Showing 60001 words to 63000 words out of 221978 words
Chapter 21 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
kicin-kicin ta sake yi da fuska sannan ta shiga gaishe da Director ɗin. Ya amsa mata da kulawa tare da mata barka da zuwa. Kanta kawai ta jinjina masa shi kuma yakai zaune yana ɗaukar file ɗinta ya shiga dubawa. Sai lokacin ta sake bin office ɗin da kallo daki-daki, idonta ta ƙarasa saukewa akan hoton AA ɗin, sai kuma ya janye ta maida kan ɗayan hoton dake kusa da nasa da bata kalla ba. Mace ce sanye cikin baƙin hijjab da niƙab, hatta idanun nata ana iya ganinsu ne kawai ta cikin sirrin farin gilashin data sanya. Hakan yasa baka isa tantance wacece a hoton ba duk iya kallon ƙurullarka da bin ƙwaƙwaƙwafi, dan hoton yasha editing ta yanda aka ɓadda kamanin komai.
A hankali ta taɓe baki da sake kauda kanta zuciyarta na ayyana ma maybe matarsa ce. Tunkuɗe tunanin tayi gefe ta maida hankalinta ga Director Mustapha dake mata magana. Umarnin biyosa ya bata, babu musu ta miƙe tare da ɗaukar hand bag ɗinta tabi bayansa. Wani office dake kusa da nashi suka shiga. Nan ma sun sami mai office ɗin daya kasance ba bahaushe ba. Bayan sun gaisa ya amshi file ɗin hannun Director Mustapha ya saka hannu. Daga haka suka fito. A ƙofa suka haɗu da wani matashin saurayi, cike da girmamawa ya shiga gaida Director. Shima ya amsa masa da kulawa yana nuna masa Maanal.
“Itama Watch Designer ce, kaje da ita department naku, sit ɗin da aka shirya jiya nata ne”.
Fuskar saurayin da murmushi yana kallon Maanal ya amsa ma Director da girmamawa. Ita ko sai wani basarwa take. Bai damu ba ya fara gaidata, sai ta amsa kamar wadda taji kunya. Shi dai director kallonsu kawai yake yana sake jinjina miskilancin yarinyar.
Saurayin daya kira sunansa da Yaqub tun'a cikin Elevator ɗin ya gabatar mata da kansa matsayin Watch Designer shima. Ɗan murmushi kawai Maanal ta masa. Dan ta fahimci yana da nutsuwa. Koda suka fito anata kallonsu, bata damu ba dan ita babu wanda take kallo har suka iso rukunin su daya kasance matsayin office. Su takwas ne, kuma duk artists ne suma ɗin, sai dai abin damuwar ita kaɗai ce mace a cikinsu. Amma sai ta dake, dan tasan zata iya zama da kowa. Ta gaishesu tana sake ɗaure fuska ganin yanda suke kallonta. Yayinda Yaqub ya gabatar da ita a wajensu shi dai. Suma ya shiga gabatar da su da sunayensu ɗaya bayan ɗaya. Kafin ya nuna mata wajen zamanta dake a farko. Sun mata maraba da zuwa cikin farin ciki, itama sai ta ɗan musu murmushi kaɗan. Daga haka takai zaune tana dudduba komai nata dake a wajen. Batare data damu dasu ba kuma wayarta ta ɗauka ta shiga ɗaukar komai na iya wajenta hoto, Ammie ta turamawa, alamar wayar a hannun Ammie take mintuna biyu ba'a ƙullaba sai ga video call ɗin Ammien ya shigo. Murmushi mai sanyi Maanal ta saki tana mai gaggawar amsa kiran sai ga Ammie tar-tar ta fito. Cikin murmushin farin ciki Maanal tace, “Uhm kaga amaryar Daddy”.
Daƙuwa Ammie tai mata itama tana murmushin ta ce, “Ungo naki nan ja'ira yau kuma nice bar tsokanrki”.
