Showing 201001 words to 204000 words out of 221978 words

Chapter 68 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

bani shawara na gaya masa gaskiyar komai dana aikata amma duk da haka yace naje gida sai ya nemeni. Wlhy hankalina a tashe yake sis... Manaal. Ina cikin damuwa matuƙa, da aikin nan nake taimakon mahaifana, dan shekarar babana uku kenan yana fama da jiyya, nine babba a gidanmu nine koman su. Na samu aikin nan ne a dalilin Dr Rafeeq, lokacin da aka kwantar da babana a asibitinsa saboda zaman shiru sai naita zane-zane shine ya gani yace zai sama min aiki kodan na kula da iyayena dan a lokacin hatta kuɗin asibitin mun kasa biya duka. Ban san alaƙarki dasu boss ba, amma nasan kina da kusanci da Dr Rafeeq sosai, dan ALLAH ki jagoranceni wajensa kozai taimakeni ya bama Boss haƙuri tunda ɗan uwansa ne jininsa, kuma yana jin maganarsa......”
Wani irin kallon takaici Maanal ke masa, wato wannan dattijon da yake magana shine yaje Giro wajen mutanen can neman aurenta, ashe akanta ne ma AA yayma Abideen haka. Ranta a ɓace ta miƙe tana faɗin, “Ai Inaga zuwa gareni bashi da wani amfani Abideen. Tunda ai kaima kana da alaƙa da Rafeeq ɗin, kamar yanda ya samar maka aiki nima aikin kawai ya sama min, kaga alaƙar tamu duk iri ɗaya ce”.
Cikin sauri yasha gabanta. Kamar zai duƙa ya ce, “Dan girman ALLAH ki gafarceni, sannan ki yafe min kuskurena. Wlhy ba rasa aikin bane kawai damuwata, cutar dake da na dingayi ta hanyar miki video ina tura masa batare da kin sani ba. Ban fahimci hakan zai iya zama illa ba sai da boss ya fargar dani. Tabbas yanda rayuwa ta lalace senator zai iya amfani da waɗan nan videos ɗin wajen ɓata miki suna ta hanyar maidasu a mummunar siga, alhalin kuma ke baki ma san an yi ba.”
Wani irin mugun bugawa ƙirjin Maanal yayi, dan ita kanta hankalinta bai kai can ba sam. Ai bama tasan ta shiga ambaton “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un”. Shi ko Abideen na faman jera mata kalaman ban haƙuri kamar zai yi kuka. Tsallake shi tai ta wuce ciki, ta barsa yana faman roƙo da magiya....


Koda ta shiga bata iya ta kula su Barrah ba dake mata oyoyo, sama-sama ta tattaɓasu ta wuce ciki. Tana shiga ɗaki ta sakama ƙofa key, sai hawaye shaaa. Haka kawai zuciyarta ke bata kamar abinda AA ɗin ya hango zai faru zai iya faruwa koma yana gab da faruwar. Tunda ita bama tasan wanene Senator Bukar ɗin nan ba ai. Ya ALLAH, tabbas ya kamata ta bincika, kuma a wajen AA ɗin kawai zata samu dukkan information ɗin da take buƙata. Wayarta ta ciro a bag, sai da ta fara sarrafata sai kuma ta tsaya cak dan tunawa da ai bata da no ɗin AA ɗin. Jagwab takai zaune a cikin sofa. Zuciyarta ce ta bata shawarar kiran RK ta tambaya number ɗin AA ɗin, sai kuma wani sashe na zuciyar ya ƙwaɓeta. Ta hasko AS, shima dai ta ce a'a. Oum. Nanma taji bata gamsu ba. Dama dai tana da layin Yaya Fawzan ne ma, shi kam ƙila ta iya tambaya. To ko RK ɗin zatace ya bata layin Fawzan ɗin?. Gamsuwa da wannan shawarar ya sata kai hannu zata ɗauka sabuwar wayarta sai idannunta suka sauka akan wayar RK daya bata.
(Mizai hana ki duba a wayar nan ko zaki samu no ɗin ma) Wani gefe na zuciyarta ya ambata mata. Ai da sauri ta ɗauka wayar kuwa ta hau binciken numbers ɗin Kai daki-daki abinda bata taɓa maida hankali tayi ba. Bawani yawane da su ba, dan kusan ma da alama duk contacts na family ɗinsa ne a ciki. Amma sam babu sunan AA babu alamarsa. Har zata ajiye cike da damuwa sai kuma ta sake scrolling ta koma tsakkiya inda taga My S1 da 2 har ma da 3. Sai kawai ranta ya bata My Son yake nufi, babban yaya 1, Fawzan 2, AA 3. Cike da tabbatarwa ta jinjina kanta. Amma gudun samun matsala sai tace bari ta ɗan gwada amma bazatayi magana ba tunda tasan dai RK zai gani ya kira shi ba ita ba.....


