Showing 213001 words to 216000 words out of 221978 words

Chapter 72 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

Hajiya Yaya da taki kishiyar😭). Zuwa yamma Alhamdullah aka samu jikin Maanal ya dai-daita musamman ta bangaren zuciyarta, ganin kuma Oum da Ammie ga Nene ga ƴan uwanta duk a tare da ita kowa na lallashinta ta sake ƙarfafa kanta. Daddy ma da Baba da kansu suka dinga lallashinta da bata haƙuri. Sai ma taji duk kunya ta kamata. To wai miye ma na damuwar, ai abinda kowa ke faɗan gaskiya ne, ai an mata fyaɗen. Tunda dai abune da bazai gogu a rayuwarta ba mizai sa ta dinga shiga damuwa dan an maimaita faɗar an mata da baki. Wanda ma ya aikata ɗin alfahari fa yake da hakan. Sai kawai taji wata irin tsanar AA ta sake tasirantuwa a zuciyata. Aiko bayan sallar isha'i ta zauna ta rubuta text massage ta turama RK akan in dai masu zuwa nema masa aurenta suka wuce gobe zata bama wani dama. Dan a yanzu auren kawai take iya kallar ma kanta a matsayin mafita..
Aiko hankalin RK ya tashi da ganin wannan saƙo nata, dan shi bai san mike faruwa ba duk yau bai duba ko ina na media ba sunje wani ƙauye da Abbu ya sai gona zai fara noma ne. can suka yini shi da Alhaji ƙarami da Abbu ɗin. Ƙoƙarin kiran Maanal ɗin yayi amma sam taƙi ɗaga masa, dole yay kiran Hajiya Majdiya tunda ta sanar masa tana kd ɗin gidansu Maanal biki. A bakinta yaji komai dake faruwa, ya kuma shiga media ya ga sauran. Hankali tashe a daren ya samu Abbu da zancen zuwansu nema masa aure Kaduna a gobe maimakon next week Friday da sukace. Babu yanda Abbu bai so ya fahimtar da shi dai ya bari Friday ɗin ba amma ya birkice, har abin ma ya bashi mamaki shi da Mah-mah. Dole suka amsa masa da cewar za'aje goben in sha ALLAHU.
A daren Abbu yay kiran Baba Sardauna suka tattauna sosai. Baba Sardauna mutum ne mai fahimta dan haka ya amince suje goben kamar yanda yarinyar ta bada dama kawai....


____________★


WASHE GARI ganin jikin Maanal da sauƙi Mamy da Oum sukai shirin komawa Abuja da safe. Hakama su Hajiya Majdiya. Dama gidan ya koma tsit duk an watse, sai amarya da ango dake can sashensu suna yin baƙi. Koda yake ango fa yana a sashen Ammie ya tare da shi ake jiyya. Sai Ammie ta korashi yake tafiya wajen amarya akan dole. Bayan wucewar su Oum Ammie tace suma su Shahidah su fara shiri su wuce. Dan ta fahimci cigaba da zaman Maanal a gidan zai haddasa wani sabon rikici ne. Tunda Yazeed yaƙi tsaida zuciyarsa waje ɗaya. To gara su wuce ɗin Maanal ɗin ta ƙarasa jiyyar a can. Haka dole badan sun so ba suka hau shirya kayansu akan zasu wuce da sassafe gobe tunda sun sami jirgi. Amaal kuwa a daren Ammien tace a ranar zata wuce gidanta....


