Showing 165001 words to 168000 words out of 194140 words

Chapter 56 - BABU SO Miya kawo Kishi Book complete by M shakur.doc

M Shakur   

26 Oct 2025

3316

*_Bilyn Abdull ce>??
*_BABU SO=?I?
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_71_*



..........Gigitacciyar tsawa Daddy ya daka musu.  Wlhy duk wadda ta sake cewa tak sai ranta yay mummunan Saci, idan kuma kunji ?arya bismillah marasa mutunci kawai. Ku har kun isa ku maidamu mutanen banza. Ku tashi kufita bama bu?atar zaman kowacce a anan .
? ? ?? Cikin Sacin rai suka mike su biyun suka fice. Daddy ya cigaba da faWa tamkar zai ari baki, da ?yar dai su Abie Win suma suka taushesa. HaWuwa sukai akan Fadwa da Shareff Win duka sukai musu tatas da faWa musamman Fadwa a matsayinta na mace. Sai kuma suka koma nasiha a garesu. Daga nan suna jiyo hayaniyar Mommy da Gwaggo Halima, hakan yasa Gwaggo da har yanzu bata tofa nata ba ta mi?e ta fita wai zata tsawata musu. Nasiha Abie ya sake musu ta fahimta data saka zukatansu samun nutsuwa, musamman ma Fadwa da taga an nunama Shareff kuskuren marinta da yayi kuma ya nuna nadamar yin hakan da al?awarin bazai sake ba. Duk da dai itama tasha nata, sun kuma nuna mata illar biyema su aunty Malika cikin hikima. Basu san babu abinda ke cizon zuciyar Shareff ba kamar maganar su aunty Safara'h Win nan. Sai dai baice komai ba dan a samu zaman lafiya, amma yay aniyar da kansa zaima tuf?ar hanci insha ALLAHU.
? ? ?
? ? ? ? Da ?yar wajen ?arfe goma suka baro gidan, dan kuwa rikici ne na gaske ya Sarke tsakanin Gwaggo Halima da Mommy har sai da Baban Fadwa ya kira waya dan baya ?asar ne shiyyasa harta samu damar fitowa. Ya kuma janye mata wancan sharaWin lokacin da zaiyi tafiyar saboda ha?uri data bashi akan komai ya wuce. Ashe akwai wani a gaba. Mommy dai taci alwashin sai ta nunama Gwaggo Halima itace ta haifi Shareff ba wani shege ya haifa mata ba. Haka itama Gwaggo Halima ta tabbatar mata cewa ita bata isa komai ba domin Shareff Win ba nata bane ita kaWai..
? ?? Kuka Fadwa ke masa tunda suka taho, dan kuwa rikicin Mommy da Mamanta ya matu?ar Waga mata hankali kuma, tana matu?ar tsoron abinda zai rabata da Shareff, tana masa so ne mai tsanani, wanda takejin in har aka rabasu zata iya rasa har ranta. Ya gaji dajin kukan, saboda shima zuciyarsa a wuya take kuma yanajin ?una da raWaWin abubuwa masu yawa. Sai dai shi jarumin mutum ne mai maida komai ba komai ba koda kuwa a ce ya zame masa komai. Dan haka har suka iso gida bai ce mata komai ba. Shine ma ya fara fita ya barta a motar, saida ta kai kusan minti huWu a ciki tana cigaba da kukanta sannan ta fito ta rufe motar. Sashensa ta bisa kai tsaye, yana a falo zaune cikin yanayi na wanda baka iya ganemawa. Cikin jan ?afa ta ?arasa gabansa, ta tsugunna tare da dafa guyawunsa.
? ? ?  Ina tsugunne ne gabanka a matsayin ?anwa Yaya Shareff, nasan ni mai laifukace a gareka tari-tari, na kuma yarda nayi kuskuren da kake son na fahimta tun kafin akai ga wannan gaSar. Wlhy bana son zumincin iyayenmu ya lalace saboda aurenmu......
? ?  Garama ya lalace, dan ta hakane kawai dake da su zaku dawo rayuwar hankali irin ta mutane. Ke kam rayuwarki naban mamaki matu?a, mamaki irin wanda nake shiga kokwanto. Ba haka nai miki zatoba sam-sam a rayuwata ba, amma bazance ki dainaba kiyi tayi, shawara Waya zan baki kuma ta ?arshe. Ya rage naki ki dawo akan ?ya?y?yawar hanya Waya tak ki gyara halayenki muyi zaman aure na gaskiya, idan ba hakaba wlhy wlhy zan Wauki mataki ne na ?arshe dan bazaki maidani mahaukaci ba. Shawara ta rage gareki, ki cigaba da biyema duk wani mai zuwa gidan nan yana Wauraki a hanyoyin da shi yake ado da su, koki zama mace tagari ki gina taki rayuwar a karan kanki. Idan kuma kika sake amfani da wani abu na kauce hanya domin mallakata, ko bani wani abu a cikin ruwan sha ko abinci ALLAH ya isa ban yafe ba! . Ya ture hanunta tare da mi?ewa ya shige bedroom abinsa.
? ?? Hawayen da take son su zuba ma sam sun?i zubar a yanzu, sai dai tasan gaskiya ya faWa mata, dan kuwa a yanzu tana rayuwa ne da rayuwar su aunty Safarah, a baya komi za'a bata ta zubama Shareff a abinci bata taSa yin hakan tunma tana gida, duk ma yanda zatai ?o?arin hanawa sai tayi, sai dai in Mama ta aikata bada saninta ba. Amma a wannan gaSar ta rikice, idonta ya rufe saboda kishiya da kanta take aikata komai dan taga haske. Sai dai saSanin hakan duhu take gani, sannan mai makon mallakarsa suSuce mata yakeyi, kenan su magungunan na ?arya sunfi yawa a cikinsu kenan? ?alilanne ake dacewa suyi aikin kuma basa wani jimawa sai kaga abubuwa sun ?waSe.  Ya ALLAH ta faWa tana mai fashewa da kukan zahiri.