Karo na farko Maanal ta sanya dariya, abinda kakan daɗe a yanzu baka gani ba a tare da ita. Duk ko sai samarin suka shagala suna kallonta duk da su basa ganin Ammie sabo a desk ta ɗaura wayar. Ita ko cikin rashin damuwa da wanzuwar su a wajen tace da Ammie, “Tom yi haƙuri Hajiya Ammie na. Ina fatan kin tashi cikin aminci da ƙoshin lafiya tare da farin ciki a wannan rana ta laraba ranar samu inji Nene”.
Sosai murmushin Ammie ya sake ƙawatuwa. Da kulawa ta ce, “Alhamdullah Auta. Ya ƙarfin jikinki? Ya kuma sabon office?”.
“Alhamdullahi Ammie na warke abuna. Sabon office kuma gashi ki sanya masa albarka daga bakinki mai tsarki”. Tai maganar tana miƙewa da wayar a hannu ta maida back camara tana haska mata ko'ina na office ɗin, sai dai koda wasa bata yarda ta hasko samarin nan ba. Sosai Ammie ta shiga yabawa da sanya albarka. Ta kumayi addu'oi sosai ga autar tata. Sannan suka ɗan yi hira sukai sallama tace ta fara aikinta. Fuskarta da murmushi ta ajiye wayar, ita kaɗai tasan irin tari-tarin ƙaunar da takema wannan baiwar ALLAH. Mahaifiyarsu dabance a cikin daban ɗin da bazai ƙididdigu a zukatansu ba. Fatansu dai ALLAH ya ƙara mata lafiya da nisan kwana masu albarka. (Tare da iyayenmu baki ɗaya. Ka gafartama wanda muka rasa ka yafe musu KURAKURANSU😭🙏 damu da muke raye baki ɗaya).
Jan kujerar tata tai har zuwa gaban kantar da aka ajiye musu a office ɗin dan kusan da ita ma aka zagaye wajen. Komai na kayan zane-zanen da zasu iya buƙata akwai a wajen. A haka ta zazzaɓo duk abinda take buƙata a lokacin ta sake burko tayoyin kujerar ta dawo da ita mazauninta. Sosai ta ringa ƙoƙarin ture komai a ranta ta maida hankalinta ga fara abinda ya kawota duk da tana ji a jikinta sauran abokan aikinta hankalinsu na a kanta ta wani sharesu tamkar ita ɗaya ce a wajen.
Wani zanen Designs na agoguna data ƙirƙira yanzun nan a kanta ta fara cike da ƙwarewa. Cikin ƙanƙanin lokaci ya haɗa su tsaf su biyu kamar ka saka hannu ka ɗauka daga takardan. Bayan ta gama zana su a dunƙule sai kuma ta koma zana ɓangare-ɓangare ɗin jikinsu kowanne tana saka masa suna da amfanin da zai yi a cikin agogon. Hakanne ya ja mata lokaci sosai dan har ƙarfe ɗayan rana. Jin ana kiran sallar zuhur daga masallacin cikin companyn ya sata sauke ajiyar zuciya da ajiye kayan aikin nata ta miƙar da hannunta da ya ɗan sage da ambaton sunan ALLAH.
Miƙewa tai zuwa window ɗin office ɗin ta leƙa batare data ma kowa magana ba, dan daga wajen ana hango masallacin. Hango ma'aikata tayi nata fita zuwa ƙatuwar harabar companyn. Ganin mazansu da matansu ne yasa ta fahimci masallacin harda mata kenan. Dan wasu ma na ƙoƙarin shigane yayinda wasu suka kasance rukuni-rukini suna hirarsu. Sai wasu dake alwala ta can ƙarshen katangar inda aka tanada domin hakan. Huci taɗan furzar daga bakinta tare da barin wajen, dai-dai suma su Yaqub na miƙewa. Sauran fita sukai gulma fal bakinsu, yayinda shi kuma Yaqub yazo inda take.
