Showing 168001 words to 171000 words out of 221978 words
Chapter 57 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
da suka taho daga Nigeria su kuma. Duk kannin abinda ya kamata an shirya shi, suka tura kaya Nigeria, a kuma wannan lokaci ne Ajwaad ya bada aka yi agogon nan da Manaal ta zana ta hanyar babban aminin Baba Sardauna dake da company anan Dubai. Kusan komai a gaban Ajwaad aka yisa, wannan kuma shine ya zama dalilin farko na fara jin sha'awarsa akan hakan. Duk da yana da nashi burin.
Sun dawo Nigeria suka iske Saheeba a gidan, wai tazo hutu. Babu wanda yay magana balle kawo wani abu a cikin ransa game da haka. Tunda dama tana ɗan zuwa jefi-jefi (Saheeba ɗiya ce ga ƙanwar Mamy). Bayan dawowarsu da kwana biyu babban yaya ya iso shima. Shirin biki fa ya fara kankama, dan ta ko'ina babu wasa. Sai dai Ammie da Baabu suna tsaka da tafka rigima saboda wasa da hankali da yaketa mata akan batun hakkinta, wato dukiyarta da iyayenta suka bar mata. Oum ce ta tausheta akan ta bar batun har ALLAH yasa su Baba Haruna suzo wajen biki, koma mi za'ayi sai ayi kawai. Da wannan ta tausheta akan al'amarin....
A ranar akai kamu, normal kamu ne dai irin namu na mutan da, ɗan turare kawai aka fesama Amaal da Shahidah, sai ƙawayensu daketa ƙunshi. A ranar gayyar mutanen Giro suka iso. Hakama can gidan su Oum mutanen Yola sun iso. Sai wanda ke anan cikin Kano ta ɓangaren su Oum data ɓangaren Mamy. Dama ƴan paris kwanansu uku kenan. Koda yake Mammah ce kawai tazo saboda yara na karatu, hatta Auta Rafeeq ba'azo da shi ba.
Washe gari aka shirya walima anan cikin gidan su Oum ta iya mata, Umma ce ta ɗauki nauyin malaman da zasuzo mata suyi lectures da abincin da za'aci. Wannan Rana itace tushen komai na wargajewar alaƙar waɗan nan ahali guda biyu. Ranar da zukata suka rarrabe cike da ƙuna da girgizuwa. Ranar da komai ya lalace, zaren ƙaddarar daya ƙullesu a waje guda shekara aru-aru jarabawar ƙaddara ta datse shi da almakashi mai matuƙar kaifi. Datsa irin ta kwaf ɗaya da har yanzu an rasa mai sake kamawa ya ƙulla shi.
Masu shirya waje sun kammala wajen ƙarfe biyu na rana, a dai-dai lokacin Maanal na daga can ƙarshen garden ɗin zaune saman lilo ita kaɗai. Tunda ta tashi bata jin daɗi yau, haka kawai kuma sai take son kaɗaici. Kwana kusan huɗu kenan tana acan gidansu, yanzu ma hayaniyar ƙawayen su Amaal suka isheta dan tana ɗakinsu kwance yasa ta fito ta dawo nan gidan su Ajwaad. Koda ta shigo ciki nan ma hayaniyar tayi yawa, sai kawai ta nufi ɗakin su Ajwaad. Cike ta sameshi da abokan su Fawzan, sai dai babu Bestyn nata. Gaishesu kawai tayi ta ɗakko wayar Ajwaad dake caji a gefen gadonsa ta fito. A hanyar fita falon suka kusa cin karo da wata ƴar budurwar yarinya kanta ɗauke da boket cike da gorinan zoɓo da kunun aya. Sosai Maanal na son zoɓo a rayuwarta, dan haka ta