win ya koma hanunsa insha ALLAH. Ba karamin farin ciki sukai ba, tare da ?ara Winkewa kamar komai bai faruba a baya. Ginin da yazo da niyyaryi a nesa da su sai suka hana hakan, suka tilastashi zuwa ya gina filin da suka rage masa tare da ?ara masa dana cikin gidansu kasancewar gidan nasu ?atone sosai kowace mace ma da part Winta, ga kuma na Umar ma da babu kowa a ciki tunda yaki zama. Dan da farko ma na Umar Win sukace ya Wauka ya?i.
? ?? Cikin ?an?anin lokaci aka fara ginin daya tada hankalin Gwaggo da Mommy, babu kunya suka tada rigimar basu yarda ba. Su su Daddy ma abin har mamaki ya dinga basu, dan sun rasa dalilin Gwaggo na son nisantasu da ?an uwansu. Basubi takanta ba, dan a lokacinma ne suka nuna mata bore, a wajen Halima kawai ta samu goyon baya dan ita dama sai a hankalice. Wannan rigima bata kwantaba kuma maganar komawar Shareff hanun Usman ta sake tasowa. Nanma dai ansha ?aramin ya?i dan Mommy haukane kawai bataiba Wanta zai koma hanun ma?iyanta. Tsiya ta dinga zazzagama Usman harda masa gorin haihuwa. Shi dai bai kulata ba kamar yanda bai kula Gwaggo da Halima ba. Iyakaci ma idan suna abun nasu sai dai yayi murmushi. A gefe kuma bai fasa shiryama Shareff tafiya ba.
? ? ? ?? A lokacin da zasu wuce dole sai sace Shareff akai daga gidan batare da sanin Mommy da Gwaggo ba, dama ita Halima tana gidan aurentane zuwa takeyi, itama dai yaranta uku ne a yanzu tana auren Wan wan gwaggon dan ita ta haWa....

? ? ? ? Humairah da Mimi sunyi farin cikin ganin Shareff, sai dai kuma sam babu cikkakkiyar tarbiyya ga yaron. Dan ba ?aramin wahala da azabarsa suka sha ba duk da kwata-kwata shekararsa tara ne a duniya lokacin. Haka Ru?ayya taita juriyar ganin ta sauya tarbiyyarsa ita da Usman. Basubi takan zagi da walakancin da Mommy ke kira a waya ta musu ba akan su dawo mata da Wanta idan sunji haushi su haifa nasu. Gorinta na musu ciwo, amma sukaita dannewa tunda sun san domin ALLAH zasuyi ai da Wan uwansu. Tunda dai sun san bazatazo ta ?wacesa ba.
? ? ?? A hankali komai ya fara daidaita, Shareff ya fara nutsuwa da son karatu, ga kulawa yana samu da soyayya ga iyayen ru?onsa. Sha?uwa kuma mai nagarta ta gama shiga tsakaninsu. Bashi da kamar Abie da Mamie yanzu a duniya sai aunty Mimi da akoda yaushe yakanje gidanta kodan yaronta data haifa Su'ad. Shareff nada shekara biyar a wajensu ALLAH ya bama Mamie ciki. Zokaga murna da farin ciki wajensu, yayinda Mommy ta shiga ba?in ciki dan taso ace sun ?are rayuwarsu ne babu haihuwa. Kuma har yanzu tana kan caccakarsu akan su maido mata Wanta. Sudai basa kulata, dan ko ?asar zasuzo basa zuwa da shi ma.
? ? ?? Mamie tasha rainon ciki har ALLAH ya sauketa lafiya ta haifo ?arta mace. Mommy da Gwaggo sun Wanji sassauci dan a ganinsu darajar mace bata kai ta namiji ba. Dan haka suka shiga shigi da fici gidan malamai kai harma da bokaye akan wai a tsaida haihuwar Humairah. Humm abin dariya, dama basu wahal da kansu ba dan iya abinda ALLAH ya rubuto a ?addarar bawa shi kaWaine rabon dazai samu ai dama. Ita dai batama san sunai ba, dan kuwa da ALLAH ta dogara. Su Daddy ne kawai sukaje Malaysia ganin gudan jinin Wan uwansu, duk da Gwaggo taso binsu ganin ?waf suka?i. Yarinya taci sunan *_Juwairiyya_*, mahaifiyar su Abie kenan amma suna mata alkunya da *_Anam (Blessings of GOD)._*

