Showing 96001 words to 99000 words out of 221978 words

Chapter 33 - AJIYA A DUHU BOOK 1 COMPLET BY BILLYN ABDULL.txt

ba in har tai kowacce salla zata gaida na kusa da ita. Shima sai ya amsa da kulawa yana murmushi tare da tambayarta miyyasa bata son zuwa cin abinci. Murmushi kawai tayi kaɗan, kamar bazata amsashi ba ta dai buɗe baki da ƙyar dan ƴan miskilancin na kusa ta amsashi da, “Ina zuwa da nawa”.
Murmushi kawai shima yayi, daga haka suka cigaba da tafiya a jere. Sai dai bawata magana ma suke ta kirki ba, amma duk wanda ya kallesu sai ya sake kallo, harda masu ƴar gulma akan ɗan kusancin nasu daya fara bayyana kansa ga kowa musamman a kwanaki biyun nan.
Sunzo gab da shiga akai kiran wayar hannun Maanal. Tsayawa tai tana kallon mai kiran, RK ɗin ne ba wani ba, dan haka ta koma gefe tana amsawa. Shima Yaqub sai ya tsaya jiranta. Cikin takunsa na ƙasaita yazo ya gitta su, sai dai kamar ance Maanal ta kalla sashen da yake kawai ta hango wata shegen harara daya zuba mata. Baki ta ɗan murguɗa da kauda kanta gefe ta cigaba da wayarta, dan zuwa yanzu tana ɗan jin nutsuwar tarayyarta da RK ɗin, duk da bata buƙatarsa a matsayin da shi yake kallon kansa a gareta, bama shi ba kowanne namiji ita bata buƙata. Basu wani jima a wayar ba sukai sallama dan shima zai shiga theater yace. Ƙarasa shiga sukai ita da Yaqub, sai dai tana zama ta samu kira daga office ɗin AS ɗin CEO wai ana nemanta. Rasama abin faɗa tayi, amma sai ta miƙe tana rufe ɗan bowl ɗin data zubo snacks da zataci. Koda ta iso tayi mamakin ganin Huznah zaune har yanzu, sai dai bata nuna ba ko'a fuska ta isa ga AS ɗin. Phone ɗin gabansa ya daddana tare da kaiwa kunne alamar kira, an ɗan jima ba'a ɗaga masa ba, ana ɗagawar kuma cikin girmamawa kamar yana gabansa ya furta, “Sir gata tazo”. Ɗan shiru yay alamar saurare, sai kuma ya gyaɗa kai yana faɗin, “Okay sir”. Yana ajiye kan wayar ya dubeta fuskarsa da murmushi.
“Sister Maanal ki ƙarasa ciki”.
Kanta kawai ta gyaɗa masa. Yayinda Huznah ta miƙe ranta a ɓace. “Wane kalar rainin wayo ne ina zaune ina jira kace wata ta shiga kuma?”.
Cikin girmamawa ya ce, “Am sorry Mss. Ita ɗin staff ɗinmu ce, ganinta nada banbanci da ke. Sannan kiyi haƙuri boss baya son hayaniya sam. Musamman a irin wannan lokacin.”
Hararar sa ta ɗan yi, yay mata murmushi da faɗin, “Kiyi haƙuri idan ya bada umarnin ki shiga kema zaki shiga”.
Tsaki kawai taja masa ta koma ta zauna. A ranta tana jin zata iya kwana a wajen har sai ta samu izinin shiga wajensa yau. Dan ta bakin Nurry sai ta buɗe masa wuta da gaske kafin ta samu kan guy ɗin nan. Zafin kansa yayi yawa da faɗin rai.....


