Showing 207001 words to 210000 words out of 221978 words
Chapter 70 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
da Babban Yaya. “Abah kasan nifa ba wani sanin Kaduna ɗin nan nayi ba.”
“Eh mu samu mai napep ai zai kaimu in sha ALLAH”.
Haka kuwa akayi, dan da mai napep duka samu ya jagorancesu har zuwa masallacin da aka rubuta a jikin katin. Sun kuwa samesa cike da jama'a, da alama akwai wasu ɗaurin auren bayan wanda suka zo.....
____★
Su Oum ma sun isa gidan Alhaji Usman Chalawa. Tun fa a kallon anguwar jikin Mamy ya fara ɗan sanyaya, dan tayi zaton har yanzu su Ammie a irin waccan rayuwar ta baya suke. Ko dataga gaban ƙaton gate ɗin da sukai parking sai tai ɗif. Godiya driver yay ma mai napep ɗin daya jagorancesu suma, Oum ta masa alheri sannan suka samu waje sukai parking a nan gefen gidan. Akwai ƴan biki dake ta shigi da fita dan haka suma suka shige. Tabass gida ne babba kuma sashe-sashe. Duk da nasu yafi ƙawa da girma sun san anan ɗin ma babu raini gidan masu akwai ne. Basu san inda zasu nufa ba dan haka Oum tai ƙoƙarin kiran layin Shahidah. Bugu biyu kuwa ta ɗaga, cikin girmamawa tai sallama da fara gaishe da Oum ɗin. Murmushi Oum tai tana amsa mata, kafin ta ɗora da faɗin, “Gamu a harabar gidan ku bamu san ina kuke ba”.
Cikin mamaki da kuma rashin fahimta Shahidah ta ce, “Oum gidan mu? Wai nan Abuja?”.
“A'a Kaduna, inda ake biki”.
Ai ji Shahidah tai tana neman rikicewa. Hakama Amal ta saki soson shafa hodan hannunta tana kallon Shahidah. Suna a ɗakin Maanal ne suna shiryawa dama. Dan sai yanzu suka samu dama saboda aiki. Cikin sauri Shahidah ta yanke kiran, ta ja mayafi Amal biye da ita suka fito. Su Ammie na falo da su Hajiya Majdiya da suka kwana anan suma. Tambayarsu Ammie take lafiya? Ina zasu haka?. Batare da sun tsaya ba sukace suna zuwa.
Cike da farin ciki Oum ta kama Amaal da Shahidah ta rungume a jikinta. Musamman ma Amaal da sai yau ne ita suka gaɗu. Itama dai Mamy murmushin yaƙe ta shiga yi, yayinda Saheeba keta wani faman taɓe baki. Nibras dai ƴar kallo ce, dan ita dama nata baƙin halin akan AA ne kawai. Sashen Ammie su Amaal suka musu jagora, inda shigowar tasu tayi dai-dai da miƙewar Ammie da Hajiya Majdiya dan zataje ɗakin Ammien tai salla. Cak Ammie ta tsaya kamar wadda ta suma. Itako Hajiya Majdiya ta shiga ƴar dariya tana kallon yanda Oum da Ammie ɗin suka tsaya suna kallon juna kamar kaji. Kai daka kalla Ammie kasan a ruɗe take, dan jin take kamar irin mafarkin data saba yi ne akan Oum ɗin. Ɗan jujjuyawa tayi ta kalla kowa a falon, ƙarshe ta sauke idonta akan Amaal da Shahidah da duk suka koma yanayin tsoro. Dan su fargabarsu basu san yanda su Oum suke a zuciyar Ammien tasu ba a yanzu. Saboda tunda aka rabu bata sake yin maganar waninsu ba..........✍️
09032345899
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖9️⃣0️⃣
______________
........Sai kuma a mamakinsu sukaga a hankali Oum ta nufi Ammie. Ai tuni itama Ammie ta zaburo kansu suka rungume juna. Hakan ba komai bane, dan duk wanda yasan tarayyar Ammie da Oum yasan alaƙace mai ƙarfin gaske irin ta yaya da ƙanwa ciki ɗaya. Ciki ɗayan ma irin wadda akafi shaƙuwa ɗin nan. Su duka hawaye suke yi, hawayen kewa da begen juna da farin cikin sake haɗuwa a gaɓar da babu zato babu tsammani musamman ga ita Ammie.
