Showing 180001 words to 183000 words out of 194140 words

Chapter 61 - BABU SO Miya kawo Kishi Book complete by M shakur.doc

M Shakur   

26 Oct 2025

3360

rufe take neman Shareff amma ta?i ganinsa. Masu aiki yasa suka shigo da ita, Gwaggo Halima kuma ya tabbatarma masu gadi ko hanunta ya taSa masa gate abakin aikinsu. A karan farko itama ta fara kuka, dan a zatonta koda yay sakin guda biyu zai ha?ura ya barta ta cigaba da zama cikin ?a?anta har a sasanta. Sanin da yay mata zata iya ?in nufar gida ya sakashi turata a mota da kansa yaja motar ya maidata gidan su Daddy da tuni ?an biki sun fara watsewa, ba kowa na Sangaren Mommy. Na Sangaren Mom kuwa da dangin su Daddy zama daram wasuma shirin tafiya dinner Win Khaleel da amaryarsa suke. Dan su Hajiyar Sudan sun shiryama wannan biki kwarai da gaske....

? ? ?? Komai ya hargitse, komai ya rikice. Burin Gwaggo na watsa biki wani yankinsa ya tabbata. Domin kuwa akan bigire na duk tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka ake. Ita dake amsa matsayin suna uwar daba tana can asibiti ?afa a ragargaje batama san inda kanta yake ba likitoci sun rufu akanta. Manyan dodannin fadarta su Mommy sun masifar tsanarta fiye da rayukansu a yanzu. Dan kuwa Mommyn da kowa kema kallo matsayin ?arta da zata iya zama magajiya a gareta na kwance bisa gadon asibiti jininta yay ?ololuwar hawa har yana son zarce abinda ba'a fata. Tana da saki guda biyu a kanta, igiya daya ce kacal ta rage mata a yanzu, kuma Daddy ya tabbatar musu daga asibiti su wuce da ita karta sake dawo masa gida. A daren daga gidan angon Aysha takardar saki ta iso a cewar iyayen ango Wansu bazai rayu da ?ar mace ba. Wannan al'amari yayi matu?ar ?ona zuciyar su Daddy har Abie na tabbatarwa sai ya kaisu kotu, da ?yar su Abba suka lallashesa. Gwaggo halima data Wauki Gwaggo tamkar uwarta mahaifiya a yanzu babu wanda tafi tsana a duniya sama da Gwaggo, a sanadinta Wiyarta mafi soyuwa a gareta ta rasa ciki ta rasa aurenta, ita a karan kanta ta rabu da ?an uwanta shekara aru-aru a dalilin huWuba ko muce tarbiyyar Gwaggo. Ta rasa igiyoyin aurenta da ?a?anta a cikin abinda bai gaza awa shidda da barinta gidan mijinta cike da fatin ciki ba.
? ?? Yayinda Aysha itama ke can tana rusar kuka tamkar ranta zai fita, dan kuwa ta tabbatar alhakin mahaifiyarta da kakartane ke bibiyar ?addararta, a ranar da aka Waura mata aure a ranar miji ya saketa ko gidansa ba'a kaita ba. mijin data Sata tsahon shekaru tana mutuwar so da ?auna.
? ? ? ?? Haka zalika Fadwa celeb.... Wadda ke ganin ko ta tashi a rayuwar da ita a karan kanta bata taSa gundurartaba balle kallonta a juye. Shareff shine dukkanin farin cikin duniyarta, da sonsa ta rayu da shi ta horu, a rana Waya dalilin makircin ?awayen data Wauka babu yasu a duniyarta da cigabanta ta rasashi. Auren mahaifiyarta da aka ?ulla tsahon shekara talatin yau ya girgiza shima a dalilin wadda suke kallo gunkiyarsu da bayan horon tarbiyya ga uwarsu suma akan zaren tarbiyyar tata suka horu.....
? ? ? Shareff da komai ya ?wace masa a wannan gaSar tunaninsa yama rasa ina zai kama ko samun mafaka, sai dai ya jure, ya danne wajen tattare hankalinsa kan matarsa da jikinta yay ruWewar da daren sai da Dr Jamal yazo ya sanya mata ruwa....,? ya kuma saka Fharhan a daren kaima su Sima, Siyyah, Amal, Bibah ?an sanda suka cafkesu, tare da doctor Win dayay aikin.
? ? Abba, Daddy, Abie, aunty Mimi. Mamakin Gwaggo da Wunbin al'ajabinta ya hana zukatansu bugawar gaggawa a ?irazansu. Sun rasa wane aji? na duniya ya kamata sunan Gwaggo ya fita, dan a iya hasashensu sun gagara kama minene dalilinta na duk aikata waWannan abubuwan?. Kenan akwai abubuwan da suka shuWe da yawa a baya dake bu?atar nazari mai faWi da neman ba'asin dalilin aikatashi ko ganinsa a aikace. Sunyi ta mazan bin su Baba Ibrahim asibiti, inda har dare ya raba suka dawo gida babu wani bayani akan jikin Gwaggon likitoci dai sun rufu a kanta sunata faman kaikawo....