Kan Maanal a ƙasa ta shiga office ɗin, yana zaune a rukunin kujerun office ɗin masu laushi da ƙyawun kallo. A one sitter yake zaune ƙafa ɗaya kan ɗaya, sai novel dake hannunsa, gefensa akan coffee table glass bowl ne cike da fruits nau'i daban-daban masu tsafta da ƙyawun kallo. Sai bottle na ruwa an zuba wani a kofin. Har ta ƙaraso kusa da shi amma akwai tazara a tsakaninsu bai nuna yasan da shigowar kowa ba. Yayinda ita kuma idonta ke akan bangon book ɗin hannunsan. Dan ta jima tana neman novel ɗin amma ta gagara samu, har kuɗi ta biya dan a kawo mata shi amma har yanzu shiru. Sai kuma gashi yau ta gani a hannun wannan mutumin.
Duk abinda take yana kallonta ta gefen ido, amma bazaka fahimci hakan ba sai ma karatunsa da yake yi hankali kwance. Yawu taɗan haɗiye tare da gyara tsaiwarta ta ce, “Good Afternoon sir. Gani, ance kana buƙatar gani na”.
Shiru bashi da alamar tanka masa balle motsawa, sai da yaja fin mintuna biyu sannan ya ɗan ɗago yana mai kai hannu ya gyara zaman gilashinsa da ƙyau, sai ta samu kanta da kai hannu itama ta gyara nata. Zuba mata idanunsa kawai yayi, dai-dai ya ɗago suka haɗa ido. Da sauri ta janye natan tana wani duƙar da kai na girmamawa. Shi kam kallonta yake kawai daga sama har ƙasa, har ta fara jin gundura da kallon amma batace komai ba.
Sai da ya gama kalleta son ransa sannan ya ɗauke idanunsa, cikin muryar nan tasa ƙasa-ƙasa ya furta, “I need a drink”.
Karon farko ta zuba masa ido kai tsaye itama, sai kuma ta kalla bottle water ɗin gefensa fuskarta na ƙara tsukewa. Kamar zatai magana sai kuma mita tuna ta bar wajen. Kai tsaye fright ɗin office ɗin mai ƙyau sosai ta nufa. Koda ta buɗe sai tai kasare tana kallon komai. Cike yake da kayan drinks kala-kala. Sai fruits suma kala-kala kowanne anyi packaging ɗinsa. Haka kawai ta samu kanta da taɓe baki, batare data zauna tantancewa ba ta ɗauka ɗaya ta dawo inda yake. Sai dai me tana ajiyewa batare daya kalleta ba ya furta, “Bana shan wannan”. Komai batace ba ta juya ta ajiye ta ɗakko wani. Shima tana kaiwa zata ajiye ya sake furta, “Changes someone”. Nan ma batace komai ba ta juya ta ajiye ta sake ɗakko wani. Shima haka ya ce mata baya so. Cikin wani irin takaici da jin zafi ta juya, sai kuma ta tsaya cak batare data kallesa ba ta ce, “Which one do you need?”.
Shiru yay mata bai tanka ba, hakan ya sake ƙullar da ita. Fuuu ta nufi fright ɗin ta sake buɗewa. Wancan ta dangwarar a inda ta ɗauka, nacan sama ta zubama ido sai dai hannunta bazai kai ba. Ta gwada ɗauka da ɗiɗɗishe amma duk tsahonta hannunta bazai kai ba. Juyawa tai tana ɗan kallon office ɗin alamar neman abin takawa, sai ko idonta ya sauka akan wani ɗan glass table da aka ɗaura ƙyaƙyƙyawan flowers a samansa. Shiko ta nufa ta sauke flowers base ɗin ta ɗakkosa gaban fright ɗin ta ajiye. Da kallon mamaki kawai ya bita, sai da ta ɗakko yaga da gaske fright ɗin ta nufa ya ɗan waro oily luluu ayes ɗinsa dake cikin gilashi.