Shine ya sanar mata tazo suje salla. Kanta kawai ta jinjina masa ta baro wajen ALLAH ya sota ta taho da hijjab kasancewar yau ma shigar Abaya ce a jikinta ƙirar Dubai ruwan ƙasa. Hijjab ɗin ta buɗe ta saka bayan ta zame hularta da ɗan kwalin abayar data naɗo a kanta ta ajiye saboda hijjabin ya rufe mata gashinta sosai. Hankalinta kwance kuma kanta tsaye ta fito a office ɗin daga ita sai wayarta kawai a hannu. Kusan duk an fice ma, dan wajen yayi tsitt, dan haka a gaggauce ta nufi elevator jin za'a tada sallar kasancewar su suna a 4th floor ne. Bata gama dai-daita tsaiwarta ba kawai taji shigowar mutum babu ko sallama. Dan haka ta ɗago manyan idanunta domin ganin wane sallamemmen ne haka........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖2️⃣8️⃣
.......Saurin janye idanun nata tai ƙirjinta na wani masifar dokawa. Sai dai ta wani dake a zahiri yayinda fuskarta ke sake komawa ciɗin-ciɗin fiye da yanda tashi take. Boss ne da kansa ba wani ba. Wato AA Darma, da alama shima ya makara fita sallar ne, dan illahirin fuskarsa da hannayensa da ƙafarsa dake sanye da slippers daya saka dan ba takalman da yazo dasu a ƙafarsa bane cover shoes sai nason ruwa suke yi. Elevator na tsayawa itace tai saurin fara ficewa dan harga ALLAH jinta take kamar an matse a cikin rami tsabar yanda ya cika ko'ina da kwarjininsa. Da kallo ya ɗan bita, sai kuma miya tuna oho yay saurin janye idanunsa shima yana fita daga elevator ɗin.
Dukansu basu samu raka'ar farko ba. Koda aka idar da sallar mafi yawan ma'aikatan sun wuce kitchen ne kai tsaye, dan ana musu abincin rana a wajen harma dana safe. A manyan dai ba kowa ne ke nufar kitchen ɗin ba sai wanda yaso hakan kasancewar suna da damar sakawa a kawo musu har office. Manaal ma daba gama sanin tsarin tai ba duk da an bata komai a rubuce tun a ranar interview karantawa ne batai ba office ta koma. Hankalinta a rarrabe sai dai tana iya ƙoƙarin ta na ganin ta saita kanta ta buɗe lunch box ɗinta ta fidda abincinta ta hau ci tana cigaba da sarrafa computer ɗinta domin maida aikin zanen da tayi a ciki. A haka a shiririce ta gama shigar da komai kafin ta naɗesa a flash drive ta ajiye. Koda an buƙacesa a wajen meeting da shi zatai amfani. Knocking ƙofar akayi, batare da ta canja daga yanda take ba ta bada iznin shigowa dan ita kaɗaice har yanzu su Yaqub babu wanda ya dawo. Wata budurwa ce da bazasu wuce sa'anni ba. Sanye take da skirt da riga na atamfa sai ɗan mayafi data yana. Cikin girmamawa ta gaishe da Maanal ɗin. Amsa mata tai da kulawa. Hakan sai ya saka yarinyar farin ciki dan yanzu ake gulmar Maanal ɗin a ƙasa cewar dagani zatayi girman kai, sai kuma ita tazo taga ba hakan ba yanzu.
“Sunana Mabaruka Rabi'u. Ina ɗaya daga cikin Sales and Marketing Department. HOD ne yace a sanar miki ana buƙatarki a ƙasa idan babu damuwa”.
Cikin ɗan sakewar fuska da ba murmushi take ba Maanal ta ce, “Okay sister Mabaruka ba damuwa gani nan tafe”.
