Showing 93001 words to 96000 words out of 221978 words

Chapter 32 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

Online Boothcamp.
https://wa.link/8al2f0
Gaskiya wanda ya koya a wurin ƙwararriya ya huta domin ko dubu 100,000 akace in biya in shiga OPERATION CINIKI DOLE ONLINE zan biya domin amfanin da na samu cikin Boothcamp bazan iya faɗaba, gashi yanzu na samu na sayi machine din delivery na maida daki guda shago cikin gida na.
Hurayyah ta taimaka da ta haɗa ni da Coach Saddiqah. OPERATION CINIKI DOLE ONLINE ya bani damar yin ciniki yadda ya kamata ba tare da wana damuwa ba.


Indai kina business ko kina son ki fara Operation Ciniki Dole Online Boothcamp shine ajin farko da Coach Saddiqah zata rike hannun ki ta nuna miki duk wani sirri da dabaru na kasuwancin online.


Daga rashin ciniki zaki koma sold out domin kuwa zaki dinga yin 6 figures monthly, in kin shiga OPERATION CINIKI DOLE ONLINE BOOTHCAMP baki ga sauyi mai kyau a business dinki ba za'a maida miki kudinki bayan 90days.
Da Naira Dubu Goma kacal Pre-lunching Price zaki samu damar shiga OCD.( Kina biya zaki fara kwasar ilimi)
Zakuma ki iya jira sai 20th January ki biya Naira Dubu Ashirin.