? ? *_WASHE GARI_*.

? ? ? ? ?? Sai a yau asabar zuri'ar MD Shareff suka sami ganin Gwaggo, sun fara shiga Wakin da aka kwantar da Mommy itama bisa matsawar Abie suka dubata, inda acan suka sami Shareff da Maheer tare da ita. Basu jimaba suka fito, Mommy da abubuwa da yawa ke cin ranta musamman sakinta da Daddy yayi ta taso ta biyosu, duk yanda su Shareff sukaso dakatar da ita ta?i yarda da hakan. Hankalinsu ya tashi da ganin jikin Gwaggo, dan ?afarta tayi wani irin mahaukacin kumbura daya ninka jikinta biyu, gashi an yanketa daga gwiwa zuwa ?asa dan can Win yayi ragargajewar da bazai ?ara aiki ba. Sai kananun ciwuka da ba'a rasa ba. Da ?yar take iya amsa musu, sai dai abin mamaki idonta a soye babu ko alamar hawaye. Bayan sun jajanta da Waukar kusan mintuna goma sha biyar a Wakin sukai haramar tafiya. Muryarta a Washe, amma hakan bai hanata fita da kaushi ba ta dakatar da su...
? ? ?  Na rikeku na muku gata fiye da uwar data haifeku, amma a dalilin kan?anin abu kuke nuna alamun juyamin baya Muhammadu. Bazan hanaku ba, sai dai ku sani bazan yafe muku wahalar dana sha a kanku ba .
? ? ?  Bakece zaki ?i yafe mana ba, mune bazamu taSa yafe miki ba Hindatu...
? ? Muryar Gwaggo Halima ta ratsa kunnuwansu a bazata. Su dukansu suka juya suna kallonta da mamaki, dan kuwa babu lallashin da basu mata ba danta biyosu tace bazata ba. Ta cigaba da takowa firingau-firingau dan a kwana Waya duk ta sususce ta fita a hayyacinta tamkar ba halima ?ar gata ba. Ta ?araso gaban Gwaggo tana mai share hawayenta.  Hindatu kamar yanda na faWa mune bazamu yafe mikiba annamimiya azzaluma. Musamman ni nan Halima. Hakama iyayenmu dake kwance a cikin kabari, da sunada damar da zasuyi magana sautin yaje cikin kunnuwanki da sun nanata miki kalmar ALLAH ya isa fiye da sau dubu. Kinga wannan ?afar taki da aka yanke, ba itace kaWai ?arshen azabar da zakisha a duniya ba. Yanzu kika fara gani, bayan WanWanar Wacin rashin haihuwa na shekaru sama da sittin da kikai a duniya, yanzu zaki cigaba da fuskantar raWaWin azaba ne mai muni tsinanniyar tsohuwa mai zubin ?an wuta.......
? ??  Ke ce dai mai zubin ?an wuta...
Cewar Mommy a hasale. Dariya Gwaggo Halima ta sanya.  Ke kumafa? Maza je kiji da kanki shasha kawai. Hawan jini da zawarci ma sun ishi rayuwarki ?ar wahala, sannan kema a gurinta baki tsira ba .
? ?  Hahaha garama ni, kuma koba komai zuwa yanzu na tabbatar miki Shareff jinina ne tunda gaki a zawarci ?arki a zawarci. Kuma yanda ya saki Fadwa itama Anaam sai ya saketa dan bazai zauna da zuri'ar waWanda basu san hallaciba. ?ar dukiyar da akaga ya tara akemawa to babu mai cinta har kai uban nasa .
? ? ? ? ? A karan farko Daddy ya Wago yana kallon Mommy, amma sai kafin yace wani abu Abba ya cafe murya a kausashe.
? ??  Mu bamu kasance marasa halacciba Nafisa. Wannan tsohuwar dake da kika rayu a gidanmu matsayin agola kune marasa halacci, kuma dukiya da kike takama Shareff ya tara bara na buWe muku zancen yau, kaso biyu bisa ukun abinda kuke ganin Shareff ya tara na Usman ne.......
? ??  Please Yaya Abubakar ba wannan gaSar mukeba...
?? Abie yay niyyar katse Abba. Amma sai Abban ya fisge jikinsa.  Barni Usman, gara wannan mahaukaciyar tasan ANNABI ya faku. Duk da ?ulle-?ulle datai domin ganin ta raba tsakaninku da Usman hakan bai hana ka cigaba da tallafa rayuwarsa ba, har take i?irari da fariyyar dukiyar Wanta. ki shiga hankalinki kuma kisan mikikeyi, daga ke har uwar taki, sakamako kuma yanzu kuka fara girba, dan wlhy Gwaggo alhakin iyayenmu kaWai bazai barki sake jin daWi ko farin cikin rayuwa ba. Tur da masu irin halinki na annamimanci da hana zaman lafiya a cikin zuri'a. ALLAH zai saka mana matu?ar sakayya a ranar da gaSoSi zasuyi magana madadin bakuna .
? ? ? Tuni Mommy da kanta ke bada wani yuuuu na haurawar jininta sama ta dafe gadon da Gwaggo ke kwance. Kallon Shareff take cike da son ?arin bayani. Lips Winta na rawa. Kansa ya jinjina mata tun kafin tace komai.  Mommy abinda Abba ya faWa shine gaskiyar magana. Dukiyar Abie ce ni nawa basu wice kudin siyan ruwa ba a cikin taron biki .
? ? ? Wata irin ?ara Mommy ta saki da faduwa ?asa daSar, Gwaggo ma tuni gadon da take a kai ya fara jijjigar shiga a tashin hankali. A halin da take ciki da dukkan ?arfin halin nata Shareff Win shine kawai gadararta a yanzu, dan ko maganar aikin da ake faWar za'ai mata na ?afarta ta gama sawa a ranta ko kowa ya gujeta suna da Shareff ai. Ashe-ashe abinda sukema gadarar ma ba nasu bane. Da tasan haka bazata taSa yarda taima su Abba hakaba. Da ta cigaba da musu fuskarta ta tun ?uruciya. Amma yanzu ta tabbatar bakin al?alami ya rigada ya bushe kuma....
? ?? Cikin ?an?anin lokaci duk sukai waje, hatta Shareff da Maheer ji sukai bazasu iya zama ba, dan dama tsananin kunyar su Daddy sukeji saboda abin kunyar da kakarsu ta jima tana tafkawa da mahaifiyarsu duk da kuwa akwai Gwaggo Halima tare da su......

