Showing 174001 words to 177000 words out of 194140 words

Chapter 59 - BABU SO Miya kawo Kishi Book complete by M shakur.doc

M Shakur   

26 Oct 2025

3274

dan farin cikine baibaye da zukatansu. A ranar akai ?unshi, sai dai tana nane da su Mamie bata shiga cikin gida ba. Washe gari kamu ta tashi duk batajin daWin jikinta tun safe. Amma sai ta danganta hakan da kewar Shareff dake damunta. Tun wajen sha biyu ta shige cikin gida, kasancewar sashen Mom dana Mommy duk cike yake da ba?i saita nufi sashen aunty Amarya dan su Aysha nacan da gayyar ?awayenta. Tuni ta shige cikinsu anata shan shafta har akai mata ?unshi da Aysha ta matsa. Tun ana lallin take complain ayi maza a gama kanta ciwo yake, Aysha na hararar ta wai ?unshinne bataso, in ma an gama anjima kaWan tare zasuje Saloon ko ta?i ko taso.
Kamar wasa tace musu jiri takeji, kuma tana ganin hayaniyar gidance, Aysha dai taita lallaSata ta shige bedroom Win aunty Amarya ta kwanta. Sai da ?awayen amarya suka gama shiri suka fita tsakar gida Aunty Rahma ta shigo ta gata ita da Aunty Bintu. Sune suka sakata tashi dole tai wanka. Amrah ta kawo mata kayanta ta shirya anan. Jin yanzu babu jirin saita fito tsakar gida inda kamu ke gudana. Dan ?arfin hali harda shiga fili taima amarya liki. Masu kiWan kwarya suka shiga koWata da kirarin Amaryar babban yaya Shareff. Ana haka Khaleel ya shigo shi da Shareff da Maheer. Anaam ta nufesu tana murmushi ta farama Khaleel Win li?i. Hakan yasa aka dawo aka baibayesu masu kiWan ?warya na cigaba da kwarzantata. Shareff dake kallonta yana murmushi baima san ya zaro nasa ?an kudaWen ba ya fara li?eta, hakan yasa shima Maheer zarowa yana musu li?in su duka uku. Aifa sai waje ya Wauka ihu, dangi aka zagayesu su duka huWun ana musu li?i. Tun Anaam najin hayaniyar sama-sama harta fara jinta nesa-nesa. Idanunta suka fara limshewa tai baya zata sulale Shareff daya farga yay saurin tarota jikinsa. A take waje ya Wau shiru. Da sauri Aunty Bintu ta kawo ruwa aka shafama Anaam Win saita kawo nannauyan numfashi. Kanta ta ri?e hawaye na ziraro mata.  Yaya kaina, kaina zai fashe Yaya .
Hankali tashe ya sungumeta akai sashen aunty Amarya da ita, dan nan Winne kawai keda karacin mutane, dama ?awayen amaryane sai danginta tsiraru kasancewar ba ?ar kano bace, kuma duk sun fito. Maheer ne yay kiran Dr Jamal. Cikin ?an?anin lokaci sai gashi ya iso, har yanzu Anaam na'a jikin Shareff tana masa kukan kanta. Yana ri?e da kan yana mata addu'a, su aunty Amarya zagaye da su. Dan hatta Mom da Aunty Mimi duk suna a wajen. Tuni kuma an kaima Mommy da Gwaggo rahoto sai dai basu fitoba. Mamie ma nacan cikin damuwa a tsakar gida amma dattakonta ya hanata shigowa taga halin da Anaam Win ke'a ciki. Su Daddy dai suna can gidan su Anaam din tare da Abie dan can Win babu mutane sosai duk anyo nan cikin gida.