Bayan sallar azhar babu zato baƙin Kano suka iso garin Kaduna. Sai dai shi Daddy yasan da zuwan nasu dan tunda safe RK yay kiranshi ya haɗashi da Abbu sukai magana. Sai Daddy yaji ya gagara yima Abbun musu, ya basu damar zuwan. Dama yasa a shirya abinci a sashen Ammie, duk da batasan na miye ba bata tambaya ba suka shiga kitchen ita da su Amaal. Manaal kuwa na ɗaki kwance dan jikinta babu ƙarfi, dan ma tana ƙoƙarin danne komai ne ta ƙarfin tsiya.
Tun kafin baƙin su iso su Amaal sunje sun shirya abinci kamar yanda Daddy ya bada umarni. Hakan yasa suka kara tunanin baƙin ta ɓangaren kasuwanci ne, dan in dai bakine da babu alaƙa haka Daddyn ke musu. Ashe a gidan Ammie ce ma kawai tasan da zuwan baƙin dan itace tai girki, sauran ko basu san da zuwan wasu baƙi ba musamman ma sashen Hajiya Yaya. Garama ita uwar ƴan tsirkun gidan Hajiya Basariyya taga alamomi. Amma itama ganin Daddyn nata dama-dama saita zata baƙinsa ne can na kasuwa maybe sukazo masa ALLAH ya sanya alkairi...
Tarba ta mutunci da mutunta juna aka samu a tsakanin Daddy da su Baba Sardauna. Da su Yaya Nuhu (Wato ƴaƴan Nene uku Da daddyn ya buƙaci suzo. Dan ita Nene tun a ɗazun da hantsi Daddyn yaje yay mata bayanin komai har gida. Ta kuma bada goyon baya ɗari bisa ɗari tare da tausar zuciyar Daddy akan ya bari Rafeeq ya auri Maanal dan haɗin Yazeed da Maanal bazai haifar da ɗa mai ido ba sam balle farin cikin da ake fata. Alhamdullah ya fahimceta shima dan jiya ya kwana ne yana auna abubuwa a ransa. Gefe kuma ga Ammie taje har ɗaki tana masa kuka da roƙo da magiya akan yabar batun Maanal da Yazeed ɗin dan ALLAH ya aura mata koma waye).
Bayan tattaunawa irin ta manya masu ilimin addini da sukaga duniya duniya ta gansu suka yanke rana har ma da sadaki a take. Dan yanda suka buƙaci ayi nan da sati uku zuwa wata guda sam Daddy baiyi musu ba. Duk da zuciyarsa cike take da rauni da tausayin Yazeed. Shi baima san ta yanda zai tunkari Yazeed ɗin da wannan batu ba. Gefe kuma shi kansa yana takaicin rashin wannan alkairi da yaso haɗawa tsakanin jininsa dana Ammie. Wata irin tsanar Hajiya Yaya da Sabuwa yaji ta ƙara faɗi a zuciyarsa. Dan wannan karon sun kaishi maƙurar da dole sai ya ɗauki mataki a kansu kam......


_________★


A Abuja kam su Oum sun tadda AA cikin matsanancin ɓacin rai da damuwa. Dan shima yaga wani kaso na abinda ke yawo a media ɗin tun jiya. Hankalinsa ya tashi matuƙa, tare da tausayin kansa da Maanal. Yata ƙoƙarin gwada kiranta amma sai ya kasa. Hakama ya gwada kiran Mamy domin ya roƙeta ta cire takunkumin datai masa amma ya kasa. Dan yayi alƙawarin koda soyayyar da yake ma Maanal zata kasance ajalinsa bazai taɓa bijire ma Mamyn ba balle akai ga tona mata asiri a wajen mutane masu daraja da suke mata kallon girmamawa da mutuntawa. Koba komai ita ɗin mahaifiya ce, tanada babbar daraja a garesa, darajar da zai iya sadaukar da koma miye akan ta. Saɓon UBANGIJI ne kawai Oum da Mamy da Abah zasu sakashi ya bijire musu, dan wannan kam har abada babu biyayya a tsakaninsa da su. Amma buƙata takai da kai ta rayuwa koda zai cutu zai sadaukar, dan haka ya amincewa kansa ne zai auri Maanal kawai da amincewar Mamy dan itace kawai matsalarsa a yanzu. Hankalin Oum ya tashi, dan ya kafe shi kada a kira masa kowanne likita lafiyarsa ƙalau. Lallashin duniya yaƙi sauraren kowa, daga ƙarshe ma yace shi zai yi tafiya ne zuwa gobe.
Ita kanta Mamy yanayin AA ɗin ya bata tsoro, amma ta zaɓi dakewa akan janyewa. Dan a ganinta ai dama sai anji wuya ake jin daɗi, dolene tabi kowacce hanya domin dawo da yaranta hannunta. Abah kuwa ransa a ɓace yake da AA, taurin kan yaron da kafiyarsa na zafafar ruhinsa. Dan haka ya tattara al'amarin AA ɗin ya watsar gefe, dan har gobe yana akan bakansa na har fa sai AA ya buɗi baki da kansa ya roƙa a nema nasa auren Maanal bayan ita kanta yaje ya bata haƙuri da neman gafarata, ya kuma sanar masu dalilinsa na bijirewa a baya..........✍️