? ? _____________&

? ? ?? Harta fara jin barci a jiya bai dawo ba, dan ita bata san tare da Fadwa ya fita ba. Koda ta shirya Wakin da Aysha ke kwana taje ta kwanta abinta. Ayshan batace da ita komai ba dan tasan yau Shareff ya koma wajen Fadwa. Ta Wanyi murmushi ganin Anaam Win sukuku, ko bata fito ta faWa ba tasan kewar Yayansu ke nu?ur?usarta. Sai dai sanin itama Anaam nada halin I don't care wasu lokutan yasa babu wannan alamar akan fuskarta sam. Sai dai kuma koda suka kwanta ta jima batai barci tanata juye-juye. Sai da Ayshan ta Wauke hankalinta da wasu labarai? sannan Sarawon yay mata kamun kazar kuku. Ajiyar zuciya Aysha ta saki mai ?arfi da kai hannu ta ri?o na Anaam Win. Tausayinta da ?aunar ?ar uwarta na ratsa mata zuciya matu?a....

? ? ?? &Kamar yanda ya saba da asuba sai da yazo ya tada su, Anaam ?in yarda tai ta kalla inda yake taima shigewarta toilet. Juyawa yay ya fita shima yana mai sakin guntun murmushi. Itama Fadwa sai da yaje ya tadasu sannan ya wuce massallaci. Daya dawo bai shiga sashen kowacce ba ya koma nasa sashen ya kwanta dan jiya ya jima bai barci ba yanata faman ?ullawa da kwancewa akan yanda zai Sulloma matan nasa. Barci yasha sosai dan sai kusan goma da wasu mintuna ya iya tashi, baiyi mamakin ganin an gyara ko'ina ba ga ?amshi na tashi, sai dai yaji sassauci a ransa dan Fadwa ta nuna masa ta yarda ta gyara abinda take shirin Sararwa a idanunsa. Wanka ya farayi ya shirya tare da baje jikinsa da ?amshin turarurrukansa masu ?amshin daWi. Koda ya fito a falo ya sami Fadwa zaune cikin kwalliya mai Waukar hankali. Tabbas ta Wauka hankalin nasa da gaske, sai dai ya basar abinsa. Gaisheshi tayi, ya amsa a da?ile, bata gazaba wajen sake jero masa kalaman ban ha?uri da tabbatar masa zata canja fiye da yanda yake bu?ata. Har cikin rai ya Wanjin tausayinta, dan yasan ya mata hukunci dai-dai da laifinta da har idan ita ba ibilisiya bace ya kamata yaga canjin. Huci ya Wan furzar tare da ware mata hannayensa. Ai da gudu tazo ta shige jikinsa. Ya saki ?aramin murmushi tare da sauke hannayensa akan bayanta ya fara shafawa alamar lallashi. Hawayene suka dinga silalo mata, ita kanta ta ?ara shaidawa Soulmate Winta zuma ne, ga za?i ga harbi. Ya Wagota yana kallon fuskarta har yanzu dai babu fara'ar da take muradin gani a garesa.
 Kin san bana son kukan nan ko? .
Kanta ta jinjina masa tana sharewa, ya raSata ya wuce yana faWin,  Ina zuwa bara na duba waWan can ya suka kwana . Kanta ta jinjina masa, ta bisa da kallo tana ?ara tsane hawayenta dake sakkowa. Ta san bawai ya gama hucewar bane, amma ko yanzu ta samu sassauci. Zakuma tabi duk hanyar data dace domin ganin ya huce baki Waya sun koma rayuwar farin cikinsu....

A falo ya samesu su duka. Anaam na tsaye ri?e da cup na shayi idonta a tv tana murmushi.  Wato blood film Win nan fa zaiyi daWi, sai dai guy Win film Win sam baimun ba shegen kunensa uwa na zomaye ALLAH . Dariya Aysha ta sanya harda ?ya?y?yawa tana le?owa daga kitchen.  Amma wlhy kinci zarafin mutumin nan, ni banga wani kunen da kike masa sheri da su ba.
 ALLAH da gaske yanada kunnuwa gasu nan, ga shegen rawan kai a wajensa uwa dangin makaWan zamanin jahiliyya, ALLAH an cuceta da aka haWata da shi .
