Showing 171001 words to 174000 words out of 221978 words

Chapter 58 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

Ga jinin proud ɗin ma da take saka ran zai zo yaƙi zuwa. Sai ta sake yarda a ranta cikinne da ita kenan.
Sun iso kano da daddare, haka suka buɗe gidan suka shiga. Ɗan kayan abincin da suka samu suka sarrafa, sannan suka shiga gyaran gidan dan an barsa ne kaca-caka lokacin da zasu tafi. Harda abinci dafaffe da duk ya ruɓe. Washe gari mutane suka dinga shigowa wai amsar kayansu da aka ara domin yin hidimar biki ba'a maida musu ba. Wasu ma harda yanka musu kuɗin kwanakin da sukayi. A bakin maƙwafciyarsu suke jin wai su Oum sun bar ƙasar ma gaba ɗaya. Wannan batu ya zafafa musu zukata, sunji tsanar su fiye da farkon rikicin. Kwanansu biyar mutane sunzo wai ai an sayar musu da wannan gida. Dan haka sun basu kwana biyu su fita. Hankalin Ammie ya sake tashi dan tasan dai wannan gida nasu ne, koma tace bata ne. Kawai washe gari sai ga kira daga Babu da Gwaggo, wai in basu tashi a gidan nan ba suka bari suka zo Kano sai sun saka an wulaƙanta rayuwarsu. Tsoro mai tsanani ya shiga zuciyar Ammie. Dan tasan gwaggo zata iya komai. Haka ta tattarasu tana jan jiki da ƙyar suka ɗauki abunuwansu masu amfani suka saida sauran suka haɗa ƴan kuɗin tace suje Minna. Gara ta koma tushen mahaifiyarta maybe ta samu ko wasu a dangin su ne na nesa.
Wannan shine mafarin barowarsu Kano, inda sukaje Minna can ma dai babu madafa. Dan sun gama zagaye-zagayen su sai da ƙyar suka samu wanda ya sanar musu ai ƙanwar mahaifiyarta Shamsiyya tana a Kaduna yanzu haka da iyalanta. Haka nan ma su tattaro suka sake juyowa garin Kaduna. Ga jikin Maanal na neman birkicewa. Dan da tayi tari sai jini. Gashi tana abu kamar wadda ƙwalwar kanta ta samu taɓuwa. Direban daya ɗakkosu a dikko jaction ya ajiyesu, suka nema motar Kaduna. Sai dai kuma kuɗinsu kona mutum ɗaya bai kai ba. Sunyi roƙon sunyi magiya amma babu wanda ko ya kallesu balle ya nuna musu tausayawa. Dan haka Ammie ta yanke shawarar yin bara maybe su samu su haɗa kuɗin motar ko zuwa safiya ne. Anan ƙarƙashin gadar dikko suka nema wajen zama ita da yaran, ga Maanal kwance bata gane komai da kowa. Hasalima numfashinta da ƙyar yake fita. Jefi-jefi masu mota na jefa musu sadakar, haka Shahidah da Amaal zasubi da gudu su tsunto idan iska ta ɗauka. Wani lokaci ma rikici ya ɓarke tsakaninsu da almajiran dake a wajen. Dare yaja sosai, dan kusan ƙarfe biyu ake magana. Jikin Maanal yayi tsanani, numfashinta yana wani irin fisga alamar rayuwarta na gab da salwanta. Su duka ukun rungume suke da ita suna kuka. Sosai kuma sautin kukan nasu ke fita saboda ƙarancin hayaniyar titin a yanzu. Babu yawan motoci, babu yawan mutane. Tsirarun mutane dake a wajen suka ɗan zagayesu suna kallo babu mai niyyar taimaka musu. A dai-dai nan wata baƙar mota wulik ta faka, dan har ya wuce su kaɗan ya dawo da baya-baya ya faka motar. Su biyu ne, a kallo ɗaya zaka fahimci ɗaya yaron ɗayan ne. Mai alamar mammalakin motar ƙyaƙyƙyawan matashin saurayi mai ginannen jiki da cikar kamala. Shine ya fara magana da tunanin ko haɗari akayi, dan haka mutanen dake zagaye da su suka dare aka bashi hanya. Mamaki ne ya kamashi ganin mace da yara ƴammata ƙyawawa duk da wahala ta ɓoye kaso tamanin na ƙyawun nasu, ga wadda ke rungume a jikinsu tana aman jini. Tashi hankalinsa yayi, bai saurari komai ba ya duƙa ya ɗauka ƴar budurwar yarinyar da bazata wuce shekaru goma sha biyar da wasu watanni ba. Sannan a cikin rikicewa yace suma su shiga mota a kaita asibiti. Ko musu su Ammie basu yi da shi ba. Dan komai basa ganewa a yanzu. Fatansu kawai shine Maanal ta rayu. Haka suka wawuro jakarsu ɗaya data rage mai ɗauke da muhimman takardunsu na karatu sai abinda ba'a rasa ba suka shiga motar. Wani irin gudu drivern saurayin yake zubawa na tashin hankali, abinka da dare sosai babu yawaitar mutane. Cikin abinda bai wuce awa ɗaya da mintuna arba'in ba suka iso Kaduna. Kai tsaye asibiti ya nufa da su. Babu ɓata lokaci kuma aka shiga baima Maanal taimakon gaggawa. Hakama Ammie da suna sauka a motar jiri ya kwasheta ta yanke jiki ta faɗi......