______________




.......Sanye take da doguwar riga ta atamfa da ɗinkin yay ƙyau sosai, tayi ɗaurin zara Buhari da yay matuƙar zauna mata kamar ta ɗauka ta ɗora a kanne ba hannu ya naɗa ba. Kasancewar kalar atamfar blue ne da fari ta ɗaura farin gyale ba wani ƙato ba sosai tun daga saman kanta sai ta baɗesa a kafaɗunta duka amma ya rufe mata ƙirji duka. Ta baya kuma rigar bata matseta ba shiyyasa sam babu ta inda jikinta ke nuna da wani zai ce ta fidda tsiraici. Kamar ko yaushe tana maƙale da sirrin farin gilashinta da ke ƙawata fuskarta da kwarjini na musamman. Yayinda sam fuskar babu alamar wasa da wani zai kawo mata wargi dan tsuke take tamau, ba wata kwalliya tayi ba a fuskar mai yawa, amma tayi ƙyau sosai. Ƙamshinta mai sanyi da saka zuciya nutsuwa. Yanda take takunta a nutse sai ka ɗauka yanga ce da tsatsar iyayi. Amma halitartace hakan sam bata da garaje ko gaggawa. Duk wanda ta haɗu da shi mace ko namiji takan gaisheshi batare da ko kallonka tayi ba ta wuce abinta. Idan kuma kai ne ka fara ambata sunanta ga ƴan wanda suka santa takan kallekan ta ɗan ɗaga maka hannu.
Isowarta ga ƙofar shiga dai-dai da tunkarowar AA shima assistant ɗinsa biye da shi da tarkacensa a hannunsa. Yayinda shi kuma waya manne a kunnensa yana magana cikin nutsuwar nan tasa kamar baya son magana.. dan ko assistant ɗin nasa bazaice ga abinda yake faɗa ba kai tsaye a wayar. Amma da yake da aka kira wayar tana a hannunsa shine ya ta miƙa masa yaga ansaka My D, Wato mahaifinsa. Yanda yake taku dake sake tabbatarwa shi ɗin tsayayyen namiji ne ingarman gaske. Mai lafiya da ji da ƙarfin ƙuruciya dana motsa jiki ya isa abin kallo ga masu kallon nasa. Balle azo ɓangaren iya ado da tsara shi. AA yasan sirrin gayu da ƙamshi, dan yana cikin manyan Handsome da duniya bazata taɓa takokin manna hotonsa ako ina ba ta faɗa da tabbatarwa. Yanda kowanne ma'aikaci sai ya ɗaura I'd card ɗinsa na aiki ƙofa ke bashi damar shigewa haka shima oga da kansa. Dan haka koda suka iso sai assistant nashi ya ɗora nasa id ɗin shi, dai-dai da itama Maanal data tsaya ciro nata a bag ɗinta ta ɗaura. Hannunta ɗaya riƙe da lunch box ɗinta, ɗayan kuma bag ɗin na'a kafaɗarta maƙale, dan mai irin kamar school bag ɗin nan ce amma ta gayu kuma ƙarama. Ɗan zubama lunch box ɗin idanunsa yayi sai kuma ya janye tare da shigewa yana magana a hankali da sai da ya ɗan gittata taji muryarsa acan ƙasan maƙoshi yana faɗin, “Yes Aba I hear you”.
Da kallo ta ɗan bisa sai kuma ta taɓe baki kaɗan tana yamutsa fuskar da ƙarasawa reception ta saka hannu kamar yanda dokar companyn take. Anan ne suka haɗu da Yaqub. Murmushi ya sakar mata da faɗin, “Good morning sister Maanal”. Kallonsa ta ɗan yi sai itama ta saki masa ɗan murmushi mai tsayawa iya motsin fuskar nan. Nutsuwar Yaqub ɗin da rashin hayaniya yasa take ganin mutuncinsa. Cikin ƴar siririyar muryarta ta ce, “Good morning ɗan uwa. Ya weekend?”.
“Alhamdullahi mun shata kam mun more”.
Malalacin Murmushin ta ɗan sake yi kawai. Batare da ta sake cemasa komai ba ta wuce. Binta yay suka jera. Duk da bawata magana suke ba sai da aka dinga binsu da kallo. Koda suka iso nasu ma office ɗin su Zaharadeen duk zuba musu ido sukai. Kallo ɗaya tai musu ta kauda kanta da faɗin, “Good morning”. A jimlace. Wasu sun amsa wasu kuma na binta da kallon dai. Ita kuma ta sake yin kicin-kicin da fuska ta gyara kujerarta bayan ta kakkaɓe ta zauna. Sai kuma ta warware tissue da ta ajiye a wajen ta fara goge abubuwanta duk da komai a tsaftace yake ƙal. Amma ita ƙa'idarta ne in har zata fara aiki saita sake goge komai nata har keyboard kafin ta fara. Batafi zaman mintuna arba'in ba ta samu kira daga office ɗin Design Director. Miƙewa tai kawai sai wayarta a hannu ta wuce. Su Zaharadeen suka bita da kallo cike da gulma. Sai dai ita bama tasan sunayi ba.
Cikin girmamawa da mutuntawa ta gaishe da Director Mustapha. Ya amsa mata da kulawa da binta da wani munafukin kallo. Kujera ya nuna mata alamar ta zauna. Bata musa ba ta zauna ɗin.
“Yauwa Sister Maanal zamuje can Workshop dan kin san aiki yayi nisa. Akwai abinda ake buƙatarki a wajen domin tattaunawa, tun jiya ma Watchmakers da horologists ɗin sukaso ganin ki sai CEO yace sai yau”.
Kai kawai Maanal ta jinjina masa a girmamame. Shima sai bai sake cewa komai ba ya miƙe yana sake jinjina girman kai da miskilancin yarinyar a ransa. Dan da yawansu a Company haka sukema yanayin maanal ɗin fassara yaransu da manyansu. A tare da shi suka isa Workshop ɗin. Wajene da yaji kayan aiki harda na tashin hankali. Dan ingantattun matchings ne da ko'a masu jajayen kunnuwan sai companyn da yaci ya ƙoshi ke dasu. Ga komai a tsare kuma a tsaftace. Cikin girmamawa suka gaisa da kowa. Tanata kallon abubuwa wani a cikin horologists ɗin na mata bayani oga kwata-kwata ya iso. Kamar dai ko yaushe AS ɗinsa biye da shi. Gaisheshi suka shiga yi cikin girmamawa. Ya amsa musu da kulawa shima. Sai lokacin Maanal da bata ko kalla sashen da yake ba ta furta, “Good morning Sir”.
A taƙaice kuma ciki-ciki ya amsa da, “Morning”. Yana maida hankalinsa ga Director Mustapha. Gaba yay suka bisa a baya har zuwa inda ake buƙatar ganninsu. Batare da Maanal ta farga ba sai ta tsinceta a kusa da shi tsaye gefensa na dama. Matsawa taso yi sai dai babu dama dan gabanta glass ne. Dole ta haƙura mayataccen ƙamshinsa na addabar hancinta. Lokacin da aka ajiye samfarin agogon data zana da hannunta sai taji notukan kanta na ƙoƙarin kwancewa. Yau mafarkinta ya zama gaskiya. ALLAH mai girma. Da ƙyar ta iya haɗiye hawayen da suka cika mata ido ta saita kanta tana al'ajabin komai da yaba ƙoƙarin Watchmakers ɗin harma da horologists ɗin, duk da kafin yau ta taɓa ganin aikinta a zahirance. Kai da ganin agogon kasan bana siye da ƙananun kuɗi bane. Bayan wanda aka haɗa ɗin sai pieces da suma aka ajiye nan fa suka shiga tattaunawa. Ɗan abinda Maanal ɗin ta ƙara musu bayani kadan ne ma, sai dai ta sake ƙayatar da su da fahimtar lallai za'aje da yarinyar a cikin Companyn dan tanada brain sosai.........


