Showing 180001 words to 183000 words out of 221978 words
Chapter 61 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt
saki ledojin hannunta tana mai bin AA da Maanal dake shigewa cikin saloon ɗin da kallo. Itama dai ƙawar tata AA Darma ɗin take bi da kallo tana haɗiyar yawu, sai da suka gama shigewa ta maido dubanta kan Nurry ɗin da faɗin, “Kanbu Nurry AA ɗinki ne fa da mace? Miya kawosa nan wajen saloon ɗin mata to ma?”.
Nurry bata tanka mata ba, sai nufar wajen saloon ɗin da tai a sukwane jikinta har rawa yake tana neman faɗuwa. Ai babu shiri itama ƙawarta ta kwashi ledojin data zubar ɗin tabi bayanta da sassarfa dan gara dai ayi komai akan idonta........✍️
_😂Tofa AA Darma kana cikin alheri yau da alama gaskiya 🥱😆🏃._
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖7️⃣8️⃣
______________
.......Shigowar Nurry dai-dai AA na jama Maanal kujerar zama ita kuma fuskarta rufe da veil ɗinta tana share hawaye. Yayinda matan dake a wajen sun zo ai musu gyara suka musu caaa da idanu. Ma'aikatan kuwa har rige-rigen tambayarsa suke yi abinda za'ayi mata. Fuskarsa babu ɗigon fara'a, bai kuma kalla kowa ba tunda ya shigo ya buɗe baki da ƙyar ya ce, “A duba mata kan idan yayi datti a wanke, sai ai kitso”.
Da sauri Maanal ta janye veil ɗin daga fuskarta tana sake ɓarke masa da kukan da kowa kema kallon na shagwaɓa da taɓara. “Ni wlhy bana son kitso, kuma kaina babu wani datti da yayi, koba ranar na wanke ba”.
Maganar take da iya gaskiyarta tana kuka tana kallonsa. Dan haka ya wani kalar ɗage mata gira da wara mata shanyayyun idanunsa irin na ki kiyaye ni. Ƙasa-ƙasa yanda ita kaɗai zataji kuma ya furta, “ALLAH idan baki daina min wannan rigimar ba tsaf zan riƙeki na matseki a wanke kan a kumayi kitson ƴan ƙanana ko zamu kwana anan. Dube ki abin kunya kina kukan kitso kamar ba ƴammata ba”.
Ai kamar ya tunzurata sai ta sake ɓarke masa da kukan da yafi na farko. Hakan ya saka wasu dariya, wasu ko na mamaki da tunanin ƙaramar ƙanwarsa ce dai halan. Yo irin wannan taɓara haka. Ya shigo yana faman shan ƙamshi da ɗaɗɗaure fuska, amma kalla yanda yake wani kashe murya ƙasa-ƙasa da ko jin abinda yake faɗa ma babu mai yi. Wanda kuwa suka sanshi mamaki suke yi, AA Darma dai shugaban matasa mai Mawaad Company ne haka available. Tab ɗin, ita kuma wacece wannan? Su dai a sannin da sukai masa baida wata ƙanwa mace da suke jini ɗaya wato iyaye ɗaya ai, hasali ma shine Auta a gidansu kamar yanda duniya ta sani. Oho basu dai da mai amsa musu duk wannan.
Cike da kwarkwasa wadda zataima Maanal gyaran ta ce, “Ranka ya daɗe za'a ɗan wanke yayi datti”. Mugun harara Maanal ta zuba mata, zatai magana yaja kujerar da aka kawo masa shima ya zauna kusa da ita sosai. Kasa cewa komai tayi sai kallonsa take tana hawayenta. Shima dai kallon nata yake cikin ido sosai yana danne dariya da ƙyar. Kafin ya janye a kasalance yana wani ɗan gyaran murya kamar wanda ke neman rasa kansa. Handku ɗinsa ya ciro fari tas yana tashin ƙamshi ya miƙa mata, cike da kwantar da murya kamar ba shine ke mazurai ba ya ce, “Yi haƙuri to daina kukan, badai nine ba zan rama miki da kaina. Ai ina nan bazan bari su miki da zafi ba, idan ma kina so zan goya ki a bayana mu tafi gida a ƙafa har gida”.
“Ni bana so duka, kaina ciwo yake min”. Ta faɗa idonta dake cika da hawaye a cikin nasa. Dole sai shine ya sake janye nasa yanzu ma. Dan data san tasirin da yanayin nata yake masa a cikin jiki data tausaya masa. Cikin ɗan ƙara samun kansa da shaƙewar murya ya saka mata handky ɗin cikin hannunta yana faɗin, “Ciwon kai ba, zan saya miki magani. Faɗa min mi kike son kici naje na sayo miki yanzu”.