Itako hajjajun babu ko ɗar ta taka ta haye samansa ta shiga jido kalolin lemukan tana tarawa a ɗayan hannunta. Ba ita zai rainama hankali ba. Bari ta kai masa duk kalolin taga iyakar rainin wayonsa. Tana gamawa ta juyo da nufin sauka sai kawai tai wani irin yin baya sakamakon kasancewarsa tsaye a bayanta hannayensa duk a cikin aljihun ya wani zuba mata mayatattun idanunsa kawai. Kaɗan ya rage ta faɗi, da ƙyar ta iya daidaita tsaiwarta tana tura baki batare data cigaba da iya kallonsa ba. Shi kam nasa idanun ƙyam a kanta ko ƙyaftawa bayayi. Kasa jurewa kallon nasa tayi, kasancewar ta a saman table tsahonsu ya dai-daita a yanzu harma ta ɗan zartashi kaɗan. Tun tana jin zata iya daurewa har jikinta ya fara rawa. Ga sanyin fright ɗin da bata rufeba na busota, ta gaba kuma ya tareta tako ina dan tsaye yake gab da ita sosai. Ga kuma drinks data tara a hannu suma sanyinsu na shigarta. Wani irin cikowa idanunta sukai da ƙwalla, cike da sarewa ta saki drinks ɗin suka tarwatse a ƙasa har wasu na faɗa masa a kan ƙafa amma bai motsa ba.
Zarrrr hawaye suka fara gudu a ƙyaƙyƙyawar fuskar Maanal. Lips dinta na wani irin motsi na son yin magana amma kuma ta kasa. Karan farko ya ɗan lumshe gajiyayyun idanun nasa tare da taɓe baki kaɗan. Sai kuma ya kai hannu a hankali ya rufe fright ɗin, yaja jikinsa yabar wajen batare da yace mata komai ba. Sauka tayi itama jikinta na cigaba da rawa zuciyarta na mata wani irin zafafa mata jin zafisa. Ko kallon drinks ɗin data zubar batai ba ta nufi hanyar ƙofa tana share hawayenta. Sai dai koda taja handle ɗin domin buɗewa sai ta jita bam a rufe. Tsaye kawai tai jikinta na sake cigaba da rawa. Hawayenta na ƙara ƙarfin gudu. Ta ƙara kai hannu taja amma still dai. Ai bama tasan ta wani irin juyowa inda yake ba, sai kawai ganinta tai a gabansa.
Cikin matuƙar ƙunar zuciya da raɗaɗi ta ce, “Mikake buƙata da ni ne wai? What is your business with me? ”.
Idan office ɗin ya motsa to shima ya motsa. Nunama yasan da ita a gabansa baiyi ba, karatunsa kawai yake yi. Hannu tasa ta fisgi book ɗin tai wurgi da shi saman kujera, cikin matuƙar tsiwa da komawa ainahin Maanal data mutu (😂injita) ta sake matsosa a kausashe, cikin ƴar tsawa ta furta “Ajwaad!! Nace mi kake buƙata da ni? Kana min abubuwa ina ɗauke kai amma na kula kai ka kasa fahimtar karatun kurma. Dole ne sai ka kasance in to my life ne? Kasan dai ni ba shasha bace da zaka taka yanda kake so kamar yanda ka iya ko, kodan kaga nazo ina aiki ne a ƙarƙashin alfarmarka kake ɗaukata a ban san mi nake yi ba? To daga yau nabar aikin, na bari tunda dama ra'ayina ya sani jin zanyi bawai rasa tallafin rayuwane ba ko talaucin da da ake kallonmu a ciki....”