__________★


Anan kaduna kam ALLAH ne yayma matafiya dawowa. Wato Hajiya Yaya da maƙarabbanta. Su dai su Ammie basu san da dawowar tasu ba ma. Sai da suka dawo ɗin tana zaune a falo Sakina na mata kitso Waleed ya shigo yake gaya mata. Duk da taji mamaki sai batace komai ba tace yaran suje su gaisheta.
Shiru Waleed yayi alamar bai son zuwa. Sai tayi murmushi tana miƙewa. Kitchen ta nufa ta haɗo abinci a cikin basket ta bashi tace suje dashi su kai. Nan ɗin ma amsa sukai jikinsu duk a sanyaye suka fita. Basu wani jimaba ko sai gasu sun dawo Hameed harda hawaye fuskarsa zane da sayin mari. Sam Ammie bata tambayesu miya faru ba, koda Waleed ma zai faɗa sai ta girgiza masa kai da nuna masa hanyar kitchen alamar yaje ya kai mata kayan abincin da suka dawo dasu ba'a taɓa komai ba.
“Amma aunty ai ya kamata kiji miyya faru? Jibafa fuskar Hameed harda sahun mari”.
Murmushi Ammien ta saki kamar bazatace komai ba, sai zuwa can tace, “Sakina kenan, to minene amfanin jin? Sakawa kai ɓacin rai ne fa kawai. Koma minene ya faru ai ya rigada ya faru ɗin, sai a barsa ya wuce kawai”.
“Hummm Aunty wlhy yanayin rayuwarki na birgeni, a ɗan zaman nan na kwanaki a gidan nan na ƙara samun ilimin zaman duniya. Zuwa yanzu na ɗaura ɗammarar ko sakina Salihu yayi na sake wani auren nima zan sake wasu abubuwa daga tawa rayuwar”.
“ALLAH sarki ƙanwata ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi to”.
“Amin ya rabbi aunty”.


★★


A sashen Hajiya Yaya kuwa tunda suka kora su Hameed da abincin da suka kawo bayan Basira ta falle fuskar Waleed da mari sakamakon maida mata magana da yayi sai suka bude sabon shafin zagin Ammie da ƴaƴanta musamman ma Maanal da tafi kowa tsaya musu a rai. Sunyi mai isarsu kafin su saki zancen su koma kan Hajiya Basariyya da taje wai gaishesu da musu sannu da zuwa.
A gabanta dai an amsa, dan a cewar Hajiya Yayan idan ma da gara gara Hajiya Basariyya ɗin duk da kuwa itama a baya ansha gwagwarmaya, amma zuwan Ammie yasa take ɗan jin sassaucin Hajiya Basariyya a yanzu. Ita kanta Hajiya Basariyya ɗin tana fitowa daga sashen ta wani taɓe baki da jan tsaki. Tana isa sashenta suka baje kolin yi da su Hajiya Yayan ita da ƴaƴanta itama.
Wannan rayuwar daga Hajiya Yaya har Hajiya Basariyya sun ɗabi'antar da yaransu a kanta tun suna ƙanana. Shiyyasa yaran sam basa ganin girman matan uban nasu idan ka cire Yazeed da Amrah da halinsu ya fita daban a cikin ƴaƴan Hajiya Yaya. Ita kam Hajiya Basariyya ma ai bata da zakkar na kirki har yanzu, ko sai nan gaba yaran sun ƙarasa kaiwa hankalin girma oho. Dan manyan su Huznah ne kawai masu shekaru....