Murmushi Maburaka ta mata tare da sake ɗan rissinawar girmamawa ta furta, “Na barki lafiya”. Daga haka ta fice a office ɗin. Ajiyar numfashi Maanal ta ɗan sauke, sai kuma ta shiga tattara tarkacen kayan da taci abinci ta maidasu a lunch box ɗin. Ruwa tasha ta ɗan gyara fuskarta sannan ta miƙe ta fice a nutsenta daga ita sai wayarta a hannu. A First floor ta samu kusan dukkan ƙananun ma'aikatan harda waɗanda ba nan ɗinne mazauninsu ba. Sai dai da'alama duk an tattarasu anan ɗinne dan har su Yaqub ma suna a wajen ashe. Duk da cika mata idon da sukai haka ta dake ta gaishe da HOD dake ta faman sakar mata murmushi. Yana ɗaya daga cikin wanda sukai mata interview. Amsa mata yay da kulawa, kafin ya juya ga ma'aikatan yay sallama. Duk amsawar sukayi duk da kuwa ba dukane musulmai ba a wajen. Ɗan juyowa yay tare da nuna musu Maanal cikin harshen turanci ta ce. “Wannan itace sabuwar _Watch Designer_ ɗin Mawaad Company da aka sake ƙaro mana in sha ALLAHU, zatai muku introducing kanta”.
Tafi suka shiga yi gaba ɗayansu. Hakan yasa Maanal ɗan sakin murmushi tana binsu da kallo, sai da suka lafa sannan ta gyara tsaiwarta cike da nitsuwa ta furta, Sunana Maanal Habeeb Giro. Junior Watch Designer kamar yanda aikina HOD ya faɗa. Ina fatan zan samu haɗin kai da yarda daga gareku baki ɗaya”.
“In sha ALLAHU!!”.
Suka faɗa cikin haɗa baki. Murmushi ta sakar musu a karo na biyu mai matuƙar taushi. Sai kuma ta haɗe hannayenta waje guda ta sake furta, “Ina mika godiya a gareku da fatan alkairi baki ɗaya. ALLAH ya bamu ƙwarin gwiwar sauke hakkin dake kayinmu baki ɗaya”.
Nan ma sun amsa mata da amin. Daga haka HOD ya ɗan ƙara mata bayani akansu. Kafin ya sallamesu kowa ya koma kan nasa aikin. Ita kuma suka nufi elevator tare da shi. Sai faman zuba mata surutu yake ita dai batace komai ba sai ɗan murmushi da take masa na karar haɗuwar farko. Conference room suka nufa kai tsaye daga nan. In da ta sami dukkanin shugabannin da alama su ake jira ma a wajen. Wajen zama duk suka nema, a dai-dai kuma lokacin CEO ya shigo AS ɗinsa biye da shi. Duk miƙewa sukai alamar girmamawa, sai da ya zauna AS ɗinsa ya ajiye masa kayan hannunsa gabansa sannan ya ɗan ɗago ya dubesu. Zaunen suka kai suma a nutse, daga haka room ɗin yay ɗan shiru na kusan mintuna uku kafin ya ajiye tab ɗin hannunsa da yake sarrafawa yay gyaran murya yana kallonsu cike da dakewa da nutsuwarsa. Suma sake nutsuwar sukai da maida hankalinsu garesa. Banda Maanal da tun kallon farko data masa a sanda yake shigowa ta ɗauke kanta bata sake ba. Gaba ɗaya jinta take a takure a wajen dan su biyu ne kawai mata. Sallama yay musu kafin ya sauke dubansa ga tab ɗin gabansa ya fara magana acan ƙasan maƙoshi. “Wannan taro ne daya haɗa ɓangarori guda biyu, wato na shugabanni da kuma ƙirƙira da zane na wannan company. Wato Executive Team da kuma Design and development. Kafin kai tsaye mu fara abinda ya kawo mu akwai sabuwar staff data shigo cikinmu zai ƙyautu ta gabatar da kanta anan”.
Ji Maanal tai kamar ta kai masa naushi dan haushi, amma sai ta dake taƙi koda motsi sai da CTO dake gefenta yay mata magana ƙasa-ƙasa. “Sistet Maanal”.
Komai batace ba ta miƙe cike da kamewa ta furta, “Sunana Maanal Habeeb Umar Giro. Junior Watch Designer in sha ALLAHU”.
Sunyi welcoming nata baki ɗaya tare da mata fatan alkairi. Bayan ta koma ta zauna ya cigaba da faɗin, makasudin shi wannan zaman akan sabon project namu ne in sha ALLAHU. Wasu sun san da shi wasu basu sani ba saboda rashin samun zaman meeting da ba'aiba a wancan satin gaba ɗaya. Akwai Companyn da zamu fitar ma sabon agogo, sun kuma bamu zaɓi kafin mu sake zama dasu. Dan haka Design and development ko kuna da wani sabon design da zaku gabatar mana mu duba?”.