Kafaɗa ta maƙe alamar bata son komai. Amma sai ya shiga lallashinta kamar ba AA Darma ba. Gaba ɗaya sun manta kansu a yanzu da matsayinsu komai ya rikiɗe musu zuwa baya, bayan data shuɗe musu da ɗunbin tarihin tunawa suyi kuka da dariya idan ya kama duk a lokaci ɗaya. Ƙoƙarin miƙewa yay siyo mata cake da tace tana so. Caraf cikin ma'aitan wata tace, “Sir basai kaje da kanka ba bara a amso mata nan kusa da mu”. Tsabar neman ɗuwawun zama ko kuɗin bata amsa ba balle jiran amsarsa tai ƙoƙarin ficewa. Amma sai Maanal da takaici ya cika ta dakatar da ita da faɗin, “Ni naka nake so”.
Dariya taso bashi amma ya danne da ƙyar baiyi ba. Batare da yace komai ba ya miƙe ya fita. Ita kuma ta harari ma'aikaciyar. A yayin fitar tasa ne ya ɗan kusa buge Nurry da tun ɗazun tai sumar tsaye saboda mamakisa daya gama cika mata zuciya da ruhi ganin yanda yake abu kamar bashi ba. Kai itafa sai taga ma kamar a mafarki take. Kai in ko mafarki ne wannan mafarki ya mata muni da yawa, ALLAH dai ya farkar da ita ta daina gannin wannan tashin hankali. Gulmar AA ɗin da wasu mata keyi a kusa da inda take tsaye dan har ya fice shi batare daya ma lura da ita ba ya sata fahimtar fa ba mafarkin bane gaske ne. Sai taji zuciyarta na neman tarwatsewa. Karan farko ta motsa jikinta kamar mara laka ta fice itama tabi bayansa. Tasan halinsa sarai baya ɗaukar raini ko rawar kai, dan haka ta tsaya har ya fito daga cikin bakery ɗin hannunsa ɗauke da ledoji guda biyu. Yanzun ma sam hankalinsa bai kai gare ta ba, dan haka cikin kwantar da murya ta ce, “Assalamu alaikum Yaya AA”.
Cak ya tsaya daga tafiyar da yake yi, sai kuma kamar mai ciwon wuya gently ya dubeta, irin duban nan na sau ɗaya ya ɗauke kansa yana shanye dukkan sassaucin fuskarsa. Da sauri ta matso inda yake sosai. Muryarta har rawa take wajen gaisheshi. Sau ɗaya ya amsa mata, har yayi kamar zai wuce sai kuma a daƙile yaɗan sake dubanta. “Mikike yi anan?”.
Wani irin sanyi taji a ranta da ƴar kulawar tasa. Saita samu kanta da sake kwantar da murya cike da yanga ta ce, “Munzo sayen snacks ne a bakery ɗin nan”.
“Okay”.
Ya faɗa yana wucewarsa. Binsa tai da kallo kamar mayya, hawaye na ciko mata idanu. Ƙawarta da itama jikin nata ke a sanyaye ta ƙaraso gareta. Batace mata komai ba ta share hawayenta sai kuma ta miƙa mata hannu ta amshi bag ɗinta. Wayarta ta ciro ta shiga laluben number yayarta. Bugu ɗaya kuwa Saheeba ta ɗauka. Sai kawai ta sakar mata kuka. A ruɗe Saheeba ta shiga jera mata tambayoyi. Da ƙyar cikin garsheƙar kuka Nuratu ta sanar mata komai. Sai dai maimakon taji Saheeba ta amsa mata sai taji muryar Mamy, ashe lokacin suna tare ne Saheeban na'a sashenta.
Cikin ɓacin rai Mamy ta ce, “Ki bisa wajen Saloon ɗin ki ɗauka min hotonsa shi da yarinyar”.
“Amma Mamy zai gane nice na ɗauka na tura muku, kuma ALLAH sai ya hukuntani”.
“Okay kinfi tsoronsa kenan akan umarni na ko Nuratu?”.
“Ba haka bane Mamy. Dan ALLAH kiyi haƙuri”.
Ƙwafa Mamyn tayi, tare da yanke kiran kawai. Hakan yasa Nurry sauke ajiyar zuciya. Ko giya tasha ai bazatayi gangancin aikata abinda Mamyn tace tayi ba. Yaya AA fa, tab ɗin wlhy dandaƙar ɗan akuya zai mata har gaban uwarta ba damuwarsa bace. Dama dai ace bai ganta bane da zata iya ta ɗauka ɗin. Amma ya ganta ta gansa har sunyi magana ai ko zata cika duniya da rantsuwa yasan itace ta aikata. Haka ta samu kanta da zama a cikin mota ita da ƙawar tata suna dakon jiran fitowarsu.....
