Showing 108001 words to 111000 words out of 221978 words

Chapter 37 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

masu taushi hakan bai hana bayyanar tahowarsa ba. Ga wani mayataccen ƙamshin turarensa mai ratsa zuciya na rige-rigen shiga hancinansu tun kan su fara ganinsa.
Ai tuni zuciyar Huznah ta fara gudu a ƙirjinta, yayinda take satar kallon hanyar ƙofar upstairs ɗin ta gefen ido. Bayan wasu ƴan sakanni ƙofar ta buɗe slowly, ya bayyana garesu. Sanye yake da wando da riga duk baƙaƙe masu kamar kayan sanyin nan dan harda hula a bayan rigar, sai dai bai saka ba ya saketa a dokin wuyansa ta kwanta. Sam babu wasa ko alamarsa a saman fuskarsa datai wani irin fayau ya ƙara haske. AA ba fari bane, amma yanada hasken fata da ko'a cikin baƙaƙen irin baƙin nan ne mai matuƙar ƙyau da shining ga wani glowing da yake tamkar jinin mutanen ƙasar Labanon. Yanada hanci dayay dai-dai da tsarin tsaka-tsakin fuskarsa daba doguwa can ba, ba kuma faffaɗa ba. Ga shi da cikar gashin gira dana ido da ko wata macen bazata nuna masa eyelashes ba. Kwantaccen gashin sajensa daya zagaye har matsaikaitan lips ɗinsa pink shine yafi komai sake ƙawatashi. Kamar koda yaushe idanunsa manne da eyeglasses ɗinsa fari ƙal da kamar ba'a amfani da shi na ƙara ƙarfin gani. Yanda oily idanun suka sake wani fita tar-tar kamar an watsa ruwan madara sabon tatsa dole kaji wani iri idan ya kalleka da su. Gashi dogo masha ALLAH.
Tunda ya gama sakkowa kallon kowa baiyi a cikinsu ba. Sai takowa da yay a hankali zuwa cikin falon sosai. A kujerar farko dake bangon daya fito ya zauna kawai, sai a lokacin ya ɗan dubi Abdull dake gaishesa cike da girmamawa. Cikin yanayin ɗan zuba masa ido batare daya amsa gaisuwar ba ya ce, “Ango ne a gidan namu”.
Murmushi Abdull ya saki mai ƙayatarwa tare da duƙar da kansa yana sosa ƙeya. Cike da jin nauyi ya sake gaida AA ɗin. AA ya girmi Abdull sosai, dan shi a yanzu bazai wuce 26+ ba gaskiya. Kawai dai an masa auren gata ne. Sai yanzu AA ɗin ya amsashi da tambayarsa iyalin. Sake duƙar da kai Abdull yay da faɗin, “Ai Uncle gata nan ma tare mukazo dubaka”.
Batare da AA ya kalli inda Abdull ɗin ya nuna ba ya furta, “Oh Masha ALLAH, Thanks”.