Ɗayan ƙaramin falon Ammie dake a rufe dan kar mutane su ɓata Amaal tazo ta buɗe. Sai da su Oum suka gaggaisa da mutane anan falon sannan suka shiga. Gaba ɗaya Ammie ita tama rikice, ta rasa ina zata kama ina zata saka su Oum. Yayinda su Oum keta sake mamakin ganin yanda ta canja, duk wanda yasan Ammie a shekarun baya ya ganta a yanzu za'a iya kwana ana gaddama da shi akan ba ita bace ba. Gaba ɗaya ta zama matar manya. Tayi ƙiba ta ƙara haske da cikar kamala. Dan ita kanta Mamy a wannan gaɓar jitai ta raina kanta. Saboda ko suturar dake a jikin Ammien ka kalla kasan lallai nagaba yayi gaba yanzu kam, na baya sai labari. Gefe kuma ga ganin Hajiya Majdiya a tare da Ammie ɗin ya sake tabbatar ma Mamy lallai dama Oum na tare da su Ammie kenan take munafuntar ta (kun san idan mutum nada halin banza kullum gani yake haka kowa yake ma😏)....
Salla suka fara gabatarwa saboda gudun fitar lokacinta. Kafin a cika musu gaba da abinci kala-kala. Kan Ammie dai a matuƙar ɗaure yake da ganin sanayya tsakanin Hajiya Majdiya da su Oum. Daga ƙarshe dai ta kasa haƙuri ta magantu. Dariya Hajiya Majdiya tayi, kafin ta warwarema Ammie komai. Matuƙar mamaki da al'ajab ne ya nema kashe Ammie, ta dinga raba ido tsakanin Hajiya Majdiya da Oum. A lallai tabbas bata san ƙannen Oum ba a fuska a tarayyarsu har suka rabu, saboda lokacin su suna ƙasar waje, amma tasan labarinsu, tana jin kuma tana ambatar ƙanwarta datai aure amma tana acan kasar wajen mijin kuma na nan Nigeria saboda yanada mata biyu a Zaria amma yana zuwa can wajenta dan yana kasuwanci a ƙasashen ƙetare. Cikin kasa daurewa Ammie ta ce, “Aunty! Dama Maman Najma ce kike yawan bani labari da mijinta ke Zaria amma ita tana can Paris”.
“Tabbas itace Asiya. Shekara shida kenan da dawowarta Nigeria har ma da su Abbu. Dan yanzu haka su suna Kano ne”.
“Ikon ALLAH kenan, shekaru biyar kenan muna tare amma bamu san akwai muhimmiyar alaƙar data taɓa haɗa ƙaddararmu ba. A lokuta da dama wasu al'amura na Maman Najma kan so sakani a ruɗani wlhy. Dan sai kita dawo min cikin idanu duk da bakwa kama ko kaɗan a fuska.”
“Gaskiya ne bama kama da Majdiya da Rafeeq sam. Garama Sulaiman shi kam da kin gansa zaki san akwai alaƙa. Mu kamar mun kwaso Mah-mah ne. Itako Majdiya da Rafeeq Abbu. Wai ni naga kowa banda Baby na fa, ko bata zo bikin bane?”.
Murmushi Ammie tayi. “Tazo, suna tare da su Najma Nene ta aikesu.....”
Dai-dai nan kira ya shigo wayar Ammie. Ganin Daddy ya sata ɗauka batare data ƙarasa maganar ba. Fuskarta da murmushi ta ajiye wayar tana kallon Oum. “Aunty dama harda su Yaya kuke tare?”.
“Ai mu duka gidan ne ba'a bar kowa ba. Halan har an ɗaura auren?”.
“Eh an ɗaura harma sun shigo. Amma inaga su basu ƙarasa wajen walima bane ba. Dan yace gasu nan a hanya a shirya musu abinci a sashensa.”