_________&

? ?? Kwanaki sun cigaba da shuWawa, ta tabbata dai Gwaggo Halima ta dawo gida da zama, dole ta share sashen Baba Umar da babu wanda yasan a duniyar da yake yanzu ta zauna. Mommy kuma ta koma gidan Baba Ibrahim kamar yanda ya shardanta mata, dan ya hana su Shareff bata wajen zaman da sukai niyya. Yayinda Gwaggo ke cigaba da jiyya mai wahalarwa a asibiti. Dan kuwa babu wani mai jiyyarta sai Nurse's dake kula da ita. Mommy din ma data raina da kanta tace bazata iya jiyyarta ba dan ?afar tata duk da likitanci na kula da ita wari takeyi matu?a. Su Daddy basuyi butulci ba tare da su Baba Ibrahim da mahaifin Fadwa ke biyan kuWin zamanta a asibitin. Hakama Fadwa na gidansu, mahaifinta ya amshe wayarta, ya kuma kwashe dukan ?an aikin gidan yanzu itace ke komai ga ?anenta, girki, gyaran gida, ya baza camaras tako ina, inma bataiba ko baya gidan zai gani, hakama waya kota ?an uwanta ta Wauka da nufin kiran wani itama tasan sauran. Duk ta fige ta fita a hayyacinta saboda kuka da tsananin ?ulafucin mijinta da takeyi, ga Gwaggo Halima ta mata nisa yanzu, ?anenta kuwa sai zuba mata rashin kunya sukeyi tunda dama a haka suka taso na ?asa baya girmama na sama da shi. Satinsa uku a gidan maganar auren Babansu ya tashi da wata hamsha?iyar mace ?ar boko mai babban mukamin gwamnati a jihar ta kano...........
'



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS=?G?
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA=?G?
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O?