____________★
“Daddy wannan shine bayanin dana samu a kansa. Sunansa Bukar Bala Ɓatagarawa. Senator ne kuma.”
Murmushi mai faɗi Daddy yayi tare da gyara zaman wayar tasa yana kallon Yazeed dake masa bayanin dan video call suke yi. Kafin ya iya cewa komai Yazeed ya ce, “Daddy wai miya haɗaka da shi ne kake masa irin wannan binciken?”.
Kai tsaye Daddy ya ce, “Maanal yake so”.
Cikin matuƙar mamaki da razani Yazeed ya ce, “Maanal kuma Daddy”.
“Ƙwarai da gaske, dan har yaje ya samu iyayenta acan Giro sun gama magana......”
Tsaf Daddy ya zayyane masa komai. A take yanayin Yazeed ɗin ta canja, idanunsa suka kaɗa jazur. Cikin tsananin damuwa ya ce, “Daddy wannan nake gudu dama tun farko. Yanzu shike nan na rasata? Wannan fasiƙin mutumin zasu bata saboda zalunci?”.
“Baka rasata ba Yazeed, sam baka rasata ba. In har ina raye in sha ALLAHU bazaka rasa Maanal ba. Ka kwantar da hankalinka kai dai kabar komai a hannuna. Yanzu yaushe zaka dawo? Kwana biyar fa ya rage ɗaurin auren nan amma babu ango babu alamarsa”.
Sai da Yazeed ya haɗiye yawu mai ɗaci sannan a sanyaye ya ce, “Daddy zan taho zuwa alhamis insha ALLAHU. Kayan dana maka bayani nake son naga saukarsu akan idona. Kuma sunce sai Wednesday zasu iso. Shiyyasa na bari alhamis sai na dawo”.
“Bazai yiwu ba Yazeed. Ka taho Wednesday ɗin kawai. Kada mutanen nan suga rashin damuwarka akan ƴarsu tayi yawa. Ita ɗin ƴar uwarka ce kada ka wulaƙantata kodan Baba da Inna dan ALLAH. Ka kwantar da hankalinka ka ƙyautata mata sai ALLAH ya mallaka maka abinda kake so cikin sauƙi. Maganar Alhaji Bukar kuwa kada ma ta dameka, dan bazatai wani tasiri ba da izinin UBANGIJI.”
“In sha ALLAH zanyi duk yanda kace Daddy. Bara naje akwai meeting da zamu shiga dama”.
“Okay babu damuwa sai na jika, ALLAH yay maka albarka. Ya azurtaka da zuri'a masu albarka da zasu maka biyayya kamar yanda kake mana”.
“Amin Daddy na gode”.
Kai kawai Daddy ya jinjina tare da yanke wayar. Sai kuma ya maida dubansa ga Ammie da tun fara wayar tasa ta shigo, har zata juya ta koma ya hanata ta hanyar dakatar da ita da hannu. Dole ta dawo ta zauna. Akan kunnenta sukai duk zantukansu, sai taji zuciyarta ta raunana da tausayin Yazeed ɗin. Yaron kirki mai natsuwa da sanin mutuncin iyayensa.. har ga ALLAH tana son Maanal ta auresa, sai dai tana tsoratar mata wahala da ƙiyayyar uwar miji dan itama ta ɗanɗana a baya tasan ciwon da hakan ke da shi......
____________★
Kafin a kammala kitson nan babu kalar fitinar da Maanal batai ma AA ba. Damma manya akayi mata shikku. Sosai kitson yay mata ƙyau, amma sai faman haɗe fuska take yi. Shi dai wanda take yi domin shi ɗin bai kulata ba. Sai hotuna da yay mata a kaikaice batare data fahimta ba. Fuuu ta fice a wajen, wanda sukai mata kitson na mata bye ko kulasu batai ba. Suma dai sunayi ne don neman fada kawai, dan zukatansu sun gama yarda ƙanwarsa ce ita. Dole ta bari ya ƙaraso ya buɗe motar dan key ɗin na hannunsa, sai dai yanda taga kamar yana tafiya slowly ga hannunsa saman cikinsa ya sata zuba masa ido dan tun ɗazun dama ta lura kamar yana shiga wani ɗan yayi na kai ciwo amma jarumar fuskarsa na dannewa. Fuskarsa ama a yanzun a ɗan yamutse take alamar dai something is happing.
“Baka da lafiya ne?”.
Kallonta yay da idanunsa da suka canja launi, sai kuma ya janye kamar baya so ya ce, “Mi kika gani?”.