Oh-oh tarnaƙi kenan🏃🏃🏃










09032345899








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖9️⃣3️⃣




______________




.........Washe gari kamar yanda AA ya faɗa ya bar gidan batare da sanin kowa ba. Yayinda Abah ya samu kira daga baba Sardauna akan batun nemawa Rafeeq aure da sukai jiya a Kaduna. Tare da batun hukuncin da suka yanke akan AA da Najeeb suma. Dan haka a weekend ɗin da za'a shiga za'ai taron family na gaggawa. Duk da zuciyar Abah ta girgiza matuƙa haka ya danne ya amsa da to, yayi kuma ALLAH ya sanya albarka. Baba na yanke kiran ya wani zube a kujera yana ambaton sunan ALLAH. A kuma dai-dai nan Oum ta shigo ta samesa tana hawaye da waya a hannu da alama itama dai ta samu batun kai kuɗin Rafeeq ɗin gidan su Maanal kenan.
“Gadanga ka gani ko, kaga abinda naketa son ka fahimta game da al'amarin nan kaƙi ko. Ni Rafeeq zaima haka ya zagaye yaje yasa a nema masa auren Maanal? Auren Maanal fa, yarinyar da Ajwaad ke matuƙar so.....”
“So?!!”..
Abah ya katseta a fusace yana mata wani irin kallo. Cikin zafin rai ta cigaba da faɗin, “So kike magana Fateema? To wane irin so Ajwaad kema Maanal? Lokaci yayi da zaki daina son kanki da yawa saboda soyayyar ɗanki ta rufe miki idanu. Shin idan Rafeeq baisa an nema masa auren Maanal ba yaya kuke son yay muku? Ki gaya min shi Ajwaad ɗin bai san akwai alaƙa tsakanin Maanal da Rafeeq bane? Tun a farko miyyasa bai ɗauki matakin nuna masa yana sonta ba? Girman kai! Ko tsabar ya rainama mutane wayau ne? Ko kuwa ita Maanal ɗin bata san ciwon kanta bane? To wlhy bari kiji, kodai ku kama kanku ke da ɗanki, kokuma ku haɗu da fushina. Kuma wannan ya zama gargaɗi na ƙarshe da zaki sake zuwa min da wannan zancen. Kuma shima na bashi kwana uku kacal ya sanar da wadda yake so dan cikin weekend za'ai family meeting, idan ba hakaba duk Wadda aka zaɓa masa wlhy, wlhy dole ya aura. Na gaji da case ɗin Ajwaad a gidan nan tunda bai san ciwon kansa ba, shi kaɗai bazai cigaba da bani ciwon kan da ƴan uwansa dake manya basa bani ba. Ke kuma kina biye masa saboda sonsa ya rufe miki ido.”
Ya tashi fuuu ya fice daga falon ma gaba ɗaya. Wasu irin hawaye masu raɗaɗi da zafi ne suka shiga sakkoma Oum da gudu, ga jiri na neman zubar da ita a ƙasa. Babu shiri takai zaune. Hayaniya take jiyowa kamar a gidan, jiki na rawa ta miƙe ko ganin gabanta batayi ma da ƙyau ta fito tana faman haɗa hanya....