*_d'
=?%?BABU SO....!!d'
=?%?_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce>??
*_BABU SO=?I?
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_79_*


..........Yanda Fadwa ke jigatuwa a gidansu haka Mommy ke jigatuwa a gidan Baba Ibrahim, dan kuwa matansa babu kanwar lasa a ciki. Basa raga mata koda da wasa. Abinci kuwa iya abinda suka bata shine zataci, bata isa cewa tak ba Baba Ibrahim zai silleta tass. Kaf ?a?anta an hanasu raSarta har su Shareff kuwa. Itama duk ta fige ta ruWe da damuwa mai tsanani, ga rashin aure, ga rashin ?a?a, ga dukiyar Wan da take ta?ama dashi ashe ta ma?iyintace. Kai ina itako zata saka kanta taji sanyi wannan rayuwa haka.

? ? ?? Gwaggo Halima kam ai zamu iya cewa ta susuce a wannan gaSar. Dan kuwa maganar auren mijin nata ya risketa dan abune da aketa faman watsasa a gidajen talabijin da rediyoyi. Bikine ake shiryawa na hamsha?ai biyu masu daidaiton ?warya tabi ?warya. Ga rashin ?ayanta tare da ita, dan kuwa itama dai su Abba sun ?wace wayoyinta, sun kuma kafa mata sharadin inhar tana bu?atar zama da su sai ta nutsu, inba hakaba zata bar musu gida, dan yanda sukayi ha?uri da ita a baya a yanzu kam bazasuyi ba.

? ?? Kwanan su Sima takwas a police station aka shiga kotu, dan duk magiya da ro?o da iyayensu ke ma Shareff ya rantse sai sunyi shari'a. Kasancewar laifinsu a bayyane yake ba'awani wahalar da shari'a ba a zama biyu kacal aka yanke musu hukuncin zama gidan yari na watanni goma shaWa. Tare da tara mai tsoka. Kafin kace mi media ta Wauka, babu abinda ke trending kamar labarinsu. Manyan yaran da akeji dasu a tiktok da istagram dama mafi yawan kafafen yanar ta gizo sunsha Wauri a dalilin shugabarsu. Ga labarin mutuwar auren Fadwa ya zama kamar wani abin izgili a bakunan wanda suke jin haushinta. Sai dai wasu hakan ya sanyaya musu jiki matuka. Dan inhar haka zata kasance ga Fadwa suma Win basu tsiraba kenan tunda duk iri aiki guda sukeyi, wasu ma nasu yafi nata muni matu?a. A take wasu suka fara goge wasu videos na rashin tarbiyya dake a shafukansu, wanda kuwa ke kai musu ji suke yanzu aka fara wasan ma. (Ya rabbi ka shirya mana zuriya damu baki Waya=?-?=?O?
Kwanan Anaam goma sha biyar a gidan Shareff ya dauka matarsa suka koma gidansu, dan ta Wanji daWin jikinta. Sai dai an sama mata mai aiki tare kuma da Aysha suka koma can dan itama tana cikin kunci da damuwa abin tausayi, dan ma Anaam Win na tsaye a kanta wajen ganin ta sakama ranta salama da daukar komai matsayin jarabawa.. Komawarsu gidansu da sati guda su Abie suka koma, dan Abie yayi iya ko?arinsa na ganin komai ya daidaita amma hakan yaci tura, ya zube kuWi masu tsoka na kula da Gwaggo a asibiti ya tattara iyalansa da su Aunty Mimi suka koma Malaysia, inda suka bar Anaam na faman kuka sai da Shareff yayta lallashi...

