Showing 141001 words to 144000 words out of 221978 words
Chapter 48 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
armashi sosai sukai shirin komawa Sokoto amma sai Gwaggo ta hana wai su zauna anan suyi wankan jego. Ganin yanda bata kawo tashin hankali ba a sunan yada baba Haruna tunanin ta sauya ne. Dan yanzu ta ɗan rage wasu abubuwan a zahirance saboda tsoron kada ta tsinke ƴar sauran igiyar ɗaya dake a tsakaninsu. Ta koma zuba rashin mutuncinta ta ƙasa, dan Habib ta koma takuramawa akan sai ya ƙara aure, ita kuma Asiya ana mata a kaikaice.
Shima dai Habib wannan karon bai damu ba ya barsu anan ya kuma yarda da batun ƙara aure, dan ya samu damar sheƙe ayarsa da sabuwar karuwarsa da suka haɗu anan Sokoto ɗin kwanan nan. Zama kamar wasa ya nema zama gaske. Dan bayan gama wankan jegon Maanal Habib bashi da niyyar cewa su shirya komawa Sokoto, sai dai yana zuwa duk ƙarshen wata yay musu weekend ya koma. A haka aka tado batun aurensa. Auren daya bama kowa mamaki ya kuma saka Ammie a tashin hankali. Amma sai Baba Haruna ya dinga kwantar mata da hankali da nasiha ta sakama kanta dangana kuwa ta rungumi ƴaƴanta. Cikin ƙanƙanin lokaci akasha biki kuwa, yarinya ƙarama da bata wuce shekara sha bakwai ba. Inda Ammie ta burge kowa shine tattara komai ta watsar kamar ma ba ita akama kishiyar ba. Sai shima kansa Habib ɗin ya dinga kiyaye duk wani abu da zai taɓa mata zuciya ba kamar yanda Gwaggo taso ba. Itama yarinya da aka ɗoro akan rashin kunya da zata dinga yima Ammie sai ta dinga jin shakkarta. Abinda ya ragema amarya armashi samunta ba'a cikakkiyar mace da Habib yayi ba, dan tun a daren farko sai da tasha maruka a wajensa a ɗaki batare da sanin kowa ba. Ko sati kuma bai cika ba na amarci ya tattara ya koma wajen aiki. Aiko akaita gutsiri tsoma wai Ammie ce tayi wani abu, dan Gwaggo har ɗaki ta sameta ta mata wankin babban bargo. Ita dai batace komai ba. Habib bai zo gida ba sai da yay wata guda kamar yanda ya saba, ya kuma murje idonsa ya sauka ɗakin Ammie, itako tanata roƙonsa bai kulata ba, ana cikin haka sai ga Gwaggo har ɗaki, tas taima Ammie da zaginta akan muna fuka ta tasa ɗanta gaba har ɗakin amarya Sailu. Ai ko ranar ma maimakon ta samu kulawa a wajensa sai duka taci a banza, dan ya fahimci bata da kunya, Habib kuwa irin mazan nan ne da basa ɗaukar raini, shi hatta macen bariki tai masa hauka duka take ci a wajensa, Ammie ce kaɗai ta tsira da irin wannan halin nasa, duk da yana shan marinta itama a wasu lokutan. To ataƙaice dai wannan aure bai rufa wata biyar ba a wani zuwa ya saki Sailuba saki har uku. Nan fa gari ta ɗauka Ammie ce ta koreta. Babu kalar abunda Ammie bata gani ba akan wannan rabuwar auren amarya da mijinta, ƴan gidan suka kara tsananta, na Gwaggo kam ai ba'a magana. Ga Habib bashi da niyyar cewa su shirya subar garin har sai da Maanal ta shiga shekara ɗaya da rabi sannan akaima Habib transfer zuwa Kano. Aiko Baba Haruna da'a yanzu ya fahimci Habib na neman matan banza yace ya tattara matarsa da iyalansa su wuce tare. Gwaggo ta nuna bata yarda ba, Baba Haruna ya nuna mata shima bata isa ba. Kamar Habib baya so haka ya wuce da su Ammie Kano, dan yasan an rage masa jin daɗinsa ne kawai. Anan ya samu gida ya kama musu haya, daga baya kuma ya saye shi da kuɗin Ammie na gado, shine dalilin komawarsu da zama garin Kano. Tunda suka koma kuma basu sake zuwa Giro ba sai dai shi yazo sau uku sai yanzu shekara kusan shidda kenan dan tun Maanal nada shekara ɗaya da wasu watanni da kaɗan ya rage sukai biyu. Ita dam bata san Giro ba bata san ƴan Giro ba....