______★


“Kamila Kano kuma? Wace irin tafiya ce haka ta ujila kin san fa gobe juma'a, kuma na sanar muku Saturday zaku rakani Kaduna ko?”.
“Hakane Abahn su, nima tafiyar ta dole ce. Kuma ai a goben zanje na dawo in sha ALLAHU. Sai nabi jirgin safe na dawo da yamma. Dan ALLAH kayi haƙuri ka barni, ALLAH idan banje a goben ba da wahala na samu lokaci”.
“Humm to wai mizaki je yi ne?”.
“Nafa gaya maka Yaya Raliya ce bata jin daɗi, tunda aka gama hayaniyar bikin nan sai a hankali. Jiya su gambo sukaje, shiyyasa nace nima bari naje gobe ai kaga dai baza'ace ba'aga mutum ba. Da harda Oum ɗin yara ma zamu je, to bana son takura mata tunda jikin bawani yayi tsanani bane ba”.
Ɗan iska kaɗan Abah ya furzar daga bakinsa tare da lumshe idanunsa ya buɗe kamar yanda AA keyi idan zai yi magana. “Shike nan ALLAH ya kaimu. Aiko sai ki daure ki ƙarasa gidan Baba dan kwana biyu yayi mura shima. Ya hana na faɗa muku ne dan kar Fateema ta tada hankalinta”.
“ALLAH ya bashi lafiya. In sha ALLAHU can ma zan fara zuwa, har Baban Yola ma saina leƙa su dan kwana biyu bamu je ba. Da bikin nan naso zuwa sai kuma tafiyar nan tamu ta ratsa”.
Kai kawai Abah ya jinjina mata ya cigaba da aikinsa. Ita kuma ta miƙe cike da farin cikin samun nasara tace masa tana zuwa. Nan ma hannu ya ɗaga mata kawai.....


_________★


Bugun shigar kiran na bugawa ne da bugun zuciyar Maanal. Sai da wayar tana gab da tsinkewa sannan aka ɗaga. Sosai ta rumtse idannunta ta kasa cewa komai, daga can shima kuma baice komai ba har na tsawon sakanni. Sai zuwa can ƙasa-ƙasa ya furta.
“Ina massallaci, idan na fito zan kira”.
Daga haka ya yanke. Da masifar ƙarfi ta saki numfashinta data riƙe, tare da buɗe idanunta. Kai anya zata iya kuwa? Kodai ta barshi kawai. Kai ina bazata iya ba, maganar videos ɗin nan sune tashin hankalinta. Kada mutumin nan yaje ya aikata abinda zai zama sanadin bugawar zuciyarta. Ganin lokacin sallah zai ƙure ya sata haƙura da tunanin ta tashi ta hau cire kaya duk da ba sallar zatayi ba, tana dai son yin azkar ɗinta a irin lokacin kamar yanda ta saba. Jiki a sanyaye ta wuce bathroom yin wanka.
Har akai sallar isha'i bai kira ba. Ita kuma ta kasa fita dan gudun kada ta fita ya kira. Bata son zuwa da wayar falo kuma ya kirata a gaban Didi da Uncle Sadeeq. Koda Linda ta shigo ta sanar mata abinci ya zama ready catai ta kawo mata ɗaki yau ta gaji ne. Ta kuma ce tana gaida Didi. Da girmamawa Linda ta amsa mata ta fita, ita kuma ta hau shirin barci. A haka Linda ta sake dawowa ɗauke da abincinta. Kasa taɓa abincin tayi, ta zauna a bakin gado ta ɗauka novel ta hau karatun dole wai duk dan cinye lokaci. Sai dai sam ba wani fahimta take ba sam.
Sai ƙarfe tara da wani abu kiransa ya shigo. Zabura tayi daga kwancen da take tana duba wayar, ganin shine ke kiranta video call ma sai da zuciyarta ta girgiza. Ji take kamar taƙi ɗagawa, amma zuciyarta na ingizata. Haka ta tashi zaune ta warware ƙaramin veil ɗin data naɗa a kanta ta rufe jikinta sannan ta ɗaga dai-dai gab zata tsinke. Ai wani irin faɗuwa gabanta yayi lokacin daya bayyana mata a screen ɗin wayar tar. Jikinta har rawa yake ta kife wayar da sauri tana ambaton sunan ALLAH numfashinta na wani sam da ƙasa da sauri-sauri.....