tsaidata tana tambayarta. Yarinya ta bata amsa da cewar mamansu ce tace ta kawoma Oum a ƙara a baiwa baƙi. Sai kuma ta nuna mata na hannunta, ta ce, “Wannan kuma zan bama yayana”. Maanal tasan yayan nata abokin Fawzan ne sosai, dan baima da wani aboki sai shi, suma dai maƙwaftansu ne. Sai kawai ta amshi na ledan ta ɗauki ɗaya. Daga haka ta fice ita kuma yarinyar tai ciki tana tura bakin haushin ɗaukar ma yayanta da Maanal tayi, babu kuma damar magana tasan zata iya dukanta, dan yaran anguwar nan kusan duk tsoron Maanal suke saboda fitinarta. Manyan ma in dai kace zaka shiga sabgarta kasha rashin kunya kuwa. Can garden ta nufa, sai da ta gama kalle gyaran da akai sannan ta wuce can ƙarshe ta zauna a saman lilo ta buɗe zoɓon ta fara sha tana game a wayar Ajwaad ɗin. Tafi mintuna biyar da zama sai gashi, sai da ya kai zaune a kusa da ita sannan ta ɗago duk da taji ƙamshin turaren da suke amfani da shi tunda ya shigo wajen. Harrarsa tayi, shima ya rama dan faɗa sukai kwana biyu kenan shiyyasa ma ta koma gidansu. Koda ya rama hararar sai ta tura baki gaba. Baki ya taɓe da ƙarɓar zoɓon hannun nata shima ya hau sha. Haka suka dinga shan wannan zoɓo babu mai ma ɗan uwansa magana har suka kammala. A lokacin ne ya fiddo wani ƙyaƙyawan box ya miƙa mata. Kallon box ɗin tayi, sai kuma ta kallesa, ta kai hannu zata amsa ya janye da faɗin, “Oh nama manta haushina kike ji fa”.
“To bana huce ba”. Ta faɗa kamar zatai kuka.
“Kin tabbata kin huce?”.
Da sauri ta ɗaga masa kai alamar eh. Sai ya sakar mata murmushi ya miƙa mata box ɗin. Wayarsa ta ɗaura masa a saman jikinsa, ta hau kiciniyar buɗewa. Da wani irin zaro idanu ta ce, “Wooow!!! Besty!. Amma agogon nan ya haɗu wlhy”.
Murmushi ya saki mai sanyi, ƙyawawan fararen idanunsa na kallonta da wani irin yanayi mai zafi. Cikin ƙanƙanuwar muryarsa data ƙara ƙanƙancewa a yanzu ya ce, “Besty, ai duk ƙyawunsa kin fisa ƙyau. Sannan kefa kika zana shi da hannunki shekaru shida kenan”.
Itama cikin sanyi ta ce, “Ni kuma Besty!”.
“Yes! Kefa”.
Ya bata amsa yana zaro wani note book a aljihunsa ya miƙa mata. Amsa tai tana kallon zanen agogon da tabbas ta tuna itace ta zana shi. Sai kawai taji hawaye sun cika mata ido. Dan zanen agogon bashi da maraba da agogon daya batan. Cikin rawar murya ta ce, “Besty!”.
“Uhmyim Bestyn Besty!”.
Ya faɗa da wani irin shauƙin da shima kansa bai san mi yake yi ba. Ga idanunsa na wani irin mata kallo mai zafi, sun kuma ƙanƙance sun kaɗe kamar ba shi ba. Itama kanta kallon nasa take tsakkiyar ido da wani irin yanayi dake cizon zuciyarta. Fin mintuna biyu suna kallon junansu kafin kiran waya ya katse su. Wayar ta kalla cike da kasala, ganin Babban Yaya ya sakashi ɗagawa murya a sarƙe. Bata san mi babban yayan ya gaya masa ba. Ya dai miƙe a raunane yana kallonta da miƙa mata wayar. “Ina zuwa ki jirani anan”.