A karo na farko da tun isowarta wajen ya ɗago mayatattun idanunsa dake cikin gilashi, gently hankali kwance ya zuba mata su. Sake hayayyaƙo masa tai har tana nunashi da ɗan yatsarta manuniya tamkar zata tsokale masa ido. Idanunsa da yake ɗan ƙyaƙyƙyaftawa ya ɗan ja kamar zai lumshe sai kuma ya sake buɗesu warrr a kanta. Cigaba take da nunasa tana masifarta har baya ma fahimtar abinda take faɗa, tsabar yanda ta birkice tuni veil ɗinta datai rolling ya warware hakama ɗan kwalin ya zame dogon gashinta baƙi siɗik dake ɗaure a tsakkiya cikin ƙyaƙyƙyawan ribbon ya bayyana sai lilo yake. Sosai ya maida idanunsa ya zuba akan gashin yana masa wani irin kallo.
Ina Maanal bata san yana yi ba, masifarta kawai take tana kuka. “Na tsaneka, wlhy na tsaneka Ajwaad. Bana son ganin ko fuskarka, da nasan ƙaddara zata sake haɗamu a duniyar nan dana roƙa ALLAH mutuwata kafin hakan. Na cigaba da yin aikin nan ne dan kawai baka isa hanani yin abinda raina keso ba a duniyata a duk inda naso hakan koda kuwa wajen mallakinka ne......”
Duk da wani irin saukar aradu da kalamanta ke masa a cikin kunne a bazata, matuƙar bazata taji tattausan hannunsa ya sauka akan yatsar ta dake neman cokale masa ido. Fisgar hannunta tayi tana sake birkice masa. Sai dai riƙon da yayma yatsar bana wasan yara bane ba. Dan fisga ɗaya ya mata bama wani da ƙarfi ba sai gata a gabansa a zube. Biyota yay da kallo har lokacin ɗan yatsar nata dai na riƙe a hannunsa.
“Wlhy koka sakeni kona maka ihu”.
Karo na farko ya saki wani ɗan iskan murmushi yana ɗan ɗage girarsa ɗaya, sai kuma ya sauke ƙafarsa duka ya ajiye a ƙasan carpet ɗin da take zaune tare da duƙowa sosai kusa da ita gab har tana jin numfashinsa da ƙarfin turarensa sosai a cikin hancinta. Jikinta taso ja baya sai dai sam yaƙi bata damar haka. Cikin sake lumshe idanu da buɗesu a lokaci guda ya motsa laɓɓansa ƙasa-ƙasa ya furta, “Bismillah yi, ba ihu ba? Maza kiyi, ai bana yau ne farko ba daman”.
Cusa kanta tayi cikin ƙafafunta ta dunƙule a waje ɗaya tana mai fashewa da kuka. Ga jikinta na matuƙar rawa. Tabbas komai dawo mata yake. Ta ƙarfin tsiya da tsiya-tsiya brain dinta da zuciyarta keson tilastata tuna baya. Bayan data jima da shafewa a tarihin rayuwarta. Bayan da bata fatan koda wata alama ta tuna shi, bayan da take kallo tamkar RAYUWA A BAYAN MUTUWA. Bayan data jima da tattarashi ta tura can bayan bayanta ta yanda bazata sake tunawaba har gaban abada. Miyyasa yake son tilastata ne? Miyyasa bazai mata adalci bane? miyasa yake son sake cuta mata da wannan DAFIN da yay ajalin ainahin Maanal. Miyyasa bazai gane komai ya canja bane, canjawa irin wadda ke shafe ƙarnuka da zamanoni tamkar ba'a yisu ba. Kaicon samuwar wannan aiki nata, kaicon amincewarta da yinsa. Ita da kanta ji take ma ta tsani kanta da kanta a wannan gaɓar.........✍️