A kallo Waya Dr Jamal ya fahimci matsalar Anaam Win, dan haka ya kalli Shareff cikin ido. Hararsa yayi yana motsa laSSansa ahankali alamar magana yayi sai dai bata fitoba kasancewar falon cike yake da su Mom. Jininta ya Wiba ya kuma bata maganin ciwon kan kawai.  Inaga zanje ai text first, amma dai tasha maganin sai taje inda babu wannan hayaniyar ta kwanta ta huta. Inba hakaba ciwon kan zai cigaba da damunta. Zuwa da safe insha ALLAHU zan kawo sakamakon  .
 Kana nufin wannan maganin kawai zaka bata ka barmin mata cikin ciwo kenan? .
Shareff ya faWa cikin suSutar baki dan ya ma manta da su aunty Mimi dake wajen. Babu wanda baiyi murmushi ba, ?anensa na gulmarsa a zuciya ina miskilancin nasa yaje. Sai dai babu mai damar cewa komai. Maheer kam jikinsa ne yay sanyi, ya dubi matarsa da sam tama ?i sakewa a gidan saboda a wajensa ma bata samu farin ciki ba. Auren watanni huWu ya kasa sakin ransa ko kusantarta ya?i yi, ita kuma ta tura masa aniyarsa duk abinda ya dace mace ta gari taiwa miji bata gazaba tana masa gwargwadon iyawarta.
Yanzun ma ko kunya babu shine ya kaita can gidansu dan acanne kawai akeda ?arancin hayaniya. Kai tsaye sama ya kaita Wakin Mamie ya kwantar a kan gado, yana daga zaune kanta bisa cinyarsa yana tofa mata addu'a a kanta aunty Mimi ta shigo Wauke da ?aramar roba da towel ?arami a ciki. Shine ya amsa, tai murmushi a ranta tana faWin, (?an banzan yara dakun cigaba da pretending da rabo ya kashe har mu bama ku kaWai ba. Dan wannan daga gani ciki ne). A zahiri kam juyawa tai tayi ficewrta ta bar musu Wakin. Towel Win ya dinga matsewa a cikin ruwan yana goga mata a goshi zuwa fuska har wuyanta da hannayenta. Sai da kanta dake zafi Wau ya huce sosai sannan ya koma kafafunta. cikin ?an?anin lokaci sai ga barci ya Wauketa. Ya sauke ajiyar zuciya da komawa gefen gadon ya tsugunna saitin fuskarta. Kallonta yake da murmushi, ?aunarta na ?ara ratsashi. Ya kai lips Winsa kan nata ya sumbata, hakama idanunta dake lumshe. Har cikin ransa yana fatan hasashensa ya zama gaskiya. Addu'a daya jima yanayi ta samun rabo daga kowaccensu ta tabbata a wannan karon. Dan ko kwana biyu ba'ai ba da gama yima Fadwa ?orafi akan hakan.
Shigowar Mamie data kasa ha?uri ce ta sashi mikewa yana shafar ?eya. Haka kawai yanzu yake jin tsananin kunyarsu ita da Abie babu gaira babu sabar. Cikin sanWa da dabara ya zare jikinsa ya gudu a Wakin.....