“Naga dai ya fito da jakka har ya saka a mota tun bayan dawowarku sallar asuba. Sai kuma ya sake cirewa ya ɗauka yazo ya fita da ƙafa. Amma wlhy ban yi tunanin akwai matsala ba duk da na fahimci ransa a ɓace yake dan ko gaisuwata ma bai amsa ba.”
Wannan furucin kawai Oum ta iya ji daga bakin maigadi sanda ta fito daga haka ta silale a wajen. Sai farkawa tayi ta ganta a gadon asibiti su Fawzan zagaye da ita. Ganin ta buɗe idanu duk sukai kanta, Babban Yaya da Fawzan na gefe da gefenta, a kallo ɗaya zakai musu ka fahimci sunyi kuka, dan idanun ƴan maza duk ya kaɗe. Hannayenta dake cikin nasu ta ƙara damƙewa, sai hawaye sharrr, muryarta na rawa ta ce, “Fadeel Ajwaad, da gaske Ajwaad yabar gida?”.
Kai kawai babban yaya ya duƙar, hawaye na ciko masa idanu dan bai san amsar da zai bata ba. Sai ta juya ga Fawzan, shiko bashi da ƙarfin zuciya irin tasu, sai hawaye sharrr, ƙoƙarin cire hannunsa yay daga cikin nata amma ta sake damƙesa. “Fawzan kuka kake kaima. Kodai na rasa Ajwaad ne, dan ALLAH ku gaya min.” sai kuma ta shiga yunƙurin tashi zaune. Da sauri suka maidata suka kwantar. Abah dake ta ƙoƙarin danne nashi tashin hankalin ya matso kusa da ita sosai ya zauna, cikin muryar lallashi ya ce, “Fateema ki kwantar da hankalinki dan ALLAH. Ajwaad fa ba ƙaramin yaron da kike goyawa bane har yanzu. Karki manta shekara ɗai-ɗai har talatin ne da shi da ɗoriya. Duk ma inda yaje zai dawo....”
Kuka Oum ta sake fashewa da shi tana faman girgiza kai. “Dan ALLAH kada kaimin haka Gadanga, ka dawo min da yarona. Kuma kun san Ajwaad nada lalura kada yaje wani waje ya shiga matsala. Wlhy bazan yafe muku ba bazan kuma yafema kaina ba....”
Kallo ɗaya yay mata ya kauda kansa gefe. Fin minti ɗaya sannan ya sake kallonta, “Nace ki kwantar da hankalinki, in sha ALLAHU a yau zai dawo gida, dan na saka a binciko min duk ma inda yake ko ƙasar nan bai isa bari ba a yanzu dan na saka an dakatar da komai nasa daga aiki, hatta account ɗinsa”.
Wani irin nannauyar ajiyar zuciya Oum ta sauke. Yayinda Mamy da takaici ya cika ta taɓe baki a kaikaice. Ita har mamakin ƙarfin halin Oum nan take a ranta, mtsoww wai su za'aima pretending. A zahiri kuwa itama matsawa tai kusa da gadon Oum ɗin ta fara lallashinta....


