Showing 63001 words to 66000 words out of 194140 words

Chapter 22 - BABU SO Miya kawo Kishi Book complete by M shakur.doc

M Shakur   

26 Oct 2025

3268

*_Bilyn Abdull ce>??
*_BABU SO=?I?
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_19_*

.......... ?agowa yay daga latsa wayar da yake yana kallonta, dan ?amshin turarenta da takunta ya sanar masa da zuwanta duk da ta kasa magana. Idanunta ta Wauke daga kallonsa tana faWin  Good Afternoon .
? ? ?? ? ?  Ni kike ma gaisuwa kina juyar da fuska?! .
? ? Juyowa tai Idanu cike da ?walla tana kallonsa.  Ni wlhy Yaya ban san mina maka ba duk kabi ka tsaneni ka takura ni. Komai nayi a duniyar nan a wajenka ban iyaba . Ta ?are maganar da sakin siraran hawaye.
? ? ?? ? Kallonta kawai yakeyi ko ?yaftawa babu. Ji tai kallon ya sake saka mata jin haushinsa, juyawa tai da nufin barin wajen.....
? ??  Kika bar wajen nan sai ranki ya Saci .?
? ? Idanunta ta rumtse tana jin wasu zafafan hawaye da sukafi na far?o na neman kufce mata. Ita kam ta rasa mita tsarema bawan ALLAHn nan a duniya, tana fatan watanin nan bakwai da suka rage mata su maza suzo ta kammala abinda ya kawota tabar ?asar nan, dama tun farko abinda ta gujemawa kenan amma su Mamie suka kasa fahimtarta. HaWiye hawayen tai batare data barsu sun zubo ba sannan ta juyo garesa, yana a yanda yake har yanzu, sai dai idanunsa masu kwarjini da kaifin dake hana ?arfin halinta tasiri na nan tsaye kanta ?yam har yanzu. Kasa jurar kallonsa tai, tai ?asa da nata, shima sai ya janye nasan, juyawa yay kujerar gefensa ya Wakko ledar dake ajiye. Mi?a mata yay kansa tsaye.
? ?? Ledar ta fara kalla tare da hanunsa dake Waure da agogo da zoben azurfarsa da ya jima yana birgeta, har addu'ar damar sace zoben ta taSa yi a zuwa na karshe da tai kafin wannan.... Saurin Wagowa tai tana kallonsa jin ya kamo hanunta cikin nasa, ya wani sake ?an?ance idanu cike da salon kallon da a duk sanda ya jefeta da shi yake firgitata, ta fara son zame hanun a hankali dan gaba Waya lakar jikinta neman daina aiki takeyi, kanta ta fara juya masa tamkar mai ciwon wuya, tana son zare idanunta daga cikin nasa amma ya?i bata damar hakan nan ma, sai kawai ta sakar masa kukan karya.
? ? Hanun nata ya saki a hankali bayan ya saka mata ledar, kamar wadda ake control da remote fitt ta Sace a wajen. Tsabar sauri har tintiSe tayi ALLAH dai ya taimaketa bata faWi ba ta dafe gate.
? ? ? ? ?? Murmushi ya saki mai Wan sauti daga ?irjinsa yana kauda kansa. Ya maida ?afafunsa cikin motar tare da rufeta yabar wajen.