________★★★
Babu wanda ya sake bi takan su Ammie a gidan duk da wasu suna son kawo musu abinci suna jin tsoro ne. Anan ƙofar ɗakin sukai sallar magrib da isha'i. Sai kusan tara saura Babu ya shigo tare da Baba Haruna. Ganinsu a inda ya barsu su da kayansu ya sosa masa zuciya sosai. Baba Haruna kam a fusace ya shiga ɗakin Gwaggon. Sosai ya mata tas da abinda tayi ɗin, ya kuma tabbatar mata wlhy a wannan karon idan tace zatai wani abu to ta tabbatar shi bazai ɗauka ba ƙofa a buɗe take gareta. Wannan kalmar na tayar mata da hankali akan mijin nata. Dan tasan igiyar nan ɗaya tak ke riƙe da aurensu yanzu. Bakuma zata so ace ya tsinketa a yanzu da suke a shekarun tsufa surukai cike da gari ba. Shi da kansa ya fito ya shiga dakin dake a mallakin Ammien, ɗakin duk tarkace ne ma a ciki, dan haka ya fita babu jimawa sai gashi da almajirai kusan biyar, su ya saka gyaran ɗakin, shi kuma Babu ga fita nema musu abinci da maganin da Maanal zata sha dan zazzaɓin ya dawo. Dandanan aka gama gyara ɗakin, aka kawo katifa da tabarmi aka saka musu. Harda turaren wuta na tsinke baba Haruna ya ɗakko a ɗakinsa aka kunna, dan yanzu shine ya mayi mahaifinsu a gidan, shine ke da almajirai yake koyarwa, dan haka ya koma ɗakin zaure inda suka samesa na mahaifinsu da zama kenan. To da yake tunda yaga Gwaggo na niyyar kashe katifar dakin Ammien sai ya saka aka ɗauketa ya maidata can ɗakin nasa aka lulluɓeta, sai idan Babu yazo ake kawo masa, daya tafi kuma yasa a maidata can.
Gajiyar tafiya tasa basu ma wani iya cin abincin kirki ba dan ma harda shayi, suna son yin wanka basu san yaya zasuyi ba, dole suka hakura suka kwanta a haka. Dama ita Maanal tuni tayi barci abinta, duk da barcin nata bana daɗi bane ba. Washe gari dai sun ɗan samu kulawar mutanen gidan sakamakon ganin Baba Haruna tsaye akan al'amarin su. Dan har koko an kakkawo musu a wasu sassan. Duk da ma dai su yaran sun kasa sha sai Ammie ce tasha. Kosan da Baba Haruna da bread ya saya musu kawai suka iya ci, sai naman jiya da Babu ɗin ya saya musu basu ci ba. Yanda Maanal ta tashi da zazzaɓi sosai dole Babu ya ɗauketa zuwa asibiti. Ƙarin ruwa suka saka mata dan jikinta duk babu ƙarfi, hakan yasa suka jima can har sai bayan zuhur ya dawo da ita. Anan ne yake sanarma Ammien Abban Fadeel ya kira shi sun gaisa, itama Oum nata nemanta wayar a kashe.