“Oh oh ji son bama mutane wahala. Maimakon su ci acan kamar kowa”. Mamy ce mai maganar. Dariya Ammie tayi, da faɗin, “Babu wata wahala Mamy, hakan ai shine dai-dai suzo na gansu shekara nawa”. Daga haka Ammie ta fice. Da wani shegen hararar ƙasan ido Mamy ta bita, sai ko karaf a idon Hajiya Majdiya. Mamaki sosai ya kama Hajiya Majdiya dan abu ne da basu taɓa gani ga Mamy ba. To kodai sunada matsala ne da Hajiya Asiyan? Kai to amma a dukkan labarin da Oum ta bata na alaƙa da tarayyarsu babu wani saɓani ai, hasalima Mamy bata da yawan shiga sabgar mutane. To kodai idonta ne ya gane mata ba daidai ba? Kai to gaskiya hakanne. Da wannan tunanin ta saki zancen a ranta suka cigaba da hirarsu.....
★ Har cikin gida motar su AA ta shigo dan suna biye da Daddy ne. Yanzu kam Fawzan ne ke driving ɗin. AA na gefensa Abah da Babban yaya na baya. A kusan tare duk sukai ƙoƙarin fitowa. Hakan yayi daidai da fitowar su Huznah daga sashensu. Cak taja wani kalar wawan birki. Itama dai cikin kwalliya take, sai dai ɗan kwalinta a hannu ta yana siririn veil a kanta. Tare take da wasu ƴammata guda biyu. Sai wata dake biye da su da makeup box a hannunta, da alama dai kwalliya zatayima Huznah ɗin. Dan su sauran biyun da kwaliyarsu raɗam a fuska. Bakinta har harɗewa yake wajen ambaton “AA Darma! A gidanmu?”.
Duk kallonta ƙawayen nata sukai, wadda ke'a gefen haggunta ta ce, “AA Darma naki da kuka haɗu a Abuja lokacin bikin Yaseerah?”.
Bata iya ta bama ƙawar tata amsa ba. Jiki na rawa ta juya sashensu da sassarfa. Wani iri zallo zuciyarta keyi kamar zata fasa mata ƙirji ta fito. Hajiya Basariyya na falo tsakkiyar ƙawayenta su Maman Yaseerah Huznah ta faɗo musu. Tama manta a cikin taron mutane suke. Yanda take ƙwala kiran “Ummy! Ummy!” yasa Hajiya Basariyya miƙewa zaram. Tareta tayi tare da girgizata tana faɗin, “K Huznah lafiyarki kuwa? Wane irin kirane wannan? Jibafa yanda kike shigowa kamar wadda aka biyo.”
“Ummy AA Darma fa na gani a gidan nan”.
Rasama inda Hajiya Basariyya zata kamo AA Darma tayi. Ta ce, “Waye kuma AA Darma?.”
“Ummy AA Darma ɗin ne baki sani ba? Mijin da zan aura na Abuja”.
Ai sosai Hajiya Basariyya ta waro idanu waje, hakama Maman Yaseerah zaram ta taso inda suke. Hannun Huznah ɗin ta kama sukai cikin bedroom, Hajiya Basariyya ta take musu baya.
“K Huznah nutsu, da gaske kike kuwa”.
“Wlhy da gaske nake Mamah.”
“Tab ɗin jan, eh lallai malam yayi gaskiya. Hakan na nufin aiki yayi kenan”. Maman Yaseerah ta faɗa tana kallon Hajiya Basariyya.......