_________★


Kwanakin su uku a asibitin suna samun kulawa mai daraja. Alhamdullah jikin Ammie yay sauƙi sosai, hakama Maanal duk da ba'a barinsu ganinta saboda doctor ya tabbatar musu kaɗan ya rage zuciyar Maanal ɗin ta buga. Amma Alhamdullah sun samu nasarar dai-daita abubuwa. Sai dai duk da haka ta kamu da ciwon zuciya mai ƙarfin da sai dai a dinga tayata da addu'a.
Matashin saurayin nan daya faɗa musu sunansa Yazeed shine tsaye akan komai, hatta abinci sau uku a rana bai taɓa gajiyawa ba. Tuni ya sayo musu kayan sakawa da dukkan ƙananun abubuwan buƙata. Kuɗin asibitinsu da komai ya biya. Hatta na aikin da akace za'ama Maanal nan da wata ɗaya. Randa suka cika sati ɗaya yazo da mahaifinsa. Mutumin kirki shima nutsatstsen dattijo mai cikar kamala da ƙyawun haiba. Shima ya bama su Ammie kulawa, shine kuma ya bincikesu ko zasu bada number wani ɗan uwa a kira. Ammie batayi musu ba ta bada number Nenen ta da aka bata, kasancewar ta mata ɓoyo na musamman aka dace. Number dattijon ya amsa suka tafi, akan komi kenan zuwa gobe zasu ji.