Sai lokacin Ammie tama tuna da wayar tata, ta bincikota a bag sai taga ashe ta mutu ma babu caji. Dole ta bama su Shahidah tace suje waje su nema yara su rakasu inda ake caji sukai mata. Badan sun so ba suka fita, dan basa ƙaunar ganin hararar da Gwaggo ke musu da kallon tsana. Sai zuwa yamma suka amso mata tai kiran Oum, lokacin Maanal ta tashi a barci amma sai ƙunci take taƙi kula kowa abinci ma sai da Ammie tace zata zaneta sannan taci sa kaɗan. Amma yanzu tana jin ance Oum tai wata irin zabura tazo ta nanuƙe Ammie. Dole Ammie ta taƙaita gaisuwar da suke da Oum ɗin ta bata wayar, dan yi take ma kamar zata warceta. Oum na jin muryar Maanal itama ta saki murmushi...
“Oh oh! My Baby I miss you”.
Cike da zumuɗi Maanal ta ce, “I miss you too Oum. Oum ina Besty?”.
Dariya Oum tayi tana mai jinjina kanta idonta akan Ajwaad dake kwance a gadonta, tunda yaji ta ambaci sunan Maanal shima ta kafeta da idanunsa. Wayar ta miƙa masa tana faɗin, “Gashi nan kin barsa da ciwon kewa”.
Baki Maanal ta tura gaba, cike da shagwaɓa ta ce, “Oum ai nima banda lafiya ina ciwon kewarsa”.
Dariya Oum ta sanya, hakama Shahidah da Amaal. Ammie kama sai ta girgiza kanta kawai. Ganin su Shahidah na mata dariya ta tashi tana harararsu da murguɗa musu baki ta fice a ɗakin. Ammie na kiranta akan ta kawo mata wayarta kar tai mata ɓarna bata dawo ɗin ba. Gwaggo na tsakar wajen nasu tana haɗama dabbobinta dusa, suna haɗa ido da Maanal ta harareta, itama ko ta rama da murguɗa mata baki ta ɗauke kanta. Ai sai Gwaggo tai mutuwar tsaye da mamakin wannan fitsararriyar yarinya. Ita zata harara ta rama wannan jaririyar ƴar?.
Oho ko'a jikin Maanal, dan kujerar Gwaggo dake a ƙofar ɗakinta ta zauna abinta. Sai kuma cikin shagwaɓa ta ce, “Besty!”.
Wata irin ajiyar zuciya Ajwaad ya sauke yana lumshe ido da ya zame masa ɗabi'a duk da ƙarancin shekarunsa. Sai kuma a cikin muryarsa mai sanyi da zurfi ya amsa da, “Oummyim!”.
“Haushina kake ji dan na tafi na barka? Banfa da lafiya nima, yau har asibiti Babu ya kaini akamin karin ruwa”. Ta ƙare maganar muryarta na rawa alamar son yin kuka. Tashi zaune Ajwaad yayi sosai, cikin damuwa ya ce, “To kar kiyi kuka, nima banda lafiyan ai, jiya saida aka min ƙarin ruwan”.
Kukan ta sakar masa kuwa, da faɗin, “Besty nidai kace Babu ya dawo dani wajenka. Ni bana son nan. Akwai muguwar mata a garin. Yanzu ma ka ganta sai hararata take...” kuka sosai yaci ƙarfinta
Sosai hankalin Ajwaad ya sake tashi daga can, sai ƙoƙarin lallashinta yake yi amma tana ƙara ƙarfin kukan harda tutturza ƙafafu. Ga Gwaggo ta zuba mata wani shegen kallo. Kukanta yasa Shahidah fitowa. Sai dai suna haɗa ido da Gwaggo ta koma ciki da sauri. Dama a tunaninsu ko wani abu akama Maanal ɗin tunda sun san halin muguwar kakar tasu sai a hankali ce. Sosai Maanal take kuka har sai da Oum ta amsa wayar daga hannun Ajwaad da duk ya rikice da kukan nata itama tana lallashinta da tabbatar mata Bestien nata zaizo ya sameta. Da ƙyar tai shiru sannan Oum ta maida ma Ajwaad waya suka cigaba da hirarsu mai cike da shirme da shiririta musamman ga Maanal dan ko yaya shi Ajwaad ya ɗan tasa ya fara hankali....