? ? ? ?? Rainon Anam ya dawo kamar a hanun Shareff ne. Bashi da damuwa a yanzu sai ta Anam, daya dawo makaranta tana hanunsa, bacci ne kawai ke rabasu shima sai Mamie tayi jan ido. A haka aka yayeta ta buWa ido da sanin Shareff matsayin Yayanta kawai. Dan kuwa duk wani gata da kulawarta tamkar ta koma hanunsa ne. Dan hatta wanka da abubuwan da uwa zatayi duk shike mata. A koda yaushe tana ma?ale da shi kamar cingam. Hatta da Abie wani lokacin ?iwa take masa sai shareef. Lokacin da take cika shekara shidda a duniya a lokacin Shareff ya kammala secondary school Winsa. Abie yay masa shirin wucewa jami'a a ?asar Indonesia. Ya shiga damuwar rabuwa da ?ar ?anwarsa, dan kuka sosai ya dingayi duk da lokacin yanada shekaru sha takwas a duniya dan ya zama Wan saurayi abinsa. Haka dai babu yanda ya iya ya tattara ya tafi badan yaso ba. Yasha matu?ar wahalar kewar Anam a ?asar Indonesia, dan da ?yar ya ha?ura ya maida hankali ga karatunsa kodan faranta ran Mamie da Abie Winsa. Fara karatun Shareff a ?asar Indonesia ya ?ara bama Gwaggo da Mommy ?warin gwiwar cigaba da shiga da fita domin ganin hankalinsa ya dawo garesu, su kuma nisantashi dasu Mamie. Zuwa lokacin gidan nasu ya ?ara haSaka da ?a?a. ALLAH kuwa ya amsa musu, dan kuwa dai a hankali rayuwar Shareff da hankalinsa suka fara dawowa Nigeria, ko hutu ya samu da yaje Malaysia dake kusa da shi gara ya wuto Nigeria. Takai yakan ma jima bai je inda su Abie suke ba. Sai dai abinka ga ikon UBANGIJI har lokacin soyayyar bayin ALLAHn nan na'a ransa babu abinda ya canja. Kawai dai baya son zuwa inda suke ne batare da yasan dalili ba, sai kuma Anam da sam a yanzu bayama ko san tunata dan babu dalili ya tsani yarinyar. ko Malaysia yaje babu abinda ya damesa da ita, wani lokacin ma kafin ya taho sai ya bugeta. Itako dama tama manta da shi tuni, rashin sakewar da yake da ita yasa basa shan inuwa Waya, ko inda yake bata kusanta balle ta nuna tama sanshi, idan kuma tsautsayi ya haWasu ko hararta yay sai ta rama saboda tsiwarta.
? ? ?? A haka rayuwa ta cigaba da shuWawa Shareff ya kammala karatunsa ya zama cikakken *_Architect Al-Mustapha Muhammad Shareff_*. Maimakon ya nufi Malaysia kodan nuna godiyarsa ga ALLAH ga waWanda suke tsaye kan Wawainiyar karatun nasa sai kawai ya nufo Nigeria. Hakan ya matu?ar bata ran su Daddynsa, yayinda Gwaggo da mahaifiyarsa Mommy suka bashi goyon baya da kariya. Sosai ran Daddy ya Saci har suka sami saSani tsakaninsa da Mommy irin wanda basu taSa samu ba. Ya kuma fito fili ya nunama Gwaggo kuskurenta. Aiko saita zauna ta dinga kuka wai su Daddy sun nuna mata ba itace ta haifesu ba. Shareta sukai, harta haWa kayanta tabar gidan, ganin abin zaiyi tsamari Mom ta sanarma Mamie, itako ta sanarma Abie. Daga ?arshe dai Abie ne yazo Nigeria ya kwantar da tarzomar tare da nuna shi bai Wauka abinda Shareff Win yayi da wani Sacin rai ba, abin birgewama sai yay zaman bashi shawarar mizai hana ya buWe company kawai basai ya zauna neman aiki ba.
? ?? Sosai Shareff yaji kunya, ya dinga bama Abie ha?uri akan shima wani lokacin yana rasa gane kansane akan nisantarsu. Murmushi kawai Abie yay dan ya jima da fahimtar komai akan farra?a yaron akai da su, bai kuma taSa yun?urin nuna ya sani ba tunda yasan dai Mommy akan abinda yake nata take han?oro mizaisa ya damu tunda shima ALLAH ya bashi tashi. Shareff bashi da kuWin buWe company, amma sai Abie ya bashi shawarar su haWa gwiwa kawai.....
? ? ? A haWin gwaiwar ma Shareff baida ko kwatar kuWin da zata gina company Win, amma sai Abie bai damuba shi ya bada duk kuWin da ake bu?ata aka kammala aikin cikin ?an?anin lokaci, ya kuma gargaWi Shareff akan baya son Gwaggo da Mommy su sani, kawai suci gaba da tafiya akan shine ya gina abunsa. Sai dai sun zauna da lauyoyinsu an ajiye komai a rubuce tare da su Daddy matsayin shaida.
? ?? Ginin wannan company yasa Mommy fara hura hanci, a ganinta karan Wanta yakai tsaiko shima. Har habaici takema su Mom da su Mamie ko kunya babu. Mamie ce kawai tasan gaskiyar lamarin, su Mom kam da aunty amarya suma duk tasu Waukar Shareff Winne ya gina da kuWinsa. Gwaggo ma ta Wau abun da zafi, dan ita taita tunzura Mommy akan su ?ara tashi tsaye su nisanta Shareff da su Abie wai kar wataran Abie yay tunanin haWa Shareff da Anam aure tunda sunga ya kuWance har yama fisa arzi?i. Wannan fanfi kuwa yay tasiri ga Mommy, dan tuni suka bazama shige-shige saboda ko'a mafarki bata fatar haWa zuri'arta dasu Abie a duniya.....