____________


Zaman cikin Workshop ɗin ya jasu lokaci mai ɗan tazara, dan sai da akai kiran azhar suka sami fitowa. Kasancewar itace ta fara fitowa kanta tsaye ga elevator ta nufa. Sai dai tana zuwa zata danna domin buɗewa ta figowa ta buɗe kanta alamar wani zai fito. Haka kawai ta samu kanta da maida hankali ga wajen. Sai ko idanunta akan Huznah data fito cikin matuƙar kwalliya data sakata yin ƙyau ainun. Hannunta ɗauke da basket alamar kayan abinci ne a ciki. Kallon kallo suka tsaya yima juna. Dan itama Huznah na fitowa idanunta akan Maanal ɗin suka sauka. Sunyi ma juna kallon fin minti ɗaya kafin Maanal ɗin ta fara janyewa cike da miskilancinta. Batare da tace da Huznah ɗin komai ba kuma tai shigewarta elevator ɗin tabar Huznah ɗin sake da baki tana kallonta. Gefe kuma masu shigi da fici ne da suka fassara al'amarin da wani abu daban can. Domin tuni sun gumtsa gulma.
Har Maanal ta koma ga wajen zamanta mamakin Huznah na mata kaikawo, shin wajen wa take zuwa ne ai a companyn nan? Wannan shine gani na biyu datai mata. Sai dai a wancan ganin ma bata san wajen wa tazo ba tunda tana shigowa ne ita kuma tana fita. Kasancewar lokacin salla ne abubuwan hannunta kawai ta ajiye inda ya kamata ta fita dan mafi yawa duk an fice salla. Sai wanda ba musulmai ba da kuma masu fashin salla kawai. Sai masu wasa da ita kuma dakan fifita aikinsu sama da tashi yin sallar akan lokaci. Duk da dokar mai kamfanin ce idan lokacin salla yayi dole ka ajiye kaje kayo in har kana cikin masu yinta kafin ka cigaba da aikinka. Amma hakan baya hana wasu tauye lokacin...


★★


Cike da takun yanga da yauƙi Huznah ta nufi office ɗin AA. Sai dai tana isowa office ɗin Assistant nashi da ke farko kafin nasa acan ƙurya sukaci karo shi ya fito. Fuskarsa sai raɓar ruwa take yana ƙoƙarin gyara hannun long sleeve shirt ɗinsa, ya cire ta cikin sai ƴar ta saman shirt ɗin kawai data kasance milk itama. Shi baima lura da ita ba sam kasancewar hankalinsa yayi wajen sallar sai da tace da shi, “Hy my boss”. Sannan. Duk da a hakan ma da farko baiko kalla inda take ba yay shirin wucewa dan bai kawo da shi ɗin ake ba. Sannan bai riƙe muryarta ba balle yasan ita ɗin ce tunda ya tabbatar ma'aikatansa babu wanda keda ido da kwallin masa wannan kiran tsagerancin. Yanda ya kama girmansa haka suke tsantsar girmamashi ako ina daga samansu har ƙasa.
Ɗan saurin shan gabansa da tayi ne ya sakashi kallonta a karo na farko, murmushi ta sakar masa da ɗaga masa yatsunta biyu cike da iyayi ta ce, “Please boss da kai fa n.....”✍️






✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖4️⃣2️⃣




______________




*TALK WITH SIDDEEQAH*
Operation Ciniki Dole
08149588205
Ni Olayyah na shiga uku na kwashe kudi na saro kaya domin in fara kasuwanci online, na gaji da zaman sai Yallaɓai ya bani kudin kashewa, kullum ni ce koma baya cikin danginsu, dukda yana kokarin sa, amma dai gwara in nemi na kaina kodan yan uwa da iyaye.