&&&

? ?? Zuwa yanzu abubuwa da yawa sun Wan lafa ba kamar da ba, Anaam da Shareff sun buWe sabon babin soyayya mai tsayawa a rai, mantawa suke da kowa da komai suna kallon kansu tamkar su kaWaine a faWin duniyar kawai. Tun Aysha da mai aiki najin kunya har da suka saba da gani. Dan kuwa dai tare da Shareff ake rainon cikin Anaam Win. Tana da sau?in laulayi, abinda kawai bata so hayaniya. Inhar waje ya cika hayaniya yanzu zata jangwaSe babu lafiya. Hakan yasa babu inda take zuwa sai bayan sati uku zuwa huWu ya kaita can gidansu ta yini. Gaba Waya ya tattara lamarin Fadwa ya ajiye a gefe. Ko tunawa da ita ma baya sonyi balle jin sunanta. A dalilin ta yay ma tiktok tsana mai tsanani, dan zuciyarsa na ayyana masa duk wanda ke a wajen mutumin banza ne irinta. (Sai da Shareff da sauran ?an uwa ba haka bane. A yanda muke kallon tiktok ba hakan bane. Shima dai dandaline tamkar kowane dandali na media. akwai na ?warai akwai bara gurbi. Kawai dai a komai bara gurbi sun fi saurin yin shura a idon al'ummarmu ne da yaWuwa. Kuma ita yanar gizo tamkar kasuwa take, abinda kai niyyar shiga ka saya shine zaka nema kuma ka samu. Dan haka tiktok akwai mutanen kirki a cikinsa masu yaWa abubuwan alkairi saSanin tunaninmu na musu kuWin goro. Fatanmu matan aure irinsu Fadwa da suka tsunduma rayuwarsu a waWannan hanyoyu ALLAH ya shiryesu. Hakama ?ammatanmu da basuyi aurenba ALLAH ya shiryesu ya basu mazaje na gari, hakama zawarawa da samarinmu baki Waya).

? ?? Watanni kusan huWu da faruwar komai aka sake Waura auren Aysha da Dr Jamal, sai dai su Abie basu zoba sun dai saka albarka. Hakama Daddy ya haramtawa dangin Mommy zuwa bikin har ita kanta Mommy din. Tako ci kuka mai zafafa zuciya, har tanajin inama bata biyema Gwaggo ba da ayanzu haka tana nan an dawo da ita gida. Sai dai kasancewar babu inda zata zauna a gidan baba Ibrahim aka haWasu Waki Waya da Mommy. Ko kallonta Mommy batayi, balle ta taimaketa koda da bada magani ne. Kullum cikin mata ALLAH ya isa takeyi. Kaf dangi an rasa mai jinyarta, dan kuwa dai ?afarta da gaske ta ruSe, a yanzu hakama ana shirin gundile har cinyar data ragene saboda imfection ya shiga.
? ? ? ?
? ?? Zuwa yanzu cikin Anaam watanni bakwai ne ciff, hakama matar Maheer an gamu, dan shima dai ya kwantar da hankalinsa zuwa yanzu ya rungumi matarsa. Matar Khaleel ma dai nada cikinta Wan wattani uku. Haka amaren suka cigaba da rainon ciki musamman Anaam dake a gaSar gangara. Shareff dai na shan shagwaSa matu?a. Dan kuwa kun san mutuniyar taku da raki. Ga kuma cikin daya fara tsufa yana yawan sakata a saurin fushi, hatta da mai aikinta taka tsantsan takeyi. kullum cikin rigimar ita a Malaysia zata haihu take. Su Abie da Shareff nata lallashinta, acewarsu suma sun kusa dawowa Nigeria. Haka dai akaita rarrafawa har ALLAH yasa aka shiga watan haihuwa da ?yar. Dole fa badan yaso ba Anaam Win ta koma gaban Mom ta cikagaba da kula da ita ana jiran na?uda. Shareff ma sai ya haWa kayansa ya koma can gidan shima. Dan kuwa dai nan Win ya masa daWi shi kaWai, yana matu?ar jin kewar ?ar darun tasa.
? ? ? A daren wani alhamis ta farka da na?uda mai tsanani, babu shiri suka nufi asibiti a daren. Sai dai fa tun ana jiran haihuwa har al'amarin yaci tura aka yanke shawarar za'a mata cs kamar yanda Dr Bilkisu ta basu shawara, dan ta tabbatar musu jikin Anaam baida ?wari za'a iya zamun matsala gaskiya. Dole Daddy ne ya saka hannu da Shareff kwata-kwata baya a hayyacinsa. Yana can ma?ale da Anaam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login