_In dai da gaske aikin nan yaci nima ai arakani wajen malamin nan zai min aiki akan makaranta AJIYA A DUHU musamman ƴan Discussion House da ƴan AREWABOOKS ina son a musu ASIRI su fara son Uncle RK🥱🥱🥱🤪🏃🏃🤣👍_
__________★
A yayinda haɗuwa ta kasance tsakanin AA Darma da Huznah, Ammie da Oum acan Kaduna. Anan Kano RK ne tare da Alhaji ƙarami yayansa da Abbu mahaifinsu suka kai ziyara gidan Baba Sardauna. Ƙyaƙyƙyawan bafilatanin dattijo mai tarin cikar kamala data addini. Anga jiya anga yau ana fatan ganin gobe. A yanzu shine uba kuma jigo da gaba ɗaya ahalin Baffa Ishaq Darma ke kallo a matsayi na kamar mahaifi. Shine garkuwa kuma shine alƙali mai tsawatarwa da zartarwa akan a tsakanin wannan zuri'a. Hakama matarsa ta karɓi wannan girma bisa ga bashi dukkan goyan baya ta hanyar amincewa ita ɗaya daga cikin wannan zuri'ar ce ba matar ɗa dake kallonsu a matsayin dangin miji ba. Dan bata da abin cewa ga wannan zuri'a sai godiya da fatan alkairi. Ita kanta mantawama take ba daga tsatsonsu ta fito ba.
Baba Sardauna ya girmi Abbu sosai, dan sai dai suyi sa'anni da Baba Umar mahaifin Abah kenan. Ga kuma girma irin na matsayin yayan mata a tsakaninsu. Harara Baba Sardauna ya makama RK bayan ya gama amsa gaisuwar Alhaji Ƙarami.
“Ni bazan amsa gaisuwarka ba ai Rafeeq. Dan lokaci kaɗan ma ya rage kai da wannan ɗan naka Ajwaad da Najeeb na sakaku a ɗaki na zane ciki da bai sannan nakai hotunanku massallaci ko za'a samu mai taimakonmu ya baku matan aure koda guragu ne. Kun wani ajiye gemunan ƙarya kamar na ALLAH. Ku yanzu dan ALLAH Moddibo da Saleem basa birgeku, da ƙananun shekarunsu amma yaran bibbiyu....”
“Ayi haƙuri Baba a mana afuwa. In sha ALLAHU zamuyi”.
“Haka kullum kuke faɗa. Har gara kai ma kana bada haƙuri da nuna zakayi, amma waɗan can biyun inaga sai mun haɗa da roƙon ALLAH dan da alama akwai iska marasa san aure a tare da su”.
Abbu dake murmushi ya ce, “Ai kaima dai ka faɗa Yaya. Ni wlhy canai idan suka wuce wannan shekarar kawai a samu wanda suka dace a aura musu sai dai akai musu ɗakunansu, ba sai suyi yacce zasuyi da su ba”.
“Shawara mai ƙyau wlhy Kasheem. Dama jiya-jiyan nan muke maganar nan da Kamila da tazo. Sai kuma ga Khadijah ta kira waya Itama tana mun complaine akan Raihana da Nuwaira.”
“To ai sai asan mafita kawai Yaya, duk da shi yazo da nasa batun ne yanzu haka wai acewarsa. Ni kasan ba kama zancensu nake ba su ukun nan dan munafukan bakinsu ɗaya da kake gani. Najeeb da Ajwaad da Rafeeq ba, ALLAH kaɗai zasu gaya min akan aure na yarda dasu”.
Dariya Alhaji Ƙarami yay da faɗin, “Kai Abbu, ALLAH kun kasa fahimtarsu ne kawai.....”
“Ohhh yanzu na gane, Sulaiman kuke ɗaure musu ƙugu kenan ku yayun nasu”.
“A'a wlhy Baba. A dai yi haƙuri, in sha ALLAHU wannan karon komai ma yazo ƙarshe. Ina kuma goyon bayanku dan muma ba son zaman nasu muke haka ba”.
“To Alhamdullah ai haka muke son ji”. Cewar Baba Sardauna yana gyara zama. Sai kuma ya kafe RK da tunda ya duƙar da kai bai ɗago ba. Cike da kulawa ya ce, “Ɗan nema, zonan naji ɗuminka, dama kwana biyu nayi kewarka kaje ka maƙale a Abuja wajen ɗan uwanka”.