Sam rayuwa a Giro batama Ammie da yaranta daɗi. Maanal ce ma dai babu ruwanta, tashin hankalinta kawai ace ta yini batai waya da Ajwaad ba. Anan ne zaka ganta kamar mara lafiya. Amma da sunyi waya sai ka walwalarta ta dawo. Sai ma ta fice wasa cikin gida abinta. Maanal dai dama jaruma ce a fagen iya faɗa da tsokala, anan ɗin ma duk da matsin da suke a ciki bata canja ba. Dan kuwa jibgar ƴaƴan mutane take yi, idan kafi ƙarfinta kasha ƙasa a cikin ido. Gwaggo kuwa idan ta harareta itama ta rama. Ɗakinta kuwa kai tsaye take shiga tace tana son abu kaza. Idan Gwaggon ta korota da zagi taƙi fitowa. Kota warto abinda take so ɗin ta fito a guje. Wannan hatsabibancin nata yasa Gwaggo tafi tsanarta fiye da kowa. Kullum cikin aibantata take da zaginta. Abin na damun Babu da Ammie sai dai babu yanda zasuyi, dan Ammie tama Maanal faɗa akan shiga harkar Gwaggon amma yarinyar nan data faki idon Ammie sai tasan abinda taima Gwaggo. A haka dai sukai sati uku a Giro, duk sun fita hayyacinsu sunyi baƙi sun rame saboda rashin abinci mai inganci. Suna a kwana na ashirin da biyar Babu yazo ma Ammie da batun wai zai yi aure. Sannan suma kawunan sa sunyi magana akan Shahidah da Amaal ya kamata a musu aure dan sun isa, musamman ma Shahidah data fara zama uwar mata. Dan haka sun yanke hukuncin ita Shahidah ta auri Lado ɗan wajen Badaru. Ita kuma Maanal Ƙasimu ɗan wajen Sagiru. Wani irin tashin hankali ne ya ziyarci Ammie. Ita ba auren Babu ɗin ne damuwarta ba, batun Shahidah da Amaal.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖6️⃣2️⃣
______________
.......Kuka sosai Ammie ta sanya ma Babu da roƙo da magiya, amma sai ya nuna mata shima bada son ransa bane. Dan bazai so yaransa suyi rayuwar garin ba, ba kuma zai so a yanke musu karatunsu ba. To amma bazai iya jayayya da ƴan uwan mahaifinsa da ƴan uwansa ba. Ina sam wannan batu bai shigi Ammie ba. Dan tasan wannan ba umarnin kowa bane sai Gwaggo. Hankali tashe taje ta samu Gwaggo da kuka da roƙo, sai Gwaggon ta rufeta da zagi ta kuma juya maganar. Dan kuka ta sanya da kururuwa wai Ammie ta sameta har ɗaki tana mata gargaɗi idan bata saka Babu ya janye batun ƙara aurensa ba sai tabi dare ta kasheta. Dandanan wajen ya cika da mutanen gidan harda makwafta. Kasancewar Ammie nada tabon fitar kishiya yasa kowa ya yarda da batun Gwaggo. Nanfa akaita cancana magana da zagin Ammie har saida Baba Haruna ya shigo gidan ya tsawatar.
Sam Ammie bata san miya rufema Babu ido ba, yana dawowa gidan Gwaggo ta faɗa masa ƙarya da gaskiya sai ya hau ya zauna. Aiko ya birkice mata yayta tujara a tsakar gida mutane naji, shi bazai yarda a raina masa mahaifiya ba. Ai ba a kanta aka fara kishiya ba. Shi ya gaji da baƙin halinta. Idan bata gode masa ba bata tsine masa ba. Shekara nawa yana zaune da ita zaman haƙuri badan ya taɓa jin sonta a zuciyarsa ba ko sau ɗaya. Sai dan kawai kar ace yama iyayenta rashin halacci ya kasa riƙeta. Shima namiji ne, yana son ya auri wacce yake so, yana son haihuwar ɗa namiji.. kai tujara dai kala-kala data sanya Shahidah da Amaal kuka sosai. Ita dai hajiya Maanal hidima bata san ma anai ba. Tana can tare da Baba Haruna daya fita da ita gaisuwa gidan wani abokinsa. Ammie tayi kuka har ta godema ALLAH, taji inama iyayenta na raye, ashe duk zaman da take da Babu ba soyayyarta a ransa har zuwa yanzu...