Amma bari in kira Besty nah Huriyyah nasan zata samu maganin wannan damuwar tawa.
Tunda na kira Huriyya na faɗa mata abunda ke hanani Bacci ta faɗa mun wani sirri da ya girgizani.


Wato ashe itama da ta fara business online kuma bata ciniki amms tunda aka bata number din Coach Saddiqah komai ya fara tafiya daidai a kasuwancin ta ( Talk with Saddeeqah).


Tunda ta shiga OPERATION CINIKI DOLE ONLINE BOOTHCAMP komai ya warware mata ciniki babu kama hannun yaro. https://wa.link/8al2f0
Ai ba shiri na nemi Coach Saddiqatu nima domin in shiga tsarinta na Saddeeqah Biz Growth Academy.
Kuma Alhamdullilah ina shiga nafara ganin canji a business dina, har ma sabon online business na buɗe daga cikin abunda na koya a Operation Ciniki Dole Online Boothcamp.
https://wa.link/8al2f0
Gaskiya wanda ya koya a wurin ƙwararriya ya huta domin ko dubu 100,000 akace in biya in shiga OPERATION CINIKI DOLE ONLINE zan biya domin amfanin da na samu cikin Boothcamp bazan iya faɗaba, gashi yanzu na samu na sayi machine din delivery na maida daki guda shago cikin gida na.
Hurayyah ta taimaka da ta haɗa ni da Coach Saddiqah. OPERATION CINIKI DOLE ONLINE ya bani damar yin ciniki yadda ya kamata ba tare da wana damuwa ba.


Indai kina business ko kina son ki fara Operation Ciniki Dole Online Boothcamp shine ajin farko da Coach Saddiqah zata rike hannun ki ta nuna miki duk wani sirri da dabaru na kasuwancin online.


Daga rashin ciniki zaki koma sold out domin kuwa zaki dinga yin 6 figures monthly, in kin shiga OPERATION CINIKI DOLE ONLINE BOOTHCAMP baki ga sauyi mai kyau a business dinki ba za'a maida miki kudinki bayan 90days.
Da Naira Dubu Goma kacal Pre-lunching Price zaki samu damar shiga OCD.( Kina biya zaki fara kwasar ilimi)
Zakuma ki iya jira sai 20th January ki biya Naira Dubu Ashirin.


____________




........Yanda ya wani kalar zuba mata mayatattun idanunsa masu kaifi da cikar kamala yasa zuciyarta girgizawa. A take harshenta ya fara rawa, sauran abin faɗar tata ya kama gabansa. Sai ta koma in ina da rawar lips. Komai baice mata ba ya raɓata ya wuce abinsa. Da ƙyar AS ɗinsa dake kallon komai ya iya danne dariyarsa. Dan shi kam dariya ma Huznah ke bashi. Da tasan manyan matan da suka sha gwagwarmaya da faɗi tashi akan boss ɗin nan nasa da bata wahal da kanta ba. Amma dai zai cigaba da bin series ɗin domin ganin inda zai kasance the end. Shine ya bata wajen zama sannan ya wuce massalaci shima a gurguje dan har an tada salla. Maimakon itama tayi hankalin cewa zataje tai sallar saita gyara zama a lallausar kujerar dake a office ɗin AS ɗin. Ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya suna charting da sabuwar ƙawarta Nurry dake bata shawarwarin yanda zatai da AA ɗin yau, dan tun jiya ta juye mata komai sai dai bata sanar mata wanene shi ba. Gefe kuma tana yi da Yaseerah itama dake ƙara ƙarfafata...


★ Kamar yanda ta saba ana idar da salla ƙoƙarin komawa kan aikinta tayi, ba kamar sauran daketa tururuwar wucewa cin abinci ba. Cikin ɗan sauri Yaqub ya cimmata, jin mutum a kusa da ita ya sata kallon gefen nata. Sai ta ɗan sauke ajiyar zuciya ganin Yaqub ne. Gaishe shi tayi kamar yanda al'adarta take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login