Daga can shima AA ɗin kife wayar yayi da sauri yana ambaton sunan ALLAH, harga ALLAH shi duk zatonsa Rafeeq ne fa, ko video call ɗin yayisa ne dan tabbatar da Rafeeq ɗin yana a Kanon ne kamar yanda yace zai je. Dan gaba ɗaya ya manta ne da maganar kiranshi da yace zai yi ɗazun sai yanzu yana cikin wanka abin yazo masa a rai, shine yana fitowa batare da tunanin komai ba ya shiga masa video call daga shi sai guntun towel daya saka iya ƙugu zuwa gwiwa. Gashi ya ajiye wayar a saman mirror ne ta yanda ta hasko jikin nashi sosai. Ya jima tsaye hannayensa duk biyu dafe da mirror ɗin yana ambaton sunayen ALLAH kafin ya samu ya ɗan dai-daita. Wayar ya ɗauka, har yanzu tana online sai dai baya ganin komai sai duhu. Zama yay da ƙyau ya katse kiran, maƙoshinsa sai yawo yake cikin wuyansa da sauri-sauri. Gaba ɗaya yama rasa wane kalar tunani zai yi akan wayar Rafeeq a hannunta. Sai duk yaji zuciyarsa ma na masa zafi. Ɗayar number RK ya shiga kira, sai dai harta katse ba'a ɗaga ba. Cike da takaici ya sake ajiye wayar, sai da ya bada wasu sakanni zuciyarsa ta ɗan sauka sannan ya sake ɗaukar wayar yay mata normal call.........✍️