Anyi haka da kwana huɗu Babu baya kulata hakama ƴan gidan kowa ya ƙara ɗauke mata wuta ita da ƴaƴanta sai ga batun yima Shahidah da Amaal wai baiko. Ranar ji Ammie tai kamar tabar duniya ta huta. Karon farko ta sami Baba Haruna da roƙo. Yayi mamakin jin bada son ranta ake shirin auren yaran ba. Dan shi Babu ya nuna masa komai da amincewarta ne. Lallashinta yayi akan hakan, yace taje zai zauna da ƴan uwansa akan al'amurin. Wannan ya sakata ɗan jin sanyi a ranta. Sai dai me, koda Baba Haruna ya zauna da ƴan uwansa duk sai suka kasa fahimtarsa, ƙarshe ma mahaifiyarsa da har yanzu tana a raye duk da ta tsufa sosai ko tafiya bata iyayi sai tace idan bai bari amma yaran nan aure ba bata yafe ba. Hauka ake yara sunyi zagada-zagada ace an barsu babu aure. Ko so yake suna a musu irin yanda Umaru yay ma ita Asiya ɗin kamar ƴar arna sai da ta shekara ashirin a gida. Wannan yasa dole Baba Haruna ya bar maganar, ya kuma dinga lallashin Ammie. Ina hankalin Ammie ya kasa kwanciya, dan ko maƙiyinta bazata so ya kasance cikin wannan zuri'ar ba balle ɗiyanta. Balle kuma yara ƙanana kamar su Shahidah. Inama ƙudan yake ballantana romonsa.
Komai yama Ammie tsanani, dan sun tabbatar mata bazata koma da su Shahidah ba. Maanal ma za'ayi mata miji da lokaci yayi su dawo da ita gida. Ranar da aka saka ranar auren daya kasance sati huɗu kacal Ammie batai kwanan lafiya ba. Dan jininta hawa yayi ƙololuwa sai a asibiti ta kwana. Duk da wannan halin da take ciki sai zaginta mutane keyi wai kishi ne. Tana kishi dan mijinta zai ƙara aure. Babu wanda yay mata uzuri akan ƴaƴanta da ake shirin musu auren fin ƙarfi. Washe gari ta ɗan samu dai-daito, iya tunaninta ta rasa wazata tunkara ya taimaketa ya kuɓutar mata da yaranta, ƙanwar mahaifiyarta Shamsiyya kawai ta sani, itama a yanzu bata san duniyar da take ba. Dan tun bayan rasuwar iyayenta bata sake ganinta ba. Minna kuwa dama ba zuwa take ba tunda babu wanda ta sani sai kakanta ko'a lokacin, sai matarsa mara mutunci, yanzu kuma babu shi wajen wa zataje?. Wannan mutanen sune dangin mahaifinta, su kawai ta sani. Sai su Oum da suka zame musu ƴan uwa yanzu a garin Kano. A wannan karon kam sai kawai ta yanke shawarar kiran Oum ɗin, dan itace kawai mafitar data rage mata.
Bayan ta gama zayyanema Oum komai tana kuka itama Oum ɗin kukan take. Da ƙyar suka lallashi juna Oum tace ta saurareta zatai magana da Aban Fadeel in sha ALLAHU za'a kuɓutar da su Shahidahn daga wannan auren. Wannan waya itace ta sanya Ammie jin ɗan sanyi a ranta, har jininta ya ɗan sauka aka sallameta daga asibitin a ranar....
Washe gari kusan azhar saiga Amaal data fita sayo mata fura ta dawo cike da ɗoki. Kallonta Ammie da Shahidah keyi, sai kuma Shahidah ta ce, “Ke kuma ina furan? Kin san fa Ammie bataci komai ba ga magani zata sha”.
Zama Amal tayi da faɗin, “Yanzu zan koma na sayo, Abah na gani a waje tare da Ajwaad”.