Alamar komawa yay ma Aysha data le?o zatai magana, tai saurin komawa cikin bin umarninsa harda turo ?ofar kitchen Win dan ta tabbatar wata taSarar za'ai. Rayuwar Yayansu na birgeta tun akan Fadwa, gashi dai mutum miskili da baya Waukar raini amma matansa nashan sharafin soyayyarsa. Cigaba yay da tsayawa a bakin ?ofar hannayensa harWe da ?irjinsa yana kallon Anaam Win kawai. Ita ko sam bata san da zamansa ba amma tanajin ?amshin turarensa a hancinta wanda take ganin hakan normal ne tunda dama yana shigowa maybe tunna baya ne. Juyowa tai zata koma saman kujera suka kusa cin karo da shi dan ya baro ?ofar. Da sauri ta Wanyi baya a zabure dan tsoroma ya bata. Cikin zafin nama ya ri?e cup Win shayin dake neman antayewa a jikinta.
Baki ta tura gaba da ?waSe fuskarta da tasha kwalliya.  Kai Yaya ALLAH ka tsoratani .
Idonsa akan lips Winta ya Wage mata gira Waya,  Kin dai so ki tsorata madam . Bakin ta ?ara tura masa tana ?o?arin janye jikinta. Hanata hakan yay ta hanyar ri?o ?ugunta, ya zuba mata mayun idanunsa cikin nata idon, tare da matso hanunta da nasa dake rike da kofin shayin yakai bakinsa.  Wayyo Yaya ni ALLAH zaka shanyemun tea Wina .
 K miyasa rowanki yayi yawa ne? .
 To kai miyasa kwaWayinka yay yawa ne .
Murmushi yayi da kai yatsarsa ya Walle mata baki,  Magananniya da ba'a kadata. Sammin lipstick Win shima Please .
 Tab ni ban saka da kai ba ni kaWai zan shanye abuna .
Dariyarsa ya danne da ?yar, ya Wan ?waSe fuska da langaSe kai gefe,  Babie Please mana .
 Na?i wayon . Ta faWa dayi masa gwalo tana tura lips Win cikin baki.  Ni kikama rashin m ko? Zan rama ALLAH . Dariya ta ?yal?yale da shi da masa gwalo.  Kafin ka rama na ?ara wani rashin m Win ma . Ta zille, ri?ota yasoyi amma tai tsalle gefe tana masa gwalo.  Zan rama ne yarinya ai zaki zo hannu. Oya muje breakfast ..
Idanu ta Wan waro,  Gashifa Aysha na mana anan .
 Kin manta tsarina kenan .
Shiru tai cikin Wan tauke fuska. Dan ta ?wallafa rai a abinda Ayshan keyi. Amma sai batai musu ba ta kaWa masa kai. Tare suka fita, sun iske Fadwa na ?ara gyara dining Win. A yau ma babu wacce ta kalla ?ar uwarta a cikinsu. Dan haka ya duba kowacce fuskarsa a tsuke.  Kun gaisa da juna? .
Shiru duk sukayi kowanne idonsa a ?asa dan a serious yay maganar. Fadwa ce tai ?o?arin dannewa a sha?e tace  Kin tashi lafiya? . Baki Anaam Win ta taSe da amsawa a sha?en itama.  Alhmdllhi . Komai bai sake ce musu ba, dan yasan a haka a haka watarana zai ci nasara. Wayarsa da yake latsawa ya ajiye, Fadwa ta fara haWa masa abincin. A daidai nan Aysha ta shigo da ?aramin tray. Wani irin ajiyar zuciya Anaam ta saki a hankali. Ya Wan saci kalonta ta gefen ido sai yaji tausayinta. Ya fahimci tana son abinda Ayshan ke musu amma tabi umarninsa ta taho, shiyyasa yayma Aysha text yace ta kawo mata. Kasa Soye farin cikinta tayi har sai da ta kalla Aysha da murmushi.  Thanks you blood . Murmushi Aysha ta mata. Itama sai ta sake murmusawa. Har Aysha ta juya zata fita Fadwa tace,  Ki dawo mu karya mana Aysha .
 No Aunty gashi can na baro kar a barsa ya lalace shima . Tai maganar tana nufar hanyar fita da Wan hanzari dan karma Shareff ya tsaidata. Batama san shi baida niyyar tanka musu ba. Abincinsa yake ?o?arin fara ci kawai............
'