Itama koda ta shiga sai da ta samu jikin wata mota ta huta tare da share hawayen ?aryarta sannan ta buWe ledar. Shawarma ce da ice-creem sai yogurt da robar ruwa. Haka kawai sai kuma ta samu kanta da sakin murmushi. A fili tace,  Ga rashin mutunci ga kirki idan yaso . Dariya ta sake ?yal?yalewa da shi dan haka kawai drama Win tasu ta yanzu take maimaita kanta a zuciyarta tana saka mata nishaWi.
Yau kam tayi aniyar kozai daketa bazata yarda tabi motarsa ba, dan haka kawai ragwantakar data nuna Wazun a gabansa ke hanata sukuni, sai dai murmushi ya kasa barin fuskarta har Yaseer sai da ya kasa ha?uri ya tambaya. ?ar dariya kawai ta masa batace komai ba. Ana tashi itace farkon fitowa, bata son bin Yaseer Win badan tana jin tsoron tabbatar hukuncin Yaya Shareff ba, ba kuma ta bu?atar shiga tasa motar shima gara ta hau napep. Sai dai kuma cikin rashin sa'a tana fitowa taci karo da motar tasa a wajen gate, kuka kawai ya rage ta fasa ta huta, tai tsaye ta kasa matsawa ga motar har tsahon wasu sakani. Sauke glass Win da dariyar Khaleel ta sata sakin ajiyar zuciya, dan tunda ta fito idonsa a kanta.  Ai ba mai motar bane sai ki taho mu tafi farar kura kawai .
 Humm ALLAH Yaya bazaka ganeba. Shi Yaya Shareff Winne ya cika takura da hana mutane sukuni suji daWin rayuwa .
 Maybe yana tsare mutuncin kayansa ne kar kiga laifinsa .
Bata wani gane mi Khaleel Win ke nufi ba, saboda da hausa yay maganar ta buWe ta shiga tana dariya kawai. Shima yasan bata gane Win ba dan haka ya dara.

____________________________

Tun daga waccan ranar Anam ta sake kafa wasan Suya da Yaya Shareff, motar Khaleel ta samu matsala, sai kawai ta koma bin school bus na yaran gidan. Kasancewar suna fitar sassafe kafin Shareff daya tsiri zuwa gidan da safe ya iso har sun wuce. Ana tashi kuma zatai wuff ta fito ta tari napep. Motar Yaseer ma dai ta daina shiga duk da yata bibiyarta da son jin ba'asi tana tabbatar masa babu komai.
Samarinta biyu da sukafi takurama rayuwarta taga sun rage manne mata. Dr Jamal da Muzzaffar. Kowannesu kuma yanada gurbi na musamman data ajiyesa dan koba komai suna sakata nishaWi a wasu Sangatorin na rayuwa. Sai dai ta gagara neman jin dalilin kowannensu akan Wan janye mata da yayi, garama Muzzaffar sukan Wanyi waya jefi-jefi ko chart wasu ranakun.
A gidan nasu kuwa bata da wata damuwa sai su Hussaina wataran, dan idan rashin kunyarsu ya tashi sukan mata sai dai bakinsu nashan bugu dan bata Waga musu ?afa. Ta daina zuwa gaida Mommy da Gwaggo sai in ta ritsa sun haWu a hanya taita sinne kai wajen gaishesu. Ko kallonta basayi, dan a ganinsu ma ?in zuwa gaishesun ta taimakesu koba komai sukan manta da wanzuwarta a gidan. Hakan baya damunta, takan wataya tsakanin sashen aunty amarya da Mom abinta. Ita da Aysha da sauran yaran gidan kuwa sai sambarka. Hakama Daddy da Abbah a koda yaushe cikin bama rayuwarta kulawa suke fiyema da yaransu, dan kullum da tsarabar da waninsu zai kawo mata gidan da kuma mata nasihar tsare mutuncinta suke.
Kusan kwanaki goma kenan basu haWu da Shareff ba, sai a yau da akai sa ranar auran Maheer da sam bata san da zancen auren ba sai da taga akwatina a sashen Mom akace na auren Maheer ne yau za'a saka rana da kai akwatinan. Tayi mamaki sai dai batace komai ba, sai daga baya Aysha ke bata labarin ai Maheer Win baya son auren Mommy ce ta takura kamar yanda ta takurama Shareff shima. Auren zumincine da Wiyar ?anwarta. Sosai Anam taita mamakin hali irin na Mommy, a ganinta ta cika takurama ?a?anta a gidan, musamman Yaya Shareff da Yaya Maheer Win. Gashi suna mata matu?ar biyayya fiye da duk sauran yaranta, dan tasha ganin Mommy nama Aysha da su Hussaina faWa suna ?un?uni. Itace ma kema Aysha faWa da nuna mata illar hakan ga iyaye. Sai kuma gashi masu mata biyayyar sunfi shan wahala a hanunta fiye da su Ayshan da sai abinda suke so sukeyi.
Batabi takan duk hayaniyar da ake a gidan ba, kasancewar ma a sashen Mom ba?in da zasuje kai kayan suke isowa, saita fito domin wucewarta sashen aunty amarya ta huta dan asabar ne. Kamar ta juya taji, lokacin dataga motarsa na ?o?arin yin fakin gab da sashen Mom Win, amma sai ta dake ta fuske zata wuce abinta.
Siririn tsakin da taji anyi dai-dai zata gitta ya tilasta ta juyowa, dan sam baiyi kama da tsakin Yaya Shareff ba. Fadwa ce a tsaye cikin shigar madam getzner shadda da taci uban aiki sai walwali take, tabbas tayi ?yau sosai. Anam ta sakar mata wani murmushin ?ularwa da kashe mata ido Waya ta cigaba da tafiyarta. Kusan Wan cin karo sukai da Shareff daya zagayo waya manne a kunensa yana magana. Shima dai sanye yake cikin shaddar fara tas datai masa ?yau da fiddosa a asalin bahaushensa Wan arewa dan harda hula. Ta Wan ja baya yayinda shi kuma ya tsaya cak dan gaba Waya hankalinsa akan waya yake baima san wainar da suke toyawa da Fadwa ba. Kallonsa tai tana wani ?ya?y?yafta idanu, sai kuma ta tunzura baki gaba ganin kallon nata da yakeyi shima tamkar idanunsa zasu cinyeta.  Good morning . Ta faWa tana gittasa da ?ar sassarfa.
Cikin basarwa ya cigaba da wayarsa, hakan sai yayma Fadwa data tsaresu da idanu daWi harda matsowa zata rungumesa ya kauce mata yana nuna mata sashen Mom. Cikin shagwaSa tace,  Ni dai ka gama mu shiga tare ALLAH kunya nake ji .
Sarai yasan ?arya takeyi, amma sai baice mata komai ba har ya kammala. Gaba yay ta bisa a baya....