Gaisheshi Yaseerah ta shiga yi da tambayarsa yaya jiki, ya amsa mata a taƙaice still dai bai kalleta ba. Dan kowa yasan wannan kam ba ɗabi'arsa bace kallon mata ko'a sanda yake a ganiyar samartakar balaga balle yanzu da wasu dalilai suka saka shi sake kame kansa ga komai, dan AA akwai tsantsar kame girma, ko wanda suka girmesa sukanga ya cika musu guri balle wanda ya girma. Sai a lokacin Huznah data kasa numfashi mai ƙarfi ta fara gaisheshi itama, AA akwai iya haddace muryan mutane da riƙeta idan yaso, dan haka ya ɗan kalla sashen da suke a karo na farko, a mamakinsa kuwa wadda yay tsammanin ce. Wato budurwar yarinyar nan mai shegen naci da iyayi data takurama rayuwarsa a kwanakin nan. Ƙoƙarin janyewa yake suka haɗa ido da Mamy data kafesa da nata idanun. Sai kawai ya kautar da kan nasa cike da basarwa. Haka kawai Mamy ta saki murmushi. Dan ta tabbatar da abinda take son tabbatarwar, da gaske AA ɗin yasan Huznah ba ƙarya sukai masa ba. Saheeba ma dai sai faman raba idanu take a tsakanin Mamy da AA da Huznah. Itama kuma taga reaction ɗin AA ɗin a sanda Huznah tayi magana. Tuni hankalinta ya ƙara tashi, wani kalar tsanar Huznah na ratsa zuciyarta.
AA ne daya miƙe ya katsema kowa tunaninsa. Dan hankalinsa kwance ya nufi ƙofa, sai da ya kama handle ɗin batare da ya juyo ba ya furta, “Abdull thanks you ALLAH ya baku zaman lafiya”. Daga haka ya shige tare da maido ƙofar ya rufe. Kusan lokaci ɗaya Yaseerah da Huznah suka saki ajiyar zuciya. Dan ita kanta Yaseerah ɗin sai yau da take ganin AA ɗin da ƙyau. Rayawa take a ranta (Ashe haka guy ɗin ya haɗu, ya subahannallah mutum kamar shi ya zana kansa da ƙyawu. Ga aji ga kwarjini. Wannan shine irin mijin da take fatanma kanta, dan Abdull yana da ɗan irin qualities ɗin kaɗan shiyyasa ta aminta da shi. Ashe ga inda ake mazan nan na gaskiya. Ya ALLAH gaba ɗaya an wargaza mata dukkan lissafinta. Sai a yanzu ta sake tantance abinda ya haukatar da Huznah ashe). A ɓangaren Huznah ma sambatu kawai take zubawa a zuciya. Wani irin ƙyau da kwarjini AA ɗin ya sake mata. ALLAH badan kar ace tayi ƙarya ba daya kalleta da wannan idanun nasa mai kamar an watsa madara da oil a ciki kaɗan ya rage ta suma. Kai dole dole ne ma ta mallaki mutumin nan, idan ba hakaba zata iya rasa ranta.
Da ire-iren wannan tunanin suka koma sashen Mamy, kasancewar lokacin sallar Asr yayi Abdull ya wuce massallaci. Su kuma Mamy ta haura dasu sama a ɗaya daga cikin bedrooms ɗin ta tace suyi salla. Ita kuma ta nufi nata.....