Kallon nasa ta cigaba da yi batare da tace komai ba. Shima sai ya basar kawai ya buɗe motar ya shiga. Kafin ta zagayo ta shiga dole ya kife kansa a steering saboda yanda cikinsa ya sake murɗa masa. Dama tun jiya haka yake sama-sama. Dauriya kawai yay ya fito aiki dan baya son ɗagama Oum hankali. Wannan yanayin nasa kuma a garesa normal yanayi ne daya daɗe ciki tsahon shekaru. Dan ma ƙaddarar rayuwa ya ɗan lafar da al'amarin nasa a baya kaɗan.
“Ajwaad”.
Maanal ta kira sunansa. Sai da ya ɗan cije baki sannan ya ɗago ya zuba mata firgitattun idanunsa da suka saka zuciyarta harbawa. Babu shiri ta janye nata da sauri. Lumshe idanun yay cikin ƙarfin hali ya motsa lips ɗinsa kaɗan.
“Bazaki daina kirana da Ajwaad ɗin nan ba ko?”.
Batare data kallesa ba ta ɗan tura baki da faɗin, “To ba sunanka bane?”.
“Sunana ne, amma ke baƙya cikin masu faɗarsa. Idan kuma kika ƙara i will teach you a lesson”.
Baki ta taɓe kawai. Shima sai bai sake cewa komai ba ya sake maida idanunsa ya rufe. Kusan mintuna biyu batare daya buɗe ba ya ce, “Har yanzu kina driving?”.
Kamar zata gaya masa baƙar magana sai kuma ta danne a taƙaice ta ce, “Uhmm”.
Numfashi ya ɗan sauke kaɗan, sai kuma ya buɗe murfin ya fita a motar. Ta side ɗin da take ya zagaya, ita dai tsoro ne keson shigarta da tunanin mike damunsa ne. Buɗe inda taken da yay ya sata juyowa tana kallonsa.
“Fito ki koma can”.
“Amma ni fa gaskiya.....”
“Please Besty bana son surutu cikina ke ciwo”.
Haɗiye sauran maganar tai kawai, ta zuro ƙafafunta ta sakko. Ɗan matsawa yay ya bata hanya. Sanda ta shigo shi har ya zauna ya rufe ma, bayansa ya kwantar a jikin kujerar idanunsa a lumshe. Sai da ta rufe sannan ta ɗan zuba masa idanu, sai kuma a hankali ta ce, “Na kaika wajen Rafeeq ne?”.
Fuskarsa ce ta ɗan sake tsukewa, sai kuma ya buɗe idanun slowly a kanta.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖7️⃣9️⃣
_____________
.........Zuba mata su yay kamar a fusace, dan haka ta janye nata.
“Nace miki ina buƙatar ganinsa ne?”. Ya faɗa cikin nuna jin haushi.
Baki ta taɓe batare data tanka masa ba, sai da ta tada motar tai reverse sannan ta fita a wajen. Idanunsa a kanta yana kallon yanda take tuƙin. Shine ya koya mata mota kusan gab da ƙaddara zata rabasu. Dan in bai manta ba bayan sun kammala jsce ɗinsu ne ta damesa tana son iya mota. Da farko Oum taƙi tace sai ta kammala secondary. Amma tai ta damunta dole tace ya koya matan. Da yake tasa kanta a lokacin cikin abinda baifi sati ba ta iya. Wani lokaci idan an aikesa ya fita da mota suka tafi tare takan matsa masa sai ya bata, idan yaƙi ta tasashi gaba da rigima dole yake batan duk da yana jin tsoro dan tayi ƙarama sosai.... Ganin tana shirin ɗaukar hanyar asibiti ya dakatar da ita. “Malama nace bazanje asibiti fa. Normal ne idan naje gida nasha lemon tsami zai daina”.
Gefen titi ta ɗan gangara, cike da damuwa a fuskarta ta ce, “Kana wasa da lafiyarka ko, lemon tsami magani ne, kuma ni ban taɓa gani ko jin dan mutum na ciwon ciki ya sha wani lemon tsami ba”.
Murmushi ya ɗanyi da lumshe idanunsa ya sake buɗesu a kanta. “Kece dai baki sani ba saboda yarinta”.
“Niba yarinya bace ba wlhy”.
Ta faɗa tana murguɗa baki.
“Oh really?”.
“Kaima ka sani ai”.
“Yanzu dai na sani ɗin kam, tunda ni dai yarinya na sanki a gabana. Amma tunda ke da kanki kin yarda kin girma zanfi kowa farin cikin hakan kodan halin da nake ciki”. Ya faɗa cike da shaƙiyanci. Harararsa tai da sake tada motar ta ce, “Kai dai ka sani.”
Murmushi yayi mai faɗi ya maida idanunsa ya lumshe da harɗe hannayensa duka a ƙirji. (Humm In ba Maanal ɗin ba wake ganin yawan murmushin AA haka arhar banza).
“Saka belt ɗin ki, ki kaini gida kafin tunani na ya canja na nema hanyar tabbatar