Showing 90001 words to 93000 words out of 194140 words

Chapter 31 - BABU SO Miya kawo Kishi Book complete by M shakur.doc

M Shakur   

26 Oct 2025

3338

A karon farko yay ?ar dariya mai sauti da faWin,  Wannan gaskiya ne, ALLAH dai ya basu zaman lafiya da ha?uri da juna tunda duk gidane, sai dai dan ALLAH kiyita ?ara nusar dashi da tausarsa tunda su duka ?an uwansa ne kar zuminci ya samu matsala azo ana hai hai babu daWi. Gaba Wayansu Waya suke a wajensa babu wadda tafi wata.......
Tunda ya fara jawabin nasa na ?arshe jikin Mommy ya hau rawa, bazata iya jin ?arshen zancem ba dan haka ta yanke wayar. Hajijiya taji tana neman Wibarta, a dai-dai nan Gwaggo da taga shiru bata dawoba ta biyota ta shigo. Salati ta saka da ri?eta da sauri.  Ke ko kina lafiya zaki kashe kanki Nafisa? .
Kuka Mommy ta fashe da shi,  Gwaggo sun kasheni, wlhy sunyi a banza, har abada jinina dana Usman bazasu zauna a inuwa gudaba. Gwaggo na rantse yau duk masifar da za'ai a gidan nan sai dai ayi sai Shareff ya saketa, ni Muhammad zai cima amana, ni Muhammad zai yaudara ya zalunta.....
 K wai miya farune kin sani a duhu?! .
 Gwaggo aure fa suka Waurama Shareff da Wiyar ma?iyana, wai ?ar gidan Usman. Kuma tabbas batun yau ba ma.
 ?ar gidan Usman?!! .
Gwaggo ta faWa a razane, Mommy bata amsa mataba ta mike fuu ta fito hanunta dafe da kanta dake juya mata. Gwaggo na ?o?arin tsaidata yanzu ma bata saurareta ba. kai tsaye hanyar gate tayi, Samira ta biyita da sauri.  Yaya! Yaya miya faru ne? Da gaske ne ko? .
Bata iya bama Samira amsaba ta fisgi gyalenta tai waje, kasancewar anata Waukar ?an biki da kawosu ta samu a napep. Daddy daya hangota da yake suna zaune a ?ofar gidan cikin runfa ya mi?e, sai dai kafin yazo har napep Win tabar wajen.......

&Tun Wazun ya farka saboda zuwan gayyar abokansa da sukaje Waurin aure. Shidai kallon mamaki yake musu, dan baiyi tsamanin ganinsu haka da yawa ba a waje Waurin auren ?anin nasa. Suko sai faman washe baki suke da tsokanarsa a sigar daya kasa ganewa dan kowa ya kasa fitowa fili yace wani abu saboda ganin Fadwa tare da shi. Ga kuma dama Dr Jamal ya rokesu kar suce komai anan Please. Basu wani jima sosai ba suka fita acewarsu zasuje cin abinci zuwa anjima zasu dawo duk da Doctor yace maybe ma zuwa dare su sallamesa. Bayan fitarsu Fadwa ta dawo kusa da shi. Ganin yanda tai kicin-kicin da fuska sai yaji wani iri, hannu ya mi?a mata alamar tazo, tai kamar zata no?e sai kuma ta nufesa ganin yay mata alamar ro?o. Jikinsa ya jawota ya rungume, ya sakar mata sumba a gefen wuyanta tare da Waura kansa a kafaWarta yay shiru. A hankali ta lumshe idanunta da haWiye kukan dake neman ?wace mata.
 Shii!! .
Ya faWa a hankali cikin kunnenta yana kai hannu ya tallafo fuskarta ya juyo da ita...... Burumm ta faWo Wakin kamar an jehota. Su dukansu sukai saurin kallon ?ofar, ganin Mommy ya sashi janye jikinsa cikin jin tsananin kunya, Fadwa kam wani irin takaici ne ya tsargi ranta kamar ta dannama Mommy zagi. Mommy kam da sam hankalinta bama yakai kan yanda suke Win ba ta jefa masa takarda da biro saman jiki......
 Rubuta mata saki uku yanzu-yanzun nan da manyan ba?i yanda iyayenta zasu gani da ?yau bama ?anana ba...
Cikin tsananin mamaki da rashin fahimta yake duban mahaifiyar tasa. Yayinda ?irjin Fadwa yay wani irin mahaukacin dokawa tamkar gagarumar aradu ta bada sautin fashewa. Ita dai tasan ita kaWaice matarsa ai........
Takarda da biron ya tattara ya Wauka, a hankali cikin muryar mara lafiya ya dubi Mommy.  First luv ban gane ba. Wazan saka? .
 Shegiyar yarinyar da aka Waura maka aure da ita a Soye mana, inba hakaba zan tsine maka Al-Mustapha, tsinuwa mai muni kuwa da a duniya ko kai bazaka ?ara morar kanka ba balle waninka!! .
A kusan tare zuciyarsa data Fadwa ta nema wantsalowa waje. Cikin rawar lips shi yay ?arfin halin faWin,  A...Aure kuma? First luv n... Ni aka Waurama aure?? .
Sake fusata ta tambayar tayi, cikin tsananin kaushin murya ta sake bashi umarni batare data amsa masa tambayarsa ba.  Bani da lokacin maka wani bayani anan, dan wlhy zan iya tsine maka Al-Mustapha. Da manyan ba?i cikin sakanni ashirin kacal ka rubuta Kai Al-Mustapha Muhammad Shareff, ka saki ?arsu Anam Saki uku har abada bakai babu ita. Inko ba hakaba shinuwa zata tabbata a kanka bayan cikar waWan nan sakannin .........
'