09032345899






*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖8️⃣8️⃣




______________


.........Harta yanke ba'a ɗaga ba. Haka ya sake kira. Kira fin biyar bata ɗaga masa ba. Ya cije lips, dan duk duniya Oum kawai yakema kira fiye da ɗaya sai ko Abah. Amma daga basu ba in har ya maka kira ɗaya baka ɗaga ba shike nan, sai in ka kirashi back, bai kuma zama lallai ya ɗaga maka ba sai yaso koda shike da buƙatar wani abu kuwa.
Samun kansa yay da sake kiran, yanzu ma har ya fidda rai sai kuma yaji an ɗaga. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke acan ƙasan maƙoshi, tare da kai hannu ya shafa kwantaccen gashin kumatunsa dake jiƙe da damshin ruwan wanka. Kamar ɗazun yanzu ma shiru tai masa, amma sai ya danne yay sallama. Amsa masa tai murya ƙasa-ƙasa, kai daga ji kasan a cikin kunya take.
“Am sorry nazata Rafeeq ne, shiyyasa na kira a wannan yanayin”.
“Uhm”.
Kawai ta faɗa a can ƙasan maƙoshi, alamar matsanancin nauyinsa take ji har ma bata son maganar. Shina ya fahimci hakan, dan haka ya saki batun kawai.
Cikin son kauda wancan yanayin ya katse shirun da sukayi da faɗin. “Kina son ganina ne?”.
Da sauri ta ce, “A'a, dama.......”
Sai kuma tai shiru. Numfashi ya ɗan sake fesarwa, kafin a ƙagare ya furta, “Daman mi?....”
Sosai tsigar jikinta ke tashi saboda yanda yake magana can ƙasan maƙoshi. Ga wani amo dake ratsa mata zuciya na fita daga cikin silent voice ɗin nashi. Daƙyar ta iya danne kanta, da ɗaɗɗaya ta ce, “D..a man akan Abideen ne”.
Lips ɗinsa ya ciza da ƙarfi, kamar wanda yake a gabanta idanunsa suka ɗan kaɗa. Muryarsa na ɗan canjawa da ƙara kauri ya furta, “Miye damuwarki da shi ɗin wai?”.
“Yazo gidanmu ne”.
“Gidan ku?”.
“Eh har ya sanar min komai daya faru. Wlhy hankalina a tashe yake da maganar videos ɗin nan. Kada mutumin nan ya cutar dani kamar yanda ka faɗa, kuma wlhy ko saninsa banyi ba, bamma taɓa ganinsa ba.”
“Amma yake iƙirarin an bashi aurenki?”. Yay maganar cike da zafi.
“Ni wlhy ban sanshi ba ƙarya yake min. Ni dan ALLAH ka bani number ɗinshi zanyi magana da shi”.
A taƙaice ya ce, “Banda”.
Shiru ta ɗanyi na wasu sakanni dan jin yanda yay maganar a Zafafa. A tunzure, kuma cike da shagwaɓa itama ta ce, “Toni ya kake so nayi?”.
Shiru ya mata, har sai da ta cire wayar a kunne ta kalla. Ganin yana online ya sata sake jin haushi. Cike da tsiwa ta ce, “Ni zaka wulaƙanta dan na nema taimakonka?”.
Nan ma shiru. Ai a fusace ta yanke kiran, tare da dangwarar da wayar. Shima a nasa ɓangaren wayar ya ajiye kawai ya miƙe. Zuciyarsa sai kumbura take a cikin ƙarji. A haka yay shirin barci ya haye gadonsa. Yana ƙoƙarin ɗaukar Alkur'ani dan yin karatu wayarsa ta motsa. Ɗauka yay da tunanin itace ta sake kira. Amma sai yaga number yarinyar nan ce dake damunsa, yayi blocking numbers ɗinta fin huɗu, amma yanzu saita koma kiransa da sabbin lauyuka. Kasancewar kusan irin wannan lokaci take kiransa a kullum yasa ya gane. Maida wayar yay ya ajiye batare daya ɗaga ba ya cigaba da buɗe Alkur'anin. Dan yanda yake jin zuciyarsa karatun kawai zai yi yaji sanyi......

_________


WASHE GARI.