Bata bu?atar zaman tunanin abinda ya shafi waninsu, dan haka tai connecting bluetooth Winta ta manna a kunne. A hankali takai kwance bisa grass carpet dake a Wan ?aramin garden Win dake bayan Wakin aunty amarya tana lumshe idanunta cike da nishaWi, dan wa?ar da take saurare tana matu?ar sonta, mawa?in Wan ?asar malaysia ne, wa?ar ma anyitane da yaren malay sai dai an cakuWa da turanci. Tayi nisa sosai wajen sauraren wa?ar fuskarta shimfiWe da murmushi, ga idanunta a lumshe sanyin inuwar wajen na ?ara girmama nishaWinta, bakinta sai motsawa yake a hankali alamar bin wa?ar takeyi....
Jin ?amshinsa ya ?ara ?arfi cikin hancinta ya sata kasa cigaba da jurewa ta buWe ido a hankali batare da tabbacin mai ?amshin bane a wajen. Sai dai kuma cin karo da shi Win tsaye ya sakata Wauke numfashi na wucin gadi. Da sauri ta tashi zaune duk tana jinta a daburce, hijjab Winta dake gefe ajiye ta Wauka ta rufama jikinta dake sanye da wando three quarter da top ?arama, zafine ya isheta ta sakasu kasancewar a Waki take, sai da taji hayaniyar mutane zasu dameta ta sako hijjab kawai ta fito, ganin babu kowa anan ya sata cirewa ta ajiye dan ta samu iska mai ?yau ta shigeta.
Rigarsa ya Wan tattare sama ya zauna shima bisa grass carpet Win dake a share tas dan aunty amarya kullum cikin kulawa take da wajen saboda tsananin son garden da takeyi. Mace ce ?ar gaye mai son hutu da gudun yawan hayaniya. Duk da Anam taji wani irin da zaman nasa wajen amma sai ta dake abinta. Sai dai ta kasa cigaba da bin wa?ar daketa maimaita kanta. Shima da tun zuwansa wajen baice komai ba kallonta kawai yayi na wasu ?an sakanni, sai kuma ya kai hanunsa kunnenta ya zare bluetooth Win ya saka a nasa kunnen. Juyowa tai tana kallonsa da mamaki, ya lumshe idanu ya buWe tare da kauda su a kanta yana sauraren wa?ar.........
'