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS=?G?
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA=?G?
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O?



*_d'
=?%?BABU SO....!!d'
=?%?_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce>??
*_BABU SO=?I?
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_72_*



.........Abincin yakeci cike da nazarin kowaccensu. Fadwa nayin komaine a taka tsantsan na gudun yin kuskure fatanta komai ya wuce. Yayinda Anaam ke komanta kai tsaye hankalinta kacokan naga abincin da takeci tamkar ta manta da zaman kowannensu a wajen ma. A haka dai suka kammala Fadwa ta fara gyara wajen, dakatar da ita yay dan haka ta koma ta zauna. Anaam data Wauka waya yayma magana, itama ta ajiye suka bashi hankalinsu. Nasiha ya fara musu a nutse tare da jan gargaWi. Daga ?arshe cikin kaushin murya da tabbatarwa ya Wan bubbuga table Win da yatsansa.
? ? ??  Bazan lalace wajen zargi akan ku balle ?in cin duk abinda kuka bani ba, sai dai zan tabbatar muku, duk wadda ta zuba wani abu koda a ruwan sha Winane domin samun wani cikar burinta ban yafe mata ba. Kuma idan na kamata bazan yafe mataba ko iya cigaba da zama da ita duk da babu tsarin rabuwa da Wayanku a zuciyata. Shawara ya rage naku, kumu haWu mu zauna don ALLAH cikin soyayya da mutunta juna, ko kuma kowa ya Wauka layin da yaga zai dace da shi a shirye nake wajen maganin duk wadda take tunanin zata iya fin ?arfi na. Na ?arshe respecting juna da kuma iyayenmu. Wlhy idan wata a cikinku ta sake kuskuren yin abinda bai dace ba akan wani ko wata a cikin iyayrenmu sai na sakata nadama ta har abada, ya rage naku ku dawo hankalinku kokuma ku Waura daga inda kuka tsaya .
? ? ?? Har ?asan zuciya kausasan gargaWinsa sun shigesu, sai dai sunfi ratsa Fadwa musamman akan zuba masa magani a abinci fiye da Anaam da wannan gaSar bama komai ta fahinta ba. Amma dangane da girmama iyayensu da juna ya shigeta matu?a, dan yanayinsa ya tabbatar musu zai iya komai. Bayan ya sallamesu kowacce ta nufi Sangarenta tana ?ullawa da kwancewa. Shima fita yay a gidan zuwa can gidansu gaida su Mommy tunda yanzu Daddy ya janye masa sharaWin hana zuwa gidan. Sai dai koda yaje ya samu Mommy da Gwaggo basa nan. Bai so haka ba, dan yazone takanas ya lallashi mommy Win da bata ha?uri akan komai ma daya faru, sannan ya yini da ita yau. Gidan su Anaam ma ya iske Mamie da aunty Mimi sun fita, dole dai ya koma gida dan gwara yaje ya huta kawai shima.