Alhamdullah washe gari kuwa sai ga Nene da yaranta maza magidanta har biyu. Tana ganin Ammie ta gane jinintace. Itama Ammie na ganinta taga kamar mahaifiyarta ce tsaye a gabanta. Nan fa suka rungume juna aka hau koke-koke..
Wannan shine silar haɗuwar Nene da su Ammie. Bayan an sallamesu suka wuce gidanta. Yayinda Maanal data koma sanyi-sanyi bata magana, komai sai dai tabi mutane da ido ta cigaba da shan magani. Duk sati kuma anlkan kaita ganin likita. Ba kowa ke kaitan ba kuma sai Yazeed da baya nuna gajiyawa. Hakama mahaifinsa lokaci-lokaci yana zuwa duba jikin Maanal, dan Ammie dai Alhmdllh nata jikin da sauƙi. Dawowar su gidan Nene bai hana Yazeed da mahaifinsa cigaba da musu hidima ba, musamman ɗawainiyar asibitin Maanal dake fama da jiyya, duk da ba'a kwance take ba daka ganta kasan tana fama da jarabawar ciwo. A haka sukai kusan watanni tara, abubuwa suka fara dai-daita musu. Babban ɗan Nene yace yana son auren Ammie saboda halin matarsa ya ishesa. Amma mi sai rigima ta nema kaurewa. Ana cikin wannan halin ALLAH ya kawo dattijon arziƙi gidan. Wato Alhaji Usman Chalawa mahaifin Yazeed. Yazo domin duba su duk juma'a kamar yanda ya saba. Ganin rikicin dake faruwa babu wani ɓata lokaci ya ce shi yana son Ammie da aure. Dan ya fahimci lallai anzo wata gaɓa dasu Ammie zasu iya fara fuskantar ƙalubale a gidan. Shi kuma haka kawai tausayi bayin ALLAHn ke bashi, kodan shima ya ɗanɗani irin makamaciyar rayuwar a bayane oho. ALLAH sarki Ammie, dan kawai samuwar masalaha ta amincewa da Alhaji Usman Chalawa. Dan bata fatan raba ƙyaƙyƙyawar alaƙar dake tsakanin Nene da surukanta da ƴaƴanta. Sannan tana ma ƴaƴanta fatan ƙyaƙyƙyawar rayuwa. Ta kuma fahimci anan gidan Nene da wahala a dace da hakan dan a yanzu hakan ma Shahidah da Amaal suyar awara suke anan ƙofar gida dan rufawa kai a siri kasancewar suna kwaɗayin komawa karatunsu.
Alhaji Usman Chalawa dai da gasken yake. Dan sati guda kacal da yin wannan magana aka ɗaura aurensa da Ammie. Sati na sake zagayowa ta tare a gidansa. Tarewar data saka suka fahimci ashe ba ƙaramin mai kuɗi bane ba. Ga kuma matansa ƴan balaja'u musamman uwar gidan mahaifiyar Yazeed yaron kirki. Amma sai Ammie ta daure ta jure kodan yaranta su sami ƙyaƙyƙyawar rayuwa. Sun kuwa samu, dan su duka Alhaji Usman ya maida su makaranta. Har Maanal data ɗan fara samun lafiya kaɗan-kaɗan. Sai dai maimakon ss3 daya kamata ace zata shiga a yanzu sun maida ta ss1. Ruwan addu'a da wadda Ammie ke mata, da jan ta ajiki da ƴan uwanta keyi da wanda Daddy ke mata, da tattalinta da Yazeed yake duk da uwarsa bata so, itama kuma bata saki jikin da shi saboda wani abun kan tuno mata Ajwaad yasa Alhmdllh ta ɗan fara sakin jikinta. Duk da dai nan ɗin ma akwai ƙalubale daga matan gidan da yara, sai dai bai cika damun su ba musamman Maanal da a yanzu ta zama shiru-shiru. Miskila, mara son magana. Idan kaga murmushinta sai Ammie ko ƴan uwanta. Ta tattara hankalinta gaba ɗaya akan karatu da ibada. A haka ta kammala secondary, a Kuma lokacin Ammie ta sake haihuwa ta biyu a gidan Alhaji Usman Chalawa, kamar yanda na farko ya kasance namiji na biyun ma namiji ne, still a kuma lokacin akaima Shahidah da Amaal aure. Kuma dukansu Daddy ne ya zaɓa musu mazan. Bayan bikin Maanal ta fara jami'a itama anan Zariya. Kullum ake kaita a ɗakkota, dan driver na musamman Daddy ya ɗauka mata. Gefe ƴan uwanta na hidima da ita, Ammie da Nene na bata kulawa. Sai dai duk da canjawar komai akwai abubuwa da yawa har yanzu sun kasa canja kansu a gareta. Musamman wasu a cikin ɗabi'un da abaya ba nata ba. Kamar karatun English novels da abaya batayi sai Ajwaad, saka gilashi a ido da makamantansu da yawa da abaya duk ɗabi'un Ajwaad ne. Ammie na lura da ita, sai dai bata taɓa mata magana akan hakan ba, dan tasan sai a hankali Maanal ɗin zata manta komai. Sai kuma yanayin ciwonta ya taka rawar gani sosai na sauƙaƙa tanka matan akan irin hakan kodan gudun abinda zaije ya dawo.
Tana shekara ta biyu a jami'a Yazeed ya fito mata da ainahin abinda ke ransa game da ita. Bata wulaƙantashi ba, ba kuma ta amsheshi ba. Ta dai cigaba da girmamashi kamar yanda ta saba. Dan sosai take matuƙar ganin girmansa da kimarsa a cikin idanunta da zuciyarta. Da farko yaso ayi bikin ta cigaba da karatun a gidansa, sai uwarsa ta tada tujarar ƙin yarda. Haka akaita kai ruwa rana dai.
A haka cikin amincin UBANGIJI ta kammala karatunta, ta fito da sakamako mai ƙyau, bata wani jima ba ta wuce hidimar ƙasa a Jos, a can ne ta haɗu da Zulaiha da Aneesa da suma hidimar ƙasar ce ta kawosu Jos ɗin ƴan Kaduna ne. Nan fa suka ƙule ƙawance duk da bawani saki jiki take da su ba. Basu fi wata guda ba ta haɗu da RK, sunje sayya wani shago shima yazo, shine ya yarda atm card ɗinsa batare daya sani ba Maanal ta tsinta ta bashi. Wannan itace farkon haɗuwarsu kuma silar tushen alƙar dake a tsakaninsu yanzu. Duk da da farko bata kulashi amma yayta naci batare da nuna gajiyawa ba koda a fuskarsa.......