__________★


A Kaduna kuwa bayan wucewar baƙi Daddy ya kira Ammie a waya, dai-dai nan itama Nene ta iso. A tare suka nufi sashen Daddy, inda yake tare da ƴaƴan Nene uku. Sosai Ammie tayi mamakin taron, amma sai ta danne suka gaisa. Babu wani ɓoye-ɓoye ko jan zance babban ɗan Nene Yaya Nuhu ya mata bayanin komai. Duk da jin al'amarin kamar daga sama taji sanyi a ranta, har bata san sanda ta saki ajiyar zuciya ba. Sai dai ƙasan ranta wani kalar abu mai nauyi take ji. Godiya ta dingama Daddy saboda fahimtarta da yayi ya janye batun Yazeed cikin sauƙi haka. Gefe kuma tanama Maanal addu'a da fatan ALLAH yasa Rafeeq ya zama sanadin kwaranyewar damuwarta. Yasa kuma iyakar wahalarta kenan. Sun tattauna sosai game da tsaida bikin sati uku kawai da akayi, dan hatta da sadaki sun ajiye abinsu. Dan haka dai babu zama shiri kawai ya kamata a fara...
A waya Daddy ya kira Maanal da Shahidah da Amaal suma. Shi da yaran Nene sukai musu bayani. Da ƙarfi Maanal ta rumtse idanunta, cikin jarumta ta shiga kokawa da zuciyarta, yayinda take ambaton sunayen ALLAH har ta samu nutsuwar da take buƙata. Ta kuma tunatar da kanta hakan shine dai-dai, shine kuma zai bata masalaha da kwanciyar hankali a wannan gaɓar. Batace komai ba dai a gabansu, hakan kuma na nufin nuna alkunya da kowa yay zato. Sai dai hankalin Shahidah da Amaal harma da Ammie na kanta. Koda suka dawo sashen duk motsinta na a idonsu, amma a mamakinsu bata nuna wani reaction ba sam. Saima a mamakinsu yanda ta ɗan warware daga kwanciya ciwon kwana biyun nan da take ciki tayi. Sai duk suka cigaba da mata addu'a a zukatansu, duk da ƙasan ransu na jin tausayinta saboda sanin har yanzu tana son Ajwaad. To amma tunda shi bai nuna yanayi ba har yanzu basu da wani dalilin damuwa da son ganin sai ta aureshi ai...
Washe gari suka shirya suka koma Abuja, suka bar Nene da Ammie da fara tsara shirin biki. Koda suka iso Abuja ma duk motsin Maanal a idon Shahidah ne, sai dai har suka kwanta bataga wani damuwa a tattare da ita ba. Washe gari kuma safiyar litinin, sukai shirin office yara makaranta suka wuce. Shahidahn da kanta ta ajiye Maanal a kamfani, ita kuma ta wuce nata aikin. Yau kam a kallo ɗaya su Zaharadeen suka fahimci Maanal ɗin a Manaal ɗinta take. Dan tun daga gaisuwa ko Yaqub bata sake kulawa ba ta shiga ayyukanta. Lokacin tashi kuma nayi tana a ƴan farko na barin kamfanin. Washe gari ma haka tai musu, bata shiga sabgar kowa da komai, aikinta kawai ke kawota. Ko'a zaman meeting da sukai sau biyu dan kamfani na shirin fitar da agogon data zana ga ƴan kasuwa a dakenta take. Sai kuma a meeting ɗin taji cewar CEO yayi tafiya, dan AS ne yay dukkan zaman a madadinsa. Batabi takan zancen ba balle ta nuna ya dame ta...


________★


AA dai bai koma gida ba. Suna kuma da tabbacin yana a ƙasar dan an hanashi fita. Amma an kasa gane inda yake. ALLAH sarki Oum duk ta fita a hayyacinta. Ita kanta Mamyn abin fa ya fara damunta. Sai dai tana ƙoƙarin ganin ta danne dan a ganinta AA nayin duk wannan abunne dan ta amince ya auri Maanal. Itako tana akan bakanta ko Oum zata mutu Ajwaad bazai auri yarinyar nan ba sai zaɓinta. Ga batun meeting na family kwanakin na sake matsowa. Nibras ma ta matuƙar tada hankalinta, duk ta rame bata da aiki sai kuka. Yayinda Babban Yaya da Fawzan suka kasa zaune suka kasa tsaye sunata kai kawon binciko inda AA ɗin ya ɓoye kansa batare da sanin Abah ba. Matsalar da aka samu ya rufe duk wayoyinsa ma ta yanda baza'a sameshi ba. Sai a safiyar alhamis babu zato kawai sai gashi ya dawo da kansa. Baki hanci idanu duk maigadi ya saki yana kallonsa, shiko cike da basarwa ya ja box ɗinsa yay ciki, dan taxi ce dama ta ajiyesa. Kai tsaye kuma sashen Oum ya nufa, su kansu masu aikin sashen Oum ɗin daya shigo duk sai da suka shiga shock. Suma bai kulasu ba balle amsa gaisuwarsu, sai tambaya daya jeho musu akan ina Oum. Baki na rawa suka bashi amsa da tana sama dama duk mutanen gidan bata da lafiya.
Saman ya haura zuciyarsa na wani kalar bugawa, ko kallon Saheeba da Nibras dake a falo suna shirya abinci a dining baiyi ba nan ma, kai tsaye bedroom ɗin Oum ya nufa, shigar sautin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login