? ? ? A Sangaren Mommy da Gwaggo gidajen su aunty Malika sukaje sukai musu tatas, inda akai hargitsi bana wasa ba har saida takai an gurfana a kotun baba Ibrahim. Shima al'amarin ya Sata masa rai, dan yajima dajin tsiyatakun da su Malikar keyi a gidajen aurensu. Sai gashi yau suna neman saka Fadwa itama kuma abin takaicin harda haWin kan mahaifiyarta. Sosai yayima Gwaggo Halima dake matsayin matar Wan uwansa faWa, ya nuna mata kuskurenta na son Waura Wiyarta akan bigiren da zai rusa rayuwarta a dunuya da lahira. Suma kuma su Mommy yay musu nasu faWan, dan tun farko da basu nunama Fadwa komai tayi a gidan aurenta dai-dai bane daba haka ba. Yanzu gashi sun WanWana mata tana niyyar zartasu kuma sun shiga damuwa, ta riga kuma ta WanWana ba lallai abin ya iya barinta ta sau?i ba.
? ? ?? Nasihar Baba Ibrahim bata canja komai a jin haushin juna da Mommy da Gwaggo Halima keyi ba. Sai ma ?ara jin zafin juna dan kowacce nada sirrin ?ar uwarta a tafin hannu. Kuma kowacce taci alwashin nunama ?ar uwarta fawa Winta akan ?a?an nasu da kuma mazajensu da suke amsa yayanninsu. Da haka aka sake rabuwa baran-baran.....

____________________________

? ? ? ? ? Ga Shareff kam tun yana shashshare Fadwa harya dai ya sakko, mata da miji sai ALLAH. Sai gasu kamar komai bai faruba aka koma faranta ran juna, dan aranar ba ?aramin rikita Soulmate Win nata tai ba, har yaji a karan kasa ta cancanci yafiya. Sai dai tsananin kishin mijinta na nan a zuciyarta. A duk sanda ta tuna akwai wata a yanzu bayan ita tare da shi takanji raWaWi mai zafi a zuciyarta. Sai dai ta Wauka al?awarin daina biyema su Aunty Safarah, bazata ?ara amfani da wani magani ba insha ALLAHU. Zata tsaya da ?afafunta wajen kishin mijinta da ?yautata masa kowacce ta ?waci kanta kawai. Dan tayi imani bazata taSa son Anaam ba a zuciyarta, saboda tunda ta tashi a rayuwa da tsanar iyayenta da ita kanta ta rayu.
? ? ? A Sangaren Anaam Win itama sosai take jin kishin mijin nata, dan akwana biyun nan da yake tare da watanta ba itaba tana matu?ar jin raWaWi da zafi. Abinda ya sau?a?a mata kawai zaman Aysha tare da ita. Amma ko shigowa yay wajensu sai tayi matu?ar dauriya take iya kallonsa har ta sakar masa murmushi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login