_________★

MUN DAWO LABARI🚪🏃🏃🏃🏃


Yanzun kam sai muga wane mai rabo ne da Maanal ɗin. AA Darma da a baya ya furta babu soyayya duk da ta'asar daya tafka?.
Yazeed daya taka rawar gani a wata gaɓa ta rayuwarsu mai tsanani da wahala shi da mahaifinsa da dukiyarsu da ƙarfinsu da mutuncinsu?.
RK daya tsinta dami a kala, ya kuma nuna juriya da haƙuri akan dukkan ja da Maanal ta dinga masa a ƙasa. Ya kuma taka tasa irin rawar shima a yanzu ko muce yake kan takawar.
Ga tarihin Maanal da alaƙarta da AA ya sani, zai kasance akan bakansa ko shi zai janye yabar ma AA da Yazeed filin ne?.
Da gaske AA ba son Manaal yake ba a wancan lokacin kamar yanda ya faɗa sai yanzun ne ya fara son nata kokuwa akwai wani AJIYA A DUHU ne daya kamata mu sani?.......✍️


_Abin fa da yawa, mudai je zuwa kawai🏃🏃🏃🏃🏃._








✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*


*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖7️⃣5️⃣




______________


Assalamu alaekum,Yan uwa barka da wannan lokaci, inde Kaya kikeso unigue Wanda bazakigannsu ajikin kowaba se yangayu toh kishiga group din mom safwan Muna turakaya ko Ina cikin amincin Allah Muna seda lace, atampa,shadda,voil,beil,sarka,kayan yara,takalmi ,jaka ,kayan yara, kayan kitchen,Kae mufa komae daruwankane Allah y bamu kasuwa me albarka nagode


Ga inda zamu iya samun mu .


09064820534.


Ga kuma link na group ɗin mu.