Su Daddy ma sun shigo dubata bayan sallar isha'i, har sannan kuma bata tashi ba tanata barci. Sun mata addu'ar samun lafiya suka fice. Sai da Abie ya rakatane ya dawo domin sake duba tilon ?ar tasa. Yana a Wakin Shareff ya dawo, ji yay duk ya daburce, dan haka yaki sakewa ya gudu, duk da Abie nace masa ya dawo shi fitama zaiyi amma ya?i tsayawa wai dama yazo ya sake dubatane zai wuce gida goma tayi.....

*_WASHE GARI_* al'ummar wannan family suka tashi da farin cikin bayyanar cikin Anaam Wan watanni biyu da wasu kwanaki da adadinsu baida yawa na cika watanni uku. Zokaga murna wajen su Mamie da su Daddy. ALLAH mai alheri, su sunsha kuka da damuwar rashin samun haihuwa da wuri ga Anaam da bata rufa watanni huWu ciff ba da ciki. Wannan rahama ce ta UBANGIJI mai yin yanda yaso a lokacin da yaso. Isar wannan al'amari kunen Gwaggo da Mommy tamkar saukar aradune a tsakiyar dare mai duhuwa. Dama dama ma Mommy bataji zuciyarta ta zafafa ba a wannan karon har hakan ya bata mamaki. Amma Gwaggo gaba Waya birkicewa tayi har bakinta ya dinga subucewa wajen sakin wasu maganganu. Koda ta kira Mommy gefe kan hakan sai Mommyn ta nuna mata ita duk da bata son Anaam da su Abie taji son cikin dan koba komai gudan jinin Shareff ne ai. Wannan furuci ya matu?ar ?ona zuciyar Gwaggo. Dan haka ta Wau alwashin sai ta Sata taron bikin nan. Cikin halin ko'in kula Mommy tai komawarta cikin danginta ta cigaba da hidimarta. Gwaggo ta bita da kallo zuciyarta na suya matu?a, ita Nafisa zataima wannan Wibar albarkar, to ai idan tasan wata bata san wataba wlhy. Barin wajen tai fuuu kamar zataci tun tuSe zuwa sashenta tana ?ulla wutar da zata kunno a gobe idan ALLAH ya kaimu.
Bayyanar cikin Anaam ta matu?ar tada hankalin Fadwa, musamman dataga kamar dai nata Shareff bai wani zumuWi ba ko rawan kai a zahiri. Amma kuma yanayinsa na son nuna kulawa ga Anaam ya tabbatar mata nunawarsa a fili bashi ke nufin baya son haihuwaba. Kawai dai hakan naturally Win halayyarsace Soye sirrin zuciya. Ba ita kaWaiba hatta Gwaggo Halima maganar cikin nan ya tada mata hankali. A karon farko sai gata gidan Shareff Win dan bata taSa zuwa ba. Cikin shirin tafiya gidan biki take, dan acewarta zataje bikin Khaleel ne bana Aysha ba, dan ita da Mommy a yanzu babu shiri kwata-kwata, saima ya?ar juna da akeyi.
Kuka sosai Fadwa ta dinga yimata akan ta shiga uku itakam, ga Anaam tazo a bayanta ta samu ciki amma ita tun miscarriage data samu babu wani bayani (Karfa ku manta ko Gwaggo Halima bata san Fadwa zubda ciki taiba. ?awayenta ne da Gwaggo kawai suka san wannan sirrin, sai ko Anaam. Gwaggo ma ita da Bibah da hajiya Luba maman Bibah kawai suka sani).
 Kinga kwantar da hankalinki a gama hayaniyar bikin nan sai mu tafi Germany kiga likita, karma ki bari wani abu ya tada miki hankali kinji shalele .
Lallashin Mamanta ya saka mata samun ?ar nutsuwa harta shirya ta bita sukaje gidan bikin, inda da ace sun san mi Gwaggo ke ?ullawa da basuje ba, sai dai bawa bai isa sanin gaibuba daga kadarar abinda zai faru a minti guda na gaibunsa sam.........
'


Humm, yau fa akeyinta=ض???=ش?


_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS=?G?
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA=?G?
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O? Chapter: 76

..........Sun iso gidan biki inda yake tan?am da jama'a. Dan maza nata shirin wucewa massallaci saboda an haWe Waurin auren waje guda har na Khaleel domin sau?a?awa mutane. Cikin takama da isa Gwaggo Halima da Fadwa suka shigo cikin gidan, anan fa kallo ya koma sama dan ko makaho ya shafa yasan naira ta zauna. Kai tsaye sashen Mom suka nufa dan ko kallon sashen Mommy a yanzu Gwaggo Halima batayi a gidan balle Gwaggo. Mom da babu ruwanta dama tai musu tarba ta mutuntawa duk da kuwa tunda aka tsira bikin sai yau kowa yaga idon Gwaggo Halima a gidan. Tadai aikoma Abba da Daddy Da mom gudun mawa. Shi kansa Khaleel mota ta dan?ara masa duk dan cusama Mommy haushi. Tuni ?ar rahoton Gwaggo taje ta sanar mata isowar su Fadwan. Tai murmushi mai alamomi da yawa tana mai mi?ewa, cikin toilet Winta ta shiga, duk da kuwa ta hana kowa shiga mata bedroom dama. Amma duk da haka bata yarda ta tsaya iya bedroom tai wayarba. Daga can aka Waga, fuskarta ?awace da murmushi cikin bada umarni kuma tace,  Ki tabbatar da an Waura aure ki tura masa, dan ina son maimakon su iso gida da labarin farin cikin an gama Waurin aure lafiya, labarin ya canja . Batako jira amsa ba ta kashe wayar gaba Waya.