Bayan Maanal akwai Watch Designers Directors har uku a wajen, sai dai dukansu kowanne nada iya limit ɗin aikinsa ta yanda baya shiga aikin wani. Hakan yasa ɗaya daga cikinsu ɗagowa ya ɗan dubi Boss ɗin. “E to Sir bamu san ko yaya tsarin project ɗin zai kasance ba. Sai musan a cikinmu wazai bada sample”
Kansa ya ɗan gyaɗa, sai kuma ya kai dubansa ga Sales and Marketing Manager. Da sauri ya miƙe dan yasan minene ma'anar kallon. Bayani yay a taƙaice, Dan haka sai duk suka maida hankalinsu ga Director Steven. Kansa ta gyaɗa shima tare da maida kallonsa ga Maanal, suma sauran duk sai suka koma kallonta. Yanda suke kallon natane ya bata mamaki, kafin ta nema ƙarin bayani Director Steven ya ce, “Wannan aikinki ne Sister Maanal. Idan kinada wani sample na zane a ƙasa company na buƙatar gani, idan kuma babu zaki iya neman lamanin samarwa”.
Gaba ɗaya sai Maanal taji ma kamar zata daburce. Amma ta shiga ambaton ALLAH tare da aro jarumta. Cikin ƴar dakiyar da nutsuwar data azama kanta ta dole ta bata ta jinjina ma Director kanta. Sai kuma ta ɗan kallesu itama ta fara bayani. “Zan iya gabatar da wanda ke a hannuna ɗin idan basuyi ba sai na sake wasu sabbi”.
Cikin gamsu duk suka gyaɗa mata kai, kafin boss ya gama shan ƙamshinsa batare daya kalleta ba ya furta, “Zaki iya nunawa”.
Bata tanka ba, sai dai ta miƙe hannunta ɗauke da flash drive data naɗe zanen ɗazun da tayi. Amsa Director Steven yayi a matsayinsa na shugaban sashenta, ya nufi ƙaton television dake kusan bango guda a room ɗin yay connecting, atake ɗan tambarin data saka na farko mai ɗauke da zanen agogo mai ƙyau da zanen fuskarta a tsakkiya ya bayyana. Remote ɗin Director Steven ya miƙa mata, dole ta fito daga inda take tsaye ta koma gaban tvn. A nutsenta ta fara danna hoto na biyu ya fito, agogone mai ƙyau da tsari matuƙa duk da kasancewar a zane yake. A take duk suka shiga ambaton, “Woow!! Woow!!” a hankali. Shi dai boss kaimai baice ba, amma fa ya zubama hoton idanu yanda ya kamata, bayani tayi cikakke akan agogon da tsarinsa da nauyinsa. Sai kuma ta koma nuna sassan jikinsa da sunayen data basu da yanda yakama ace ingancinsu ya kasance. Da ƙarshe tai bayanin yanda agogon zai iya buƙatar ingantaccen aiki kafin fitar da shi. Tafa mata suka shigayi tamkar conference room ɗin zai buga shima. Dan har ga ALLAH tayi matuƙar gama birgesu, tayi dukkan bayanin da har sauran ɓangarorin zasu iya yi. Ashekaru kaf ɗinsu babu wanda bai bata fin shekara goma zuwa ashirin ba, dan itace ƙarshen ƙanƙanta da ƙarancin shekaru a cikin nasu, hatta da ɗayar macen zata iya girmar Shahidah ma balle ita. Taji daɗin yanda suka yaba mata duk da shi mai gayya da aikin baice komai ba dai. Sai da duk suka lafa itama ta dawo ta zauna a nata mazauni kafin yay ƴar gyaran murya.
“Zamuyi nazari akan wannan ɗin, amma WD Maanal zata iya samar mana da wasu samples kamar uku bayan wannan daga nan zuwa gobe