____________★


Senator Bukar dai yaje Kebbi cikin garin Giro, bai kuma sha wahalar samun ainahin gidan kakannin su Maanal ba. Dan gidane sananne a cikin garin. Alhamdullah kuma ya samu tarba irin wadda bai mayi zato ba. Dan cike da farin ciki suka dawo garin Abuja dama jirgi yabi shi da Rabilu da Oler. Yanda yake ta famar washe baki da zumuɗi ya saka uwargidansa a tashin hankali, dan ta tabbatar ya samo abinda yake so. Batace da shi komai ba yay shiri ya wuce gidan matarsa ta biyu dan yau itace da shi...
Itama dai a yau ya zazzage mata batun ƙarin aurensa, a ɓangarenta mace ce mara haƙuri da iya shanye abu, dan haka tun a daren sukaci uwar watsi ƙarshe kowa a part ɗinsa yay barci. Dan ya tabbatar mata akan Maanal fa zai iya saita mata hanya ne shi ba damuwarsa bane. Dole taja bakinta ta kulle dan tasan kaɗan daga abinda zai iya aikatawar kuwa.....


_Ikon ALLAH miya faru a Giro🥱 to?._


_____________★


Yanayin da take jin jikinta Alhmdllh yasa ta ce Shahidah taje gida kawai ta huta yau zata kwana da nurse. Da har Shahidah ɗin taƙi Dr Ranjet yace karta damu taje ɗin. Dama asibitin bawai suna barin masu jiyya bane ba ai kawai dai sune oga ke bari. Zuwa yanzu Shahidah ta fahimci asibitin nan mallakin RK ne. Duk da yanata dojewa bai son su sani. Dan haka koda Dr Ranjet ya ce ogan ta fahimci RK ɗin yake nufi.
Mijinta ne yazo ya ɗauketa, basu tafi ba sai da ta tabbatar ta mata duk abinda take buƙata duk da jikin nata Alhmdllh sannan. Bayan tafiyar tasu Maanal ɗin na zaune tana karatun novel ɗin data ɗauka na AA ranar a office ɗinsa, dan yau ta matsama Shahidah ta kawo mata shi asibitin tare da glass ɗinta. Sosai take zumuɗin karatun book ɗin saboda labarinsa da aka bata. Tayi matuƙar zurfi a karatun dan tana jin daɗinsa, bata damu da shigewar lokaci ba dan kusan 11 ma da rabi. Sai can ƙasan zuciyarta dake ɗan kawo mata tunanin ina RK, rabonta da shi tun safe da ya shigo ya dubata a gaggauce ya fice. Tana son tambaya tana tsoron kar Didi tai mata wata fassara daban dan haka taja bakinta tayi shiru. Sai dai lokaci-lokaci yana zuwa mata a rai.
Kaɗan-kaɗan wani irin daddaɗan ƙamshin turare ke shigo mata hanci, tun tana fuskewa da cigaba da karatunta har dai yanda turaren ke sake ƙarfi a ɗakin ya addabeta. Cikin nutsuwarta da rashin rawar kai ta ɗago idanunta kaɗan tana bin ɗakin da kallo, dai-dai saukarsu inda ƙofa take ƙirjinta yay wani irin motsawa alamar zuciyarta tayi zallo. Sosai ta zuba masa ido tana masa kallo irin na mamaki ko ruɗani zamuce oho. Sai dai fuskarta a dake babu alamar wani shock a kanta. Sai ma janye idanun tai a slowly ta maida ga littafin kamar bataga komai ba.
Gently shima ya lumshe nasa oily idanun da ke a ɗan kumbure kaɗan da kuma ɗan sirkin ja a cikinsu dan har yanzu basu komai dai-dai ba saboda ciwon kai yaƙi barinsa. Sai dai da ɗan haskensu fiye da jiya da yake a halin ciwo sosai. Sake buɗesu yay a kanta yana mata wani irin kallo mai wahalar fassara. Fin mintuna biyar suna a haka baka jin komai a ɗakin sai sanyin ac da aka saka mata kaɗan daya gauraya da ƙamshin mayataccen turarensa mai kashe garkuwar jiki. Gaba ɗaya kallon ya gundiri Maanal, dan jinsa take har cikin ɓargon jikinta da magudanan jini. Tuni ta daina karatun kallon rubutun kawai take, sai dai fuskarta ta sake tsukewa.