????Cike da farin cikin sake aurar da yaransu lafiya su Daddy suka bar gida, tare da tawagar sauran ?a?ansu su Shareff da ango Khaleel da tarin abokansa da ?an uwa da abokan arzi?i. An fara yin sallar juma'a, sannan aka Waura auren Khaleel matsayinsa na babba, sai na Aysha da nata angon. Nan fa bakin kowa ya washe anata gaisuwa musamman su babban Yaya Shareff da Maheer. Anguna kam ai ba'a magana. Bakunansu har kunne ko gonar audiga albarka. Daga massallaci aka kwashi tawaga zuwa hall Win da aka shirya walimar cin abinci ta iya mazan kawai kamar yanda su Daddyn kanyi a duk aurarrakin ?a?ansu.

???Ana tsaka da cin abinci sa?o ya?shigo masa. Shi dama ba abincin yakema ci ba, yana charting ne da Anaam ta WhatsApp. Baibi takan sa?on ba ya fita da nufin rufe datan sai Anaam ta sake turo massege, ya koma da nufin buWewa ya gani hanunsa ya buWe wancan a mistake. Ganin videos da yawa ya bashi mamaki, sai yay tunanin shiga Waya a ciki yaga minene. Gabansa yay wani irin faWuwa sakamakon cin karo da Fadwa, best ce sanye jikinta fara da dogon wando, kanta babu Wan kwali, da sauri ya fito, mikewa yay zai bar hall Win dan bai kamata ya gani a gaban wani ba. Ya fito sai ya samu wasu a abokan Khaleel tsaye su kusan huWu tsaye, da alama suma sun fitone susha iska. Suka gaisheshi ya amsa musu da fara'a, harya gota su sai ya tsinkayi muryar wani a cikinsu na faWin,

??? Tabb bala'i, Mubeen da'alama yau zamusha kallo a tiktok. Gasu Sufi nan sun taSo mutuniyarka Fady Babie .

??Wanda aka kira Mubeen yaja tsaki,  Shegiyar yarinyar nan ai su Sufi Winne dai-dai da ita. ?awartace jiya taima ?an soja wani Comment Win rainin wayo shine fa yay mata tatas ya kuma ce yanada video Winta da taje Wakin wani guy, idan bata kama kantaba ana gab da cin kasuwarta a tiktok, shine ita mai bakin akku Fadwan ta maida murtani jiya da dare, ai shagalin nan ne yasa bakama luraba, tun jiya aka fara faWan har suna zasu Wakkoma su M soja ?an sanda, shine shi Sufi Win ya shiga faWan .

??? Oh dama haka akai, taSWi jan. Ai dama ina fatan naga wanda zai kawo ?arshen ?an iskan yaran nan, musamman Fadwa Win nan ta cika Waukar kanta wata tsiya. ?ar iska tayi auren ma kamar batai ba .

??? Ai bazaka ganeba yarinyarce ta haWu, wlhy da farko ban yarda bahausa bace ?ar arewa. Irin zu?a?an matan nan ai dole suyi girman kai dan ALLAH ya basu. Idan fa tai shigar ?anan kaya kamar wata balarabiya .

???Dariya mai maganar farkon yayi,  Shege ka ?yasa kenan, to tana dai da aure, akwai wani room mate Wina, ya rantsemin idan yaga yarinyar nan har hankalinsa tashi yake, har saida takai sai ya dinga wassafata a ransa ya bu?atarsa ta biya yake samun nutsuwa .

???A tare suka kwashe da dariya.  Kai wlhy bashi kaWaiba. Akwai lokacin datai wani shegen shiga tabi wa?ar mara mutuncin nan ranar jinai inama-inama, bara kaga video Win ALLAH yasa bata gogesa ba.

???Jiyay kamar jiri na Wibarsa. Amma kun san halin ?an mazan sai ya dake ya nufi samarin domin tabbatar da Fadwa Winsa ko wata. A hankali ya iso ta bayansu batare da sun fargaba. Wanda aka kira Mubeen na nuna musu video da yake faWa. Ba ?aramin tsinkewa zuciyarsa ta shigayi ba, dan ko'a magagin barci aka nuna masa video Win zai shaida wacece a cikinsa. Da baya-baya ya dinga tafiya har ALLAH ya bashi ikon jingina da motar dake kusa da shi, dai-dai nan Khaleel ya fito da babban abokinsa. Cikin salo irin na abokai yake ?undumoma abokan nasa zagin mi sukeyi anan. Ganin basuma ko jisa ba ya karaso inda suke.