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS=?G?
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA=?G?
0913484810_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS=?G?
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA=?G?
09134848107 ko[10/24, 1:39 PM] Marsy=??: *_Typing=???_*




*_d'
=?%?BABU SO....!!d'
=?%?_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce>??
*_BABU SO=?I?
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_20_*


......... Waye mawa?in nan? .
Cikin shakku da mamakin ta kallesa. Ganin zai kallota tai saurin janye idanunta a kansa, ta bashi amsa cike da basarwa.
? ? ?? ?an Murmushi yayi dan ya riga ya ganta.  Ya iya wa?a gsky, kuma cikin nutsuwa da ma'ana .
? ? ?Itama Murmushi tai a karon farko tana dubansa.  Shiyyasa nake son wa?o?insa sosai nima ai. Bashi da hayaniya, sannan duk abinda zai faWa yakan dace da furicin zuciyoyi .
? ? ? ? ?Tsareta ya Wanyi da idanunsa, hakan yasa ta kauda nata.  Wane furucine ke dacewa da ma'anar zuciyoyi? .
? ?? A yanda yay tambayar tamkar mai raWa ya sata juyowa ta sake kallonsa, sai kuma ta janyesu har yanzu murmushinta bai Sace ba.  Yaya bai zama lallai tunanina dana kowa yazam iri Waya ba ai, zata iya yuwuwa nice kaWai ke fassara haka ko fahimta a lokacin da nakejin wa?o?in nasa .
? ? ?  Uhhm nice. Kinga nima sai ki turamin maybe na fahimci irin taki fahimtar ko! Ki samun duka wa?o?in sa ta WhatsApp .
? ? ? ? ??  To ai bani da number ka .
? ?? Cikin ido yake kallonta, ta risinar da nata dan bazata iya jurewa ba. Shima sai ya Wauke nasa ya maida ga tsuntsaye biyu dake shan ruwa a Wan kaskon da aunty amarya kan zuba dan su.  Baki so hakan bane shiyyasa baki da ita .
? ?? Murmushi kawai tayi, amma batace komai ba, ta dai cigaba da kallon tsuntsayen kamar yanda shima har yanzu idonsa na kansu. Shiru kusan mintuna uku, tashin tsuntsayen ya sashi katse shirun nasu da faWin,  Zanyi tafiya zuwa China, kuma zan jima dan zan samu a ?alla kwanaki Wari acan ko ?asa da hakan insha ALLAH .
? ? ?? Mamakinsa ya sata Wagowa ta dubesa, kasancewar nasa idon na kanta ya sashi Wan lumshewa alamar tabbatarwa... Bata da zaSin daya wuce kaWa masa nata kan itama.  ALLAH ya tsare hanya, ya kuma bada abinda za'aje nema mai albarka. Ya tsareka daga haramun, ya haWaka da halal .
? ?? Ajiyar zuciya yaja mai ?arfi, har takai ta sake Wagowa ta kallesa, murmushi ya sakar mata, irin wanda zata iya rantsewa bata taSa cin karo da shi a gareta ba. Ta Wanyi tsammm tana kallonsa, gaba Waya ganin al'amarin nasa take na yau kamar almara. Lakace mata hanci da yay ya sata saurin Wauke kai cike da kunyar kanta. Ya Wan murmusa yana gyara zamansa.  Zaki koma gidana k da Aysha ku zauna har na dawo .
? ? ??  What! Yaya ni Win? .
?? A yanda tai maganar ya sashi kafeta da idanunsa sosai.  Bazakije ba kenan? .
? ?? Fuska ta Sata da tura baki gaba,  To ai ni dai kasan bama shiri da matarka .?