_Hummm ni Balki, wai shin...🤔 To bara dai nayi shiru kada ace na cika takale-takale 🥱😌😩🏃_






✨ZAFAFAN DAI ✨


1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)




Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000


0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070


Kati MTN:- 09032345899


Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070








*_ALLAH ka gafartama iyayenmu
😭🙏_*
*_Typing📲_*
















*_💞AJIYA A DUHU....💞_*








*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*




*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._


*_My TikTok account 👇_*


https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1


*_Instagram👇🏻_*


https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv


*_Arewabooks_*


Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30


*_WhatsApp channel_*


https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R




_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_




🅿️➖4️⃣3️⃣




______________




........Shima da gaba ɗaya kansa ke juya masa, al'amura masu nauyi da suke lulluɓe a zuciyarsa na sake zaburowa, a hankali ya saki mata yatsan yana rumtse idanunsa da ƙarfi. Wani irin ratsa zuciyarsa da ɓargo kukan nata yake yi. Sai dai bazaka taɓa fahimtar hakan a fuskarsa ba idan ka cire idanunsa da sukai matuƙar kaɗawa. Tawani fannin kuma zai iya cewa kukan yake so tayi, dan zai rage mata nauyin zuciya dana zafinsa da yasan take ji. Fin mintuna biyar suna a haka kafin ya miƙe a wajen, veil ɗinta dake yashe a ƙasa ya ɗauka, ƙamshinsa na sake ratsa hancinsa, kanta ya ɗan rankwafo ya yafa mata veil ɗin a saman kanta batare da yace komai ba ya wuce ainahin office chair ɗinsa, batare daya zauna ba ya ciri ƙaramar pepper yay ɗan rubutu, sai kuma ya ɗauka shopping bag ƙarama dake a saman desk ɗin. Rigar suit ɗinsa dake a hanger ya cire itama tare da tattare wayoyinsa. Gabanta yaje ya ajiye shopping bag ɗin nan da shot note ɗin da yayi batare da yace mata komai ba ya nufi ƙofa. Sai da ya kai hannu zai danna maɓallin buɗe ƙofar batare daya jiyo ba ya furta, “Ki tabbatar kin shiga restroom kin gyara fuskarki”. Daga haka yay ficewarsa cike da takunsa na nutsuwa da ƙasaita.
Da wani irin sauri Huznah dake zaune cikin takaici da damuwa ta miƙe. Hakama AS ɗinsa daya san wannan ba lokacin fitowarsa bane miƙewa yayi. Baiko kalla inda Huznah take ba, sai Assistant ɗin nasa ya kalla. “Zanje airport ɗaukar su Mamy. Take care of everything”.
“Okay Sir ALLAH ya tsare”.
Kansa kawai ya jinjina masa yay wucewarsa. Har kuma yayi taku uku sai ya tsaya cak jin ana binsa a baya. Ɗan waiwayowa yay tamkar mai jin ciwon wuya ya zuba mata ƙasaitattun idanunsa da gaba ɗaya suka sauya kala da launinsu. Dan farin gilashin fuskarsa bai zam ya ɓoye komai ba daga garesu. Kasa jure kallonsa Huznah tayi, sai ma jikinta dake neman fara rawa. Amma tai ƙoƙarin riƙe kanta da tsiya, sai dai muryarta na ɗan rawa ta ce, “A zahiri bakayi kama da mai wulaƙanta mutane ba, why ni nake neman zama ƙasƙantacciya a yayin zuwa ganinka? Please ka duba ni, ka bani dama muyi magana dan ALLAH”..
Karo na farko ya lumshe idanun nasa da buɗesu. Hakan tuni ya zame masa ɗabi'a musamman a yayin son yin magana. Cikin cool voice ɗinsa mai fidda ƙaramin amo da kasancewa ƙasa-ƙasa tamkar ba namiji ba ya furta, “Mi kike buƙata?”.
“Kai! Kai nake buƙata AA. Ina son yin magana da kai Please”.
Lips ɗinsa ya ɗan ciza sai kuma ya janye idanunsa daga kanta. Ƙoƙarin wucewa yay batare daya tanka mata ba yana kallon Designer agogonsa da sai ka gama karaɗewa baka samo sa ba, dan shi duk wani agogon sakawarsa ana masa shi a companynsa kuma shi kaɗai, sai idan wani ne yace yana so ayi irinsa daga nan shi kuma yabar saka Design ɗin sai kuma wani. Da sauri ta bi bayansa suka shige cikin elevator daya buɗe. Anan ɗin ma dubansa tayi da son yin magana sai dai ta gagara sakamakon ganin fuskarsa babu alamun wasa. A haka suka fito tanata ƙoƙarin ganin ta daidaita tafiyarsu. Aiko hakan yaja hankalin ma'aikatansa matuƙa. Dan duk inda suka gitta idanu yuuu akansu. Masu ƙus-ƙus nayi masu jinjina kai nayi. Yayinda zukatan mafi yawansu suka sake yarda da eh lallai da gaske itace boss ɗin nasu zai aura kuwa. Dan abune da basu taɓa gani ba boss da mace kamar haka. Ina dai ka gansu da wata to lallai abokiyar kasuwanci ce, dan shi hatta a cikin family baya kula ƴar kowa, in dai kina sama da shi zai yi respecting ɗinki. Suna gama ficewa sai ƙus-ƙus ɗin ya ƙaru, yayinda wasu suka maida hankalinsu ga hotunan dake akowacce kusurwa ta Company ɗin na mace mai niƙab da hijjab. Wadda da yawansu sun gagara tantance hoto ne ko zane ne. So suke su tantance ko wadda suka fita taren ce. Sai dai sam babu wani alamu ko kamanni daya nuna hakan. Dan baka isa tantance ainahin wacece a hoton ba tako ina....


Yana fitowa drivern sa dake can wajen securitys suna hira ya miƙe da sauri. Sai dai koda ya iso garesa sai ya miƙa masa hannu murya ƙasa-ƙasa yana faɗin, “Don't worry, give me the

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login