? ? ?? Abubuwa da yawa sun faru bayan wannan, ciki harda karatun Anam da ko Nigeria Win ma sai jefi-jefi ake kawota, dan idan har suka zo ta dinga kuka kenan zafi-zafi. Anam yarinyace ?ya?y?yawa black beauty, tana tsananin kama da mahaifinta a komai, sai dai akwai kamannin Mamie tattare da ita ta wasu wajajen. Yarinyace mai ?iriniya da rashin ji, ga tsiwa. Sam ?ar babu ragice, dan ko cikin yaran da suka girmeta bata bari a cuceta balle sa'aninta, tanada baki sosai. A Sangaren karatu kuwa sam bata da wani ?o?ari saboda kasancewar ta yarinya mai son wasa, sai da su Abie suka mi?e kanta sosai sannan ta fara fahimtar karatu. Shekaru na karuwa gareta rauni daga idanunta na sake bayyana, dan takai idan abuna'a nesa da ita bata ganinsa, hakama da daddare idan waje babu haske mai ?arfi bata ganin abu har saida lalube. Lokacin da su abie suka fahimci wannan matsala hankalinsu ya tashi, sai dai babu Sata lokaci suka dangana ga likita, ya tabbatar musu idanunta nada raunin gani, amma zai Waurata akan magani da gilashi dazai taimaka mata. Wannan shine dalilin kasancewar eyeglasess a idon Anam koda yaushe. Abin mamaki kuma sam basa shan inuwa guda da Yaya Shareff. Hasalima haduwarsu tayi matukar wahala, idan ya fisge yaje Malaysia ma bata barin su haWu sam, hakama idan tazo Nigeria baifi su haWu sau biyu uku ba shikenan, a kuma duk haWuwar tasu sai ya mata muguntar datake jin ?arin tsanarsa a ranta kamar yanda shima haka kawai bai son yarinyar saboda tsiwarta da rashin kunya ido fi?i-fiki injisa. Idan ma tana waje ya dinga Waure-Wauren fuska kenan kamar an aiko masa da mutuwa, ko gaishesa tai sai ya gadama ya amsa shiyyasa tama daina gaidashi take nuna bama tasan ?urar data kwasosa a duniya ba. Tuni company ya fara aiki cikin lumana da nuna ?wazon shugaba kwata-kwatansa wato Architect Al-Mustapha Muhammad Shareff. Da mafi yawan mutane sukafi sani da *_MM Shareff_* a ta?aice. Company ne da aka haWa masu ?wazo kuma ?uraye, dan Ya Shareff bai yarda ya Wauka ma'aikatan banza ba sannan sam baya wasa da aikinsa bai bama ma'aikatansa damar yin wasan kuma.
? ?? Jajircewar tasa tai matu?ar birge Abie, ya kuma ?ara tsayawa tsayin daka ta bayan fage yana bama Shareff Win gudunmawa dan yana matu?ar kaunar yaron har cikin ransa tamkar Anam Winsa ?a Waya tilo.
? ? ? ? To ayanzu dai ga Anam ta dawo Nigeria da shirin zaman shekara guda domin yin saves da su Mamie suka takura mata. Ga kuma Seranta da tuni yayi nauyi a Nigeria kodan hidimar kamfanin da mahaifinta keda kamasho mai ?arfi a cikinsa da shares batare da Mommy da Gwaggo dake hura hanci sun sani ba.........
'