Yau juma'a, koda Maanal taje office signing kawai tayi ta fito. Dama tama tsayar da mai taxi ɗin daya kawo ta. Tana ƙoƙarin shiga taxi ɗin motar AA ya shigo. Kallo ɗaya taima motar ta ɗauke kanta ta shige abinta. Sai dai tana ƙoƙarin rufe murfin taxi ɗin idannunta suka sauka akansa. Shima kallona yake cike da wani yanayi na tuhuma-tuhuma, mamaki, da kuma kewa. Fuska ta yamutsa tare da ɗauke idanunta a kansa tace ma mai taxi ɗin, “Muje”. Mai taxi da bai san mike faruwa ba yaja motarsa yay gaba...
Daga Mawaad Company wajen gyaran jiki aka sauketa. Dan Didi nacan tare da Barrah. Itama gyaran jikin aka shiga yi mata, dan Manaal ƴar gaye ce. Aka mata ƙunshi dai-dai misali baƙi da ja kaɗan da yay mata ƙyau kamar itace ma amaryar. Dan Didi sai tsokanarta take yi. Ita dai murmushi kawai take yi batare da tace komai ba. Basu baro wajen ba sai la'asar. A gajiye suka shigo gida. Nan ma kuma basu zauna ba suka ƙarasa shirinsu. Biyar da rabi a train station tai musu. Sun iso Kaduna ana magriba. Amal ce da su Munaya suka zo ɗaukarsu. Ai fa Munaya ta maƙalƙale Maanal dan ALLAH ya haɗa wannan ƙauna. Gashi kuma Munaya na kama da Maanal ɗin sosai.
Sun iso gidan cike da mutane, dan yau za'ai mothers event. Ɗazun akayi Sister & brothers event da ƙannen Yazeed suka shirya ma amarya. Kusan ma duk danginsu ne a wajen sai ƙawayen amarya. An kuwa rankwashe an ƙwalle dan ango kansa dole ya halarci wajen bisa tirsasawar Hajiya Yaya. Kasancewar su Maanal na wajen gyaran jiki basu maida hankali a gani ba. Koda yake ita bama tana bibiyar komai bane, Didi ce idan ta gano da Amaal ke bata labari.
Koda suka fito a mota da yawan mutane sukai musu caa da idanu. Wasu ma har suna ɗan ƙus-ƙus. Cikin ikon ALLAH kuma Maanal na fitowa akan Yazeed ta fara sauke idanunta. Ya fito daga sashen Daddy abokansa kusan shida da duk ta sansu zagaye da shi. Yayi masifar ƙyau cikin shadda ɗinkin tazarce, ga hula ya murza fuskarsa na fidda wani annurin gyaran fuskar da yasha. Sosai ya zama wani sakwakwa saboda ganin Maanal. Har takai suma abokan nasa duk suna zuboma inda sukaga yana kallo idanu. Suma dai kamar sun ɗan shiga shock da gannin Maanal ɗin, sai sukai duru-duru.
Ɗauke kai Maanal tai tare da jan hannun Munaya da Barrah tai wucewarta sashen Ammie. Haka kawai ta ɗan ji ɗaci a ranta. Sai faɗi take, (yace bai son aure amma gashi yana faman zuba kwalliya da washe baki kamar tsohon gwauro) a fili kam miskilar fuskarta ta shanye komai. Suna shiga ta saki su Barrah ta ɗane Ammie.
“La'ila yarinyar nan wai karyani zakiyi ne dan ALLAH”.
Ammie ta faɗa tana kai mata mintsini. Dariya Maanal ta sanya da sake mamaye Ammien sosai. Sai kuma ta mata kiss a gefen fuska tana faɗin, “I miss you sweetie na”.
Dariya ƴan falon suka sanya. Dan dangin Daddy ne da suka sauka anan sashen Ammie ɗin. Sai yanzu Maanal ta farga da mutane. Sai kuma taji kunya ta shiga ɓoye fuskarta a jikin Ammie. Nan ma dariya kowa ke mata har dasu Amaal da suka shigo. Sai kawai ta janye jikinta ta nufi bedroom ɗinta da gudu. Dan tasan duk rintsi Ammie tasan zasu zo bazata bari kowa ya shiga ɗakin ba tunda ma akwai na baƙi ai. Aiko babu kowa ɗin, an dai gyarshi tsaf yanata ƙamshi.....


Bayan sun huta Ammie ta sakasu shiryawa domin zuwa wajen event ɗin. Maanal taso ta turje. Amma Ammie taita lallashinta. Dan bata son Manaal ɗin ta zauna a gida a fassara zaman nata da wani abu daban. Haka badan taso ba ta shirya tsaf cikin wani swiss lass fitted gown datai masifar zauna mata a jiki. Ta zauna tai kwalliya dan a ɓangaren kwalliya ma Maanal artist ce sosai. Ta koya kuma ta iya saboda sonta da ado, dan ma yanzu kura tayi lafiya. Su Amaal ma har Ammie duk itace ta musu kwalliyar, tai ɗauri daya saka kitsonta fitowa ɗas kamar ka lashe.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login