*_=?F???=ض? ? ? ??



_ZAFAFA BIYAR_

*_INAYAH_*
_MamuhGee_

*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_

*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_

*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_

*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_

_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*


YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS=?G?
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070

SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902

IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA=?G?
09134848107


*_ALLAH ka gafartama iyayenmu=?-?=?O?



*_d'
=?%?BABU SO....!!d'
=?%?_*
_(Miya kawo kishi?)_



*_Bilyn Abdull ce>??
*_BABU SO=?I?
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718


*_35_*


_ASSALAM ALAIKUM DEARIES ... BARKAN KU DA KOKARI .. KAMAR KODA YAUSHE. WANNAN KARON MA MUNA BARAR ROKON KU WAJEN TEMAKAWA CHANNEL DIN SUDEIS DAKE MANHAJAR YOUTUBE_

_YARO NE DAYA TASHI DA SON KARATUN ALQURANI ME GIRMA. YA KE KUMA KWADAYIN GADON ME SUNAN SA SHEIKH SUDEIS. DAN ALLAH A TEMAKA A DANNA MASA SUBSCRIBE. A KUMA YI VIEWING DA LIKING. A TEMAKA DA SHARING MA... JAZAKUM ALLAH KHAIRAN AS YOU DO...=ؕ?_

Assalamualaikum dear sisters and brothers.

Welcome to ummu sudais YouTube channel>?p?
A channel where the Holy Quran is been recited from different Angles.
Click on this link and listen to the Beautiful recitation that will melt your heart
https://youtu.be/Lafgc749sK8

Your subscription to our channel is of Great important. Please help us grow our channel by subscribing and liking our videos fisabilillah.
Thank you so much