???A firgice yace,  What!!? .

Yana mai fisge wayar. Shi kansa zuciyarsa ce ta shiga tsitstsinkewa, idanunsa sun gaza cigaba da kallon videon dan koba komai matar Yayansa ce. Yayan nasa kuma mai tsananin kima da mutunci a idonsa....

?? Kai lafiya kuwa? .

Mubeen ya faWa yana fisge wayarsa. Dariya sauran suka kwashe dashi. Anas yace,  Ka sani ko shima ya shiga tarko ne. To ka rufa mana asiri an jima zamu kaika ga taka wannan dai kwalelenk....

??Ai Khaleel baima san ya kaima Anas Win mari ba. Su duka suka zabura da waro idanu. Khaleel ya nunasa a zafafe.  Ka iya bakinka Anas, kasan Win ita wacece a wajena? To matar yayana ce, idan ?azamin bakinka ya sake faWar wata magana mara daWi zan fasashi .

???Sun tsorata ?warai da gaske da rikicewar tasa. Mubeen ya dubi Khaleel Win a karo na farko cin son yin tunani.  Khaleel dan ALLAH kwantar da hankalinka. Wlhy sai yanzu dakai maganar matar yayanka wani abu ya Wan dawo min a zuciya. Tabbas sanda ta Waura wani hoto nata tunanin a ina nasan mutumin, hakama da take daurasa matsayin mijinta na jima ina son hasasowa amma sai na kasa. Saboda sau Waya na taSa ganin Yayan naka shima ba wani mun jima bane. Da gaske wannan shashashar yarinyar ce matar Yayanka? Kasan kuwa wacece Fadwa a tiktok? A Sangaren shaiWanun tiktok da a kullum ake ALLAH wadai da su da ganin sakacin duk wani na kusa da su wlhy Fady na sahun farko, dan ita a karan kanta mata uwar shaiWanuce mai zaman kanta. Amma domin tabbatarwa maza ka shiga shafin nata ka duba zakafi yarda dani dai .

???Gaba Waya Khaleel yayi mutuwar tsaye, dan kuwa tun fara maganar Mubeen idanunsa suka hango masa Shareff dake tsaye alamar komai da suke yana jinsu. Shi a karan kansa Khaleel Win baya tiktok, bawai dan yana kallon tiktok Win baida amfani bane, a'a, a komai na rayuwa akwai mutanen banza a waje akwai na kirki. Shi bai taSa ?alubalantar tiktok ba ko yima jama'ar dake mu'amulantarsa kuWin goro. Ya tabbata idan aka shiga tiktok za'aci karo da abubuwa masu amfani kamar yanda za'a samu na banza marasa amfani. Kawai dai shima bamai ra'ayin yawan biye-biyen shafuka bane kowanne iri. idan ma ya kama sai yabi abinda ya kaisa kawai yake zuwa yayi saboda aikinsa na cimasa kaso mafi yawa na lokacinsa. Da sauri yabar inda su Mubeen suke ya nufi Shareff daya shiga mota da alamar barin wajen zaiyi. BuWewa yay ya shiga gefensa.

??? Please yaya k.....

Hannu ya Waga masa alamar kar yace komai.  Ka gafarceni Yaya, ka bani to na tu?aka . Bai sauraresa ba ya tada motar ya fice dasu da gudu. Duk magiyar da Khaleel ke masa bai nuna yaji ko daya ba har suka iso gidansa cikin ?an?anin lokaci. Tun a gate mai gadi ya sanar masa Fadwa ta fita ai tare da wata mata. Reverse yayi, nanma Khaleel nata ro?onsa amma ya sharesa. Kai tsaye gidansu Fadwan ya nufa, dan baiyi tunanin taje gidan bikin ba. Sai dai anan Win ma dai maigadi ya sanar musu bataje ba, sai dai sunga hajiya ta fita zuwa gidan biki. Khaleel da yasan ba saurarenaa zaiyiba yace,  Bara mu bincika ko tana can gidanmu din . Bai tankaba nan ma. Khaleel kuma bai fasa kiranba. Cikin sa'a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login