Murmushi RK yayi, tare da miƙewa ya isa gaban Baba Sardauna, zai zauna ƙasa ya kamashi ya zaunar a kusa da shi, tare da ɗan rungumesa. “Fitinanne wai ni kake jin kunya kuma?”.
Dariya RK ya fashe da ita, hakama Alhaji ƙarami da Abbu. Aifa nan baki ya buɗe aka shiga gaisuwa. Sai kuma hira ta ɓalle. Suna cikin hirar sai ga Baba Umar. Shima dai nutsatstsen mutum mai cike da kamala. Dan zasuyi shekaru ɗaya da Abbu. Shi mutum ne da baida yawan magana. Dan duk cikinsu ya fisu haƙuri. Bazaka taɓa cewa ya haifi kamar Abah ba, abinka da ana jin daɗi.
Sosai suka tattauna akan al'amarin dake damunsu na rashin auren RK, AA, da Najeeb daya kasance ƙani ga Abah. Shima dai yaƙi auren, har ga ƙannensa biyu sunyi har da yara. Shine ƙani na uku a wajen Abah, sai Saleem da Moddibo sannan matar Alhaji ƙarami data kasance Auta. Shi yama girmi su AA ɗin. Sosai Baba Sardauna da Baba Umar suka ji daɗin kawo matar aure da RK yayi. Sun kuma tabbatar da babu wasa a satin nan zasuje Kaduna nema masa aurenta. AA da Najeeb kuwa su zasu zaɓa musu matan aure dan ayi bikin rana ɗaya dana RK ɗin.
A wani irin farin ciki mara misali RK ya tsinta kansa. Har ji yay ya ƙagara su baro gidan Baba Sardauna dan ya samu ya kira Maanal ya sanar mata wannan albishir, duk da yasan suna a cikin biki yau. Kasa haƙuri yayi tun suna a gidan ya tura mata daddaɗan text massage, Dan basu baro gidan Baba Sardauna ɗin ba sai da sukai sallar isha'i a massallacin ƙofar gidansa. Suna ƙoƙarin fitowa kuma sai ga Hussain yazo gidan tare da matarsa da yaransa biyu shima. Nanfa kuma aka sake zaman sabuwar gaisuwa, dan RK da Hussain ɗin sun jima ba'a haɗu ba. Ƙarshe dai sai goma suka baro gidan.
Sanda suka iso har Mah-mah da Rufaidah da yara sun gaji da jiransu sunci abincinsu. Suna a falo suna hira, yara kuwa sun tafi sun kwanta. A rayuwar Mah-mah da Rufaidah sam babu surukuta, zama ake irin na uwa da ƴa. Dole rayuwar gidan su Rafeeq tai matuƙar birgeka, dan rayuwace mai cike da so da ƙaunar juna. Babu munafunci, babu makirci. Kowa na ƙoƙarin bama ɗan uwansa hakkinsa dai-dai gwargwado. Zama Abbu da Alhaji ƙarami sukai anan falo wajen Mah-mah, yayinda RK yay sashensa dan burinsa kawai yay kiran Maanal ya mata albishir........✍️
09032345899
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖9️⃣1️⃣
______________
........A falon Daddy akama su AA masauki, kafin Daddyn ya ɗaga waya yay kiran Ammie akan a kawo musu abinci. Da to Ammie ta amsa masa, tare da ajiye wayar suka cigaba da haɗa abincin ita da su Shahidah da Hajiya Majdiya. Hakan kuma yayi dai-dai da shigowar su Maanal, Amrah, Najma, Aneesah, Zezaah (ƙawayen Maanal kenan na sarvese). Dole ne matasan ƴammatan kai musu kallo ɗaya ka ƙara. Dan babu wacce batai ƙyau cikin tata shigar ba. Taku suke cike da nutsuwa sun kamo kuloli na waina masa da Ammie tasa akayi a gidan Nene, yayinda Almajirai uku ke biye da su da wasu kulolin manya da sukafi biyun da suka kamo. Gaishe da mutanen dake a falon sukayi sannan suka ƙarasa kitchen inda akace musu su Ammie na nan.
“Kai yaran nan ALLAH yay muku albarka, kamar kun san yanzu nake