--------------------

..........Cak numfashin Fadwa ya Wauke daga ?irjinta, idanunta suka fara ganin duhu-duhu, tai baya luuu zata faWi dan wani irin mugun hajijiyace ta lulluSe ganinta da jinta saboda maganar tazo mata ne tamkar saukar nokiliya.... LaSSanta matu?ar rawa suke na alamar sonyin magana, amma bushewar yawun dake taimakawa ma?oshinta ya hanata damar hakan. Sai faman raba idanu take a tsakanin Mommy dake tsaye tamkar bajimar zakanya taga abin farautarta da Shareff da alamu suka nuna shima yayi ?amewar wucin gadi ne saboda wani dalili na mamakin furicin Mommy Win ko wani abu daban da bata hasaso ba.....
? ?? Shigowar Daddy Wakin tamkar an jehosa ta maido Shareff a tashi sumar tsaywar jinin data riskesa tabbacin hasashen Fadwa, dan shima dai jinsa da ganinsa a take suka rabu da gangar jikinsa baki Waya, sai idanunsa ne kawai tsaye ?yam akan Mommy na tabbacin bashi da maraba da sumamme.
? ? ? ?  Bazan hanashi bin umarninki ba, sai dai nima a nawa umarnin, wlhy! Wlhy! Wlhy!! Idan har Al-Mustapha ka saki Mamana! Nima zan saki uwarka dai dai da adadin sakin da ta sakaka ka rubuta!!.......
? ?  Dana haWa jini da Usman da Ai'sha gara na barka har abadan abidina Muhammad!! . Mommy ta tari numfashin Daddy a tsawace.
 Okay fine! Haka kikace ko?. Kai Al-Musta.......... Shigowar Abba da Dr Jamal ta hana Daddy ?arasa faWar abinda ke bakinsa, sai dai wani irin mugun kallo da yake bin Mommy da shi, har cikin ranta yake ratsata, sai dai zuciyarta tayi bushewar da take jin zata iya Waukar koma minene daga garesa akan wannan auren da rabashi shine kawai samun nutsuwar ruhi a gareta. Gwaggo ta ri?o hanunta tana faWin,  Altine kina lafiya kuwa? Kai Muhammadu karka sake cewa komai kumuje gida .
? ? ?? Mommy ta fusge hanunta daga ri?on da Gwaggo taimata.  Wlhy Gwaggo babu inda zanje sai Al-Mustapha ya saki yarinyar nan, dan bana bu?atar auren nan ya sake minti guda a kansa!! .
? ? ? ? Dr Jamal da gaba Waya ya rikice cikin ro?o yace,  Dan ALLAH Mommy kiyi ha?uri, bara na basa sallamar sai aje gida wannan maganar bata nan bace ba . Kafin tace wani abu Gwaggo taja hanunta suka fice, ganin shima Daddy ya fita ya sata yarda ta bita. Abbah ya kama Shareff shi da Doctor Jamal. Wata Nurse kuma ta kama Fadwa da har yanzu babu alamar ta dawo hayyacinta.......