Kanta kawai ta iya jinjina masa. Sai da bayan ya wuce ta iya sauke numfashi. Sai kuma cikinta yay wani irin murɗawa. Fuska ta yamutse da sakin ƴar ƙara tana dafesa da hannu biyu. Sai kuma jikinta ya kama rawa. Tama rasa yanda zata fassara ciwon cikin nata. Ta jima tana matse-matse kafin ya saki mata. Sauka tai akan lilon ta wuce cikin gidan neman Oum danta faɗa mata cikinta na ciwo. Sai dai koda ta shiga ɗakinta cike yake da baƙi, ita kuma bata a ciki. Fitowa tai domin nemanta cikin nata ya sake murɗewa. Da ƙyar ta iya kai kanta ɗakin su Ajwaad dan gara ta nemosa shi sai ya nemo mata Oum ɗin. Cikin ɗakin yanzu kam babu kowa saɓanin ɗazun, ga cikinta yay matuƙar ƙullewar da tafi ta farko, dole ta durƙushe gaban gadon Ajwaad ta dafe cikin nata hawaye masu zafi na rige-rigen sakko mata daga idanunta zuwa kumatun ta. Tun tana fahimtar halin da take ciki har komai ya fara mata nisa. Sama-sama taji ƙarar buɗe ƙofa, tare da ƙamshin turaren Ajwaad. Kamar muryarsa taji yana kiran sunanta a rikice, sai kuma taji ya ɗagata gaba ɗayanta ya maida saman gadon, tana ƙoƙarin yimasa magana taji ya kwanto mata a jiki ya rungumeta, duk da a yanayin da take sai da taji hankalinta ya tashi, dan abune da kullum ake musu nasiha a kansa. Oum tayi, Ammie tayi, Abah da su babban yaya da su Didi suyi. Jikinta ne ya kama rawa jin yana ƙoƙarin cire mata kaya, ga lips ɗinsa na ƙoƙarin sauka akan nata. Ƙoƙarin turashi take amma bata da wani ƙarfi, sai ma kama hannunta da yay duk biyu ya murɗe da ƙarfin da har sai da taji zafin har a cikin ƙwalwar kanta da tsakkiyar zuciyarta. Ya kuma danne mata baki ta yanda ta kasa ihun datai niyyar yi. Daga haka bata sake fahimtar komai ba sai wata irin rikitacciyar hayaniya da ihun mutane mai hawa saman kai......
A hankali ta shiga buɗe idanunta da sukai mata nauyi, hakama jikinta kamar ba nata ba, ga wani irin zafi da take ji acan ƙasanta. Akan Oum dake a rungume da ita tana kuka ta saukesu, sai kuma ta fara bin mutane da kallo. A tsakar gidansu ne, saɓanin gidan su Oum data san ta shiga. Ba kowa ke hayaniyar nan ba mai ban tashin hankali sai dangin su na Giro, gwaggo har riƙeta ake saboda yanda ta birkice tana zage-zage daga ita sai bujen cikin zani da riga. Amma zani da ɗan kwali duk ta wancakalar. Gefe su Shahidah ne ke kuka suna rungume da Ammie dake kwance kashirɓan. Sam Maanal ta kasa fahimtar komai, face cigaba da kallon kowa da sauraren ihunsu da sam bata fahimtar komai a ciki. A haka Abah da baba Sardauna da likitan data san family doctor ɗin su Oum ɗin ne suka shigo. Abah da shima yake a matuƙar damuwa ne ya bama Oum umarnin ɗaga Maanal zuwa ciki. Amma sai Gwaggo tace Oum bazata shiga musu ba, kuka Oum ɗin ta sake fashewa da shi mai ban tausayi. Hakan bai sa Gwaggo taji tausayinta ba, ta saka ƴaƴanta biyu kama Maanaal zuwa ciki, a haka doctor ya bisu bisa umarnin baba Sardauna.
Fin mintuna ashirin sannan doctor ya fito, zuwa sannan gidan ya ɗan lafa bisa tsawatarwar baba Haruna da basu jima da isowa ba. Doctor ya buƙaci ganin iya su Abah, amma gwaggo tace sam ba'a isa ba, ya faɗi duk ma abinda zai faɗa anan gaban kowa. Dan ita bata son munafunci. Ganin yanda take nema tada sabuwar tarzoma Baba Sardauna yace ya faɗa ɗin. Cikin damuwa doctor ya tabbatar musu amma Maanal fyaɗe. Kuma dole ai gaggawar zuwa da ita asibiti saboda jinin dake zuba a jikinta yana ƙara yawa. Wata irin kururuwar tashin hankali gwaggo ta fasa ita da sauran ƴan Giro, yayinda Oum ta yanke jiki ta faɗi. Dole aka kwashi Oum zuwa gida, Maanal da Ammie kuma asibiti.