A cike da ƙasaita ya miƙe daga jinginar da yay a jikin ƙofar hannayensa duka zube cikin aljihun farin jeans ɗin sa, daga sama ma baƙar rigace mai hi neck data ɗame masa murɗaɗɗan jikinsa, sai dai ya kawo jacket mai ƙyau baƙa da adon fari kaɗan a jikinta ya ɗaura. Kasancewar zip ɗin gabanta a buɗe yake har ƙasa ne ya bayyana rigar cikin da faffaɗan ƙirjinsa zuwa lafaffen cikinsa. Yanda yake takowa takalman ƙafarsa masu ƙyau da ɗaukar hankali na bada ƙara haka zuciyarta ke motsawa a ƙirjinta da ƙarfi. Cike da izza ya tura kujerar gaban gadon gab da gadon sosai da ƙafa, kafin ya matsa gab da gadon har Maanal najin tamkar zai faɗo mata akai sannan ya kai zaune. Yanda ya ɗan rankwafo a kanta sanda zai kai zaunen yasa hucin numfashinsa dakar fuskarta, yayinda ƙamshinsa ya gama mamaye illahirin iskar da take shaƙa. Dole ta ambaci sunan ALLAH a zuciyarta.
Anan ɗin ma zaman ƙasaitar yayi, dan ya wani harɗe ƙafafu ɗaya kan ɗaya tare da kwantar da bayansa a jikin kujerar hannayensa duk biyu dafe da hannuwan kujerar. A har yanzu ɗin ma idanun nasa na'a kanta ne sai faman lumshesu yake da buɗewa daga cikin fari tas ɗin gilashinsa dake sake ƙawata masa fuska. Rumtse idanu Maanal tayi tana mai danne dukkan abinda ke yunƙuro mata. Batare data sake ko kallon sashen da yake ba a kausashe, a kuma tsiwace ta furta, “What are you looking for here?”.
Maimakon bata amsar data buƙata sai kawai ya zuba ma lips ɗinta idanunsa har adams apple ɗinsa na ɗan motsawa a maƙoshinsa. Wani irin takaici ne ya sake ratsa Maanal. Tai wani irin juyowa da rinannun idanunta da suka juye lokaci guda ta saukesu a kansa. Slowly shima yaja nashi dake kallon lips ɗinta ya daidaitasu a cikin natan. Kallon cikin tsakkiyar idanu sukema juna. A hankali a hankali na Maanal suka fara ƙyalli alamar taruwar hawaye. Wani ɗan iskan murmushin gefen baki ya saki yana sassauta girman idanunsa dake cikin nata. Tamkar wanda akama dole ya motsa lips da Muryar nan nasa can ƙasa-ƙasa kamar abin dole ya furta, “Because you need me”.
“Never! Har abada kai baka cikin abinda rayuwata take buƙata Ajwaad”.
Wani ɗan killer Smile ya saki yana mai janye idanunsa gefe, fin sakan biyar sannan ya sake juyo da idanun nasa a kanta. “Really! You don't need me in your life?”.
“Kana tantamar hakan ne?”.
Ta faɗa a zafafe.
“Sosai ma kuwa? Inda har baƙya buƙatata in you life kuma da baki cigaba da ajiye wannan ba”. Ya ƙare maganar yana buɗe tafin hannunsa wani sliver agogo ya bayyana. Kallon agogon take zuciyarta na bugawa da ƙarfi a cikin ƙirjinta, agogonta ne fa, agogon da ta saka a randa zasuje Zaria ita da Ammie da Yaya Yazeed da Amrah. Tabbas tasan ta ciresa a hannunta, daga haka bata sake tuna ina yake ba. Kai hankalinta ma sam bai kai garesa ba sakamakon haɗuwa da RK da tai acan ya harmutso ta.....
“Hyy”.
Ya katse mata tunani cike da son tunzurata. Harararsa kuwa tayi ta ɗauke kanta gefe batare da ta ce komai ba. Murmushin sake samun nasara ya saki kaɗan yana wani ƙanƙance idanunsa a kanta.
“Wannan pretending ɗin naki ya isa haka. K Bestyn AA ce har yanzu, ko ki yarda ko karki yarda idanunki na nuna hakan ga kowa......”
Wani irin wurgar da littafin hannunta tayi, a bazata kawai ta ganta a gabansa ta dirgo daga gadon. Wani irin lumshe idanu yay ya sake buɗewa sakamakon shigar ƙamshinta mai daɗi cikin hancinsa. So yana matuƙar son traditional perfumes, zai iya cewa ma itace ta koya masa amfani da su ita da Oum..........✍️












✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖4️⃣8️⃣




______________




........Akan ƙyawawan ƙafafunta da ƙumbunan ke a gyare fes-fes suna ƙyalli ya saukesu. Kafin ya tafi da kallonsa har saman baƙin wandon data saka irin mai manne jikin nan, yana gab da gwiwarta rigar asibitin ta bayyana, itace har zuwa sama fara da ɗigo-ɗigon jaa, tsabar neman magana da salon iskanci ya wani sauke a saman ƙirjinta ya kafe wajen da ido tare da ɗan datse lips ɗinsa. Da sauri ta koma saman gadon taja bargo ta lulluɓe jikinta gaba ɗaya tana furta, “ALLAH ya isa wlhy da mun kallon da musulunci ya haramta”.
Murmushi yay mai fidda ɗan sauti sai dai sam haƙwaransa basu bayyana ba. Sai kuma ya taɓe bakinsa cikin halin ko in kula ya furta, “Daga baya kenan. Idan kin manta bari na tuna miki na san komai A to Z tun kan ki zama abin kallo. Ko kin manta wannan hannun ya miki wanka, ya wanke miki pupu, ya share miki majina, ya wanke miki pants, ya wanke miki blood na period. Ya.....”
“That's enough malam. Kuma ka bar ɗakin nan tun kafin na maka ihu wlhy.”
Murmushi ya sake yi yana taɓe baki da wani ɗan ɗage gira. Babu alamar zai ma motsa balle yayi abinda tace ɗin. Saima cikin tsareta da idanunsa da suka kaɗe ga jijiyoyin kansa duk sun sake fitowa. Muryarsa can ƙasa ya ce, “Ke baki gajiya da faɗa? Why are you being stubborn ne?”.
Harara ta balla masa da faɗin, “Anyi faɗan da taurin kan, in baka son a maka ka fita rayuwata mana”.
Sai da ya ɗan lumshe idanu ya buɗe akanta. Yanda yake mata wani shegen kallo tamkar idanunsa zasu narke a kanta ya saka tsigar jikinta tashi, kauda kanta tayi gefe da sauri, shi kuma ya ɗan ciza lips ɗinsa yana wani jan numfashi a hankali.
“Nima ki fita tawa rayuwan mana. Kinbi duk kin hanani sukuni, kin hanani aure, kin sa duk nabi na tsani yaran mutane babu hujja”.
Ai bama tasan sanda ta wara manyan idanunta a kansa ba tana harararsa, rasa abin cewa yasata faɗin, “ALLAH zai saka min sharrin nan da ka min”. Sai kuma ta sake sakkowa a gadon tare da fisgan hijjab ɗin sallarta ta saka. Ƙofa ta nufa fuuu dan gara dai ta bar masa ɗakin kawai sai yaci kansa yasha baƙin ruwa. Sai dai me ƙofar gam alamar saida ya rufe sannan. Ranta ne ya sake ɓaci, har takai hannu zata bubbuga sai kuma ta fasa saboda tunawa a asibiti suke kada ta shiga hakkin sauran majiyata. Dawowa tai inda yake cikin da tsantsar masifa da tsiwa ta balbalesa da masifa.
Yanzu kam gaba ɗaya dauriyarsa ƙwacewa tai, dole ya kai hannu saman kansa dake wani irin sara masa da masifar ƙarfi ya dafe, dama tuni dauriya kawai yake yi, shi kaɗai yasan azabar da kan nan ke masa, dan shi dama a ciwonsa ciwon kai yafi yawa. Sam masifa ta rufema Maanal ido, sai cigaba da zazzaga masa take, “Please Besty my head ki daina min ihu”.
“Anƙi a daina, tunda baka so ka fita mana, waya kawo ka nan ɗin?”.
“Ya ALLAH” ya faɗa da wata sassanyar murya yana kai ɗayan hannun ma ya tallafe kan gaba ɗaya. Dan da gaske ji yake kamar kwalwar ciki zata zazzago.
A karo na farko gaban Maanal ya faɗi, dan yanda ya kira sunan ALLAH ɗin da tallafe kan sai kuma hankalinta ya tashi. A hankali ta fara haɗiye masifar tata tana kallonsa. Yayinda shi kuma ke cigaba da jujuya kansa a cikin hannayensa yana cigaba da kiran sunan ALLAH, sai kuma ya koma faɗin, “Please Besty my head, kaina Besty zai fashe ki riƙe min, dan ALLAH ki riƙe min”.
Ai tsabar yanda jikin Maanal ke rawa batama san takai hannunta saman nashi ba, ta ture ta maye gurbinsa da nata tare da duƙawa a gabansa tana leƙen fuskarsa da faɗin, “Na shiga uku mike damunka? Miya samu kan naka? Ka tashi muje wajen likita na roƙeka”. Sai hawaye sharrr.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login