? ? ? ?? Sun sami gida ya gama hargitsewa shima. Dan Gwaggo Halima da komai yaje kunnenta gaba Waya ta haukace, sai zagin Abie take da tone-tone, dan waje ta fito tana faWar maganganu marasa daWi, Abie ya mi?e ya shige cikin gidansa, amma sai ta bisa har can. Jin zagi da tonan asirin yayi yawa Aunty Mimi ta kasa ha?uri duk da kowa ya santa mutumce mara faWa da son hayaniya. Amma zagin mahaifiyarsu da Gwaggo Halima keyi bazata iya jurewa ba ta fara tayata. Cikin ?an?anin lokaci hayaniya mai tsanani ta tashi dan dangin Mommy irinsu Samira tuni sun shigo gidan suna taya Gwaggo Halima.
? ?? Ran Daddy ya ?ara Saci, yayinda hankalin Abbah dana Shareff sukai matu?ar tashi su kuma. Da ?yar Gwaggo ta hana Mommy shiga gidan, yayinda Dr Jamal ya taimakawa Shareff zuwa ciki, wasu mata kuma suka kama Fadwa da zuwa yanzun ta fara kuka sai dai babu uhhm babu uhhm-uhhm.
? ? ? Daddy kam daya faWa gidan Abie lafiyayyun maruka guda biyu ya sauke akan fuskar Gwaggo Halima. Tamkar ?iftawar idanu gidan yay tsittt, ya kuma sauke mata wasu biyun da suka saka zukatan mafi yawan mutane girgiza. Gwaggo Halima maiji da kanta, Gwaggo Halima babbar mace hamsha?iya mai ta?ama da tun?aho da sunan mijinta da mu?aminsa koda a tsakkiyar cikin dangine, yau itace ake saukema waWan nan marukan, dole ne gida yay tsit. Daddy ya Waga hannu zai sauke mata na huWu Abie ya ri?e masa hannu. Cikin tsananin damuwa yake girgiza masa kai alamar ro?o. ?agowa Gwaggo Halima tai tare da ware hannu zata mari Abie taji an ri?e mata hannu tare da murWesa. Abbah ne da wannan aikin, ransa a matu?ar Sace tamkar bashi ba.....
 Ko'a mafarki kikai tunanin wannan kuskuren sai mun tabbatar da nadama a rayuwarki Halima!! . Kalaman Abbah dake amsa sunan ?ani a gareta sukai matu?ar ratsa kunnuwanta dama duk wanda ke a wajen.
? ? ? Sosai fa gida ya ?ara harmutsewa da ruWewa. Har hayaniyar ta saka Anaam dake barcin wahala farkawa. Tun farko ma Mamie ce da hankalinta ya tashi ta rurrufe windows yanda bazai kawo kunnen Anam Win ba, sai dai ?urar data sake tashi a yanzu tafi ?arfin ta farko. Da ?yar aka fidda Gwaggo Halima dake cigaba da Wurama Abie da Mamie da Aunty Mimi harma da su Daddy zagi daga gidan. Sai dai can cikin gidan ma Mommy ce ke borin sai Shareff ya saki Anam. Shiko ya shige bedroom Win Daddy ya kulle kansa sai faman dukan ?ofa take da tabbatar masa zata tsine masa.
? ? ?? Yana jinta, sai dai baya gane mi take faWa saboda hajijiyar dake juyawa da kansa. Yana zaune bakin gado hanunsa dafe da kansa hawaye na zirara akan fuskarsa. Tunda yake a rayuwarsa bai taSa ganin makamancin irin wannan tashin hankaliba. Daddy da gaba Waya idanunsa sun rine da Sacin rai ya fisgo Mommy dake faman jijjiga ?ofarsa tana jaddama Shareff ya buWe kota tsine masa. Babu zato ko tsammani ya sakar mata nata lafiyayyun marin itama da iyakar ?arfinsa. Dan tsabar azaba da firgita sai da ta faWa kan kujerar dake daura da ita hannunta duk biyu dafe da wajen da ya maretan.
? ? ?  Muhammad ni ka mara?!! .
 Idan kika ?ara cewa tak ma, zan iya miki dukan mutuwa ba mari kawai ba!! .
Kalamansa sunyi matu?ar razana duk wanda ke'a falon. Sai dai shi a garesa babu ko gezau ya sake tabbatar mata ta hanyar faWin  Idan kuma kinji ?arya bismillah gwada na tabbatar miki!! .
? ?? Bakin kuwa tai shirin buWewa zatai maganar dan zuciyarta ta rigada ta bushe Gwaggo tai saurin toshe mata shi, dan ita kam taga tsantsar wutar bala'in dake ci a cikin idanun Daddy irin wadda bata taSa ganiba a rayuwarta. Duk yanda Mommy taso Gwaggo ta sakar mata baki ta?i, nanfa suka hau kokawa, sai dai ALLAH ya ta?aita abun a dalilin shigowar yayun Mommy maza da Abbah yay kiransu a waya harda wanda ta kira Wazun taji komai a bakinsa da ?anin mahaifin Fadwa.
? ? ? A tsakar gida dai ?an biki masu gudun tashin hankali tuni sun fara zare jikinsu suna guduwa dama Magrib tayi, wanda kuwa zasu kwana anan da ?an son ganin yaya za'a ?are na zaune jugum-jugum, ?an bani na iya kuma nata ?us-?us. Fitowar su Daddy zasu wuce massallaci ya saka gidan Waukar tsit dan ko'ina akwai hasken wutar nefa, sai dai wasu basu daina magana ?asa-?asa ba sosai musamman waWanda ke'a Wan nesa da su.....