Anan gidan su Oum ɗin ma dai a harmutsen yake. Ga Ajwaad ya kulle kansa a ɗaki anyi-anyi ya buɗe yaƙi. Sai da aka ɓalle ƙofar. Samunsa sukai kwance wanwar a ƙasa babu numfashi, ga jikinsa duk ya ɓaci da jini, shima dole aka kwashe shi zuwa asibitin....
_____________★
Komai ya dagule, dagulewa mai ban tashin hankali ga waɗan nan ahali guda biyu. Ɗaurin aure dai bai yiwuba washe gari. Dan anyi zama a tsakanin manyan ana tuhumar Ajwaad da tun a daren jiya ya farfaɗo akan wannan ruɗaɗɗen al'amari. Ya jima bai tankama kowa ba, kafin ya buɗe baki da ƙyar yace musu eh ya aikata.
Wannan amsawa tashi ta matuƙar birkita kowa. Ajwaad ɗan shekara ashirin da ɗaya a duniya, da yarinyar da suka rayu tun ƙuruciya. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un. Ran baba Sardauna a ɓace ya ce, “Shike nan tunda ya amsa ya aikata ɗin sai a ɗaura musu auren yau suma su tare kawai kamar sauran ƴan uwansa. Amma mi, a mamakin kowa sai Ajwaad ɗin ya shiga girgiza musu kai da faɗin, “Aure? Baba kuyi haƙuri ban taɓa kallon Maanal da sigar zama matar aure a gareni ba. Ita ɗin ƙanwata ce ai..”
Cikin ɓacin rai Baba Sardauna ya katsesa da faɗin, “Amma ka keta mata haddi?!!”.
“Kuskure aka samu”.
Ajwaad ya bada amsa babu ko ɗigon damuwa balle nadama a tattare da shi. Wani irin mari Abah ya fara sauke masa. Da ƙyar aka iya riƙesa dan hadda hauri ya fara kai ma Ajwaad ɗin. Da ƙyar aka samu ya zauna yanata zaginsa ga hawaye ba zuba masa. Tabbatarma Ajwaad yake dolene ya auri Maanal. Dan haka babu fashi za'a ɗaura auren yau ɗin na na su duka ukun. Zaram gwaggo tace sam bazasu haɗa zuri'a da su ba. Idan kuma har Babu ya amince babu ita babu shi har abada sai ta tsine masa wlhy..........✍️
_Tofa wannan fa shine rikici._
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖7️⃣4️⃣
______________
........Hankalin kowa ya tashi a falon. Aka shiga ƙoƙarin fahimtar da ita amma tace bafa zai yiwu ba, tana kan bakanta. Babu ya rasa yanda zai yi, jikinsa sai rawa kawai ma yake yi. Wannan ɓacin rai yasa Baba Haruna yanke jiki ya faɗi a falon, ga shi yanzu baida iko a kanta tunda babu aure tsakaninsu. Dama yana da hawan jini. Babu shiri aka kwashesa zuwa asibiti, sai dai kafin ma akai rai yayi halinsa ALLAH yay masa rasuwa.
Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, wannan rasuwa ta sake harmutse kowa. Duk yanda su Abah suka kai da son a sake zaman sassantawa bai yiwu ba. Dan baba Haruna kafin ya rasu yabar wasiyyar a maidashi tushensa a biznesa dan ALLAH. Wannan yasa tun a ranar kaf mutanen Giro har su Ammie da su Maanal dake a cikin wani birkitacen yanayi kama hanyar Kebbi. Kwana sukai a hanya, sai washe gari kusan sha biyu suka isa Giro. Haka aka sallaci gawar baba Haruna bayan an masa sutura aka kaishi makwancinsa na gaskiya.