https://chat.whatsapp.com/CuYcnxM1Z7VCYL5tqnyuL7


_____________


.........Daddy shine ya lallaɓa Maanal da su Shahidah fitowa wajen baƙin Giro. Gwaggo kakarsu, sai Babu mahaifinsu, sai Malam Aƙilu ƙani ga Baba Haruna. Wanda bayan barowar su Ammie Giro ya aure gwaggo.
Zama kawai su Maanal sukai batare da sun kalla kowa ba balle gaishesu. Sai da Daddy yay musu magana sannan suka gaishesu ciki-ciki, dan Maanal ma kam bakin kawai ta motsa. Baabu ne kawai ya amsa cike da zumuɗi idanunsa cike da ƙwalla yana kallon ƴaƴan nasa, farin cikin rayuwarsa. Ita kanta Ammie ɗin satar kallonta yake. Zuciyarsa na matuƙar rawa da ganin ɗunbin canjawar da tayi. Canjawar da a yanzu idan yace ya taɓa aurenta wani sai ya gallara masa maruka kafin ya ƙaryatashi. Dan shi duk ya rame ya lalace tsufa ya taso masa saboda ciwo. Ga zaman ƙauye da canjin rayuwa tamkar bai taɓa zama aji ba a rayuwarsa, ga fitinar yara guda biyu da ALLAH ya bashi tare da Sailu amaryarsa. Ɗansa namiji shalele ya zama fitinanne a garin Giro da kewaye, sai mace dake bimasa itama dai marabarta kaɗan da namijin..
Daddy ne ya katse shirun da gyaran murya. Kafin ya ɗaura da sallama. Duk suka amsa. Cigaba yay da faɗin, “Alhamdullahi da kasancewar mu anan, kafin komai zan fara da nasiha a garemu baki ɗaya musamman akan ku yarana. Ina roƙon ku kuyi haƙuri da koma minene zukatanku suke tunawa da suka faru a baya. Ba'a fushi da iyaye, ba kuma a ƙin su sai idan akan abinda zai zama saɓon ALLAH ne. Koma minene ya faru ya rigada ya farun ya wuce. To a barsa a ya wuce ɗin a tari gaba. Yau ga mahaifinku sunzo garemu da muhimmiyar magana kamar yanda suka faɗa, sai dai dama bamu kai ga tattaunata ba ALLAH ya kawo ku. Dama a nawa shirin shine na buƙaci ganinku a gobe idan ALLAH ya kaimu, sai kuma komai ya sauƙaƙa.” Sake maida hankalinsa yay ga su Babu, fuskarsa da murmushi ya cigaba da faɗin, “Inaga tunda ALLAH ya sauƙaƙa gasu sunzo kafin ma mu nemesu ya kamata mu tattauna ko”.
“Hakane”. Cewar Kawu Aƙilu yana gyara zama. Sai kuma cikin dakiyar murya ya cigaba da faɗin, “Kamar yanda ka faɗa abinda ya faru ya riga ya wuce hakane Alhaji, dan haka maganar tuna baya da anyi kaza ko anyi kaza babu zancen maimaita shi ko tada shi. Dama munzo nan ne akan batun ita Maanal, wanda yake neman aurenta yaje garemu a satin daya gabata kuma mun bashi. Saboda dalilan ganin shi ɗin mutumin kirki ne da muke da tabbacin zai riƙeta da mutunci kamar yanda muka samu sauran ƴan uwanta a mutuncinsu.......”
Cikin mamaki da ruɗani Ammie da Nene da su Maanal duk suka kallesa. Yayinda Daddy ya kasa jurewa shima dan shi zatonsa haƙuri suka zo basu da neman yafiyar su Ammien akan abinda suka aikata musu a baya, ashe wata fitinar ce suka zo da ita kuma. “Me neman aurenta kuma? Wanene shi haka da mu anan bamu sanshi ba?”. Cewar Daddy da mamaki.
Wani irin ɗaure fuska gwaggo tayi, Babu zai yi magana ta hararesa. Cike da isa ta ce, “Sunansa Alhaji Bukar. Sanata ne babba a ƙasar nan, kuma mun bashi, munzo nan ne ma saboda mu tabbatar muku mun bashin sannan mu wuce da ita can Giro dan nan da sati biyu za'ayi biki kamar yanda ya buƙata”.
Tuni zufa ta gama wanke Daddy, ya dai daure da ƙyar ya maida dubansa ga Maanal da take ma su gwaggo wani irin shegen kallo, sai dai uffan batace ba. “Manaal” Daddy ya kirayi sunanta a hankali. Juyawa tai tana amsa masa.
“Waye kuma Alhaji Bukar?”.
“Daddy ban sanshi ba nikam, bana kuma buƙatar saninsa. Sai dai ina roƙonka cike da girmamawa ka faɗama waɗan nan mutanen su bar mana gida su koma inda suka fito. Idan ba hakaba wlhy wlhy wlhy sai na kawo musu human right.” sai kuma ta miƙe a hankali tana duban gwaggo da wani irin ƙasƙantaccen kallo. “Ke kuma idan kina buƙatar mutuncin furfurar kanki kiyi gaggawa tarkata komatsanki ku kama gabanku. Ashe kina da baki ko ido da kwallin kwaso waɗan nan ƙazaman ƙafafun naki zuwa garemu? Kin manta mu ba jininki bane? Kin manta a yawon tazubar uwarmu ta samo mu? Kin manta bazaku haɗa zuri'arku da lallatacciya mai ɗauke da cikin shege ba? Kin manta... Kin manta.... Da yawa. To karki yarda ki bari na tuna miki, dan tunawar na nufin shiga ukun ki, tun kina iya banbance su waye a gabanki ki koma inda kuka fito. Inba haka ba kuwa.....” ta saki wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login