Bayan sallar isha'i duk wani mai faWa aji a gidan ya hallara a sashen Daddy ne. Dan hatta Anam da bayan farkawarta kunnenta ya jiye mata wasu maganganun da harta Wan fahimci abinda ke faruwa da akema jidalin tana wajen. Sai dai kuka take har muryarta bata fita, dan kunnenta ya jiye mata wasu manya-manyan zagi da Gwaggo Halima ta dinga jifan iyayenta da su. Gashi kuma Mamie na kuka ita da Aunty Mimi da babban yaron Aunty Mimi Win da Amrah. Tsabar kukan da take har amai tayi dan ji take kamarma ta mutu itakam ta huta, sai dai taci alwashin bazata taSa zaman aure da Shareff ba itama.....
? ? ? ? Yayan Mommy da suke kira da Baba Ibrahim ne ya gama ?arema kowa kallo, ganin babu Shareff a wajen ya tambaya. Anan ne Abbah ya mike ya nufi ?ofar bedroom Win Daddy. Zaune yake a kan sallaya hanunsa dafe da kansa dake matu?ar sara masa kamar zai faWi, sallarma da ?yar ya iya tashi yayita ganin lokaci zai shige dan har magtib ya haWa. Jin muryar Abba ta sashi mi?ewa da ?yar ya nufi ?ofar ya buWe, Abba dake kallonsa cike da tausayawa ya Wan ri?o kafaWarsa.
? ? ??  Yaya dai Babana kanne ke ciwo? .
?? A hankali ya iya jinjin kan nasa da Wago idanunsa da sukai jazur ya Wan kalli Abban. Murmushin ?arfin hali yay ya maida kansa ?asa ya risinar. Sannu Abban yay masa cikin tausayawa da ri?osa suka fito, kusan kowa sai da ya zuba masa ido a falon, shi kam bai yarda ya kalla kowa ba ya zauna kusa da ?afafun Abba.
? ? ?? Baba Ibrahim ya buWe taro da addu'a, kafin ya fara magana cikin nasiha dajan hankalinsu akan muhimmancin zuminci a musulunci da zamantakewar rayuwa. Ya Wora da faWin,  Wannan aure a ganina abin alfaharine a gareku dan koba komai ya dun?uleku ne waje Waya a matsayinku na jini guda. Fatan alkairi da ?arfafa gwiwa kawai ya rage kuyi ga shi Shareffuddeen da nauyin ya rataya a kansa, amma ba wannan shirmen ba, gaba Waya yaran nan fa a ?ar?ashin ikonku suke, bazakuyi fatan bijirewar waninsu gareku ba in har kunada hangen nesa. Amma ke Nafisa minene naki na tada jijiyar wuya yaro ya saki matarsa?? .
? ? ?? Mommy dake cike fam da nasihar Yayan nata ta saki kuka,  Wlhy ni dai Yaya bana bu?atar wannan haWin, inhar nice na haifi Shareff to ina umartarsa ya saki yarinyar nan hakan zaifi mana zaman lafiya a gidan nan bana bu?atar wannan kwamacalar. Taya yana auren ?ar wajen Halima kuma ace ya auri wannan ai an haWa husumane dan kishi ba wasa bane, babu wani zama tsintsiya maWaurinki Waya da hakan zai kawo sai ma wata sabuwar musibar. Kuma wannan ai munafunci ne, inba munafunci ba miyasa zasu Waura auren bada sanin kowa ba....
? ? ?  ALLAH ya rabamu da ita. Ban san hujjarki na kawo wannan misalan ba, ba kuma na bu?atar sani, sai dai zan miki adalci Waya, shine jin ta bakin shi Shareff da ayanzu ikon zartarwa ke hanunsa akan matarsa, dan nasan su dai su Muhammadu da yardarsu da son su sukai wannan haWin alkairi, kuma basu Soye dan munafuntarku ba sai dan kawo masalaha saboda sanin halinku. Dani kuma aka Waura auren tun waccan ranar kafin a Waura na ita Wiyar halima da kike magana, domin kuwa da safe muka Waura na ita Juwairiyya iya mu kaWai batare da sanin ko shi kansa Shareffuddeen ba, kafin a Waura na ita wannan yarinya Fadwa bayan sallar juma'a......
? Baki ta buWe zatai magana ya Waga mata hannu, dole tai shiru dan tana bala'in shakkarsa. Kallonsa ya maida ga Shareff da kansa ke ?asa har yanzu bai Wago ya kalli kowa ba, sai dai komai na shiga cikin kunensa kamar kowa, yayinda jawabin na Baba Ibrahim ke shigarsa tamkar almara, taya ya kasa gane an Waura masa aure da Anaam? Miyasa kuma aka zaSi Soye masa shima?......  Shareffuddeen! . Ya kirayi sunansa cike da kulawa.
? ? ? Bai Wago ba, sai dai ya amsa da  Na'am Baba . Cikin dasashshiyar muryarsa dake tabbatar da baida lafiya.  Nasan kanajin komai basai na ?ara maimaici ba, iyayenka sun baka mata domin ?o?arin ?ara ?arfafa zuminci a tsakaninsu da ku da suka haifa, shin kai ka amince da hakan a matsayinka na Wa a garesu ko kuwa kanada ja tamkar mahaifiyarka? .
? ? ? Tsitt falon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login