A wannan zaman makoki ne aka fasa batun fyaɗe da akama Maanal. Tare da tabbatar da a dalilinsa ne baba Haruna ma ya rasu. Mutanen ƙauye sai addu'a. Nan fa zaman gaisuwa ya zama zaman ƙananun magana da tsogumi. Takai ko fitowa Ammie da ƴaƴanta basu isa yi ba. Dole suka koma ƙumshe kansu a ɗaki. Ga Ammie babu isasheiyar lafiya, hakama Maanal ta koma yin abu kamar wadda brain ɗinta ke neman taɓuwa. Sai ta nuna kanta ta fashe da kuka tana faɗin, “Ni! Ni! Maanal Ajwaad yayma fyaɗe. Ni Manaal Ajwaad ya lalatama rayuwa? Ni Manaal Ajwaad yace bazai aura ba, bai taɓa sona ba. Nima bana sonsa, ban taɓa sonshi ba ai”. Sai ta saka dariya, kota fashe da kuka. Tun su Shahidah na ɗaukar al'amarin wasa har ya fara basu tsoro. Ga Babu tunda suka zo baiko shiga sabgarsu ba. Ko kallo basu ishe shi ba. Haka itama Gwaggo. Ga Ammie a kwance babu lafiya. Sun rasa wazasu tunkara da matsalar Maanal ɗin ma. A haka aka gama zaman gaisuwa kowa ya watse sai al'ummar gidan. Maanal dama su Shahidahn kansu suka fara fuskantar sabuwar ƙyara da tsangwama da habaici ga mutanen gidan. Takai yanzu abincima babu mai basu, sai in an gama girki an ajiye tukwane subi dare suna karto ƙanzon tuwo. Wadda ta kamasu kuma ta shiga musu terere a gidan da kiransu ɓarayi. Haka za'a fito ana zaginsu da musu gorin iskanci. Wai suma su Shahidahn waya sani ko tuni an lalata su, ALLAH ne ya tona asiri akan Maanal ɗin. Abinda zai baka mamaki da tausayi Babu duk yasan mike faruwa. Amma ko'a jikinsa ta ɗansa kawai yake da amaryarsa. A haka suka cika wata guda a gidan cikin wata irin wahalliyar rayuwa. Sai Maanal ta wayi gari da zazzaɓi da ciwon ciki, sai amai. Wannan salonta ne a duk sanda zatai period, amma sai Gwaggo ta fasa kururuwa ta tara kaf jama'ar gida da maƙota. Kai harma da sauran matan anguwa da suka dinga shigowa da gudu. Batare da tayima kowa bayani ba duk wanda ya iso yaga Maanal dake jikin Shahidah na huttan amai data gama sai a hau ƙus-ƙus. Su Shahidah basu fahimci abinda ake nufi ba sai washe gari da zance ya fara yawo wai Maanal nada ciki. Wannan abu ya birkita su Amaal da Ammie dake kwance cikin matsanancin ciwo. Sai dai basu san suma ta hanyar da zasu tabbatar Maanal nada cikin ko bata da shi ba. Zancen cikin ya sake ƙarfafa ciwon Ammie matuƙa. Yayinda komai ya sake musu tsanani. Sati guda suna cikin wannan uƙuba ta mutanen gida dake zaginsu da cin zarafin su da gori manyan gidan suka taru akansu. A gaban kowa Baabu yay ma Ammie saki biyu ya zama uku, ya kuma ce subar gidan dan shi baima da tabbacin su Shahidah ƴaƴansa ne. Dan abinda ya faru da Maanal na nufin itama ƙila Ammie ɗin tanayi tun da can. In ba hakaba miyyasa yaran basa kama da shi sai ita, sai Maanal ɗin data ɗan ɗebo duhun fatarsa. Dan haka suje su baza'a haifa musu ɗan dakan kuka ba a cikin zuri'a.
Duk da halin da Ammie ke ciki haka ta dinga kuka tana roƙonsa da manyan gidan amma kowa ya nuna babu ruwansa. Sai ma fara watso musu kayansu da akai waje. Dole suka tattara abinda zasu iya suka fito. Da ƙƴar suka samu wani mai akori kura dake ɗibar icce a garin ya ɗakkosu zuwa Suru. ALLAH ya taimakesu da ƴan kuɗi a jikinsu da Amaal ta kwaso a ɗakin gwaggo. Haka suka samu motar Kano, kuɗinsu ma bai kai ba direban dai ya taimaka musu a hakan ganin Ammie da Maanal a halin ciwo. Dan Maanal tunda zancen tana da ciki ya ɓullo sai ta sake birkice musu.