_Ko yaya wasan zai kasance>??? Kudai kawai ku zamto tare da littafin *_BABU SO...! MIYA KAWO KISHI? dan jin yaya cakwakiyar zata kasance. Littafine da yazo da wani irin sabon salo na musamman da nake tabbacin ni Bilyn Abdull ban taSa zuwa muku da kalarsa ba sai yanzu. Domin kuwa ya taSo zahirin rayuwa ne da zamanin da muke ciki a yanzu da rawar da tarbiyyar ?a?anmu ke takawa a social media batare da saninmu ba ko da sanin namu. Kar dai na cikaku da magana my guys, kumuje zuwa kawai dan duk wanda akai babu shi lallai ruwa tasha da shi kawai, saboda Zafafa biyar da gaske da zafinsu suke=? ?>?p?>?p?=??=ض?

KU DAI KU GARZAYO A DAMA DAKU A CIKIN WANNAN ZAZZAFAR TAFIYAR CIKIN SALON NA ZAFAFA BIYAR MASU ZAFIN GASKE.

DUKKA LITTAFAN AKAN NAIRA DUBU DAYA (1k) KACHAL

IDAN KUMA DAYA KIKE SO (300)
BIYU (400)
UKU (500)
HUDU (700)

KARKU BARI A BAKU LABARI, DAN WANNAN SALON NA DABAN NE KUMA TAFIYAR MA TA DABAN CE!

ZAKU TURA KUDIN A WANNAN ACCOUNT DIN ME DAUKE DA SUNAN

HAFSAT UMAR KABIR
ZENITH BANK
2270637070

SAI A TURA SHAIDAR BIYAN

07040727902

IDAN KUMA KATI NE KU TURA TA WANNAN NUMBER HADE DA SHAIDA

09134848107


KARKU BARI AYI BABU KU, KU GARZAYO MU DAMA A CIKIN WADANNAN GWALA-GWALAN LABARAN MASU MATUKAR SANYA NISHADI.

MUNGODE DA ZABIN ZAFAFA BIYAR A KOWANNE LOKACI.

SAI MUN JIKU MUTANEN AMANA!=؃?




*_ALLAH ka gafartama iyayenmu_*=?-?=?O?



*_d'
=?%?BABU SO....!!d'
=?%?_*
_(Miya kawo kishi?)_



Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login