? ??  Idan kikaje zama yanzu ai sai ku fara shirin kafin na har abada .
Ba wani fahimtarsa tai sosai ba saboda da hausa yay maganar, amma sai ta girgiza kanta.  No bazamu taSa shiri da matar can taka ba. Dan nama kusa fara kai mata naushi idan tana cigaba da min kallon banza. Karta Wauka tsahonta da girman jiki zai razana ni .
? ? ? Yanda take maganar cike da masifa da tsiwa ya bashi dariya sosai. Ya kauda kai gefe yana murmushi. Kafin ya sake juyowa fuska a haWe yana kallonta.  Matar tawa zaki nausa? .
? ? Batace komai ba, sai dai ta sake tura baki gaba. Zaiyi magana ring Win wayarsa ya dakatar da shi, Mommy ce, dan haka yakai kunne cike da ladab yay sallama.
? ??  Kana ina ne wai Shareff? Ga matarka sai amai take anan duk ta galabaita kazo kuje asibiti .
? ? ? ? ?  Ya ALLAH! .
? ? Ya faWa a hankali yana lumshe ido.  Okay Mommy ina zuwa. Amma bara na kira Jamal kin san yau weekend ne ba lallai mu samu yanda muke so a asibitin ba .
? ?  To ya hanzarta dan ALLAH .
 Okay bara na kirasa Win .
? ?? Koda ya yanke wayar kasa ha?uri Anam tayi, dan bata san wa akace baida lafiyar ba.  Yaya waye za'a kai asibiti? .
? ? ? ? ? ? Yana ?o?arin kiran Dr Jamal ya bata amsa kai tsaye.  Fadwa ce keta amai wai, duk ta galabaita .
? ? Sosai ta nuna jimaminta kasancewarta mutum mai tausayi.  Ayya ALLAH ya bata lafiya, dama bata da lafiya kuma ka yarda ta fito Yaya?, ai da ka barta a gida tunda kowa yasan ciwo .
? ? ? ?? Numfashi ya Wan furzar, rashin Waukar wayar Dr Jamal Win ta bashi damar bata amsa.  Bawai kwance take ba, yanzu ma inaga taji ?amshin abinda bata so ne shine aman yazo .
? ? ? Kallonsa tai cikin mamakin amsar tasa, sai dai kafin tace wani abu kiran Mommy ya katseta. ?agawa yay yana mikewa.  Mommy na kira bai Waga ba maybe baya kus... Yauwa gashi ma yana kira ina zuwa . Yankewa Mommy tai, shi kuma ya samu damar Waga kiran Dr Jamal Win. Ya Wan matsa da ga wajen Anam Win suna magana. Da kallo ta bisa, sai kuma ta Wan Wage kafaWa da Wauke kanta cikin Wan taSe baki. Hijjab Win da taketa faman ?udundune jikinta ta warware ta sanya da ?yau itama ta mi?e da nufin komawa sashen aunty Amarya tai kwanciyarta kawai ko Wan chart tayi da ?awayenta na Malaysia.
? ? ? Ya gama magana da Dr Jamal ya juyo kawai ya hangota har takai ?ofar baya ta kitchen Win aunty amarya. Idanu ya tsira mata harta Sacema ganinsa. Ya Wan ja numfashi tare da barin wajen shima.

&&&

? ?? A sashen Mommy Fadwa sai sake langaSewa take ganin yanda Mommy da Mamah suka rikice. Dan itama Mamah (Gwaggo Haliman) tazo wajen saka ranar ta Maheer. A haka ya shigo ya samesu zagaye da ita. Sai kawai ta fashe masa da kuka tana mi?a masa hannu wai itafa yazo zata mutu. Cijewa yay yayi kamar baiga hanun da take mi?o masa ba, koba komai ai sa raga dan iyayensu. Sannu yay mata tare da zama yana gaida Mahmah. Cikin kulawa ta amsa masa itama.  Dama bata da lafiya ne haka Babana? .
? ?? ?an duban Fadwan yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login